TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 35-36

 3⃣5⃣----3⃣6⃣








Wata dariya naji har ƙasa na girgiza ashe wannan halittar ne ke busar dariyar, can ya tsagaita kamar ruwa ya ɗauke ya fara magana ji kake kamar ƙasa zata tsage


 


"Karki yarda ayi auran!!! Karki bari ayi auran!!! Idan kuma ba haka ƙarshenki yazo Zulfa'u,yaaazoooo ƙarshenki Zulfa'u!!! "




Da saura ta ɗago kanta tana kallonsa don a gaskiya ita batasan da wani aure ba,to wani aure yake magana akai,kasa haƙuri tayi ta tambayesa cikin girmamawa tare da ƙan-ƙan dakai



"Ya kai Sarkin matsafan duniya, yakai Boka Burumbuɗu wani aure ne zan hana afkuwarsa"(daman sunan wannan halittar Boka Burumbuɗu,tabbb yaci sunnansa kuwa🤔🤔🤔😂😂😂😂)



Dariya ya tsintsire dashi  har ƙasa na girgiza,sai kuma ya fara kuka ko'ina na ɗakin rawa yake can ya tsagaita  tare da cewa 



" Karki bari!!! Karki yarda!!! A hir ɗinki ki bari  ayi auran jikarki da ɗa daga tsatson maƙiyiyarki,domin idan kika bari auran ya tabbatu,hooo hoo hoooo,asirinki na gab da tonuwa!!!



Tsuru-tsuru Haj. Zulfa'u tayi da idanu tana sauraransa,a zuciyarta tana cewa. 'Na shiga uku ni Zulfa'u daga wancan sai wancan,da wanne zanji,da farko ance karna bari muhadu da tsatsonta,yanzu auran da ma bansan da wanzuwansa ba ake cemin karna sake ayi auran,yau naga ta kaina'. Kamar Boka Burumbuɗu yasan mai take ayyanawa aranta ya ce



"Zulfa'u duk abinda muka sanar miki tabbatacce ne in har baki bi umarninmu ba! Kisani munyi iya yinmu domin mu halaka sauran ahalinta ammaa.....!!!



Wani irin gigitaccan kuka ya fashe dashi wanda duk ilahirin ɗakin na girgiza gashi shi kanshi ƙarar kukan babu daɗin ji,kai in taƙaice muku kamar saukan ruwan sama mai ƙarfin gaske haka kukan nasa yake.Yakai tsawan mintuna 10 yana wannan kukan,ita kuma Haj. Zulfa'u abin duniya ya mata katutu a yuwa,kanta a duƙe tana sauraran kukan nasa,sai kuma can ya tsagaita tare da cewa cikin amon muryarsa mai firgitarwa 



" Basa wasa da sallolinsu biyar a duk rana,suna azkar ɗin safe da na yamma,suna nafilfilun dare,sun tsare yaransu da addu'o'i masu ƙarfi,mun kasa Zulfa'u!!! Mun kasa!!! "



Jinjina kai Haj.Zulfa'u tayi saboda abinda Boka Burumbuɗu zaice ya kasa to ba ƙaramin abu bane,tabbas ya zaman mata dole tayi taka tsantsan kar asirinta na shekaru aru aru su bayyana dako kashinta ya bushe,dole ta hana faruwan wannan auran duk da batama san dashi,wannan dole ne ta hana,haka tayi ta ayyana abubuwa a ranta kafin daga bisani Boka Burumbuɗu ya ƙara da cewa



"Zamu barki yanzu! Sai bayan shekara biyu wanda a lokacin zamu linka miki kariyar da muke baki sosai,domin lokacin abubawa zasu fara rincaɓewa,dole mu kareki Zulfa'u! Dole mu kareki domin kina mana biyayya tare da bin umarninmu haɗi da sharudɗanmu! Zamu tafi! Zamu tafi Zulfa'u! Sai bayan shekara biyu! Muna ƙara jajjada miki ki kula! Ki kula Zulfa'u kar iya auran jikarki da ɗa daga tsatson maƙiyiyarki Zulfa'u! Karki bariii!!! Karki bariii!!! Mun tafiii!!! Sai watarannn!!! "



Ɗif kamar walƙiya ya ɓace a lokaci guda hasken ya ɓace sai duhu ya mamaye ɗakin bayi ɗaga,a cikin duhun ne Haj. Zulfa'u ta lallaɓa ta kunna bulb ɗin ɗakin sannan ta harharɗa kayan tsafinta ta sakasu a cikin ƙayataccan akwati ƙarami mai kyawun gaske saita saka akwatin a wani akwati babba shima mai kyau saita maida a ƙarƙashin gadonta.Sannan ta hau tanƙameman gadonta na alfarma ta kwanta,ta kai tsawan awa ɗaya amma ɓarawo bacci yaƙi ziyartatta sai kusan sallar subhi bacci ya ɗauke ta,ba ita ta farka ba sai wuraran 11:23am na safe kasancewar babu sallah a tsarin rayuwarta hasalima tun tana da shekara 35 a duniya tayi sallama da bautar Allah hatta zuwa Hajji tun a wannan lokacin ta daina saidai bautawa aljan tare da zubar da jinin baƙaƙyan karnuka 50 a duk shekara.



