TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

👬🏻 TAGWAYE 👭🏻 19 & 20

 Episode Nineteen: The Real Princess


An kusa zuwa dai dai gurin. Lol


Jin tayi shiru bata ce komai ba ya saka yayi saurin chanza topic din. "Ina son ganinki sosai Sumayya, amma ban san yadda za'a yi in ganki ba. Ko kina da shawara?" Ta girgiza kanta tana kokarin kawar da shock din waccan maganar tace "bama gidan da ka sani yanzu mun tashi" ya ce "what? Kina nufin duk zaryar dana ringa yi da karawa wuyana tsaho ko zan hango ki a banza nayi ta kenan?" Tayi dariya shima yayi sannan tace "mun tashi daga unguwar" yace "to ina kuka koma?" Tace "naji Hassan yace gobe zaku hadu dashi, ka tambaye shi sai ya baka full address din, ni am not familiar with unguwar har yanzu dan haka ba zan iya yi maka kwatance ba" yace "wannan mutumin? A gurinku ne fa ku yammata yake sakin fuska har da dariya. Da naje office dinsa har na fito banga hakorinsa ba" Sumayya ta sake dariya tace "haba dai, yana da kirki fa sosai. Shi ya siya mana sabon gidan nan da muka dawo" Adam ya taya ta murna sannan ya bata labarin yadda suka yi da Hassan a office dinsa ranar nan, sannan ya kara da cewa "yace gobe inje in same shi. Maybe ya gama binciken nasa ne zan je inji result. Pray for me please" 



Tayi masa alkawarin addu'a da kuma fatan alkhairi, a ransa yana so ya tambaye ta game da hadin Ruqayyah da Hassan da har zai siya musu gida amma sai yaji kamar yin haka zai zama stepping on the boundary tunda dai ba abinda ya shafe shi bane ba. Sun jima suna hira, yana ta bata labarin yadda yake zuwa unguwar su nemanta baya ganinta. Tana ta yi masa dariya yace "ni ko? Zan rama ne. Dadinta ma kema gashi kin kasa hakuri kin nemi number ta kin kira ni. But Wait, wai layin kine wannan?" Tace "oho maka. Tunda gori zakayi min" yace "to ko ba layin ki bane ba kiyi wa mai layin albishir cewa baccin sa is now limited, dan zanyi ta kira ne ba kakkautawa" sun jima suna hirar su freely like old friends, har sai da ta ji alamar shigowar Ruqayyah palo sannan tayi masa sallama ta kashe wayar, amma ta kasa cire murmushi daga fuskarta.


Ruqayyah ta shigo tana binta da kallo, sannan ta kalli wayar tace "sai yanzu kika gama wayar? Tun dazu wayar kike yi" Sumayya tace "a tambayo" tace "wa za'a tambaya? Ke nake tambaya ai" Sumayya tace "shi bai gaya miki number din waye ya bani ba?" Ruqayyah ta zauna tana cewa "ina zai gaya min? Shi bayan maqon kudi ma har maqon magana yake yi. Kwaji dashi daga ke har shi, shi ce min yayi wai wani abokin sa ne ni kuwa nasan ya za'a yi ni bansan kowa a abokan sa ba amma ke ki sani har kuke exchanging numbers" Sumayya bata kula ta ba ta fara chanja kayan ta zuwa na bacci, sai data gama sannan ta zauna a bakin gado tace da Sumayya "Sumayya so nake in ya sake dawowa jibi ki je gurin sa dan Allah kuyi maganar bikin nan, ni bansan me yake shirya wa ba kuma kinga lokaci yana ta kurewa. So nake ya bayar da kudin da za'a siyawa kawayen mu anko kowa a kai mata ba wai ace mutum ya siya ba, nima kuma ya bani kudin kayan fitar biki. Sannan kuyi maganar events din da za'ayi, da event centers din da za'a kama tunda kinga gidan nan ba zai isa ba. Ku dai yi maganar sosai Sumayya ni na kasa yi masa".


Sumayya ta tashi zaune tana cewa "to baki sani ba ai koya gama shirya komai. Amma dai zanyi masa maganar ai. Ke ma tun tuni nake miki maganar kawayen nan a samu a gaya musu, a fitar da anko kin ƙi" Ruqayyah ta tabe baki tace "ni so nake yi in na samu aka sai musu ankon sai a kai musu har gida, ai yafi a mutunce. Zan baki list din wadanda za'a siyawa sai ki fada masa number din, in aka yi musu kala biyu ai ya ishe su ko? dasu za'a yi duk events din".


Washegari da wuri Adam ya shirya ya tafi office din Hassan, tun kafin 12 din tayi dan kar yayi late ya kara laifi akan wanda yasan already ya riga yayi, dan yasan Hassan ya samu labarin da baya so ya samu din. Yau bai jima yana jira ba, 12 din tana yi aka aiko kiransa. Ya shiga da sallama sannan ya zaune, still fuskar Hassan ba yabo ba fallasa ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace "kamar yadda nace maka zan sa a yi min background check to anyi din kuma zance kusan komai yayi dai dai da abinda ka gaya min except your name, ance ba sunan ka Adam ba, traditional name dinka Gbenga, Christian name dinka Joseph. To bansan inda ka samu Adam din ba" Adam yace "it is my Islamic name" Hassan ya daga kafada yace "but baya reading a duk takardun ka" Adam yace "zan gyara ai, so nake in na samu shiga makaranta zan gaya sai in cigaba da using" Hassan yace "it is okay, kawai dai so nake inyi confirming cewa kai din ne ba using info din wani kai ba, duk da dai description din duk irin naka ne sai dai wancan is a Christian kai kuma musulmi. Or aren't you?" Adam ya bata fuska, ransa ya fara baci yace "I am" Hassan yace "an samu misinformation kenan. Sai na dauka cewa ko ba dai dai naji ba sanda kace min you are a muslim, saboda wancan is a Christian daga shi har parents dinsa". Ran Adam ya kara baci yace "to amma shi mai baka info din bai gaya maka cewa Joseph yayi converting to Islam ya chanja sunan sa zuwa Adam sannan ya bar gida two years ago ba? Maybe you should dig dipper" Hassan ya danyi murmushi kadan sannan yace "nasan wannan, just want to confirm, kuma an gaya min Joseph yana da bad temper" Adam ya mike tsaye yace "so does Adam" sannan ya juya ya fice daga office din tare da bugo kofar.


Ransa a bace yake har yaje gida, bai san neman aikin zai zamar masa terere ba da bai fara ba tuntuni. Yasan dole zai digging that part of him tun sanda ya gaya masa zaiyi bincike a kansa but bai san zai zauna yayi ta jifansa da kananan maganganu ba, tunda har ya binciko Christian name dinsa kuma ya gaya masa Adam is his Islamic name ai ba kuma sai ya bashi labarin cewa he is a convert ba. Wannan tambarin shi yasa ya bar kano, ya bar iyaye sa da siblings dinsa da friends dinsa gabaki daya saboda ya kasa belonging, to the christians suna kallonsa a matsayin wanda yayi wa addininsa ya kuma yi musu butulci dan haka har farautar rayuwarsa suke yi, to the Muslims kuma suna kallonsa a matsayin wanda yake da wani bakin penti da komai yawan sallarsa da ibadar sa ba zai iya goge shi ba. Wannan yasa ya bar kano ya dawo Kaduna, to burry his past.


Asalin iyayen Adam mutanen jahar imo ne, neman kudi ne ya kawo babansa kano, anan aka haife shi a matsayin first born sannan aka haifi brother dinsa Samuel sai kuma sisters guda biyu Gloria da Martha. Lokacin da aka haifi Adam mahaifinsa bashi da kudi sosai, sai daga baya dukiyar sa tayi ta habaka kamar an sakawa flour yeast, dan haka Adam ya tashi ne tare da sauran yaran unguwa, wadanda yawancin su hausawa ne kuma musulmai. Duk gidan da Adam yake shiga wasa gidajen musulmai ne, makarantar da yake zuwa malaman da daliban yawancin su musulmai ne, a na kuma koya musu islamic studies har shi da ba musulmi ba. Kuma wasu lokutan idan abokansa zasu je islamiyya yana binsu ya zauna a aji tare dasu yaji karatun da ake yi musu, Tun daga nan yake son musulunci.


Alokacin takaicinsa shine sunday tayi mamansa da babansa su tafi dashi church suje ayi ta waka da kida da rawa, shi a zuciyarsa sai yake ganin a dira goshi a kasa kamar yadda musulmai suke yi a sallah yafi kama da ibada akan ayi rawa ayi waka. Shi kalaman da yake ji ana karantowa a cikin Alqur'ani sunfi yi masa kama da kalaman ubangiji akan abinda pastors dinsu suke fada musu a church. Behavoirs din da yake gani a gurin musulmai tafi yi masa kama data mutanen kirki akan wadda yake gani a gurin iyayensa da sauran Christians.


