TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Tsantsar so page 8

 *Ep_Eight.*

*❣️ TSANTSAR SO.❣️*

*The Pure Love.*



_❣️Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love.❣️_




~_From The Pen Of Nainarh KD Writer Of Sarauniyar Kyau And Aneeserh (Innocent Girl.)_~



*Dedicated To Princess Teemarh [Star Lady.]💋*






A hankali ta juya ta kalla Teema dake zaune gefe da ita saman tabarma da aka shimfiɗa musu lokacin da suka ƙari so gidan, tayi Murmushi kaɗan tana kuma bin gidan da kallo, maganar da taji an yi ne yasa ta juya domin ganin mai maganar.



"Lah Anty Samira kece a gidan namu lale lale."



Tayi Murmushi ganin wannan cutie Girl ɗin ne da har zuwa yanzu batasan sunanta ba, buɗe baki tayi zatayi magana Kakus ta riga ta da faɗin.



"Allah mai iko daga shigowa babu sallama balle gaisuwa  kin zo kin cika mana kunne da ihu."



Arissa tayi Murmushi bayan ta ƙari sa wurin su ta zauna daga saman tabarman ba tare da ta kalle Kakus ba ta ce.



"Uhum ai nayi sallama kece kawai baki ji ba. Ina wuni Anty Samira ya ƙarfin jikin naki ya ƙafar?."



"Alhamdulillah naji sauƙi kina lafiya?."



Samira ta amsa ma ta sannan ita ma tana tambayar ta.



"Lafiya Qlau wallahi bari na cire hijabin nan Nazo muyi fira.".

Arissa ta faɗa tana tashi tsaye ta cire Hijabin islamiyya da ta dawo dake jikinta sannan ta kai Alkur'ani mai girma Ɗaki ta a je, ta fito tana faɗin.



"Teema yau baki tafi Tahfiz na yamma ba ina fata lafiya?."



Teema taja ajiyar zuciya ta ce.



"Kedai Arissa bari kawai Hadda ne ban wani mayar da hankali na iya ba, shi ya sa ma ban je ba domin kuwa nasan yadda zata ƙare ni da Malam Mahmoud karon ba zai mana kyau ba."



Ta ƙarishe maganar tana dariya ita ma Arissa Dariya take yi domin kuwa sarai tasan Teema da irin show da ake kwasa tsakaninta da malamin ajin nasu wato Malam Mahmoud.




"Ki dage dai nasan baki manta muna gab da yin sauka ba ki daure ki mayar da hankali."



Arissa ta faɗa.



Teema ta amsa da. "Shikenan in sha Allah zan gwada."



"Sannun ku bayin Allah na barku zaune ina tuƙa tuwo ke Arissa zo ta nan ki tayani kawo ma baƙi tuwo miyar kuɓewa nasan dai ba zasu ƙi ci ba."



Amsawa Arissa tayi tana Miƙewa tsaye yayin da Samira ta bita da kallo Teema kuwa ta ɗauki Ruwan dake gabansu wanda shigowar su gidan Kakus ta kawo musu bayan sun ma ta Bayanin godiya suka zo yima wanda ya taimaki Samira godiya acewarsu, har take faɗa musu baya nan sannan ta ce su zauna susha ko ruwa ne sun kwaso tafiya shi ne ta shimfiɗa musu tabarma ba tare da gardama ba suka zauna.




"Anty Samira ga fa tuwo raɓa raɓa Allah ya sa kin san shi?."



Arissa ta faɗa lokacin da ta ƙari so wurin sannan ta a je kwano da tuwo ke ciki sai kuma wata roba daban miyar kuɓewa ɗanya yaji haɗi sai ƙamshi take fitarwa a ciki.



"Nasan shi mana sai dai ban taɓa ci ba, amma me yasa kika ce ko zan iya ci?."




Samira ta jefowa Arissa da ta zauna gefan su bayan ta a je musu tuwon tambayar tana kallon ta.



"Ah bakomai kawai saboda naji ance daga ƙasar waje kika zo ne shi ya sa."



Arissa ta bata amsa tana dariya.



"Allah Sarki ai Mommyna tana yiwa Daddyna domin yanaso sai dai ban taɓa ci ba ita kam tana ci sosai."



"Ikon Allah."