Bayan ta farka daga baccin ta nufa hadɗan toilet ɗinta mai shegen kyau tayi wanka haɗi da brush sannan ta fito ta shirya cikin lafiyayyan atamfanta super holland wanda tasha duwatsu a duk ilahirin dokuwar rigan,ga gwalagwalen da ta saka a wuyanta da kunnenta harda awarwarayansu guda shida,flat shoe ne ta saka sannan ta fito daga ɗakinta,kai kai kai ta haɗu iya haɗuwa wallahi idan ka ganta zakayi tunani ƴar shekara 50 ba 78 a duniya ba,domin jikinta kwata-kwata bai nuna alamun tsufa ba ko kuma furfara a gashinta wanda zai nuna tsohuwa ce,tafiya take mai cike da taƙama da izza,zakayi tunanin ƴar sarki ce har ta isa dining room wanda tasan already mai aikinta ta gama shirya mata kayan kalaci a  food warmers,zama tayi a ƙayattaciyan kujerarta wanda babu irinta a wurin,serving kanta tayi duk da kaɗan ta saka abincin kasancewar yau tana cikin damuwa sosai saboda ganawar da tayi da Boka Burumbuɗu, shiyasa yau ta tashi da kalasa a cikinta.Haka taci abincin kaɗan sannan ta koma falo ta zauna haɗi da kunna television, kallon tv kawai take amma babu abinda take fahimta na daga abinda suke cewa,lulawa tayi cikin tunaninta tare da nema ma kanta mafitar yadda auran jikarta da ɗa daga tsatson maƙiyiyarki bazai faru ba.Haka tayita zama a falon ita kaɗai kasancewar daga ita sai mai aikinta ne a gidan sai kuma in yaranta da jikokinta sunzo mata ziyara.



Wurin ƙarfe 3:09pm na rana Haj. Zulfa'u na zaune a falon taji alarm ɗin ƙofa na ƙara alamun ana son shigowa,mai aikinta ne da sauri da fito daga ɗakinta zuwa ƙofar tare da buɗewa,baki ta sake tana kallon baƙin sai kuma ta ce



"Laaa!!! Ƴan ƙasar waje a gidan,oyoyo sannunku da zuwa"



Tayi maganar tare da basu wuri suka shigo ɗakin,Fadila ce da Amminta suka musu zuwan bazata,da gudu Fadila ta shiga falon tare da daka tsalle ta rungume kakarta don tsabar farin ciki.Haj Zulfa'u dake zaune ta lula wani sabon tunanin jin ƴar aikinta ta ce ga baƙin ƙasar waje,wato autarta Hannatu da Fadila kenan, 'wayyo na shiga uku ni Zulfa'u, ya tabbata Boka Burumbuɗu, kenan maganar auran ya kawosu,dole na hana auran nan,dole ne'.   Tana cikin zancen zuciya taji an wani rungumeta,tasan wannan aikin bana kowa bane illa na Fadila,ilai kuwa ita ce.Fadila ce ta ce cikin murna



"Oyoyo Granny wallahi nayi missing ɗinki sosai,ke kuma naga alama bakiyi missing ɗina ba"



Tana maganar cike da shagwaɓa irin na ajebos rainon ƙasar waje,murmushi Haj.Zulfa'u tayi duk da ba a cikin yanayi mai kyau take ba amma dole ta kula da jikarta wacca tafi soyuwa a gareta a duk jikokinta,cewa tayi



"Ni awa naƙi missing ɗin jikata wacca tafi soyuwa a gareni,ai kullum da kewarki nake kwana kuma da ita nake tashi Fadilatuwa tahh! "



Suna cikin hirar ne saiga Ammin Fadila ta iso gunsu da fara'arta,samun kujera one seater tayi ta zauna tana ganin dramar Mamanta da ƴarta,hakan na sata nishaɗi sosai,katse musu hirar tayi ta cewa



"Hajiyarmu mun sameku lafiya? "



