TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

👬🏻 TAGWAYE 👭🏻 8 & 9

   Episode eight : Kidnapped


Hasken da ya shigo ta window ne ya sauka a dai dai fuskarsa. Ya kikkifta idon sannan yayi kokarin amfani da hannunsa gurin tare hasken amma sai yaji ya kasa motsa hannun nasa. Wani irin ciwo jikinsa yake yi masa tamkar wanda aka kwana ana duka da ƙulki. Ya bude idonsa da kyar, su kansu eyelids dinsa sunyi masa nauri kamar an dora wani abu akan su. Idonsa ya sauka akan window din da take kallonsa ta inda hasken ranar yake shigowa. Ya sake rufe idon da sauri saboda hasken daya kashe masa ido amma already yaga tagar kuma a ransa ya fahimci cewa bai san ta ba. A ina yake? Ya sake kokarin motsa hannunsa amma yaji ya kasa, wannan ya tabbatar masa da cewa hannayen sa a daddaure suke sannan ya fahimci ƙafafuwan sa ma haka. Bakinsa ma a like yake ta hancin sa kawai yake numfashi. Ya juya fuskarsa gefe sannan ya bude idonsa yana numfashi sama sama cikin tsoro, a hankali ya zagaye gurin da yake da idanunsa sannan ya fahimci cewa toilet ne, ya kuma fahimci shi kadai ne a gurin. Sai a lokacin tunanin abinda ya faru dashi ya dawo masa.


Farkon abinda ya fara fahimta shine har ya kwana ya hantse kenan, tashin hankalin sa shine wanne hali yan'uwansa suke ciki? Wanne hali Hussain yake ciki? Shin kidnappers din sunyi contacting dinsu ko kuwa? Abu na biyu daya tuna kuma shine bai yi Sallah ba, bai yi magrib ba bai yi isha ba baiyi assuba ba. 


Ya ja ƙafafuwan sa ya lankwasa su yana jin tamkar zasu karye saboda sandarewa da suka yi ga kuma azabar ciwo da suke yi masa, ya yi kokari ya jingina bayansa da jikin bango sannan yabi bangon ya mike zaune yana jin jikinsa gabaki daya yana amsawa saboda ciwo, ciwon tafiyar da akayi dashi a booth din mota, daure shin da akayi for hours da kuma kwana da yayi akan tantagaryar sumunti. Ya sake karewa ban dakin kallo yaga bashi da wani girma sosai daga kofar da take a rufe sai yar karamar tagar da take can sama a rufe itama da glass. Kasa kasa yake jin muryoyin mutane yana shigowa ta kofar.


Ya muskuta a hankali har yaje jikin kofar sannan ya jingina jikinsa da kofar ya kasa kunnen sa yana so yaji abinda suke cewa amma har kansa ya fara ciwo saboda stressing kunnensa da yayi bai samu ya fahimci komai a maganganun nasu ba saboda can kasa suke maganar. Ya fara buga kansa a jikin kofar, yana jin kan yana kara yi masa ciwo amma yana so yayi calling attention din wadanda suke waje in mutanen kirki ne su taimaka masa in kuma holders dinsa ne ya nemi su kunce shi yayi sallah. Sukayi shiru da maganganun su a lokaci daya sannan suka taho bakin kofar da sauri suna gyara abinda suka rufe fuskokinsu dashi. Katon ne ya bude kofar da sauri yana auna Hassan da bakin bindigar da take hannunsa "Will you stop banging that door?" Ya fada murya can kasa kamar me rada. Hassan ya fara kokarin magana amma sai ya kasa saboda bakinsa yana rufe. Mutumin ya saka hannu daya ya cire abin bakin Hassan, Hassan yaji tamkar ya cire ne tare da fatar bakin gabaki daya saboda zafin da yaji amma babu hannun shafawa dan haka kawai ya runtse idonsa har zafin ya lafa, sannan yace "ina son zanyi Sallah dan Allah" mutumin ya sunkuyo fuskanta kusa data Hassan yace "kaga nayi kama da mai yin Sallah? Reserve your sallah kayi ta addu'a twin dinka ya biya mu kudin da muka nema and you will be out of here kaje kayi ta sallolinka".