Arissa ta faɗa. Tana shirin sake magana Kakus ta riga ta da faɗin.



"Ku Dena biyewa wannan kuji tuwon ku kunji domin kam ita bata ci sam 'yar gayu ce na lura so take ta hanaku ci."



Samira da Teema suka yi Murmushi tuni Teema ta janyo kwanon tuwon gaban ta, Arissa da ta miƙa musu ruwa da roba da zasu wanke Hannu ta ce.



"HHhH Kakus shagali kishi kike dai banacin tuwo balle nayi saurin tsufa kina kishi kar ɗan mijin naki ya susuce."




Ta faɗa tana dariya.



"Ja'ira Kawai."



Cewar Kakus tana ɓallawa Arissa harara na wasa.



Samira ta yi Murmushi tana ganin Drama da ake kwasa tsakanin cutie ɗin da taji Teema ta kira da Arissa da kuma Dattijuwar da take da tabbacin Kakar Arissa ɗin ce.


"Anty Samira kici mana."



Cewar Arissa tana kallon yadda Samira ta zubawa kwanon tuwon ido tana kokwanton ci.



"Yanzu kam a ƙoshe nake amma nayi alƙawari idan na dawo next time zan zage naci na ƙoshi."



Suka yi dariya gaba ɗaya har da ita. 

Suna ɗan taɓa fira sama sama da mafi yawa Arissa ce take yi da ita Kakus nata Samira Sai dai ta bisu da ido, yayin da Teema ta zage ta buɗe ciki taci tuwo ta ƙoshi domin kuwa ba ƙaramin daɗi ya yi ma ta ba dama tayi missing tuwon Kakus sosai domin rabon ta da gidan an kwana biyu.



Bayan Teema ta kammala ta wanke Hannu suka miƙe da niyyar tafiya suka yi musu sallama sannan suka fito domin tafiya.



Idanunta suna kallon ƙasa daidai lokacin da suka fito daga gidan taji ta yi karo da Mutum ga wani daddaɗan ƙamshi da ya ziyarce ilahirin ƙofofin hancinta.


Ta sauke ajiyar zuciya ɓoyayyiya tana ɗa go softly Blue eyes nata masu matuƙar shaining tare da ɗaukar hankali ta sauke su saman kyakyawar fuskarsa mai cike da tarin annuri da haiba, sam batayi tunanin da shi tayi karo ba sanadin haɗuwar da idanunsu suka yi ya haddasa ma ta jin Damm bugu da ƙirjin ta ya yi. Ta lura da yadda ya waro ido yana bin ta da kallon mamaki sai dai tayi mamaki jin bai ce da ita komai ba koda yake duba da yanayinsa na kamala kallon farko zaka masa ka fahimci baya daga cikin waɗan nan mutanen masu hayaniya balle kuma surutu, ta sauke ajiyar zuciya a karo na ba a dadi tare da faɗin.




"Barka dama kuwa kai nake nema."



Ta faɗa idanunta akan sa fuskarsa ta nuna tsantsan mamaki bata bari ya ce komai ba ta ci gaba da cewa.



"A wancan lokacin sanadin wannan gunguren da muka yi ƙafa ta ta gurɗe shi ne sanadin da nake riƙe da crutches yanzu kuma dama kai nayi ƙoƙarin ceta har hakan ta sameni saboda haka kai ne kake da alhakin kula dani har ƙafar tawa ta warke, abin nufi shi ne kaso hamsin na lokacin ka zai koma kana kula dani da su ne har ƙafa ta ta warke duk da Doctor ya ce ba daɗe zatayi sosai ba warke ba ina fata ba zaka min mummanar fahimta ba daga gobe Deal ɗin namu zai fara."



Shiru Taufan ya yi ya harɗe hannu bibbiyu a ƙirji cike da mamaki yake bin ta da kallo sai dai ya kasa furta komai tsaban al'ajabi.



Samira tayi Murmushi tare da yin gifgif da ido ta ce.



"Zan tafi gida yanzu Gobe mu haɗu anan misalin ƙarfe Biyar na marece zuwa lokacin nake so na ɗan yawata cikin garin nan kuma Kaga yadda ƙafata take saboda haka kaga sai mu tafi tare."



"Okay."