"Lafiya lau auta,ya kuke da mijin naki"



" Duk muna lafiya ya ce ma a gaidaku,shima yana nan kan hanya idan ya gama abinda yake, zaizo har nan ku gaisa in shaa Allah "



"Maa shaa Allah, toh Allah ya kawoshi lafiya"



"Ameen ya Allah"



Kallon Fadila Haj. Zulfa'u tayi tana murmushi sannan ta ce



"Kwana biyu da banganki ba sai naga kin ƙaramin girma da kyau"



Murmushi Fadila tayi don Fadila na mugun son a yabi kyaunta,sai ta ce



"Awwwn Granny,shiyasa nake ƙara sonki Muah! Muah! Muah! "



Hannunta ta sumbata har sau uku alamun kiss tare da hura ma Grannyn nata,haba mai Hannatu da Haj.Zulfa'u zasuyi inba dariya ba,don idan da Fadila a wuri ka dinga shan dariya saboda shirmanta yayi yawa.Haj .Zulfa'u ce tace



"Ku tashi ku watsa ruwa nasan kafin kugama angama abinci sai kuci ku huta,da daddare mayi hirar da hujja,babu musu suka tashi don watsa ruwa suji daɗin jikinsu,bayan sun fito sukaci abinci kana kowa ya baje don huta gajiyar jirgi da suka sha.



Da daddare su Fadila da Amminta sukaje ɗakin Haj. Zulfa'u don yin hirar yaushe gamo,sun sameta tana zaune akan sofa a tare da ita kuma coffee ne tana kurɓa,zama suma sukayi a sofar dake kusa da ita,a lokaci guda suna gaisheta amsawa tayi cike da kulawa tare da cigaba da kurɓar coffee ɗinta,a sannan ne Hannatu ta gyara zama don su tattauna akan maƙasudin zuwansu Nigeria.



" Hajiyarmu kin kusa aurar da  jikarki fa"



Murmushi a fuskar Hannatu take sannarwa Hajiyarta,ita kuma a lokacin da kurɓi coffee ɗinta kenan taji ance ta kusa aurar da jikarta wato Fadila dai ta bokanta yamata kashedin karta bari ayi auran,habawa da sauri da zubar da coffee dake a bakinta, ƙirjinta na dukan uku-uku tare da cewa



"Da gaske!!!"



A tunanin Hannatu duk murna ce ta sakata zubar da coffee na bakinta,sai ta ƙara da cewa



"Da gaske Hajiyarmu,a can ƙasar yaron yake karatu,babu laifi yanada tarbiyya don Daddyn Fadila har Nigeria ya aiko aka tambayi halayyarsa tare da asalinsa,ɗan Kebbi ne yaron,gasu da dukiya gida da waje"



Da sauri Haj. Zulfa'u ta dakatar da Hannatu da cewa



"Yaron waye a Kebbin? "



Caraf Fadila ta cafke wacca tunda aka fara maganar bata tsoma bakinta ba sai yanzu ta ce



"Granny Mum ɗinsa jikar Alhaji Kabir Dikko ne sannan Daddynsa sunansa Alhaji Dauda Gali mai Nass.........."



"Dakata Fadila!!! "



Jikin Haj. Zulfa'u na rawa jin tabbass yaron daga ahalin maƙiyiyarta ce batasan sanda ta daka ma Fadila tsawa ba,hankalinta a tashe ta fara magana



"Inaa!!! Inaa!!! Bazaiyu ba auran nan,kunsan halinsu kuwa Auta da zaku kai Fadila gidan,duk da binciken da kukayi ba komai kuka sani akan wannan mugayan ahalin ba sai ni Haj.Zulfa'u"



Tare da nuna kanta,ƙarya ce ta sumbuɗo musu akan ahalin basu da kirki bayan ita ce ma ta rushe musu farin cikinsu,yanzu kuma tana niyyar goga musu baƙin fenti duk don a fasa auran,domin tama kanta alƙawarin bazata taɓa bari ayi auran ba inhar tana araye.Dole ta ɗau mataki don auran ya rushe ko ta halin ƙaƙa.Fadila da tunda Haj Zulfa'u ta daka mata tsare tayi gummm da bakinta bata sake magana ba sai yanzu da taji kakarta na niyyar tasa a fasa auranta da masoyinta,wani malolan baƙin ciki ne ya tsaya ma Fadila a wuya batasan sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tana cewa



"Wallahi yana da kirki ga addini,ina sonsa,karku rabani a masoyina"