Dayan ya matso yana turawa Hussain robar abinci data ruwa gasansa, ya kunce masa daurin hannunsa sannan yaja baya, mai bindigar yace cikin gurbatacciyar hausarsa "mu na nan a bakin kofa, if you dare try to make any sound I will fill your brain with bullets" and Hassan knows he means it.


Sai da suka rufe kofar sannan ya dauke ganinsa daga kansu ya mayar kan hannunsa yana shashshafa shi, bringing back blood, sai da yaji hannun ya danyi masa dama dama sannan ya jawo kafarsa yana noticing yadda ta kumbura ya fara kokarin kunce ta, da kyar ya iya kuncewa saboda karfin daurin da suka yi masa da kuma kumburin da kafar tayi. Ya jawo ta yana shashshafa ta sannan yayi kokarin mikewa yayi alwala da ruwan da suka bashi, bai san inane gabas ba kuma ko ya tambaya ba zasu gaya masa ba dan haka sai ya zabi guri ɗaya yayi niyya ya tayar da sallah sa, saboda shi addini mai sauki ne, ubangiji masani ne kuma mai rahama ne.


Bayan ya idar, yayi dogayen adduoi sannan ya zauna ya runtse idanunsa yana kokarin tuno yana yin da ya hango cikin dakin da mutanen suke. Dakin bashi da girma kuma da alama ba'a kammala shi ba dan jikin bangon babu penti kuma tagogin babu frames. Yayi assessing yadda yaga situation din, mutane biyu ya gani amma yasan su uku suka dauko shi, ina dayan? Ya tuno da muryar da yaji a mota, muryar da yaji kamar ya sani. Shin mai muryar ne baya nan? Ya tuna da yadda yaga suna magana cikin rada, da kuma yadda suka buga masa warning din kar yayi making sound, hakan yana nufin cewa a cikin gari suke, a cikin mutane suke. Ya kalli window din da take saman toilet din, glass ne, yana fasawa zasu ji kara kuma kafin ya gudu zasu harbe shi, dan babu imani sam sam a cikin idanun wannan katon. 


Yayi ajiyar zuciya ya jingina kansa da jikin bango yana shafa fuskarsa yana jiyo maganagun su kasa kasa a cikin dakin, his only option is to wait har Hussain ya basu abinda suke so su sake shi. Ba shi da ko digon kokwanto cewa Hussain zai biya kudin, ko da kuwa zasu nemi dukkan abinda ya mallaka zai basu, ko da zasu nemi ya bada kansa zai basu, ko da wani aka kama ba shi ba Hussain zai iya biyan kudin ransom ya ceto mutum. Shi mutum ne da dukiyarsa sam bata dame shi ba. 


Hassan ya yanke shawarar zai jira, yasan jiran ba zai yi masa dadi ba amma bashi da wani option than that. Zai jira har sai Hussain ya biya kudin sannan su sallame shi ya koma gida sannan kuma ya yanke shawarar yana komawa gida zai yi aure. 


Five days later...............


Tunda Hussain ya dawo Nigeria yake jiran barayin Hassan su sake kiransa amma shiru, ba kira babu message babu komai, shima kuma in ya kira number din Hassan din bata tafiya. Hankalin sa in yayi dubu ya tashi kuma commissioner of police ya gaya masa abinda suke so kenan, so suke su gama tsorata shi yadda duk abinda suka ce yayi zaiyi. 


Hussain ya girgiza kansa yace "then they don't know me as they claimed they do. I will give up anything for Hassan. One billion naira suka ce masa suna so in dollar bills kuma gata nan na hada na zuba a irin jakar da suka ce in zuba su kawai naje jira su gayamin yadda zanyi da ita" ya karasa maganar yana mikewa yana zagaye dakin. Haka yake tun sanda ya dawo daga China, baya taba zama na minti biyar a guri daya zai mike kamar wanda ake mintsinin sa, fuskarsa tayi baki, idonsa yayi ja kuma ya fada ciki saboda rashin cin abinci, rashin bacci da kuma rashin kwanciyar hankali.


