TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Tsantsar so page 2

 *Ep_Two.*

So



"Ke! Ke! Mamana menene kika dawo yi anan gidan ko har kin gama aikin naki ne wai ma bakiji irin kalamin da nayi Miki kafin ki tafi ba ne da zaki dawo mana gida Yanzu da safiyar nan?."




Shiru tayi tana daga tsaye tsakiyar gidan nasu da ko arzikin siminti na ƙasa babu hatta ga jikin bangon gidan yaɓe ne na jar ƙasa, ban da kyaf kyafta ido babu abin da take yi tare da turo baki ba tare da ta ce komai ba, tana ji ya cika gaba da sababin, idan da sabo ta saba da irin halin Mahaifin nata na shegen son abin Duniya.


Sai da ya gama surfa ma ta tsiya son ransa tana tsayen yayin da Mahaifiyarta ke daga gefe ta zuba ugan tagumi ba ta ce komai ba, domin tasan tana furta wani abun kanta zai dawo. Har sai da ya gaji dan kansa sannan ya yi shiru, sai kuma cikin sassauta Murya ya fara faɗin.




"Mamana kin gama aikin naki ne a gidan Sarkin da kika dawo da wuri haka?."



"E, Baba na gama ne shiyasa na dawo kuma wannan Baturiyar da a ka ce tazo daga America ta ce zan rakata domin ta zagaye Garin nan. Yauwa Sunan ta ma Samira.. e haka ne amma sunan guda uku a haɗe ko kuma mai daɗi na manta sauran."



"Yauwa Ɗiyar albarka yanzu abin da nakeso dake shi ne ki ci gaba da maƙale ma ta ko'ina zata je cikin garin nan kuna tare kinji Mamana?."



Ya ƙari sa maganar cikin sakin Dariya haƙoransa da suka dafe tsaban cin goro suka bayyana.




Da mamaki ta ce.



"Saboda me ke nan Baba me yasa zan maƙale ma ta ɗin ko'ina muna tare?."



"Kajimin mara yawon Yarinya mana, yo idan kina maƙale ma ta ko'ina kuma kina yawan bata labarin mu da irin talauci da muke fama da shi kika sani ko sanadin haka ta tausayamin ko Hakimi a bani. Ke Yarinya ce ba zaki gane komai ba koda nayi miki bayani"




Fashewa Teema tayi da dariya har da buga ƙafa jin ta inda ya ɓullo wato Hakimi cabb.



"Tohm Babu in sha Allah zan yi iyakar ƙoƙarina kan hakan."



Ta faɗa tana saita kanta ganin wani mugun kallo da yake bin ta da shi.



Cikin zuciyarta kuwa faɗi take.


"Chabbb lallai ma wannan Baban yo Ina ga ko Dogare ma ba za'a baka ba balle kuma Hakimi."




"Yauwa 'yar albarka wannan ita ce mai Sunan Mamana in miki na turawa suka ce that's my daughter."😅

Ya faɗa cikin washe baki Ganin bakinta na motsi ne ya ce.


"Mene ne abin da kike cewa."



Da sauri ta ce.



"A'a Baba cewa nayi Allah ya taimaka daga Hakimi ka zama har Sarkin garin nan ma."



"Ja'ira Kawai."



Ya furta yana sa kai ya fice daga gidan.



"Mama kinji wannan mijin naki wai Hakimi Lallai ma."



"Fateema ke nan ki dena biye masa ma fa."



"HHhH Mama ai kawai kallon sa nake. Amma ya jikin naki?."


Ta tambaye ta cike da kulawa.








___________________________________________



*CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT.*




Tana tsaye daga harabar airport ɗin daura da wurin da a kayi da rubutu jikin allo mai launin ruwan ɗaurawa da manyan baƙi NEW ARRIVALS.


Hannu takai tare da cire Glasses dake idanunta tana kare fuskarta daga hasken Rana. Sannan ta ƙari sa wurin iyayen ta da suke tsaye kowannen su fuskarsa ɗauke da farin ciki na kammala karatun ta da dawowarta garesu. A tare tayi hugging nasu cike da farin ciki take faɗin yadda tayi missing nasu.


"Baby Ambrah Yarinyata kin kammala karatun ki cikin Nasara gashi kin dawo gare mu sosai nayi farin ciki da kasancewar hakan."



Murmushi tayi kaɗan tana faɗin.



"Abhie na! finally am back and nayi kewarku sosai sai dai bai kai rabin yadda nayi kewar Bro Taufan nawa ba, idanuna babu abin da suke da muradin gani a halin yanzu fa ce su yi karo da kyakyawar fuskarsa, sai naji gaba ɗaya na ƙosa mu tafi gida na huta sannan na shirye na wuce kai tsaye zuwa gidan General Tajudeen Ozan domin nayi arba da sahibina."