Tun daga nan ya saka musulunci a ransa, har ya girma ya shiga secondary school, a nan ne ya fara fitowa da abinda yake zuciyarsa yana nunawa a fili. Kullum ya samu musulmi sai yayi tayi masa tambayoyi akan addini, in ya shiga cikin abokan da basu san shi Christian bane ba sai yayi basaja ya bisu suje masjid suyi sallah. Anan ya iya sallah complete dinta, ya iya karatun wasu daga cikin surorin Alqur'ani kuma yake karantawa a cikin sallar kamar yadda yaga anayi. And he finds peace duk sanda yayi sallar. He finds peace in the masjid.


Tun daga nan ya sani har zuciyarsa cewa musulunci shine addinin gaskiya ba Christianity ba, yasan cewa kuma one day he is going to walk in cikin wani masallaci ya samu imam din yace a musuluntar dashi. Already yasan abinda ake reciting in za'a musulunta din ma kuma ya iya. Already har ya zabi sunan Adam a matsayin sunan da zai zaba. Ya daina zuwa church. Tun daga nan trouble dinsa ya fara, tun daga nan iyayensa suka gane halin da yake ciki.


Farkon abinda suka fara yi masa shine cire shi daga school sannan suka dauke shi gabaki daya suka mayar dashi gidan pastor, akayi ta masa wa'azi irin nasu ana yi masa adduoi irin nasu aka rarrataya masa cross iri iri a jikinsa but duk abinda suke yi shiga yake yi ta kunnen hagu yana fita ta dama. The more suka yi masa magana akan Jesus Christ da Bible da Christianity the more yake kara fahimtar cewa it is wrong. Yana kara jin cewa he never belong there, haifarsa kawai akayi a can.


Bayan ya dawo gida iyayensa suka fahimci babu chanji sai suka sake daukarsa suka mayar dashi imo gurin kakanninsa suna ganin cewa zama cikin musulmi ne ya jawo musa halin da yake ciki. A can imon kakanninsa suka dora daga inda iyayen suka tsaya, suka kara da binne binne da tsaface tsaface da preaching, pampering, promises amma a banza, a lokacin ne babansa yayi masa kyautar motar da yake ja yanzu saboda yaga yadda yake son mota da kuma alkawarin in dai ya cire musulunci daga ransa zai kai shi kasar waje yayi karatu acan saboda yasan yadda yake son karatun. Anan ne Adam ya nuna musu ya sauko, ya fara binsu zuwa church ana ayyukan ibada tare dashi, ganin haka yasa iyayensa suka dauko shi suka dawo dashi kano tare da su. A lokacin mahaifinsa yayi arziki sosai da sosai


Abinda Adam ya fara yi a ranar da suka dawo shine ya shiga cikin masallacin unguwarsu ya durkusa a gaban limamin masallacin yace "ina so a musuluntar dani" and that was it.


Babansa a ranar cewa yayi sai ya yanka shi. Limamin unguwar sune ya dauke shi ya boye shi sai ga uban da police wai an sace masa da. Inda ya samu sassauci kawai shine he was 19 years then dan haka he can stand up for himself legally, dan haka ya zamanto his words against his father's words. Ya fada cewa shi baya son komawa gidansu saboda babansa yace zai kashe shi tunda ya musulunta kuma yasan zai iya aikatawa. Wannan yasa dole aka barshi a gidan Imam din but still his father started to hunt him, har makaranta ya aika yan daba su kamo masa shi Allah ya taimaka masa ya gudu, sai liman din ya dauke shi daga unguwar ya mayar dashi hotoro gurin kaninsa. Ananne ya samu ya fara karatun addini ya kuma kammala secondary school dinsa, but anan ne ya fara fuskantar kyama daga gurin musulmai da kuma christians, hatta gidan da ake rikon nasa kyamatarsa suke yi basa barin yayansu su zama close to him. Akwai wata budurwa a gidan da mamanta ta taba zanewa saboda ta shiga dakin da yake ta kai masa abinci.


Kuma wani abinda yafi damunsa a lokacin shine in mutane suna kyamar sa sai ya tuno da family dinsa, ya tuno da irin soyayyar da suke yi masa musamman iyayensa shine favorite dinsu Saboda kwazonsa a makaranta da kuma kyawun halittar sa, haka siblings dinsa, ya shaku dasu sosai and he misses them everyday. Sai yayi taji a ransa cewa yana so ya gansu, yana so ya koma gidan su. Sai dai ya kasa chanza ra'ayin sa akan addini, fata kawai yake yi cewa suma su gane gaskiya suyi joining dinsa.


Shekarar sa daya a wannan gidan ya fahimci cewa zaman ba zai yi masa haka ba, and that's when his mother found him ashe nemansa take yi tsahon shekarar nan bata huta ba, tunda ta gane inda yake kuma bata huta ba ta cigaba da zarya tana rokonsa ya dawo gida, har siblings dinsa take kawo masa har cikin gidan da yake akan dan su ja ra'ayinsa ya dawo din amma bata saka ubansa a ciki ba saboda shi yayi fushi sosai. 


Ganinsa da ake yi da mahaifiyar sa sai aka kara kyamatarsa a unguwa ana ganin kamar komawa zaiyi zuwa Christianity, wadansu ma cewa suke yi ya koma, wannan ya saka mai rikon sa ya kirawo shi ya buga masa warning cewa in uwarsa ta kara zuwa gurinsa zai kore shi daga gidansa. And that's when he decided to leave Kano for good. Ya hada kayansa ya je har gidansu lokacin da yasan duk suna church ya sato motarsa ya saka kayan a ciki ya kama hanyar Kaduna. A hanya ne ya dauki waɗansu mutane zuwa Zaria suka biya shi kudin mota, sai kawai yayi deciding cewa he is going to be a taxi driver a haka har ya tara kudi ya kai kanshi makaranta.


But kudin sunki taruwa. Sannan yasan karatun ma kuma ba zai zo masa da sauki ba. That's why he needed aikin gurin Hassan saboda yaji possibility na komawa school, but yanzu yana jin cewa he doesn't need it anymore.



A ranar da Ruqayyah da Sumayya suka shirya zasu hada kai su tunkari Hassan da Maganar shirye shiryen biki, a ranar da rana sai ga kannensa mata sunzo gidan gabaki dayansu su biyar. A tare dasu akwai akwati guda biyu masu dan girma. Suka shigo da fara'ar su da kuma sallamar su, abinda Ruqayyah ta fara aiyanawa a ranta da taga akwatinan shine; "ba dai wannan ne lefen nawa ba". Daga nan sai ta tashi ta shige daki tun kafin su shigo palon. 


Inna Ade da Sumayya suka tarye su sosai suma da fara'a, suka gaggaisa Inna tana tambayar su Aunty suka ce tana lafiya lau kuma tana gaisheta. Sai suka fara neman Ruqayyah "ina amaryar tamu take? Sumayya ta waiga tace "tana jin shogowar ku ta gudu daki" Nafisa tayi dariya "ba dai kunyar mu take ji ba? In kuwa har kunyar mu take ji to kuwa na tausaya mata dan kuwa ni ana gama bikin a cikin bedroom dinta zan tare" Hassana ta harare ta tace "kar ku ce zaku takurawa takwara ta dan kungan ta shiru shiru bata da magana, gashi kuma bana nan ballantana in tare mata" Sumayya tace "wacece shiru shirun? Lallai ba ki san Ruqayyah ba alkunya takw yi muku amma in ta saba daku sai kunyi mamaki, watarana sai kunji kamar ku dauki ta ku dawo mana da abarmu" suka yi dariya Safiyya tace "abarku ku abarmu? Ai daga an daura ta zama tamu ku da ita sai tarihi" Inna Ade da take jinsu tana ta murmushi tace da Hassana "ke ce daya amaryar ko?" Hassana ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi, Inna Ade tace Allah ya sanya alkhairi kinji? Allah ya baku zaman lafiya bakiɗaya".