A ranar da aka sace Hassan, Hussain Yana sauka a Beijing ya kira Hassan da niyyar ya gaya masa ya sauka, a lokacin kidnappers din suka dauka kuma direct suka gaya masa cewa yana hannunsu, suka bashi umarnin ya dawo Nigeria sannan suka gaya masa adadin kudin da suke bukata. Sai kuma suka turo masa hoto, hoton Hassan a daddaure a yashe a bandaki, hoton da har yau shine yake yawo a kwakwalwar Hussain, shine yake hana shi bacci. 


Ranar da ya dawo Nigeria gidan su ya cika da police da yanuwansu na Gombe da sauran abokan arziki da abokan aiki, kusan duk uncles dinsu da aunties da cousins dinsu sun zo. Yana shiga gidan zai gansu duk a zazzaune da charbi suna ja kamar gidan makoki, sai gidan yake nuna masa kamar Hassan ya mutu ne, sai yake tunawa da mutuwar Abban su.


Wannan ya saka ya tattara kayansa ya bar gidan ya kama daki a hotel duk kuwa da nuna wa da Aunty tayi cewa bata yarda da hakan ba, tana jin tsoron kar wani abu shima ya same shi. A hotel din ne commissioner of police ya same shi kuma ya hada shi da SS dan suke tsaron lafiyar sa "bamu san menene nufin su na yin shiru haka ba, maybe tarko suka dana, maybe kai suke nema mistakingly suka kama Hassan". 



Bayan kwana biyar da kama Hassan ne kidnappers din suka sake contacting Hussain da wayar Hassan din. Message suka tura masa 


"Kana so ka sake ganin twin dinka? Ka cire police daga gidan ka sannan su daina zuwa hotel din da kake zaune, SS din da suke gadin ka ma ka sallame su idan ba haka ba zamu dawo maka da Hassan, but in PIECES" 


Ya ajiye wayar a gefe ya mike ya fara pacing dakin da yake ciki yana yarfar da hannayen da, sai kuma ya shiga toilet ya yo alwala ya dawo ya gaya wa Allah sannan ya dauki wayar sa yayi wa commissioner forwarding message din na su. Jima wa kadan kira ya shigo daga commissioner din ya dauka baice komai ba. Commissioner yace "barazana ce suke yi maka kar hankalin ka ya tashi ba zasu iya yi masa komai ba tunda suna bukatar kudin ka" Hussain ya lumshe idonsa ya bude, he is not going to take that risk, yace "ku janye mutanen ku. I will do this thing alone, zan iya" commissioner yayi ajiyar zuciya yace "I understand, zamu matsa, but Please keep us updated, daga an karbe shi kuma zamu yi moving in mu kama su mu dawo maka da kudin ka" Hussain yace "alright. Nagode" ya ajiye wayar tare da saka hannayen sa ya rufe fuskarsa. 


A lokacin wayar Gimbiya Fatima ta shigo, she had been very supportive dan sau biyu tana zuwa Kaduna gurin sa tare da brother dinta. Mai martaba ma ya aiko takanas anyi masa jaje kuma yayi alƙawarin saka Hassan a cikin adduoin sa da kuma umartar malamai suyi ta addu'a akan lamarin. Ya dauka wayar ya gaya mata duk halin da ake ciki. Cikin shigar lallashi tayi ta bashi baki tare da bashi shawarwari har sai da taji alamun ya dan daidaita sannan suka yi sallama.


Dare yana yi yabi shawarar da Gimbiya ta bashi, ya kira Salisu ya taya shi hada kayansa sannan ya zame jikinsa ya bar hotel din ba tare da sanin kowa ba, ya koma wani hotel din ya saka Salisu yayi masa reserving daki secrectly ya shiga yayi zamansa. 


Washegari da safe wani message din ya shigo. 


"Ka dauki kudin, da karfe goma sha biyu na dare ka saka a back seat din motarka ka fita kai kadai, make sure police basu bi ka ba, kaje kofar companyn ka, inda muka dauki Hassan kayi packing motar daga gefen katanga ka bar key a jiki ka fita ka hau babur ka koma gida. Ko Aunty ka gaya wa zamu sani"


Ya karanta sannan ya ajiye wayar, a ransa yana noticing yadda suka ambaci Aunty da sunan Aunty. 


Sai ya dauki wayar yayi musu reply


"Then how do I get my brother?"