A hasale Haj .Zulfa'u ta ce



"Masoyin Ubanki! Nace masoyin Ubanki! Wawuya don ana taimakon rayuwarki karta faɗa ga halaka amma ke baki gani,kaunar da nake miki ne yasa nake faɗa miki illar auran wannan ahalin amma ke gamai masoyi kin fara kuka,waya sani ma ke kika fara cewa kina sonsa"



Kuka Fadila take sosai domin a gaskiya tana ƙaunar Sadam sosai,gashi yanzu taga Amminta ta yarda da maganar kakarta har tana cewa gobe zata kira Daddynta ta sanar masa kawai ya fasa zuwa Nigerian daman saboda maganar auran Fadila ne yasa yakeso yazo wurin danginsa su tattauna amma yanzu kawai ya fasa zuwan Allah ya kawo mata miji na gari.



Haka akaita drama a wannan family a kan batun auran Fadila da Sadam wanda Haj. Zulfa'u ta nace akan Fadila bazata auri Sadam ba saboda ahalinsa ba mutanan arziƙi bane,kowa a family ya yarda da zancen Haj. Zulfa'u har Daddyn Fadila domin shi dama yanada wanda yakeso Fadila ta aura amma taƙi ita sai Sadam, ita ko Fadila  yanzu ne wutar so da ƙaunar Sadam ke ƙara ruruwa a cikin zuciyarta.Anyita bata haƙuri akan ta haƙura da Sadam amma ina.wannan kenan




Bari mu leƙa Birnin Kebbi🙃🙃🙃





             @@@ @@@@@@@





KEBBI




Motoci ne har biyu na alfarma sukaje Airport ɗin AHMADU BELLO INTERNATIONAL AIRPORT  wanda yake a Sokoto state domin ɗaukar Sadam Dauda Gali Mai Nasara,sun isa a international Airport ɗin a daidai lokacin jirginsu Sadam ya sauka,saida akayi tsawan mintuna 30 kafin mutanan cikin jirgin suka fara sauka,VIP section na jirgin ne suka fara sauka,wanda Sadam yake a ciki,mutum daya-biyu- uku na hudun ne wani ƙyakkyawan gaye ya fito daga jirgin yana taku cike da izza da jarumta irin na masata masu jini a jika,taku yake har ya sauko daga jirgin yana riƙe da briefcase baƙa a hannunsa,shi kuma ya saka black suit mai shegen tsada,ga  gemunsa da gashin kansa duk sunsha gyara,daga gani kasan ana kashe musu maƙudan kuɗi,duk inda ya gilma sai an kallesa saboda kyau da kwarjini da Allah ya masa,a can naji wasu yara ƴan biyu lokaci guda suka ce



"Uncle!  Uncle! Uncle! "



Inda yaji ana cewa Uncle ya waiwaya habawa kafin ya gama tantan ce yaran tuni sunyo kansa da gudu suna masa oyoyo oyoyo Uncle,rungumesa sukayi tsabar murna saboda a lokacin da yake gida yana ɗaukar yaron yawan shaƙatawa,shiyasa suke sonsa kuma koda ya tafi karatu,kusan kullun sai sun dami Mom ɗinsu akan yaushe Uncle ɗinsu zaizo ya kaisu shopping.Shima rungumesu yayi sosai tare da shafa kansu,a sannan ne Aunty Sakina da Kamal abokinsa suka zo inda suke da murmushi a fuskarsu sannan kuma a bayansu akwai body gaurd kasancewar yanzu Daddyn Sadam ya ƙara shahara sosai,fuk inda  zaije saida bodygaurd masu kare lafiyar,shiyasa a sanda zasuzo daukar Sadam aka tafi da mota biyu haɗe da body gaurds.



"Ai sai kubari mu ƙarasa gida kuyi mishi oyoyon dakyau "cewar Aunty Sakina tana murmushi



Ɗago kansa yayi yana kallonta tare da mayar mata da martanin murmushi yana cewa



" The great Aunty! Wallahi nayi missing ɗinku sosai,kai duk wanda yabar gida, wallahi gida yabarshi"



Dariya Kamal yayi yana cewa



"Kaga Malam yunwa nakeji tun ɗazu muke jiranku,don haka bar zancen in munje gida kwarasa,don ni ƴar Gusau nakaji wallah"



Daƙuwa Sadam yama Kamal yana murmushi tare da cewa



"To Sarki ƴan yunwa sai mu tafi kafin ka cinyemu ɗayye,nida nasha tafiya banyi ƙorafi ba sai kai"



Dariya dukkaninsu sukayi sai Sadam ya riƙo hannuwan twins bayan yaba Kamal briefcase ɗinsa,haka suka isa Birnin Kebbi kasancewar  jirginsu a Sokoto ya sauka,buɗe musu katafaran gate akayi domin da jiniya suka iso gidan,bayan sun sauka ne sai suka ɗunguma zuwa cikin gidan.