"Yanzu dai ba wannan ba tukunna finally you are back saboda haka mu shiga Mota Domin zuwa gida koma menene ya biyo baya."



"Okay, Oum na."



Ambrah ta faɗa sannan gaba ɗaya suka shishshiga cikin motocin nasu suka bar Airport ɗin tare da Guards kai tsaye har suka ƙari sa zuwa gidan katafaren gidan  Prof... Yusuf El_ Mustapha ke nan shararren mai dukiya na ƙin ƙarawa kaf Yankin Egypt da kewaye kuma tsohon professor ne a Babban University dake Cairo. Matarsa ɗaya tal wato Dr Aadnah Taj Ozan sun kasance yarinyar su ɗaya tilo Ubangiji ya azurtasu da ita wato Ambrah Yusuf El_ Mustapha shekarunta Ashirin da ɗaya ta kammala karatun ta a ƙasar Jamus ɓangaren tattalin arziƙi. 

Prof... Yusuf El_ Mustapha da Matarsa Dr Aadnah Taj Ozan sun kasance suna masifar son wannan tilon Ɗiyar tasu Ambrah kyakyawar Balarabiyar Budurwa mai ji ƙuruciya ga kyau ga kuma Dukiya suna son ta fiye da komai na Rayuwa domin ita ce ma Rayuwar tasu Yayin da gaba ɗaya tunanin Ambrah da Soyayyarta ta ɗaura a kan Taufan jika wurin General Tajudeen Ozan sannan kuma Mahaifinsa Ali Taj Ozan Yaya ne a wurin Mahaifiyar ita Ambrah ɗin. Ambrah tana matuƙar son Taufan fiye da komai domin har karatun ma da kyar ta tafi wata ƙasar ta zauna ba tare da tana a kusa da shi ba. Finally gata ta dawo kuma Brother Taufan nata  har yanzu yana ran ta. Bata da wani Buri sai ganin kyakyawar fuskarsa da shi kansa.

Domin




"Wai kuwa baka ganin akwai ƙura a ƙasa Ambrah ta dawo gashi Taufan baya ƙasar ma gaba ɗaya ni tsoro ma nake a kan abin da zai iya biyo baya."




Ajiyar zuciya ya sauke jin maganar ta sannan ya kamota ta zauna kusa da shi gefan Bed ɗin. Tabbas gaskiya ta faɗa akwai ƙura idan Ambrah ta fahimci Taufan fa baya nan.



"Nasan da duka waɗan nan sai dai ina ga kin manta wata ɗaya kacal ya rage Shekara ta cika da hakan yake nuni da Taufan ya kusa dawowa ke nan."



Da sauri ta kallesa fuskarta na wadatuwa da ƙayataccen Murmushi sam ta manta ma sai yanzu da ya faɗa.



"Kin ga yanzu sai mu san yadda zamuyi da Ambrah har nan da one Month before Taufan ya dawo musha shagali biki irin wanda ba'a taɓa yi a Cairo ba kuma ba za'a taɓa kalansa ba."




Shiru tayi Murmushin dake fuskarta bai ɗauke ba sai dai tana nazarin wannan lamarin ba tajin koda Taufan ya dawo zai amince da Ambrah matsayin Future wife tasa domin tsayin lokacin nan a matsayin Ƙanwar sa Kawai yake kallon ta ba da wani matsayin da ya wuce wannan ba.



General Tajudeen Ozan ya kasance tsohon soja ne kuma haifaffen ƙasar Egypt Mazaunin Cairo yana da mata ɗaya Dr Shazam Taj Ozan. Yaransu Biyu a Duniya Ali Taj Ozan shi ne Babba yana da yara Biyu Taufan sai kuma Arissa da suke kira Cutie. Matarsa mai suna Aamalah ta rasu shekara ɗaya baya sanadin ciwon Cancer matakin ƙarshe. Sai kuma Dr Aadnah Taj Ozan da ta biyo Mahaifiyarsu ita kuma 'Ya ɗaya tilo gare ta wato Ambrah. Tun lokacin da Aamalah Matar Ali Taj Ozan ta rasu ya bar Cairo ya koma New York da zama yayin da Yaran sa biyu ƙaddara tayi silar rabuwa tsakanin su, sun yi nesa da shi domin cika wasiyyar da mahaifiyar su Aamalah ta bari.




*WANNAN KE NAN...*



____________

*JOS NIGERIA.*



Cikin wani madaidaicin gida na masu rufin Asiri ginin bulon siminti da ya sha fenti ciki da waje ƙaramar ƙofar gate ne da Gidan sannan ɗakuna huɗu ne cikin Gidan sai kuma ban ɗaki dake gefe sannan sai ɗakin girki sai ɗakin a je tarkace sannan sai rijiya dake can gefe cikin Gidan.