Daga nan sai Inna Ade da Sumayya suka fara hidimar bakin su, suka kawo musu duk wani abin sha da abinci da yake available a gidan, su kuma bakin suka diba kadan suka ci banda Khadijah da tace ta koshi. Bayan sun gama ne Hassana tace "dama Aunty ce ta aiko mu, tace mu kawo muku wadannan kayan inji ta, akwati daga kayan amarya ne na fitar biki akwati daya kuma naku ne kuma ku saka da biki. Tata gudummawar kenan" Inna Ade ta rike baki tace "me yasa ta wahalar da kanta har haka? Da ta barshi ma Baban biyu duk zaiyi mana" Hassana tace "ita dai gashinan to ta riga shi samun ladan". Inna da Sumayya suka yi musu godiya sosai sannan kuma Hassana ta kara da cewa "kuma tace mu tambaye ku menene tsarin ku na hidimar biki? Kuma in akwai wata al'ada da kuke yi bayan lefe ku fada kar azo ba'a yi ba tunda bamu sani ba" Inna Ade tace "aa babu wata al'ada wallahi, mu lefen ma da dan tamu ne ai zamu iya cewa Hassan ya barshi" Nafisa tace "ai kuwa lefe kan an riga an gama hada shi, jira kawai ake yi lokaci yayi azo a kawo" Inna Ade tace "maganar biki kuma ki gaya mata mu nan kamu kawai zamuyi sai yini, shikenan sai ku zo ku dauki amaryar ku" Hassana tace "ita amaryar ba zata yi komai ba?" Sumayya tace "jiya muka yi Magana da ita, ita wai kunyar angon ta ke ji ta kasa tambayarsa ko akwai abinda yake shirya musu" Hassana tayi dariya tace "lallai an gaishe ta, to ki gaya mata wallahi sai ta shafawa idonta toka ta cire kunyar nan, dan in dai yaya H1 ne na tabbatar babu abinda yake shiryawa. Gwara ita ta shirya sai ta gaya masa" Sumayya tace "to insha Allahu zan gaya mata" Hassana ta kuma cewa "Inna, kuma Aunty tace in rokar mata ku, dan Allah tana son za'a dauki amarya ranar juma'a da daddare, saboda assabar ne yinin da za'ayi a kano na amaryar yaya Hussain, to Aunty tana so a tafi harda ita Ruqayyah din mu kwana acan lahadi sai a dauko waccen amaryar a dawo" Inna tayi saurin cewa "babu komai ai insha Allah, in babansu ya dawo zan gaya masa kuma shima nasan ba zai ki ba. Sai a daura auren juma'a da safe in yaso da daddare sai a dauke ta".


Daga nan suka cigaba da tsare tsaren bikin, maganar kawo lefe da sauran su. Nafisa ta mike, "ni ina ne dakin da yayar tawa take ne inje in ganta, dan ita nazo kuma ba zan tafi ba sai na ganta" Sumayya ta nuna mata kofar dakin da Ruqayyah take ciki sannan ta juya suka cigaba da maganganun su. Sai da suka gama sannan Sumayya ta mike ta shiga zata kirawo Nafisa. Tana shiga dakin ta gansu dare dare akan gado suna hura har da dariya, da alama tasu ta zo daya. Nafisa tana cewa "wallahi ina baki labari, shi yasa wannan karon da Aunty zata tafi dubai karaso siyayyar kayan lefen ki naki binta sai ta tafi da Zulaihat. Kinsan ita Aunty bata son tafiya ita kadai tafi son ta dauki wata a cikin mu ta yafi da ita, shi yasa muke shifting in ya tafi da wannan yanzu wata tafiyar kuma sai ta dauki wata. Kinga in akayi bikin ku kema sai ki shiga layi ake yin shifting din da ke" Ruqayyah baki har kunne, already har ta fara hango kanta a Dubai tace "eh wallahi, sai mu shiga layi dani da wannan yarinyar da Hussain zai aura, Fatima sunan ta ko wa?" Nafisa ta bata rai tace "yarinya? Gimbiya Fatima ba yarinya bace ba dan tare suka gama service da yaya Hassana. A England tayi karatun ta ma ita." Murmushin fuskar Ruqayyah ya dauke, tace "Gimbiya Fatima? Ke ma bakin Hussain kike bi kike ce mata gimbiya?" Nafisa tace "to ai gimbiyar ce, ya ce fa a gurin maimartaba sarkin kano kuma naji ance ita ce favorite dinsa. Kinsan kuma yadda suke da kudi, shi yasa yaya H2 ya zage dantse sosai gurin hada kayan lefenta dan kar azo aji kunya. Jiya ma naga sunzo sun bude gidan sun shiga, wata kila a cikin satin nan zasu fara kaso kayan dakinta. I can't wait to see irin kayan da zasu yi mata" idanuwan Ruqayyah suka chanja kala "you mean she is a real princess?" Nafisa tace "ta gasken gaske ma kuwa"




Wannan littafin na siyarwa ne, in kina so WhatsApp 08067081020Nineteen: Shattered Dreams


Yadda Ruqayyah ta bude bakinta a haka ta barshi, magana ta kasa fitowa. Sumayya tayi saurin cewa "Nafisa ki zo suna jiranki zaku tafi" Nafisa ta sauko daga kan gadon tana gyara skirt dinta sannan ta dauki mayafin ta. "To yayata. Na ganki naji dadin hira dake kuma. Zamu koma sai mun dawo daukan ki" ta fada da yanayin tsokana, but Ruqayyah is in no mood for wasa, Sumayya tayi dariya tana distracting Nafisa tace "haba dai, yanzu kina nufin ba zaku zo komai ba sai daukan amarya? Nafisa tace "ai kinsan can din ma wasu events din ne, kin san biki uku ne zamuyi amma dai nasan ko bamu zo duk ka ba zamu zo wasu abubuwan" Khadijah ta budo kofa tana cewa "to suda me bakin magana, ki taho mu tafi" sai ta kalli Ruqayyah tayi mata murmushin da yafi kama da yake itama Ruqayyah ta mayar mata da irin sa, tana jin murmushin yana kokarin bude fanfon emotions din da take ta kokarin rufewa. Nafisa da Khadijah suka fita a tare, Sumayya tayi wa Ruqayyah alamar ta taso suje su raka su amma sai ta makale kafada ta kwanta ta ja bargo, Sumayya ta fita da sauri tana yi musu Allah ya kiyaye hanya tare da kara yi musu godiya. 


Ruqayyah ranta kuna yake yi, kalmar Princess ce take ta yawo a cikin kanta, wai yar sarkin kano, sarkin kano fa? Sarkin kanon da take ganin pictures dinsa yanzu a social media, sarkin kanon da tasan kudin takalmin sa daya zai iya siyan duk sutturar da Baba yake da ita har da ciko, yarinyar da akace tayi karatu a kasar waje bayan ita a Nigeria tayi nigerian ma a makarantar gwamnati kuma iyakacin secondary school sannan secondary din ma ko waec bata yi ba saboda talaucin ubanta? Gaskiya akwai aiki a gabanta. Ta tuno maganar Nafisa na she can't wait to see kayan dakin Fatima, ita kuwa babu wanda yake zancen nata tunda kyauta ma za'a yi mata kayan dakin, kuma ta tabbatar watarana sai an goranta mata. Dadin abinma kudin na mijinta ne, shi kansa Hussain din da ake zancen ya hada kayan kefe na gani na fada saboda zai kai gidan sarki ai da dukiyar mijinta yayi, dan zai auri yar sarki hakan bai chanja komai ba, dole ne ta shafawa idanunta toka kafin ta shiga gidan nan kuma dole ta kwatarwa kanta yanci a gurin Hassan dan in babu hadin kansa ba inda zata je za'a mayar da ita ne kamar takalmi kowa ma yake takata da wanda ya isa da wanda bai isa ba. 


A haka Sumayya ta dawo ta same ta a kwance idanunta a rufe, ta zauna akan bedside tana kallon ta a ranta tasan tunanin da take yi sai tace "it doesn't mean anything. Dan tana yar sarki ke kina yar malam Yusuf mai gadi ba komai bane ba, dan tana gimbiya Fatima ke kina plain Ruqayyah doesn't mean anything, rayuwarki daban rayuwarta daban, Allah ya halicce mu different for a reason, we are all unique for a reason, Allah yana amfani da uniqueness din mu dan yayi testing din mu, dashi yake jarabtar mu dan yaga yadda zamuyi. Idan mukayi kokarin copying others, ko muka yi kokarin comparing kan mu da others to kuwa zamu fadi jarabawar mu saboda mu da su ba daya bane ba. You are Ruqayyah, yar malam Yusuf da yake aiki kullum ba weekend babu annual leave yake ciyar da ke da duk sauran bukatun ki, ita kuma Fatima yar sarkin kanon da shima a sarautar aka haife shi ba wahala yasha ya samu ba, let her be gimbiyar ta matar Hussain while you be Ruqayyah matar Hassan cos that's your role, that's what............" Ruqayyah ta yaye rufar ta ta mike ta shiga toilet tana wanke fuskarta maganganun Sumayya ciwo suke kara wa kanta. Tana fitowa daga toilet din bata kalli inda Sumayya take ba ta wuce palo.