Mom ce da Daddyn Sadam suna zaune suna jiran isowarsu gidan saboda sunyi waya da Sakina ta ce musu suna hanya,bayan sun shiga falon da sallama a bakunansu Mom ta miƙe da sauri haɗi da rungume autanta tana farin ciki,shima ƙara rungumeta yayi yana farin ciki,suna cikin hakane sai Daddyn Sadam ya ce



"Wato kaga Mom ɗinka ka manta dani ko"



Dariya Sadam yayi tare da nufa inda Daddyn sa yake haɗi da rungumesa yana cewa 



"I really miss you Dad,nayi kewarku sosai Dad"



Mom ce da murmushi fuskarta tace 



"Kaje ka watsa ruwa muna jiranka a dining room"



"Ok Mom"



Tafiya yayi ya watsa ruwa ya sako sassauyar jallabiya fara tas ya fito,haka wannan familyn suke jeru suna cin abinci cikin farin ciki da annashuwa wanda ko ba'a faɗa ba saboda dawowan Sadam ne daga UK,bayan cin abinci sai suka ɗunguma zuwa falo,anan suka fasa hirar yaushe gamo,sai wurin Asr kowa ya miƙe don yin sallah,wanda Sakina ta tafi gida da yaranta,shi kuma Kamal sai dare ya wuce gida saboda bayan da sukayi sallar Asr ɗakin Sadam suka wuce,sun ɓata lokaci suna hira wanda sai dare Kamal ya tafi.



Bayan kwana biyu lokacin Sadam ya huta sosai Daddynsa ya kirasa part ɗinsa,a lokacin daya shigo falon ya tarar da Mom ɗinsa tana zaune itama,samun wuri yayi a ƙasa ya zauna tare da musu barkha da dare,cike da kulawa suka amsa masa,Daddyn Sadam ne yayi gyaran murya sannan ya fara magana



"Alhamdulillah ala kulli halin,yau gashi Allah ya nuna mana kammaluwan karatunka Sadam cikin nasara da aminci,muna ƙara gode masa da wannan ni'imar da yayi mana,sannan yau zan danƙa maka companies,plazas haɗi da gidajan mai wa'inda mallakinka ne tun a ranar da aka haifeka,akwai companies guda uku,ɗaya a kaduna wanda ake sarrafa shinkafa,biyu kuma a kano,sannan akwai gidajen Mai guda huɗu,biyu a hanyar Zaria,ɗaya a cikin garin nan sai ɗayan a Zamfara,wanda dukkaninsu suna aiki tare da manya-manyan motocin mai guda shida,sai kuma Plazas guda Uku dukkaninsu suna kaduna,don haka ka jajirce ka maida hankalinka akansu,a da nasu sai kayi Masters kafin zan danƙa maka su amma sai wani tunani yazomin akan gwara ka fara gudanar da kasuwancinsu kafin daga bisani ka koma ƙaro karatun"




Kasa magana Sadam yayi saboda wannan kyautar bazata da ya samu daga Mahaifinsa,tabbas dole ya maida hankalinsa kacokar a kasuwancinsa domin Daddynsa yayi alfahari dashi,cikin murna Sadam ya fara magana



"Dad bansan wasu kalmomi zan saka wurin gode maka  da wannan kyauttukan bazatan da kamin ba,ina godiya sosai, Allah yasaka da alkhairi,ya ƙara buɗi da nisan kwana,tare da lafiya mai amfani,ina godiya sosai da sosai Dad,kuma in shaa Allah zan maida hankalina sosai a kasunwancina,in shaa Allah zakuyi alfahari dani sosai,Mom ki tayani godiya ga Dad"




"Karka damu Auta,ai tuntuni na miƙa godiyarka ga Dad ɗinka"

Kallon mijin nata tayie haɗi ta sakar masa murmushi mai ƙayatarws'a, shima murmusawa yayi sannan ya ce



"Bayan haka,magana ta gaba ita ce maganar auranka,shin akwai wacca kama alƙawari ?"



Duƙar da kansa yayi irin yaji kunyar nan,ya ce



"Eh Dad akwai wata wacca muka haɗu da ita a can UK amma ita a can take da iyayenta,sunanta Fadila Marwan Ɗan galadima,sannan suna da kaka a Abuja,wacca take zuwa hutu wurinta,nasan ƙila Mom kinsanta,sunanta Hajiya Zulfa'u Sani Mai Gad........."