Hajiya Sumayya Dattijuwar mace mai kimanin shekaru sittin da ɗauriya tana daga zaune saman tabarma yayin da Mijinta Alhaji Muhammad Ali da aka fi sani da Nakowa yake daga kwance saman tabarman a gefanta ya lumshe ido yana tunanin Rayuwa. Radio dake rataye saman wani dogon katako tana faman aiki yayin da gaba ɗaya hankalin Hajiya Sumayya yake a kan Radio ɗin tana sauraren shirin Duniya Tumbin Giwa.



"Assalamu Alaikum."



Suka yi sallama a tare lokacin da suke shiga gidan sannan suka ƙari sa wurin kakannin nasu. Fuska ɗauke da murmushi bayan sun amsa musu sallama Arissa ta ce.



"Heyyy Kakus ana ta fama ke nan da Radio kin bar ɗan tsohon mijinki da tunani an ya kuwa kina kula mana da Grandfa yadda ya kamata na fara zargin wani abu fa."🙃



"E, a haka ɗin yake maƙale dani ni ɗaya babu ƙari ki gama sa idon ki mijina yafi ƙarfin ki da jar fatar ki a wurin."



Dariya Arissa tayi yayin da take ƙoƙarin shiga wani madaidaicin ɗaki ta ce.


"Kakus ke nan bani na kar zomon ba ai menene ma zan yi da wannan tsohon kedai da kikaga zaki iya sai a ɗaura niyya. My Yaya T.A ko ya kace?."


Tayi maganar tana mayar da kallon ta kan Yayan nata kuma farin cikin ta.



"A'a ai kun fi kusa babu mai shiga tsakanin ku domin ko an shiga ma kunya za'a kwasa."


Ya yi maganar cikin sassanyar Muryarsa mai daɗin saurare kuma a taƙaice, kyakyawar fuskarsa ɗauke da Murmushi kaɗan da bai bayyana haƙoran sa ba. 

Dariya tayi sannan ta shige ciki.



"Fatan kun shigo lafiya?."


Hajiya Kakus ta faɗa tana mayar da kallon ta kansa.


"Alhamdulillah."



Ya furta yana gyara zama so yake ya mayar da hankalinsa wurin sauraren Radion duk ba ra'ayin sa ke nan ba amma zama da waɗan nan Dattijawan Biyu ya saka ya fara. Sai dai ganin kamar da magana a bakin kakannin nasa ne yasa shi nutsuwa tare da mayar da gaba ɗaya hankalinsa gare su musamman ma Alhaji Nakowa.




"Lokaci yana ja cikin lokaci ƙanƙani shekara ɗaya tana neman zagayowa da hakan ke nuni da lokaci ya kusa a ƙiyasina bai fi nan da kwanaki ashirin da Takwas ba komai zai faru kuma ya ƙare."




Shiru ya yi domin shi ba mutum ne mai son yawan surutu ko hayaniya ba. Yana sauraren maganganun da suke fitowa daga bakin kakan nasa wato Alhaji Muhammad Nakowa da ya kasance Asalin ɗan Garin Jos ne gaba da baya matar sa ɗaya ita ce Hajiya Sumayya sai 'yar su ɗaya tilo Aamalah da ƙaddara tayi sanadin rabuwar su shekaru masu yawa Baya sanadin karatu da ta tafi ƙasar waje....





__________________________________________


"Anty dama na dawo ne domin na rakaki zagaye Garin kamar yadda kika buƙata."



Teema ta faɗa tana kallon Samira Adila Dina Baturiyar baƙuwar tasu kuma kyakyawar gaske, kwanaki biyu da suka gabata ta shigo Garin ta sauko cikin masarautar Garin Gidan Sarkin Garin wato Muhammad Raees sarki mai adalci ga Al'ummar sa matan sa uku Hajiya Bilkisu ita ce ta farko tana da yara uku Junayd Muhammad Raees mahaifin Hamrarh da Amrarh kuma sanannen Alƙali ne mai gaskiya a Aikin sa matar sa ɗaya Miss Asfiya kyakykywar bafulatana da kyawunta ya zamo silar afkuwar ƙadarori da dama cikin Rayuwar su sanadin haka wani baƙin sirri da babu wanda ya san da shi ya mamaye Ahalin. Dr Salma ita ce ta biyu cikin yaran Hajiya Bilkisu sannan sai Alhaji Nawaz da yake zaune a garin tare da Iyalansa yaran sa maza biyu Ustaad Arkan da kuma Althaf.

