TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Nacina ya jawo mini page 47-48

  🏵️ *NACINA YA JAWO MIN* 🏵️





*Narrnarhh Bukar* 

( *The Amazing Pen* ✍️)





*TASKIRA WRITER'S FORUM*

*T.W.F*





*WATTPAD*

https://www.wattpad.com/user/AISHAABUBAKAR812?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends



*AREWABOOK*

https://arewabooks.com/book?id=6615ba31404e6e2687888ab9



*TELEGRAM*

https://t.me/+439Pdx2UbLZlOTNk



*WHATSAPP CHANNEL*

https://whatsapp.com/channel/0029VaRTjCw8vd1HiLjaNK2y




*BOOK 2*




4⃣7⃣----4⃣8⃣






Kasancewar yau Juma'ah babu Islamiya,su Iklima na tsakar gida tare da iyayensu suna hira cikin farin ciki da annashuwa ga cikin Maman Jummalo sai girma yake,suna cikin hirar sukaji sallama tare da shigowa,maza ne su biyu sun saka nose mask suna riƙe da wata mata wacca na kasa gane wace ce har cikin gidan inda su Iklima suke da iyayansu suka kai matan tare da ajiyeta,da sauri su Iklima da su Umma Kande suka miƙe tare da toshe hancinsu saboda uban warin da matan take sai kace kashi,cikin tashin hankali Umma Kande tace


"Wazan gani ni Saratu!!! Nusaiba kece haka!!! Meya sameki!!! Wayyo!!! Wayyo ni Sarere na bani na lalace!!! Yiiiiiiii!!! "


Kowa a wurin hancinsa a toshe yake saboda warin kashin da jikin Nusaiba yake,duk ta rame ta koɗe tayi baƙi sosai,idanun nan nata duk sun shige ciki saboda muguwar ramar da tayi,ita bama jin mai suke cewa take ba,domin tana a cikin mawuyacin hali ne.Kowa a wurin saida ya tausayawa halin da Nusaiba ke ciki,Umma Kande ai kuka take sosai tana ƙara duba ƴarta,ita bama ta warin da yake fita daga jikin ƴarta take ba a'a yadda ƴarta ta koma ne hankalinta ya tashi akai.Mutanan da suka kawota ne wani daga cikinsu ya ce


"Ni ba Hausa ooo,daga Lagos muke ooo,so na help we help say make we bring gam to her family make you kuku take her hospital me she no die ooo"


Idanu suka tsira ma bayaraban,domin a cikinsu babu wanda yake jin turanci,yooo Islamiya ma ba zuwanta suke ba ina ga boko akwai ƙura,gwara shi akan ɗayan,haka mutumin ya ƙara tambayarsu still da turanci


"Bucket with water make we wash the pupu she do for our car"


Bucket kawai suka iya ganewa a duk cikin maganarsa,Jummalo ce ta ɗauko mishi bokiti haɗi da ruwa a ciki ta miƙa mishi,fita sukayi babu jimawa suka dawo da bukitin tare da yimasu sallama.


Tashin hankali wanda ba'a samai rama,hauka ne kawai Umma Kande batayi ba,gashi mikin mutuwar Musa saida ta fama,ji kake tana ihu da kururuwa kamar wata motsattsa,tana cewa


"Shikenan na mutu na lalace!!! Waye gatana a duniya yanzuuuu ni Sarere jikan sarkin ruwa!!! Wayyo na shiga uku na lalace!!! Shikenan masu tallafamin sun ƙare!!! "


Maman Jummalo ne ta harziƙa saboda ihu da kururuwan da take,domin wa'azin da sukeji wani malami yayi bayani akan babu kyau idan wata musiba ko mutuwar wani naka ya sameka kayi ta kururuwa ko kuma iface-iface,anfiso ka yawaita salati tare Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un,ko kuma Allahumma ajurni fi musibati haka wa aklifni khairan minha.Hakuri tayita bata tana cewa


"Haba Umma Kande wannan kururuwan da iface-ifacen da kike ba ita bace mafitarmu a yanzu,ɗaukarta ya dace muyi mu kaita asibiti don neman lafiyarta,don Allah kibar kukan nan ki kwantar da hankalinki,da izinin Allah zata samu sauƙi"


Ita sai yanzu ta tuna da wata aba wai asibiti,ai kamar an tsikareta haka ta miƙe tana cewa


"Iklima maza-maza ki tare mana keke napep yanzu mu kaita asibiti,yi sauri,yanzu-yanzun nan"


Da sauri Iklima ta fita tare da nema musu keke napep,ita kuma Umma Kande da Maman Jummalo tare da Jummalo suka cicciɓe Nusaiba zuwa bayi,tare da yi mata wanka a gurguje,kayan Iklima suka saka mata,suna cikin shiryata saiga Iklima ta shigo tana ce musu an samu keke napep ɗin,sauri-sauri sukayi suka saka mata kayan tare fesa mata turare saboda warin da jikinta yake,kashi ne yake fita daga duburarta babu full stop,ga kashin da shegen wari,haka suka cicciɓeta har cikin keke napep ɗin,Maman Jummalo da Umma Kande ne suka shiga ciki,sai ita Iklima ta taran musu wani tare da amsar ATM card ɗin Umma Kande saboda ciro kuɗin da za suyi amfani dashi a asibiti.