Suka amsa


"Zai dawo gida da ƙafafuwan sa, that's in kayi abinda mukace, if not, zaka tsince shi somewhere"

 

Hussain bai kira commissioner ba kuma bai yi niyyar kira ba. Da magrib ya fita shi kadai a mota ya koma gidan su, an tafi masallaci dan haka mai gadi ne kadai yaga shigarsa shima kuma ya gaya masa kar ya gaya wa kowa yazo. A dakinsa bayan yayi sallah ya bude safe box dinsa ya dauko jakar da ya zuba kudin ya sake kirgasu ya tabbatar sun cika sannan ya ajiye ya kwanta akan gado ya rufe idonsa. 


Sai karfe goma ya tashi yayi wanka yayi sallar ishai sannan ya zauna yana kallon agogo yana ticking har ya sauka kan 12 sannan ya mike ya dauki jakar ya fita. Babu wanda ya ganshi sai salisu sai kuma mai gadi. Ya dauki hanya har zuwa inda suka gaya masa yayi packing ya tabbatar babu wanda yake ganinsa sannan ya fita ya danyi tafiya a kasa sannan ya tari babur ya hau ya koma gida, yana sauka sako yazo masa "very good boy, aikin ka yayi kyau. Ka zauna ka jira zuwan danuwanka".


Ya mayar da wayar cikin aljihun sa ya shiga gida ya zarce Bedroom dinsa ya sake wanka ya zabi kaya masu kyau ya saka, ya saka hula, agogo, socks da takalmi ya fesa turare ya dawo palor ya zauna, idanunsa akan kofa, waiting......



Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account 

First Bank

Account Name : Alhassan Musa Sadiq

Account Number : 3189669587 


Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin

09135803002 


Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin

09135803002 


Dan girman Allah banda kira, WhatsApp only




Saura Episodes biyu mu gama free 😊👬🏻 TAGWAYE 👭🏻



By



Maman Maama




Free Episode




Episode Nine : Gun shots


Kwanakin nan guda bakwai sune one of the worst kwanaki da Hassan ya taba gani a rayuwarsa. Sau daya suke bashi abinci ruwa ma sau daya, sunce in yaci ya koshi zai iya kokarin playing hero. Ruwan da suke bashi kuma shi yake cancanawa yayi alwala dashi saboda bashi da ruwan alwala, wanda ya rage kawai shine wanda yake sha sai gobe kuma. Wanka kuwa tunda yazo jikinsa bai ganshi ba, shi lanshi yasan jikinsa warin datti yake yi dana gumi, saboda toilet din da yake rufe a ciki babu hanyar iska sai ta cracks din kofa.


Addu'a ita Hassan ya rike a ransa, Alqur'ani kuma shine abokin hirarsa, shi yake debe masa kewa tunda bashi da wanda yake magana dashi sai dai in sun shigo sau daya, in suka shigo ɗin kuma babu magana a tsakanin su sai tsoratarwa a kan in yayi trying wani abu, suna kuma lissafa masa abubuwan da zasuyi masa idan har dan uwansa bai basu kuɗin da suke nema a gunsa ba.


Sannan ga kafar sa guda daya da take damunsa, har yanzu a kunbure take, yana tunanin wani kashin ya samu matsala wanda yake bukatar attention din likita, da yayi musu complain sai suka yi dariya suka ce "you won't be needing the leg in bamu samu kudin mu ba, so worry about our money not your leg".


A ranar da ya cika kwana bakwai ne suka yi masa albishir da cewa "yau zamu karbi kudin twin dinka, yau zaka tafi gida one way or another, in yayi abinda muka ce zaka tafi gida da ƙafafuwan ka in kuma bai yi ba........." Suka kwashe da dariya. Tun lokacin hankalin sa yake tashe, yasan halin Hussain sarai yasan zai bayar da kudin amma kuma yana da kankanba, yana da taurin kai kuma bai fiya bin umarni ba koda kuwa umarnin daga Aunty ya fito balle daga wadansu garorin unguwa, but since his life is at stake maybe, just maybe, zai zama careful for once.


Magrib tayi, yayi sallah, yaji ana kiran ishai itama ya tashi yayi sannan ya zauna ya mike kafar sa yana kallon guri daya, waiting..........