Sumayya taji zuciyarta tayi babu dadi, ta jima a zaune a gurin hannayenta tallafe da kuncinta sannan tayi ajjiyar zuciya ta mike ta tafi palon itama. Abin mamaki sai ta samu Ruqayyah kace kace cikin kaya tana ta bubbudewa ita da Suleiman da ya shigo yanzu. Inna tana gefe tana kallon su. Tan fitowa Ruqayyah ta kira ta. "Zo ki taya ni zaben wanda zan saka ranar kamu, kina ganin wannan lace din yayi?" Sumayya ta zauna tana karbar lace din tace "too heavy, kamu ai atamfa ya kamata ki saka. Wannan kuma kya saka ranar yini. Yauwa ga wani yadi can sai ki hada dashi. Kai! Kinga wani takalmi? Amma ya shiga da lace din nan" Ruqayyah sai murmushi take yi tana lissafa irin kyan da zata yi. Gimbiya Fatima is in for a surprise.


Da daddare Hassan yazo zance, kamar yadda suka shirya tare suka fita gurinsa. Suna gaisawa da Sumayya yace "mutumin ki fa yayi zuciya, ya tafi kuma bana jin zai sake dawowa" Sumayya ta bude ido tace "me ya faru? Lafiya?" Ya daga kafada yace "maybe na fadi abinda baiji dadi ba I don't know, maybe I was unintentionally rude to him amma ki kirashi ki ba shi hakuri on my behalf please, ina da interest akansa sosai and I like him a lot. I found out something about him da baya son a sani and it pissed him off, ni kuma abinda na samu din shine ya kara min karfin guiwa a kansa. Tell him that dan Allah and make him come back to my office" Sumayya ta dan bata rai tana kokarin hasashen abinda ya hada su amma Sai kawai ta bar maganar saboda bata son Ruqayyah ta shiga ciki amma sai da ta shiga. "Wait, you two, wai maganar me kuke yi ne? Maganar wa kuke yi wanda ku biyu kuka sanshi amma ni bn san shi ba?" Hassan yana kallonta yace "saurayin Sumayya ne,tace kuma kar in gaya miki ban kuma san dalilin ta ba amma zan rike mata amanar ta, it is her call, ita ya kamata ta gaya miki" ya juya yana kallon Sumayya yace "amma zan rike amanar ne daga nan zuwa bikin mu, in akayi biki to I can't promise cewa zan iya boye wa matata wani abu kuma" ya kare maganar yana murmushi, Ruqayyah ta sunkuyar da kanta tana murmushi a ranta tana cewa "you better not".


Sumayya ce ta shigar masa da maganar biki, ta tambayeshi plans dinsa, sannan tayi masa bayanin kayan da Aunty ta aiko musu dashi takuma yi godiya. Ya gyada kai yace "yeah, Aunty ta gaya min dazu da naje gida. Ina ganin ku shirya duk abinda kuke son yi ni amma personally babu abinda nake shiryawa gaskiya, akwai dai dinner da zamuyi gabaki dayan mu ranar Sunday bayan an dauko Fatima, dinner ce for dukkan couples din uku da friends din kowa da kuma family din kowa. To ita kadai zanyi attending gaskiya, sai daurin aurarrakin duk ukun. So, in kuka tashi sai ku shirya abinku da friends din ku kawai".


Ruqayyah taji tamkar ya kwada mata mari, taki gaya wa friends dinta maganar auren su saboda tana son tayi showing dinsa up a bikin su, amma yana ce mata ba zaiyi attending komai ba, ita kadai zata je ba miji, kamar wadda akayi wa auren dole?" Sumayya tace "it is okay" Ruqayyah tayi saurin juyowa tana kallon ta tana jin kamar ta makure ta, it is definitely not okay. Ita da ta kirawo ta saboda ta taya ta fighting shine zata yi saurin giving up? Yace "duk abinda kuke so fa ku fada kar ku boye min. Zan aiko muku da kudin da zasu ishe ku komai, in na baku kuma ko bai ishe ku ba ku gaya min sai in kara muku, ai nasan ba zakuyi abinda bashi da muhimmanci ba ko Hassana?" ta gyada kanta da sauri tana kirkirar murmushi, ba haka taso ba amma sai zuciyarta, har dark heart ta hana ta yin magana, a take kuma ta kitsa mata abinda zata yi.


Washegari kuwa sai ga sakon kudi ya aiko musu dashi, kudade ne masu yawa a idon Sumayya da Inna Ade da sauran mutanen gida, but as usual a gurin Ruqayyah taga kankantarsa duk kuwa da cewa bata taba rike kudi masu wannan yawan ba, ita kawai position dinsa take hangowa tana ganin yafi karfin wannan kudin. Sai ta saci jiki ta shiga daki ta dauki wayar Sumayya ta rubuta masa sako kamar haka.


Assalam. Yaya Hassan ina yini? Munga min gode sosai Allah ya kara arziki. Sai dai muna so ko za'a karo mana wasu dan ina ganin kamar wadannan din ba zasu ishe mu ba, kawayen mu suna da yawa, zamu yi arabian night da bridal shower kuma zamu basu soveniers gashi muna so muyi musu anko kala bibbiyu. Ruqayyah tace a barshi kawai amma sai nace bara ni inyi maka magana tunda kace in basu isa ba a gaya maka. Nagode

Sumayya



Ta tura masa sannan ta goge message din ta juya tayi kwanciyar ta. Ba'a jima ba ya kira wayarta, ta dauka ta gaishe shi sannan tace "munga sako dazu, mun gode sosai. Nace amma wadannan kudaden ai kamar sunyi yawa ko? Me zamuyi da kudi har haka, da rabin su ma ka bayar ai da sun isa" sai taji ya yi dariya, muryar sa cike da farin cikin da zuciyarsa take ciki, yace "dariya na baka ko?" Yace "nooo ba ke kika bani dariya ba, zuciyata ce cike da murna da farin cikin samunki a matsayin matata, a yanzu haka bani da buri illa inga ranar da za'a daura auren mu in ganki a gida na a matsayin matata, gaskiya daga ranar banajin ina da sauran wani buri a rayuwa dan nasan with you by my side my life will be completed" murya can kasa tace "so will mine".


Yace "yanzu na samu sako daga Sumayya, tana zancen wai kudin ba zasu ishe ku ba" Ruqayyah tace "what? Amma lallai wannan Sumayyan...." Yace "it is okay. Kowa dama ai da halinsa da kuma kalar tunanin sa. Sumayya kanwa tace dan haka ba zan watsa mata kasa a ido ba saboda nasan duk danke take yi sannan kuma yarinta ma tana damunta wai harda cews za'a yi wa kawayen ku anko kala bibbiyu" ya sake yin dariya, "babu wani abu, zan sake aiko da wasu kudin but kiyi monitoring dinta kar tayi almubazzaranci da yawa" Ruqayyah ta karya murya "ni wallahi da ka barshi ma. Wannan ai ni ta bawa kunya wallahi" yace "kunya, mijin naki kike jin kunya?" Tayi dariya, yace "kar kiyi mata maganar,kar ma ki nuna mata nace bata yi dai dai ba, dan mu take yi kinji? For you, I will do anything" tace "nagode. Allah ya bar mu tare har abada" yace "ameen, ni har gaban abada ma nake so muje tare. In naje office gobe zan aiko da sakon".


Washegari sai ta zama alert, tasan zai aiko da sakon kuma bata son wano ya rigata karba, dan haka a hannunta dan aiken ya danka envelope din. Ta wuce daki ta kirga taga dai dai yawan wadancan ne, sai ta bude cikin kayanta ta dauko wadancan kudin da take ta ajiiyar su na wajen Hussain ta hada da wadannan a ranta tana cewa, "in kasan wata ai baka san wata ba. Dole in tara kudi ko dan in kankarowa kaina mutumci a gurin yan uwanka da sauran mutane".


Sau ta debi kadan ta bawa Sumayya tace "inji Hassan, wai ko zaki yi wani abu" Sumayya tace "ni me zanyi? Duk abinda zanyi ai tare dake zamuyi. Shi dai kawai ya fiya kirki". Next zuwan da Hassan yayi suka hadu da Sumayya yace "sako na yazo miki ko?" Ta yi murmushi tace "yazo fa, na gode sosai" yace "asha biki lafiya".