" What!! Hankalinka Sadam!! Jikar  matsafa zaka kawo mana!!! "



Mom ce da wannan maganar jin an kira sunan wacca tayi silar rugujewar farin cikin ahalinsu,wacca tabar musu tabo a zukatansu,wacca har su mutu maza su manta da illar da ta musu ba,inaa Inaa.ƙarawa tayi da cewa




"Ban yarda ka auro jikar matsafa ba gidan nan,tun daga kan Hausawa, fulani,shuwa arab,ethopia,india,saudia da dai sauran ƙasashe kaje ka auro amma ban yarda da auro jikar matsafa ba "




Sadam da tun sanda ta daka mai tsawa,yayi shiru yana sauraron faɗan da take masa,wanda ya daɗe rabon Mom ɗinsa ta sama irin wannan faɗan,in fact idan zai iya recalling to tun yana ƙarami rabonsa da tayi masa faɗa.Buɗe baki Sadam yayi zaiyi magana  Dad ɗinsa ya dakatar dashi da hannu tare da cewa





"Have patient Sadam! yi haƙuri da wannan yarinyar domin ni kaina ban yarda ka aureta ba,sannan kayiwa Mom ɗinka biyyaya ka naimi wata,Allah ya zaɓarma wacca tafita zama alkhairi a gareka"




"Na haƙura da ita Mom,Allah ya bani wacca ta fita"




"Ameen"




 Daddynsa ya amsa,ita kuwa Mom duk da taji daɗin biyayyar da yayi mata,amma tuno a abubuwa da dama da suka faru shekaru aru aru,yasata zubda ƙwalla,murmushi tayi masa haɗi da cewa




"Allah ya maka albarkha Auta,ya haskaka gobanka,ya kareka daga sharrin masu sharri,naji daɗin yi mana biyyaya da kayi,in shaa Allah sai Allah ya baka wacca tafiya komai"



"Allah ya yarda Mom"




Daddy ne ya kallesa sannan ya ce




"Gobe sai kazo muje court domin kayi signing ƙaddarorinka in shaa Allah,sannan idan naga ka bada himma da ƙwazo sauran ƙaddarorin zan danƙa mata don cigaba da kula dasu tunda yanzu tsufa ya fara tasomin"




"In shaa Allah Dad,ina godiya sosai Allah ya ƙara nisan kwana da lafiya mai amfani"




Da Ameen suka amsa masa kana yayi musu sallama ya wuce part ɗinsa wanda yake sama,duk da Fadila ce ta fara cewa tana sonsa amma yanzu kuma sonta ya fara shigarsa kaɗan-kaɗan





Waiwaye





*****A lokacin da Sadam yake a shekararsa ta uku a UK ya haɗu da Fadila,ita kuma tana a shekarar ta biyu,a wurin taron musulman Nigeria suka haɗu,kasancewar shi ne AMEER ɗin ɗalibai a makarantar,abinda yaja hankalin Fadila shi ne kyaunsa,ƙwaƙwalwarsa da miskilancinsa shi yake burgeta,gashi yanada saje a fuskarsa mai ƙara masa annuri haɗi da kwarjini.




Bata ɓoye ba ta cuci kanta ta samesa,shi kuma a lokacin yana tare da abokinsa Sadiq suna zaune,tayi musu sallama haɗe da gaishar dasu,Sadiq ne ya amsata amma Sadam ko kallon inda take baiyi ba,ya cigaba da sabgarsa,a nan  ne ta bayyana soyayyar da take masa,wanda a ƙarshe daƙyar Sadiq ya shawo kansa akan babu kyau wulaƙanta mutum,sai a sannan ne ys aminta suka fara soyyaya,har iyayen Fadila suka san da Sadam,Daddyn Fadila har Nigeria yasa akayi bincike akan Sadam,sannan ya aminta da auran nasu,wanda a yanzu komai ya taɓarɓare a duka ɓangarorin guda biyu*****






Cikin labari





Bayan ya zauna a saman sofarsa ya kira Fadila don sanar mata suyi haƙuri da junansu tunda iyayensu basa so,daman duk rikita-rikitar da take faruwa a gidansu Kakarta Fadila duk ta sanar masa.




Haka dai suka haƙura da juna duk da a ɓangaren Fadila ba haƙura tayi ba saida babu yadda ta iya tunda Sadam ya fita daga sabgarta,yayi deleting komai nata a wayarsa.