Sai matar Sarki ta Biyu Hajiya Safiyya Yaranta Biyu, Canal Nubaid dake zaune a Lagos da iyalansa sai kuma Barrister Aeshah da take Auren wani ɗan kasuwa kuma ɗan kwangila bata taɓa haihuwa ba kuma suna zaune ne a birnin tarayya Abuja. Sannan sai matar Sarki ta uku Hajiya Asiya ɗa ɗaya tilo gare ta sannan ya daɗe da rasuwa shekaru masu ɗan yawa Baya.



Kamar yadda aka saba duk ƙarshen Shekara a gidan mai Martaba Sarki Muhammad Raees gaba ɗaya yaran nasa masu Aure a ƙasashen waje da wasu States ɗin gaba ɗaya kowa yake hallara da iyalan sa a gidan domin gudanar da hutun anan. To haka ma wannan ƙarshen Shekara ta kasance gaba ɗaya Yaran Sarki da Iyalansa sun kasance sun zo daga mabanbantan States da suke kuma tare da iyalan su domin gudanar da hutu anan kamar yadda aka saba sai dai wannan shekarar da ban mamaki lamarin ya kasance sanadin zuwan bazata da Samira Adila Dina ɗiya wurin Sulaiman Mutallab Raees tayi kowa ya yi mamaki da zuwanta duba da Irin abubuwan da suka faruwa a Baya. Sai dai kuma sun yi farin ciki da tazo sai dai ba tare da iyayenta tazo ba. Mahaifiyarta ta kasance Haifaffiyar ƙasar Turkey ce kuma acan suke zaune a halin yanzu. Samira tazo Nigeria ne ba tare da sanin iyayenta ba...



*WANNAN KE NAN KAƊAN DAGA CIKIN LABARIN TSANTSAN SO.!*

*WITH FULL OF...*



```_-_Life with Destiny, Struggle, Inclination, Merciless, suffering, Excruciation, and Negate Pure Love._```




____________________________________________

*Present Day....*




Kallon Teema Samira tayi da kyar ta gane maganar nata domin ba sosai takejin harshen Hausa ba. Tayi ƙoƙari sosai ma da ta iya harshen domin ba'a cikin masu magana da harshen ta taso ba.



"Oh sorry Ina ga zagayen Garin nan zamu barshi sai zuwa Gobe fa domin yau kam ina tare da 'Yan uwana musamman ma Hamrarh da Amrarh."



"Tohm Anty Allah ya kaimu Goben."



Teema ta faɗa tare da ƙoƙarin fita daga katafaren palon domin ji take ta tsargu ganin Irin kyawawan mutanen dake ciki maza da mata duka jikokin mai martaba sai dai bataji duk kyansu duka sun kai kyan wannan Baturiyar wato Samira.



"Ina zakije kuma Teema?."



Juyawa tayi ta kalle da murmushi ta ce.



"Zan koma gida ne domin Mamana tana can tana jirana Allah ya kaimu Goben in sha Allah da wuri zan zo."



Teema ta faɗa silently domin ita ɗin mace ce mara son hayaniya shiyasa ma inkiyarta yake Teema silent.


"Okay Bye ki gaida su Mama."




Samira ta faɗa tana mayar da kallon ta kan 'yan uwan nata da suke cike da Palon bayan Teema amsa sannan ta fita daga Palon sauri sauri.



_______________

*HAZEL POV.*


Dawowarta daga school ke nan a gajiye ta shiga gidan nasu na ginin bulo da ko arziƙin fenti bai samu ba. Granny ta hango zaune daga tsakiyar gidan tana faman Aikin wanke tumatur dake cikin bokiti da alama sun fara lallacewa ne take cire masu kyau daga ciki.

"Granny sannu da aiki."



"Yauwa Sannu kin dawo lafiya."



"Lafiya qalau Father bai dawo daga Church ba ke nan?."

Hazel ta tambaya tana a je littatafan karatun ta saman wani dogon table daga cikin baranda na gidan.



"Bai shigo ba tukunna ina ga ayyuka ne suka riƙe sa."



"Okay, bari na shiga ciki na watsa ruwa sannan na dawo na tayaki."



Hazel ta faɗa tana shiga cikin ɗakin ta, ta sauya kaya sannan ta fito ta ɗiba ruwa a baho ta shiga wanka lokaci ƙanƙani ta gama sannan ta shirya cikin t-shirt mai garejen hannu da wando mai faɗi baƙi na shan iska sannan ta saka hular Bat ta rufe dogon gashin kanta. Fitowa tayi ta kama ma Granny suka ci gaba tsince masu kyau daga cikin tumaturan...




Post a Comment

0 Comments