Tun ranar da Hassan ya gaya wa Sumayya yadda suka yi da Adam take neman layinsa amma yaki dauka, sai bayan kwana biyu sai ta tura masa text


"In na sake kiran ka baka dauka ba ba zan sake kiran ka ba"


Mintuna kadan bayan nan sai gashi ya kira ta, tana dauka yace "why? Me yasa ba zaki sake kirana ba? Saboda abin da ya gaya miki a kaina ko?" Tace "me ya gaya min a kanka? Ni babu abinda ya gaya min a kanka kawai dai yace kayi fushi in kira ka in baka hakuri on his behalf, yace kaje ka karbi aikin" taji yayi ajjiyar zuciya sannan yace "naki daukan wayarki ne saboda bana son inji kalmomin daga bakin ki, na dauka ya gaya miki, na dauka kin kira ni ne kiyi robbing abin a fuskarta" tace "wanne abin kenan? Menene abinda baka so in sani?" Ya danyi shiru sannan carefully yace "ba wai bana so ki sani bane ba, ina tsoron yadda zaki yo reacting ne idan kin sani ɗin" tace "idan nasan me? Ba zaka gane ya zanyi reacting ba har sai ka gaya min tukunna" murya can kasa yace "reacting to the fact that I am a religious convert. I was a christian before..." Ya rintse idonta tare da kwanciya akan gado. She suspected as much, amma tafi son ya furta mata da bakinsa. 


Tace "you said it yourself, you said the word "before' before yana magana akan past, past is in the past, you are a muslim now, and that's all that matters. Kaje ka karbi aikinka, yace it doesn't matter" yace "I don't care about the job, I care more about you, zaki iya cigaba da kula....zaki ke kula....." Ya kasa fadan kalmar sai tace "kula musulmi? Idan ban kula musulmi ba wa kake son in kula Adam?" Ya lumshe idonsa ya bude "but my parents are still......" Tace "your parents are not you. Kai daban su daban, ba'a taba judging wani a bisa laifin wani. It doesn't matter who you were, what matters is who you are. And you are a muslim, you are Adam. And I like you" ya sauke ajjiyar zuciya mai karfi yana dora goshinsa akan stirring motarsa. Tun ranar nan, ranar daya saka kafafuwansa cikin masallacin nan ya karbi kalmar shahada bai taba jin wani ya gaya masa wadannan kalmomin da sune abinda yafi so yaji fiye da komai ba, cewa his past doesn't matter, kowa nuna masa yake yi kamar past dinsa wani rubutu ne a goshinsa da ba zai taba gogewa ba. Shi kuma tun kafin ya karbi addinin a dan ilimin da yake dashi akan Islam yasan cewa duk wanda ya musulunta tamkar sabon jariri yake, duk abinda ya aikata ya wuce kamar bai taba yi ba, an bude masa sabon littafi. But nobody made him feel like that, sai yau, sai Sumayya. Yace "thank you" yadda yace thank you din kawai yasa ta fahimci daga can wani lungu na zuciyarsa ya fade ta. Taji itama maganar ta taba tata zuciyar. 


Tace "kaje ka karbin aikin Adam, you need it" sai ta danyi dariya tace "kuma kasan me? In ka karbi aikin we will be closer tunda Ruqayyah zata yi aure a gidan" yayi dariya shima yace "you mean zan ke ganin ki ba tare dana yi dogon wuya ba" suka yi dariya a tare.


Adam yaje gurin Hassan, ya kuma karbi aikin personal driver na Hussain. Kallo daya Hussain yayi masa yace "he is strong, young and handsome. I like him" daga nan ya shiga daki ya kwaso masa kayan sawa jaka guda da takalma da huluna yace "a cigaba da gayu daga inda aka tsaya" 


Lokaci ya tura, satin biki ya kama. Tun farkon satin yan'uwa da abokan arzikin Inna Ade da Baba suka cika gidan, da yawa sunzo ne dan su kashe kwarkwatar idonsu akan zancen da suka ji na wanda Ruqayyah zata aura. Ita kuma Ruqayyah sai da ta tabbatar duk wanda yazo gidan nasu, ko a kawayen data gayyato ko kuma a yan'uwa ya san wa zata aura."CEO ne na H & H group of companies" daga nan sai ta bi sakakkun bakunan su da kallo tana jin cewa she have made it in life. Ruqayyah duk tayi abubuwan da take son yi da First kudin da Hassan ya bata, ta zabi friends na fita kunya, most of them ma ba kawayen ta bane ba kawayen Minal ne. Suka shirya bridal shower dinsu a gidan Aunty Hafsa yayar Minal aka ci aka sha aka yanka cake akayi hotuna, shigar da Ruqayyah tayi kowa sai ya tabbatar da abinda take fada akan mijin da zata aura, kowa ya tabbatar shi din ne dai.


Akayi yini anan gidan su ranar Alhamis, a ranar ne kuma aka kawo lefen Ruqayyah. Hatta ita kanta Ruqayyah duk abinta sai data yadda cewa tabbas anyi mata lefe, dan bata taba ji ko ganin lefe irin nata ba. A hankali a hankali take jin burikanta na rayuwa suna cika.


 Ranar juma'a da safe aka daura auren Hassan Aminu Abdullahi da Ruqayyah Yusuf Mu'awiyah. Farin ciki a gurin ango da amarya ba zai misaltu ba, kowa da abinda yake zuciyarsa, kowa da sirrin da yake zuciyarsa. Sai dai muyi mudu fatan zaman lafiya da zuriya mai albarka.


Gobe zamu kai amarya dakinta insha Allah, daga nan kuma sai muje kano mu dauko daya amaryar.


Wannan littafin na siyarwa ne, duk wanda yake so ya neme ni through WhatsApp ta wannan number 09135803002




Episode Twenty : Shattered Dreams 2


Yinin ranar nan murmushi ya kasa daukewa daga fuskar Ruqayyah, kowa in ya ganta sai yaga ta burge shi ga kyau, ga kwalliyar da ta ci ta gani ta fada, ga gyaran jiki da taje ta kashe kudi aka yi mata sannan ga farin ciki lullube da zuciyarta da kuma fuskarta. Yau ce ranar da burikanta suka fara cika, yau ce ranar data taka wani matsayi wanda zai zamo mata jagora zuwa ga matsayi na gaba a rayuwarta. 


Sumayya kuma tunda aka gama daura auren taji jikinta yayi sanyi matuka, ita kawai lissafin rabuwa da yar uwarta rabin jikinta take yi, bata jin tun da aka haliccesu sun taba rabuwa ta cikakken kwana daya amma wai yau Ruqayyah zata tattara ta koma wani gidan da zama kachokan. Tsakanin su sai dai ziyara, ziyarar ma tasan Baba ba barinta zai ke yi tana yi akai akai ba kamar yadda bata ga alamar Hassan zai zamo mai barin mata tana yawo koda yaushe ba. Sai data shiga toilet tayi kukan rabuwa da yar uwarta, amma ita yar uwar tata ko a jikinta, hirarta kawai take yi a cikin kawayen aronta suna ta dauke dauken hotuna tare da shirin dinner din da za'a yi ranar Lahadi da daddare. Already dama Hassan ya kawo mata cards na mutum hamsin, wanda sai da suka yi rigima da Sumayya dan boyewa tayi ta hana yan uwansu da suka zo biki "zuwa zasuyi wallahi su tsinka ni a cikin mutane, wasu fa ko cin abinci da chokali basu iya ba, gwara mu aro mutanen da zasu je a matsayin yanuwana shikenan mun huta. Mu dan dauki kudi mu basu sannan mu basu kudin liki" amma Sumayya taki yarda, dan me bayan ga yan uwanka sannan zaka tafi kaje kayi hayar yan uwa? Ita bata ga logic a cikin maganar ba. Ta gayawa Inna Ade ita kuma ta kira Ruqayyah tace mata "bani katinan" dole ta dauko ta miko mata tana kunkuni. Inna Ade ta bata guda ashirin na kawayenta sannan sauran ta rabawa duk wanda take ganin in ya dace yaje yaci arziki ya bar arziki a mazauninsa.


Juma'a din tunda yamma aka fara shirye shiryen kai amarya, Ruqayyah ta hada kayanta kaf a guri daya, ita bata yi wani alkunya ma ba na kin hada kaya ta bar Sumayya ta hada mata a'a tare suka hada ɗin, tana tunawa Sumayya akan duk abinda ta manta. Ita bata ga wani abinda zai saka ta bata ranta ko tayi wani kuka ba a ranar da ya kamata tayi farin ciki fiye da wanda take yi a kowacce rana, a ranar data yage rigar talauci ta lulluba ta arziki? 