Wadannan sune awannin mafi ya tsaho da Hassan ya gani a rayuwarsa, gashi babu agogo balle ya duba yaga lokaci, a zaune kawai yake yana sakawa yana warwarewa. Mutum daya daga cikin kidnappers din yana lekowa gurinsa yayi reminding dinsa cewa yana nan fa, kar yaji shiru ya dauka babu kowa, sai Hassan ya fahimci cewa shi kadai ne maybe sauran sun tafi karbar kudin ne, sai yaji yana jin tsoron kar suyiwa Hussain wani abu. 


After the long hours yaji tsayuwar mota a gaban gidan, jikinsa ya bashi cewa this is it. Yaji maganganun su a dakin suna magana kasa kasa da dariya. Sai yaji yana son jin maganar da suke yi, Allah yasa ba wani abin suka yiwa Hussain ba, ya mike tsaye jikinsa babu isasshen karfi yaje bakin kofar ya jingina kunnen sa yana son jin abinda suke tattaunawa akai. And then something happened...........


Jinginar da yayi a jikin kofar ya saka kofar ta bude da kanta, ashe wanda ya shigo dazu ya manta baiyi locking dinta ba, sai kawai ga Hassan ya fado cikin dakin kamar an jefo shi, ya fado tsakiyar kidnappers din, gaban jakar kudin da suke budewa fuskokin su cike da farin ciki da murnar cikar burinsu na shiga layin masu kudi. Farko tsorata sukayi duk suka mimmike kamar yadda shima ya tsorata, sai kuma tsoron fuskarsu ya rikide zuwa wani rikitaccen yanayi yayin da nashi tsoron ya koma mamakin abinda idanunsa suka gani a gurin.


"Salisu?" Ya fada da wata irin murya, "me kake yi a gurin nan? Ko kai Hussain ya turo ka kawo musu kudin?" Salisu ya mike tsaye daga durkushen da yake a gaban jakar, fuskarsa dauke da yanayin tashin hankali da kuma tsantsar rashin gaskiya yace "am oga....ai wato oga.....oga me kake yi anan?" Ya fada cikin inda inda. Sai yanzu Hassan ya fahimci muryar da yake ji, sai yanzu yayi placing muryar, yaji zuciyarsa tayi sinking, yaji gwuiyoyinsa sunyi masa sanyi sun kasa daukan sa har sai daya durkushe a gurin yana jin zuciyarsa tana yi masa zafi.


"Salisu? Me yasa? Me yasa zaka yi mana haka ni da danuwana? Wannan wanne irin cin amana ne? Menene bamu yi maka ba? Menene bamu yiwa iyayenka ba? In kudi kake so mai yasa ba zaka tambaye ni ba? Me yasa ba zaka tambayi Hussain ba? Duk abinda kake so zai yi maka" 


Salisu ya shafa kansa yana girgiza kansa yace "zaku bani kudi na sani amma ba irin wadannan kudin ba" ya fada yana zaro wrapper ta dollars ya jefa a gaban Hassan "irin wannan kudin na keso, irin kudin da zan ke chanja motar da naga dama a lokacin da naga dama kamar yadda oga Hussain yake yi" Hassan yana girgiza kansa shima yace "akan kuɗi? Akan kuɗi zaka ci amanar mu? Akan kudi zaka saka rayuwata acikin hatsari salisu? Menene kuɗi? Is the money really worth it? Is this money really worth haɗa rayuwarka data irin wadannan mutanen?" 


Ya fada yana nuna sauran mutanen guda biyu, maganar ta makale a bakinsa sanda ya hada ido dasu, duk su biyun shi suke kallo kuma idanuwansu babu ko da digon imani a ciki sannan bakin bindigarsu yana saitin sa, zuciyar Hassan ta sake bugawa yana kara fahimtar situation din daya ke ciki. Yanzu ya tabbatar ba zasu barshi da rai ba, ya gan su yaga fuskokin su, asirin Salisu kuma ya tonu yasan yana da hannu a ciki, babu yadda za'a yi su barshi da rai.