Sadam yanzu ya maida hankalinsa complete a harkar kasuwancinsa wanda maa shaa Allah komai yana tafiya yadda ya kamata.wannan kenan






              @@@ @@@@@@






KADUNA




A ɓangaren LOVE BIRDS🕊️ wato Sauban da Maryam abubuwa ƙara zafafa suke.Kasancewar yanzu su Maryam suna IT kuma da wuri take dawowa gida,halayanta munana sai ƙara bayyana suke,gashi yanzu kwata-kwata basa shiri da surukarta kuma duk saboda halayanta ne.




Yau Saturday Sauban na gida suna hutawa a falo,ya dubi  Maryam ya ce



"Dear ki shirya abinci ajima abokaina zasuzo,don Allah Maryam karki bani kunya gun friends ɗina musammam Captain Fu'ad wanda tun asali ba son auranmu yake ba,please Maryam kiyi girki mai daɗi wanda zasu yaba ba irin wanda kullun kikeyi muna asarar kayan abinci ba,na roƙeki "




Hannu bibbiyu yake roƙan Maryam don yasan idan aka samu matsala,shikenan Captain Fu'ad ya samu abin tsokanarsa.




Haka Maryam ta saka apron irin ƙwararrun kuku ɗin nan ta shiga kitchen,tayi alƙawarin yau zata birge mijinta.(Har ni mai ɗaukan rahoto zanci hadɗan girkin Maryam kuku🙃🙃🙃)



Tayi tsawan awa huɗu a kitchen tana kwaɓe-kwaɓe wanda ni kaina bansan mai take kwaɓawa ba,duba da yadda take sharɓan uban gumi,ta ɓata tukane da robobi  sun kai biyar ƙananu da manya,ga wani juice data haɗa wanda bansan wani iri bane,ƙila sabon fitowa ne ohon mata🤔.Haka da sakasu a food warmers sannan ta jerasu a dining table,ta wuce ɗaki tayo wanka ta shirya tsaf don tarbar baƙin mijinta.




Da sallama suka shigo falon su uku,wato Sauban,Captain Fu'ad da kuma ɗaya abokinsu wanda yake aiki a Abuja sukazo.A falo suka babbaje suna hutawa sai Sauban ya miƙe don kiran amaryar tasa, gaban da dukan uku-uku akan Allah yasa tayi girkin hankali kar yaji kunya,samunta yayi tana chatting a wayarta tasha kwalliya abinta,kiranta yayi akan tazo su gaisa da abokansa,babu musu ta tashi zata fita,Sauban yayi Saurin ce mata



"Da alama baki da hankali,da wannan shigar zaki je gun abokaina,wai yaushe zakiyi hankali ne Maryam,nidai na shiga uku an kawomin rainon yarinya,ke kullum sai ance miki kiyi kaza,kibar kaza haba mtsw!!! "




Fita yayi ita kuma ta saka hijab ta fito suka gaisa da abokan nasa,cewa yayi suje dining suci abinci,babu musu suka miƙe musamman Captain Fu'ad wanda ya ɗebo yunwarsa,yazo yaja girkin amarya.(hmmm Captain Fu'ad a shirya cin girkin Maryam kuku😂😂😂🙃)





Zama sukayi a dining room ɗin sai Sauban yayi serving ɗinsu,kasancewar ya umurci Maryam ta wuce ɗaki,serving ɗinsu yake amma zuciyarsa na dukan tara-tara bama uku-uku ba,ganin yadda colour ɗin abinci yayi so scary babu kyan gani,gashi baya fidda wani aroma mai daɗi sai uban ƙauri,haka dai ya gama serving ɗinsu shima yayi serving kansa sannan ya samu guri ya zauna.




Captain Fu'ad ne farkon fara kai spoon ɗin abinci a bakinsa wanda a lokaci guda amai ya tasa sama jin wani uban ƙarni,ga yajin data zambaɗa a ciki,kai kai kai,amai Captain Fu'ad yake kwarawa babu ƙakƙautawa lokaci guda ya ɗau gorar ruwa ya kwankwaɗe,baiji yajin ya daina masa zafi a baki ba,ya ƙara ɗaukar wata sabuwar goran ruwan ya shanye,su kuma Sauban ganin yadda Captain Fu'ad ya rikice lokaci guda suka kasa cin abinci tare da miƙewa suka nufo inda yake suna masa sannu.Bai amsa musu ba ya miƙe ya dauki key ɗin motarsa ya fita,har waje Sauban ya bisa yana basa haƙuri haka ya ƙyalesu suka tafi,a fusace ya shigo falon har bedroom,lokacin Maryam na kwance abinta,batayi aune ba taji saukan zafafan maruka har guda huɗu lokaci guda,habawa a haukace a miƙe tare da sakin wani razanannan ihu,bai ƙyaleta ba saida ya mata dukan tsiya tare da ce mata ta tafi gidansu gobe,sannan ta tabbata ta goyi girki tare da gyaro munana halayanta kafin ta dawo gidan.Fita yayi baibi takan kukan da take ba ya wuce wani ɗakin ya kulle tare da kwanciyarsa.