Tun da yamma Inna Ade ta aika aka kirawo Hassana zuwa dakin Baba, suka tafi tare da Sumayya, tun kafin suje Ruqayyah ta riga tasan dalilin kiran, tasan fada ne za'a yi mata a kan zaman aure ita kuma tana ganin kamar bata lokacin su zasu yi su kuma bata bakin su, su fa irin zaman auren talakawa suka sani dan haka akan irinsa zasuyi ma ta fada, wannan kuwa aure na na masu abin hannunsu wadanda basu dawata sauran damuwa a duniya sai dai suci mai kyau su sha mai kyau su kuma kwanta a mai kyau. Ita tuntuni ta gama yiwa kanta fada akan yadda zata yi wannan zaman auren, ta riga ta kama bakin zaren Hassan ta fahimci cewa ba zata iya yi masa musu ba saboda yayi mata kwarjini dayawa amma zata iya cigaba da lullube kanta da hijabin daga riga ya santa dashi sannan tana jan zaren sa a hankali ta karkashin kasa kamar yadda tayi masa a lokacin karbar kudin hidimar biki. Let someone else take the fall, someone else, in dai har ba ita bace ba. Anyone. 


Suna shiga dakin sai taji Baba ya fara tsokanar ta, abinda ta jima bata ji yayi ba, da alama shima yana alhinin rabuwa da yar tasa ne. Sai da ya saka su duk yi dariya gabaki dayan su sannan ya fara magana.


"To Hassana, alhamdulillah, gashi kamar yau Allah ya bamu ku keda yaruwarki amma gashi cikin kudirarsa yau zaki bar gidan nan zuwa gidan mijin ki. Babu abinda zamu cewa Allah sai dai godiya tunda munsan kudirarsa ce kawai ta hada ku keda Hassan sannan ta saka soyayyar ki a zuciyar Hassan din. Dan girman Allah Ruqayyah kar ki bamu kunya, ina tsananin ganin girman yaron nan wallahi kuma in da zaki bi ta ta shi na tabbatar ba karamin zaman lafiya zaku yi ba tunda yana son ki sosai. Da farko shi aure bautar ubangiji ne, ita kuma bauta ita ce abinda ake yi dan a samu shiga aljanna, ita ce kuma abinda idan an ƙi yi sai a halaka a fada wuta Allah ya kiyaye, wannan kadai ya nuna miki darajar abinda kika yi, aure. Aure sunna ne, amma abinda ake yi a cikinsa farilla ne, dole ne ki bi mijinki Ruqayyah indai kina son lahirar ki tayi kyau, dole ki sauke wannan bakar zuciyar taki da wannan saurin fushin naki kiyi masa biyayya Hassana idan ba haka ba ina tausaya miki, ina tausayawa duniyar ki da lahirar ki baki daya" 


Baba ya jima yana ta yiwa Ruqayyah fada, fadan daya saka Sumayya kuka amma ba Ruqayyah ba. Bayan ya gama yayi mata adduoi na fatan zaman lafiya a gidan mijinta sannan yayi musu sallama ya fita. 


Bayan ya fita ne Inna da yanuwanta da suka zo daga zamfara suka dora da nasu, suka yi mata doguwar nasiha akan zaman aure da kuma hanyoyin da za'a kyautatawa miji ta hanyar magana mai dadi, godiya, ladabi da biyayya, nuna soyayya da kulawa "ki mayar da duk abinda ya shafe shi ya zama top priority dinki, yan uwansa su zama naki, shimfidar ki ta zama abinda kullum yake muradin komawa ga, abincin ki ya zamanto shi kadai yake iya ci yaji dadi, wadannan sune manyan abinda namiji yake bukata. In dai har kin rike wadannan to kuwa ba kya bukatar boka ko Malam akan mijinki. Zaki juya kayan ki yadda kika ga dama musamman idan yana sonki" Daga nan kuma sai suka dauko nata tsarabar da suka taho mata da ita suka fara bata, dake dake ne da kulle kulle iri iri, wasu a leda wasu a robobi da kwalabe ko wanne an rubuta yadda za'a yi amfani dashi. Gwoggo Habibah tace "bamu baki su bane ba saboda bamu san kalar halittar ki ba kema kuma baki san ta mijin ki ba, dan haka sai kinje gidan kin kwana biyu kin fara gane yadda abin yake sannan zan kira ki in kara miki bayanin abinda kike bukata da kuma yadda zaki yi amfani da shi sosai. Ko wacce mace da irin halittar ta haka suma mazan, in akaje akayi ta bawa yarinya abubuwan da suka fi karfinta sai azo a zamu matsala kuma. "


Bayan sun gama nasu sannan sauran yanuwa kowa yazo ya dora da nasa, hakuri, biyayya, girmama wa, soyayya, su akayi ta maimaita wa Ruqayyah har sai data ji ta haddace kalaman tsaf a kwakwalwar ta. Abinda Ya rage mata shine yin amfani na kalmomin.


Bayan magrib akazo daukan amarya. Aunty ce da kanta tare da hajiyan Kano, kanwar baban su Hassan su suka jagoranci sauran mata zuwa dauko Ruqayyah, Ruqayyah har tayi wankan ta ta shirya cikin wata green atamfa mai adon pink wadda tayi matukar karbar ta, dinkin yayi kyau sosai a jikin ta, sai a lokacin taga Sumayya tana kuka sannan nata jikin ya fara sanyi, sannan ta fara tunanin zata yi missing Sumayya da sauran yan gidansu, sai kuma tayi saurin kawar da maganar ta hanyar gayawa kanta cewa ai zata ke yawan zuwa tana ganinsu, suma kuma haka musamman in suka je gidan nata suka ga daular da taje ciki. Kuma zata saka Hassan yazo ya roki Baba ya bar Sumayya ta koma can da zama.


Sai a lokacin taga ana fito kayan gararta, ita bata san ma cewa anyi mata garar ba kuma bata da idea a inda Baba ya samo kudin yin garar. Ta daiji Aunty tana cewa "haba malama Sa'adatu, dan me zaku takura kanku kuce lallai sai kunyi gara? Ai da kun barta kawai" Inna Ade tace "aa auntyn yara, ai babu wani takura kai wallahi, kayan dakin ma dan dai an saka lokacin ne gajere Amma da babansu duk zaiyi dai dai iyawarsa".


Bayan anyi duk abubuwan da akeyi na al'ada cikin barkwanci da wasa da dariya tsakanin bangarorin biyu sai aka bayar da Ruqayyah Aunty ta rungumo ta ta fito da ita ta saka ta a motar da tazo a cikinta ita da hajiyan kano da gwoggo Habibah sauran motocin da suka zo daukan yan uwan amarya suka mara musu baya. 


Sumayya ta tambayi inna ta hada yan kayanta a karamar jaka, tana so zata raka Ruqayyah kano, so take sai an gama bikin gaba-daya sannan zata dawo gida. Tun da ta fito kofar gidan ta samu gefe daya ta tsaya hannunta rike da jakarta tana ta sharar hawayen ta tana bin mutanen da suke ta turereniyar shiga motoci da kallo, sai kuma taji tana jin haushin kanta na damuwar da tayi, ita me auren ma ko a jikinta dan ko digon kwalla bata gani a idanuwan ta ba amma ita har nata idanuwan sun kumbura saboda kuka.


Tana tsaye taji mutum a kusa da ita, ta gefen idonta ta gane namiji ne dan haka ta yi saurin juyowa side dinsa a tsorace, ya jefe ta da best smile dinsa, ta ji half of damuwarta ta tafi amma sai ta kara bata rai "har da kai aka zo za'a dauke min yar uwa ta ko Adam?" Yayi dariya "mu menene laifin mu? Gidan miji fa zamu kaita, at least ai yanzu zata daina runton kudin mota" Sumayya ta harare shi "be careful, matar ogan ka ce dai yanzu, or else you get fired" ya saka hannu ya kama bakinsa ya ce nayi shiru, ba zan kara cewa komai ba" Sumayya ta nuna shi tace "you better, kasan Hassan baya wasa da yara" yace "yeah, ba sai kin tuna min ba na sani, Hussain ne mai wasa da dariya, dadinta kuma shi na ke yiwa aiki ba Hassan ba" tace "amma Hassan din ne ya dauke ka aikin kuma he can fire you" yace "to mai mijin sister, naji, can we go now" yayi kasa kasa da murya yace "daga ni sai ke, na boye motar da nazo da ita" ya kashe mata ido.