Ya tsinci kansa da faɗin hakan a gajarce.



Tayi Murmushi sannan ta riƙe hannun Teema suka yi gaba. Arissa dake tsaye gefe babu wanda yasan da wanzuwar ta a Wurin ta tuntsire da dariya da ya saka Taufan da ya yi nisa a Duniyar al'ajabin Samira ya juyo ya kalleta.



"Mene ne kuma kike ma Dariya?."


Ya tambaya yana ɓata fuska.



"A'a ba komai kawai dai mamaki nake yi yadda ka kasa koda magana ne a gaban Anty Samira sai ma amsa ma ta umarnin da kayi kamar yaro da uban gidan sa."


"Umarni kuma?."


Ya tambaya da mamaki.



"E mana Yayana haka nake nufi ai yadda Anty Samira tayi maganar kuma baka mata ja'inja ba kowa ya gani kai tsaye zai ce umarni ta baka."



"To kaska uwar surutu naji mu shiga daga ciki."



Ya faɗa tare da riƙe hannunta suka shiga cikin Gidan yana shafa stubble short hair style na fuskarsa.



*_Samira Sam kuwa_*



Suna tafe babu um bare um um har suka ƙari sa masarautar Raees a tafiyar da suke yi a ƙasa domin ba wani nisa ba ne na azo a gani tsakanin gidan su Arissa da masarautar. Aka buɗe musu gate suka shiga ciki suna gafda da shiga Apartment ɗin da aka warewa 'yan matan kuma suke zaune ita da Hamrarh da Amrarh da sauran 'yan matan dangin Raees a ciki ta dubi Teema ta ce.





"Mene ne abin da kika sani game da Arissa da Yayanta kuma mene ne sunansa. I mean Tarihin su kuma Kinga ai ban san sunan su ba."




Tayi maganar tana kallon Teema.




Teema tayi Shiru kamar mai nazari sannan ta ce.



"E, to abin da na sani dangane dasu dai kaɗan ne kuma Sanadin Arissa ce da muke Class ɗaya da ita a Tahfiz. Abin da na sani shi ne kuwa. Shi dai sunan sa Taufan Arissa tana kiransa da Yayana ita kuma kamar yadda kika sani Sunanta Arissa wasu suna kiranta da Cutie domin kyau da Ubangiji ya halicce  ta da shi, Alhaji Muhammad Ali Nakowa da Matarsa Hajiya Sumayya da Arissa take kira da Kakus muma muka kama. Aamalah ita ce kaɗai 'ya a wurin Muhammad Ali Nakowa da Matarsa Sumayya. Yayin da Taufan da kuma Arissa suke 'ya 'ya a wurin ta magana dai jikokin Kakus da Alhaji Nakowa."




"Ikon Allah amma me yasa suke zaune tare da Kakannin su na wurin uwa kuma Mahaifin su fa da ita mahaifiyar tasu Aamalah?."


Samira ta tambaya cikin sauri.



"E, to abin da na sani dai shi ne Aamalah ta tafi ƙasar Egypt domin karatu na University bata dawo ba sai da yaro da kuma wasu Larabawa kuma sojoji ne wai tayi Aure a can ne kuma ta haihu shi ne a lokacin Alhaji Nakowa da Matarsa ransu ya yi mugun ɓaci na abin da Aamalah tayi Aure ba tare da ta sanar da kowa ba har suka ƙi kulata daga ƙarshe ma suka koreta. Daga nan ba'a sake jin labari akan ta ba. Sai shekara ɗaya da ta wuce Arissa da Yayanta suka zo nan ƙasar wurin Kakannin nasu nan ne suke basu labarin sun zo ne su zauna da su tsawon shekara ɗaya daga nan zasuyi musu bayanin dalilin dawowarsu garesu ba tare da Mahaifiyarsu ba. Wannan shi ne abin da zan iya ce Miki na sani Dangane da Arissa da Yayanta nima dai a wurin Mamana nakejin wasu abubuwan."



Samira tayi Shiru cike da mamaki tana nazarin wannan labarin da Teema ta bata.





Daidai lokacin kuma suka ƙari sa bakin entrance na Apartment ɗin shiga ciki suka yi da sallama Aikuwa Samira tayi kyakykywan gani.




Post a Comment

0 Comments