Ya girgiza kansa da sauri yana daga hannayen sa sama "babu wanda zan gaya wa, ku dauki kudin ku kuyi tafiyar ku nima zanyi tafiya ta babu wanda zai ji komai daga bakina" Dayan yace "ai ba yau aka haife mu ba Malam, kana fita daga gurin nan zaka bawa duk wanda zai tsaya ya saurare ka labari a kanmu, zaka kwatantawa police kamannin mu da bayanin gidan nan. Niyyar mu mu sake drugging dinka mu mayar da kai har kusa da gidan ku inda za'a tsince ka a mayar da kai gidan ku, but you seems to be in a hurry, shine ka fito ka rusha pland din mu. Kai kayi asara, mu mun riga mun karbi kudin mu".


Salisu ya kalli Hassan sannan ya kalli sauran mutanen biyu, sai ya tsallaka ya shiga tsakani "ba zaiyi magana ba, bamuyi haka daku ba, kuɗi muka ce zamu karba kuma gashi mun karba bamuyi daku cewa zaku kashe shi ba, na gaya muku brother dinsa zai bada kuɗin kuma gashi ya bayar. Let him go".


Babban ya saka hannu ya ture shi yana cewa "bamuyi Yarjejeniyar cewa zai ga fuskar mu ba, yanzu yaga fuskokin mu kuma yaganka, the deal is off, dole ya mutu" 


Nan take musu ya kaure a tsakanin su, shi Salisu baya son a kashe Hassan, so yake a barshi ya tafi in yaso sai su gudu su bar kasar, su kuma basa son taking that risk. A lokacin ne Hassan ya ga dama ta same shi, ya lura da yadda mutumin ya rike bindigar a sassauce dan haka yayi yunkuri ya doke bindigar ta fadi kasa can karshen dakin, cikin second daya duk su ukun suka kaiwa bindigar wawaso, shi kuma a second din ya kama window ya haura, ba tare daya jira komai ba ya doshi kofar shigowa gidan a guje duk da ciwon da kafarsa take yi masa.


Yana fita daga gidan yaji karar harbin bindiga, bai waiga ba kuma bai tsaya ba sai ma kara mai da yayi yayi hannun dama ba wai dan yasan hanya ba sai dan neman Sa'a.


Kamar yadda yayi tsammani, gidan a cikin unguwa yake, duk da dai ya dan yi gefe kadan kuma kwangwaye ne a zagaye dashi kuma shi din ma kusan kwangon ne, inda ya hango gidaje sosai nan ya dosa duk kuwa da cewa duhun dare ya ratsa sosai dan ma dai akwai hasken farin wata wanda yake haska masa hanya, layikan babu kowa, duk gidajen mutane da shaguna a rurrufe, a lokacin yaji zafin wani abu kamar an saka karfe a wuta an goga masa a gefen wuyansa, zafin yazo tare da sake jin wata karar bindigar daga bayansa. Bashi dako tantama yasan cewa harbinsa akayi kuma bullet din ya wuce ta gefen wuyansa.


Kwanar daya gani a gabansa ita ya sha a guje, yana shan kwanar yaga wani gida a zagaje da langa langa sai ya samu kansa da bude gefen langa langar ya shige cikin gidan, yaji tsinin wani abu ya shige cikin kafarsa dako takalmi babu, azaba ta saka shi ya fadi kasa yana rike kafar tasa da hannu biyu yana tunanin cewa koya tsira daga wannan halin zai iya rasa kafarsa. Ya saka hannu ya shafa kafar yaji kusa ce ya taka ta shige cikin kafar, ya kama ta ya zare daga jikin kafar yana rintse idonsa cikin azabar zafi sannan kuma ya saka hannu daya ya rike gefen yuwansa da yake zubar da jini, daya hannun kuma ya rike kafar tasa itama da take zubar da jini. A hankali ya zame ya kwanta a gurin yana mayar da numfashi.