Yayi gaba, da kamar ba zata bishi ba sai kuma ta juya tana waige waige sai data tabbatar babu wanda hankalin sa yake kanta sannan ta bishi inda taga yayi, tana zuwa ya zagayo ya bude mata kofar front seat ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga gurin driver ya tayar da motar. Sai kuma ta juyo tana kallonsa da budaddun idanunta tace "gidan amaryar zaka kaini ai ko?" Bai kalle ta ba yace "yeah, sure" ta kuma cewa "ba wani gurin zaka kaini ba ko?" Ya juyo yana kallonta da guntun murmushi a bakinsa yace "babu inda zan kaiki, daga nan straight zuwa gidan oga Hassan" tace "ka rantse" yace "I cross my heart and hope to die" ta bata rai tace "da Allah ai nace ka rantse" seriously yace "na rantse da Allah ba sace ki zanyi ba. Can we go now?" 


Dogon convoy aka hada ana ta sharara gudu akan titinan garin Kaduna, manyan mata suna ta rangada guda yayinda samari da yammata kuma suke kara volume din kida suna rausaya a cikin motoci, amarya kuwa motarta na tsakiya tana jinta kamar a cikin gajimare take tafiya ba wai a cikin mota ba. Ta lullube fuskarta da mayafinta amma da yake ba mai duhu bane ba tana hango gabanta, a haka har suka isa low cost, har suka shiga jerin gidajen da a cikin films da kuma social media ne kawai take ganin irin su. Ta bude ido sosai zuciyarta tana bugawa da karfi tana son ganin wanne ne nata a ciki, a haka taga anzo kofar gidan tun daga wajensa zata iya cewa kaf jerin gidajen babu wanda ya kaishi kyau da tsari. Aka bude gate, mutane da yawa a ciki mata suna ta guda, wannan ya tabbatar mata da cewa wannan shine gidan nata, sai da motar taje gaban gidan sannan ta lura gidajen guda biyu ne a jere amma ko kusa basu yi kama da junan su ba, na farkon yayi ukun na biyun, tayi murmushi a ranta, maybe na biyun na Hussain ne, ko daga nan wannan so call gimbiyar zata gane tayi mata zarra. 


Amma sai me, sai taga an wuce katon an tafi ga an karamin, sai a lokacin ta lura cewa kofofin katon a rufe suke fitulun sa a kashe karamin kum komai a bude yake tana iya hango mutane a ciki ma. Ta juya side din Aunty, zuciyarta tan agaya mata t tunawa Aunty cewa anyi mistake ba nan ne gidan Hassan ba nan gidan Hussain ne. Amma sai taji aunty tana cewa "alhamdulillah Ruqayyah Allah y kawo ki gidan ki lafiya, sai kiyi masa godiya sannan ki fito da kafar dama tare da bismillah" sai wata zuciyar ta gaya mata to ko nan part din Aunty da yara ne aka kawo ta ayi mata fada sannan a kaita part dinta? Yes, that must be it.


Ta fito da bismillah kamar yadda Aunty tace, sannan Hajiyan Kano ta kama hannayenta tana tafiya da ita yan uwanta ta suka rako ta suna take musu baya. A palo ne taga hoton su ita da Hassan wanda suka dauka last week yace enlargement za'a yi musu a kafe musu a palon su. Kafafuwanta taji sun kasa daukan ta, jikinta yayi sanyi kwakwalwar ta tana neman toshewa. Ta tafi kamar zata fadi, Aunty tayi saurin riketa "subhanallah. Ruqayyah lafiya? Sai ta taba wuyanta, wuyan da lokaci daya da dauki mugun zafi ta ce "ya salam, jikinta zafi, dama bata jin dadi?" Goggo Habibah yayar Inna Ade tace "anya kuwa, kamar lafiyar ta kalau" Ruqayyah ta fara kuka a hankali irin wanda sheshsheka ce kawai take fitowa, tana jin tamkar duniya ce gabaki daya take ruguzo mata aka, tana jin kamar duk mafarkanta suna tarwatsewa a gaban idonta. Zuciyarta tana rada mata wata magana, wata mummunar magana. 


Hussain shine CEO na H and H ba Hassan ba.


And that explains alot of things. Tayi saurin tana girgiza kanta kamar mai fada fa zuciyar tata. No, no, no. Ta ringa maimaitawa 


 She felt her dreams shattering. Ta sake girgiza kanta trying to comport herself, wani barin na zuciyarta yana gaya mata "ba haka bane ba, kinsan Hassan da makale aljihu, shine zai zabi gina karamin gida ba wai dan ba shine mai Company ba" sai daya barin yace "kuma sai yabar kaninsa ya gina babban gidan da ya fi nashi?" Nan take sautin kukanta ya karu


Kuka take yi kamar ranta zai fita, Hassan ya yaudareta yaci amanar ta, yayi mata karya dan ya aureta. Zuciyarta zafi take mata, zuciyarta ciwo take yi mata, anya kuwa ba ciwon zuciya ne zai kama ta ba?


Tana jin maganganun mutane a kusa da ita, yawancin su hakuri suke bata, sama sama kuma tana jin dariyar wasu. Sai ta fahimci sun dauka kukan barin gida take yi. "Kaji yarinyar nan, har muna yabonta muna cewa yarinya karama amma bata yi kuka ba ashe kukan zuci take yi sai yanzu zata yi na fili" "kiyi hakuri Ruqayyah, muma duk da haka muka sossoma wai kuturu yaga mai kyasbi" suka kwashe da dariya wasu daga ciki suka yi guda, "ni sanda za'a kaini gidan nawa mijin ma guduwa nayi, sai da akayi ta nema na aka rasa har aka hakura sannan na dawo, ina dawowa kuwa aka kama ni aka kaini" aka sake wata dariyar.


Ruqayyah taji tamkar ta samu bindiga Ak47 duk ta bi su da bullet goma goma. Dan dai tasan sun fi ta karfi ne da babu Abinda zai hana ta tashi ta rufe duk mutanen gurin da duka. But bata son ta bata rawar ta da tsalle, zargi ne ai kawai take yi, bata tabbatar ba lokacin taji muryar Nafisa a kusa da ita, "kiyi hakuri kiyi shiru kinji yayata kar kanki yazo yana yi miki ciwo, kinga duk su Aunty tsokanar ki suke yi" sai itama tayi dariyar sannan kuma ta juya tana waigen neman Sumayya tace "ina Sumayya? Wata kila ita zata iya rarrashinta"


"Kaga Adam kazo ka mayar dani inda ka dauko ni ko kuma ka kaini inda zaka kaini, ka daina yawo dani a titi" yace "sai kinyi dariya tukunna. Haka kawai dan Ruqayyah tayi aure sai ki zauna kiyi ta kuka har idonki yayi wannan kumburin? Kinga fuskarki kuwa?" ta kuma hade rai "ni bana cikin mood din dariya, dan Allah ka rabu dani" yace "in rabu dake fa kika ce? Kamar fa kina nufin in rabu da wani sashe na jikina in daina amfani dashi kenan fa? Kina ganin haka zai yiwu?" Ta kara hade rai "kaga fa za'a neme ni a can, in aka fahimci yawo na tafi kuma za'a yi min fada. Dan Allah ka kaini, ni jikina bani yake yi kamar Ruqayyah tana nema na" yace "Ruqayyah da aka kai dakin miji, maybe ma suna can suna zuba soyayya ita da mijin ta ke kina nan kin hana ni ganin hakorinki" tace " koma dai me take yi ni ka kaini in ganta, dan Allah" yace "sai kin yi dariya" ta sake hade rai yace "Please, pretty please!" Ta dauke kanta gefe daya sai ya saki stirring ya hade hannayensa alamar roko "Please Please Please" da sauri tace "Adam zaka yar da mu fa?" Yace "kiyi dariya to" ba shiri ta yangare baki daga gani kasan dariyar karya ce, ya kama stirring yana dariya yace "bara dai in kaiki, ba dan halinki ba" sannan ya juya kan motar zuwa gidan su Hussain.


Suna shiga idanunta suka sauka a kan gidan Hussain, ta saki baki tana kallo sai taga kuma gidan Hassan, sannan sai taga sunyi packing a kofar Hassan, ta juya tana kallon gidan Hussain sai kuma ta sake dawowa ta kalli gidan Hassan, tagan shi a bude mutane suna ta hada hada, daga ciki ta jiyo an rangada guda. 


Gabanta ya fadi, ta juyo da budaddun idanuwa tana kallon Adam fuskarta da alamun tambaya. Yace "can gidan oga Hussain ne, he Calls himself "dangoten Kaduna" . Nan shine gidan Ruqayyah, gidan oga Hassan kenan. Nan zaki shiga". Sumayya bata jira sauran wani karin bayani ba ta bude kofar mota ta fita da sauri, ko rufewa bata tsaya tayi ba, yace "hey, babu thank you balle goodnight? Kin bar jakarki a ciki" bata ko kalle shi ba ta shige gidan da sauri.