Washe gari Maryam ta tattara kayanta ta nufi gidansu,wanda Sauban yasha tsinuwa a hannun iyayenta kasancewar ƙarya da gaskiya ta faɗa musu,su kuma babu bincika ba sukaita zaginsa.Wannan kenan






                @ @@@@@@@@@





Ɓangarensu Umma Kande da Maman Jummalo da alama basuyi nadamar abubuwan da suka faru da yaransu ba,domin har yanzu ƙiyayyar Umman Sa'eeda da ita Sa'eedar na nan daram! A zukatansu.




Suna zaune su duka da yaransu wato Iklima da Jummalo,sai Umma Kande ta ce




"Kodai mu ƙara komawa gun Boka Sankeru ne muji a ina aka samu matsalar"




"Tabb wallahi ko kusa Mama karku fara,yanzu duk abinda ya samemu bai zamo muku isharaba,harda rasa ɗiya kikayi amma bakiyi ladama ba Mama"




Cewar Iklima wacca ta harzuƙar sosai saboda halin uwarta ta domin  haushinta take ji sosai,Maman Jummalo ce ta ce




"Haba Iklima daɗi da hutu muke nema muku ai,wannan ma matsala aka sam....."




"Matsala! Matsala! Kika ce fa Mama, wallahi bazamu sake biye muku  ku kaimu ga wahala ba,da alama kema kamar yadda Iklima ce bakiyi nadama ba,to bara kuji tun a asibiti ni da Iklima muka shirya komawa Islamiya,don ƙara sanin Allah da addinin mu,wanda kuka kasa bamu"




"Tabbas kuwa Jummalo zan tambayi Sa'eeda yadda karatun islamiyarsu take"




Umma kande ce ta hayayyaƙo Iklima da masifa tana cewa




"Ɗiyar maƙiyiyata zaki nema shawara wurinta Iklima"



"Maƙiyiyarki ko ko ce maƙiyiyarta,wani irin asiri ne baku musu ba,amma gashi sai cigaba suke, ku kuma kuna nan jiya iyau"cewa Iklima




"Rufemin baki dan Ubanki,da hassadar Umman Sa'eeda aka haifeni sannan yanzu ma na fara nuna mata ƙiyayya wallahi, koya kika ce ƙawas"




"Ƙkkkwaraiii da gaske yanzu muka fara nuna mata ƙiyayya"



Suna cin hakane akan kira numban Umma Kande wanda tsabar masifa bata duba mai kiranta ba ta amsa kiran



"Hello"



A can ne ake mata magana,wanda lokaci guda ta rikice tana cewa



"Mai wayar!!! "



A can aka ƙara tabbatar mata,habawa sakin wayar tayi a ƙasa haɗi da zaman ƴan bori,tana ihu da kururuwan ta bani ta lalace shikenan ta mutu.Kanta su Maman Jummalo sukayi suna tambayar lafiya mai ya rafu,cikin kuka haɗi da majina take cewa



"Na shiga Uku ni Sarere jikar Sarkin ruwa!!!na mutu na lalace wayyo ni Saratu!!!! Yanzu..................











Mu haɗu a pages na gaba My Esteem Fans🙃🙃🙃🌹🌹🌹









****Wata sabuwa inji ƴan caca,wani  bala'in ya kuma saukar ma Umma Kande ne???.....







****Anya Zaman Sauban da Maryam zai cigaba da wanzuwa ganin yadda tun kan aje ko'ina an fara kai duka tare da tafiya gida???.....










****Shin Fadila zata haƙura da Sadam kamar yadda ya haƙura da ita koko yaya???......







*****Shin wasu abubuwa ne suka faru shekaru aru aru a baya wanda Momin Sadam da ahalinta suka kasa mancewa???........








Ku cigaba da zubo ruwan comments🤗🤗🤗🙃🙃🙃💝💝💝,Ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku da zafafan updates wa'inda zasu nishaɗantar,ilmantar tare da faɗakar daku🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️










Ina matuƙar alfahari daku my Esteem fans,Allah yabar ƙaunar🤗🤗🙃🙃💝💝🌹🌹🌼🌼🏵️🏵️💖💖💗💗💓💓





Post a Comment

0 Comments