********************************************


Tun farkon dare Ruqayyah da Sumayya suka dauko littattafan su suna karatu saboda yanayin jarabawar da suke ciki. Babu wanda yake magana a cikin su sai dai lokaci zuwa lokaci sukan dan tambayi junan su abinda basu fahimta ba kuma suyi wa junan su bayani har su samu su fahimta din. Lokaci zuwa lokaci kuma Ruqayyah takan yi tsaki "yar wayar nan ma ta zama ni bamu da ita, ballantana mu ringa shiga yanar gizo muna duba abubuwan da bamu sani ba kamar yadda sauran ɗalibai suke yi" Sumayya tace "Rukee ki gode Allah. Ke ta waya kike yi, wani ta abincin da zaici yake yi, wani haka ya kwanta yau bai ci komai ba, wani ma kuma bama ya zuwa makarantar gabaki daya" Ruqayyah tace "kaina na sani Sumayya, abinda yake damuna nake fada ba abinda yake damun sauran mutane ba. Idan ba kyason ji ki to she kunnuwanki" daga nan Sumayya bata kara tanka mata ba suka cigaba da karatunsu har dare ya raba sosai sannan suka yi adduoin su suka kwanta. Bayan sun kwanta ne suka ji wata kara mai kama da harbin bindiga. Sumayya ta mike zaune da sauri "Ruqayyah? Kinji abinda naji kuwa? Kamar karar bindiga nake ji" Ruqayyah ta gyara kwanciyar ta "ke kika sani, karar bindiga kuma Allah na tuba a zamanin nan ai ba bakon abu bane ba" Sumayya ta jawo jiki tazo ta makalkale a jikin Ruqayyah "ni wallahi tsoro nake ji, kar fa ace yan fashi ne suka shigo unguwar nan" Ruqayyah ta ture hannunta, "dan Allah malama ki bar ni inyi bacci na, in yan fashin ne ma nan gidan zasu shigo? Me zasu dauka a nan gidan? Alluna ko ƙasa?" A lokacin suka sake jin karar wani harbin na biyu, Sumayya ta takure a guri daya tana adduoi, Ruqayyah kuma tayi tsaki tana gyara kwanciyar ta. Sai kuma ta mike zaune kamar wadda aka mintsina tana cewa "ni fitsari nake ji ma, toilet zanje" Sumayya ta rike ta "harbi fa ake yi Hassana, ke wacce irin zuciya ce dake?" Ruqayyah tace "to ni tunda bani ake harbi ba ina ruwana, ko so kike yi inyi fitsarin a kan katifa? Ki kwantar da hankalin ki ba anan kusa bane ba can layin bayan mune maybe ma police ne suke training" Daga nan ta fita ko fitila bata dauka ba saboda dakakkiyar zuciyarta.


Da addu'a a bakinta ta shiga toilet din, ta tsugunna bakin rariya tayi fitsarin ta tayi tsarki sannan ta tashi tana gyara rigarta, anan ne taga abu kamar jini, tayi shiru tana kallon abin sannan idonta ya sauka akan langa langar da take a bude kamar an dube ta da karfi, tabbas an shigo gidan nasu kuma wanda ya shigo din yaji ciwo. Ta mike da sauri tana buɗe baki da niyyar yin ihu sai taji an saka hannu an toshe mata baki ta baya an saka wani hannun an jata baya zuwa cikin inuwar da take jikin katanga, ta jita a jikin mutum, ya hada ta kirjinsa, shi kuma ya jingina da jikin katangar.


Daga karfin hannun daya riketa ta fahimci namiji ne, daga warin da take ji yana tasowa daga jikinsa na datti tasan ba daga guri mai kyau yake ba, daga kuma bugun zuciyarsa da take ji tana bugawa da sauri sannan da kuma karfi a kirjinsa tana bugun bayanta tasan cewa a matukar tsorace yake. 


A lokacin ne taji motsin wasu sun shigo kwanar gidan su a guje, daya yana tambayar dayan cikin hausa marar kyau "ka tabbatar nan kaga ya shigo?" Dayan yace "nan ya shigo, am very sure" suka wuce da sauri. Mutumin daya rike ta ya sassauta rikon da yayi mata, sannan ya kawo fuskarsa dai dai kunnen ta a hankali yace "help me, please. Ki taimakamin, dan Allah" 


Ga masu son siya zasu iya turo kudinsu ₦300 ta account 

First Bank

Account Name : Alhassan Musa Sadiq

Account Number : 3189669587 


Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin

09135803002 


Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin

09135803002 





Saura Episode daya mu gama free😊👬🏻 TAGWAYE 👭🏻



By



Maman Maama

Post a Comment

0 Comments