Tun a bakin kofa ta jiyo gunjin kulan Ruqayyah, gabanta ya fadi. Innalillahi, wannan wanne irin rashin ta ido Ruqayyah take nuna wa? Ba tare da tunanin komai ba ta ratsa mutanen da suke palon har zuwa gaban Ruqayyah da har yanzu take durkushe a kasa tana ta risgar kuka da iyakacin karfin ta. Nafisa tace "alhamdulillah, ga Sumayyan nan ma, zo ki yi mata magana ko zata yi shiru" Sumayya ta durkusa a gaban Ruqayyah sannan ta tallafi fuskarta a hannayenta tana jin yadda fatarta tayi zafi, ba tare data ce mata komai ba sai ta kama ta ta mikar da ita tsaye ta rungume ta a jikinta ta fara tafiya tace "ina za'a kaita?" Nan take aka yi mata jagora zuwa Bedroom din Ruqayyah da yake sama. Ta zaunar da ita a bakin gado kamar yadda ake zaunar da ko wacce amarya sannan ta goge mata hawayen fuskarta ta ja mayafi ta rufe mata fuskarta ta kuma zauna a kusa da ita ta rike hannun ta a cikin nata, a hankali Ruqayyah tace "Sumayya, Hassan ya yaudare ni" Sumayya tayi shiru bata bata amsa ba saboda mutane da suka fara shigowa, suna ta tsokanar Ruqayyah da sunan amarya mai kuka, yan uwansu da suka kawo ta suka yi mata sallama abokan wasa suna tsokanar ta, kusan kuma duk wanda yazo yi mata sallama sai ya yabi gidanta "Ruqayyah ki godewa Allah, kinga kyawun gidan ki kuwa? Masha Allah. Wannan miji naki ba karamin sonki yake ba, ki rike kayan ki hannu bibbiyu Allah kuma ya baku zaman lafiya" Sumayya ce mai amsawa da ameen.


Sai da aka ragu saura kawayensu da suke palon kasa suna ta dauke dauken hotuna dan a samu na burga sannan Sumayya ta rufe kofar dakin ta dawo kusa da Ruqayyah ta zauna tace "Ruqayyah me nene hakan kika so ki aikata? Wannan wanne irin abin kunya kika so ki jawo wa kanki ki jawo mana?" Ruqayyah ta bude fuskarta data kumbura cikin dasashshiyar murya tace "abin kunya? Abin kunya kike magana akai? Shin baki kalli gidan can ba? Kin tambayi kanki gidan waye kuwa?" Sumayya tace "ba kaina na tambaya ba, mai motar daya kawo ni na tambaya kuma ya gaya min cewa gidan Hussain ne and so what? Me yasa za ki juya ki kalli gidan Hussain bayan ga gidan Hassan kina cikin sa? Me yasa ba zaki kalli abinda yake hannun kin a matsayin mallakin ki ba sai kike juyawa kina kallon abin hannun wani? Ba ki ji abinda yanuwan mu suke fada ba? Cewa badu taba ganin gidan da yake da kyawun naki ba? Ni ma kuma haka, ban taba shiga gida mai kyan wannan ba, ban taba zama a kan gadon mai kyan wannan ba. Which of the favors of your God do you deny?" 


Ruqayyah tace "amma ba kya ganin kasancewar gidan Hussain yafi na Hassan yana nufin ba Hassan ne mai Company ba?" Sumayya tace "and so what? Hassan kika aura ko kuma Company kika aura? Ni I don't get you Ruqayyah. Na kasa gane kanki. Me kike so ne? Hassan mutum ne mai nagarta da kamala da sanin ya kamata, mai addini mai asali mai kyawun sura, mai lafiya mai aikin yi da rufin asiri, no ba rufin asiri ba, mai arziki. What more do you want" Ruqayyah ta mike kamar an mintsine ta tace cikin daga murya "but he made me believe cewa Companyn sa ne. He made a fool of me" Sumayya tayi saurin yi mata alama da tayi shiru, ta na leqa window sannan tace "yaushe? Ban sani ba ko kunyi maganar sanda bana tare daku amma ni ban taba jin ya jingina kansa da H and H ba, ni ban ma taba jin ya ambaci sunan kamfanin ba" Ruqayyah ta dafe kanta tan zama a bakin gado tare da cigaba da kuka tana jin kanta kamar zai tsage, Sumayya ta dawo ta zauna kusa da ita tace "kin taba zama kinyi tunanin ma'anar H and H?" Ruqayyah ta juyo tana kallonta amma bata ce komai ba, ita bata taba tunanin me yake nufi ba. Sumayya tace "ni ma ban sani ba, but ina tunanin Hassan da Hussain yake nufi" Ruqayyah tayi saurin cewa "meaning nasu ne su biyu right?" Sumayya tace "maybe, maybe not, but you will soon find out tunda kin auri daya daga cikin su. Am sure zai gaya miki koma na waye a cikin su. But Please Ruqayyah ki kwantar da hankalin ki, dan Allah kar ki nuna masa cewa hakan wani abu ne" 


Ruqayyah ta rike hannunta tana hawaye "dan Allah Sumayya ki kwana anan. Ni goben nan tsoron zuwa Kanon nan nake ji, ban san me zan gani ba acan. Dan Allah ki zo muje tare" Sumayya ta goge mata hawayenta tace "tare zamu tafi, na taho da kayana ma jakata can a mota, tare zamu tafi ba zan tafi in barki ba. We are going to get through this together" ta samu ta lallabata ta kwanta sannan ta fita neman Adam ta karbi jakarta. Sai kuma ta sanarwa da kawayensu na kasa cewa Ruqayyah bata jin dadi ta kwanta bacci. Amma sai suka bita da tambayar "nan ne gidan Ruqayyah? Can kuma gidan waye? Ko gidan dan'uwan mijinta ne da ake bikin su tare? Waye mai Companyn ne wai a cikin su? Ruqayyah tace mana mijinta ne CEO haka ne?" 


Da sauri Sumayya tayi excusing kanta tace bako ne da ita a waje ta fita, a ranta tana tunanin tabbas baki shine yake yanka wuya, Ruqayyah ta saka igiya ta daure wuyanta ta mika wa mutane bakin igiyar.


Bayan saukar Sumayya ne wayar Ruqayyah tayi kara, ta daga kai da kyar tana kallon sunan Hassan a jikin screen din "mijina" kamar yadda tayi saving. Tayi tsaki tana jin wutar data kwanta a kirjinta tana dada ruruwa. "Munafiki" ta fada a fili sannan ta kife wayar ta juya bayanta. Can kuma sai ta juyi ta daga wayar ta saka a kunnen ta "hello" ta fada da murya mai sanyi. "Hassana" ya fada da murya mai cike da conceri. "Yanzu Aunty ta kira ni tace kina ta kuka wai ko zan zo in rarrashe ki. Me ya faru? Waye ya taba min ke inzo in nuna masa matsayin sa?" Ruqayyah tayi shiru, a ranta tace "kamar gaske" yace "Please kiyi min magana mana inji dadi, in baki magana ba yanzu zan ajiye duk abinda nake yi in taho" a hankali tace "kana ina?" Yayi murmushi yace "gidan yafi karfin mu, baki sunyi yawa shine muka kama hotel mu da friends din mu. Kin gansu ma duk suna ta tsokana ta wai na kasa rufe baki saboda an kawo min amarya ta" bata ce komai ba saboda bata jin zata iya gaya masa magana mai dadi, dan haka shirun yafi. Yace "ba zaki gaya min abinda ya saka ki kuka ba? Ko sai nazo na gani da idona? Inji kuma da kunne na?" 


Ta gyara kwanciyar ta tan jin cewa bata son ganinsa kwata kwata, at least not today, tace "na dauka a can zakuyi zamanku? Tunda nan din akwai mutane da zasu kwana saboda tafiyar da za'ayi kano gobe ko?" Ta shafa kansa yana runtse idonsa yace "yeah, right. Haka ne. But what about siyan baki and other traditional stuff?" Tace "it can wait ai......jibi in akayi dinner din kowa kaga zai watse ai, sai ku zo kuyi ta siyan bakin ku" yace "hakane......but ni kuma fa? Shikenan ba zanga matata ba? Ni fa yanzu ba gwauro bane ba fa" tace "ko? You will see me tomorrow ai in ka shigo da wuri kafin mu tafi" yace "ni ba wannan ganin nake nufi ba ai....." Tayi shiru, yace "ko abinda kike wa kuka kenan dazu?" Tace "good night" yayi ajjiyar zuciya yace "to ya zanyi da raina, ba haka dai aka so ba" tace "kanin miji ya fi miji kyau ba".


Post a Comment

0 Comments