*Waiwaye*



Abinda su Umma Kande basu sani ba shi ne,hanyar da Nusaiba ta ɗaukoma rayuwarta ba mai ɓulle mata bane,domin kuwa babu abinda Nusaiba batayi kama daga sex,lesbian,luwaɗi,shaye-shaye da dai sauransu harda biyan buƙata da kare,duk ta haka tanayi,har ƙungiya ta kafa na tatattun ƴan duniya a Lagos area na Hausawa,domin tun sanda Alhaji Sagir ya fita da ita ƙasar waje abubuwa suka ƙara dulmiyar da ita,ya haɗata da gogaggun ƴan bariki maza da matansu,masu harkoki kala-kala tun kama daga lesbian,luwaɗi,shaye-shaye dama masu biyan buƙata da karnuka(Wa'iyazubillah,ke duniya ina zaki damu🤔🤔🤔)


Haka ita ma ta goge a cikinsu harda tattoo take dake a wuyanta da mazaunanta, ta zama shugaban kanta,babu irin abinda batayi, gasar cin duri ne,gasar amfani da kare ne duk babu wanda batayi,shiyasa kuɗaɗe suke shigo mata kamar hauka,tana kashesu kamar iska,tare da turo ma Umma Kande maƙudan kuɗade ita kuma Umma Kande tana sa mata albarka tarw da murna,ƙarin daɗi rashin faɗan Umma Kande ga Nusaiba ne yasata ƙara shiga halaka,gasarta da ƙarshe wanda daga shi ne Allah ya jarabceta da yoyon karshi,anyi gasar yin amfani da kare ne,wanda ashe karan yanada cuta wanda ba'a sani ba,sai bayan an gama gasar ne har Nusaiba ta dawo Lagos sai ta fara yoyon kashi,abu kamar wasa sai ya tsananta,komai nata ya ƙare har takai ta kawo bata iya fita daga ɗakinta,wa'inan bayin Allah ne suka tausaya mata ganin kowa ya guje ta,tayi musu kwatancan gidansu a Kaduna sai suka kawota.




*Cikin Labari*


Mai keke napep ɗin sai masifar yake saboda warin da keke napep ɗin yake har suka isa asibitin,bayan ya sauke sune sai Maman Jummalo ta biya kuɗin keke napep ɗin,suka cicciɓeta zuwa cikin asibitin,shi kuma mai keke napep saida ya nemi inda ake ɗiban ruwa ya wanke keke napep ɗinsa saboda warin kashin da cike ilahirin keke napep ɗin. Duk inda su Umma Kande suka wuce da Nusaiba sai an toshe hanci,haka har suka isa cikin asibitin inda nurses suka sakata a gadon marasa lafiya zuwa cikin emergency room,likitoci ne har biyo suka duƙufa a kanta,wanda basu suka fito ba bayan awa biyu lafiyayyu,cikin ɓacin rai da takaici wani likita ya umurci su Umma Kande su biyoshi Office,haka suka bishi kamar raƙumi da akala har Office ɗinsa,ko zama baiyi ba ya fara zazzaga musu ruwan masifi,ta inda yake shiga ba nan yake fita ba,tsuru-tsuru su  Umma Kande sukayi,yoo basuda abin faɗa,sai can kuma likita ya zauna tare da ce musu su zauna,cikin sanyin jikin haka suka lafe a kujerun kamar kajin da ƙwai ya fashe musu a ciki.Cikin natsuwa likitan ya fara musu bayani game da ciwon Nusaiba yana cewa


"Saidai kuyo haƙuri da yanayinta a yanzun,domin ciwonta ya zama chronic babu yadda muka iya,zamu bata gado,amma fa zaku sha aikin siyan *pampers* ɗin manya saboda yanzu dashi zata dinga zama koda kuwa jikinta ya samu sauƙi,dalili saboda duburarta ta tashi aiki,abinda yake controlling fita da tsayuwan kashi ya lalace ta hanyar abubuwan da takeyi ko kuma mu'amalar da akayi da ita a bayanta,so blame yourselves na rahin kula da tarbiyyarta,don ta dinga amfani da *pampers*  kenan har ƙarshan rayuwarta,zan rubuta muku magani tare da allurorin da zaku siya"


Shiru kowaccansu tayi tana tunani kala-kala aranta,musamman Umma Kande wacca take tunanin ayya ba Sammu aka mata ba ita da ƴaƴanta,taya komai nata zai dinga taɓarɓarewa,katse musu tunani likitan yayi da miƙama Umma Kande wata ƴar paper tare da cewa


"Gashi kuje pharmacy ku siya sannan karku manta da pampers ɗin da nace ku siya domin shi take buƙata cikin rayuwarta a yanzun"


Amsa su Umma Kande sukayi tare da barin office ɗin zuwa pharmacy don siya abubuwan da likita ya rubuta,sai Umma Kande ta ce Iklima taje ta siyo pampers ɗin manya wanda za'a saka ma Nusaiba.


Satinsu biyu a asibitin tukunna aka sallamesu bayan Nusaiba ta samu sauƙi sosai,saidai kuma ramar da tayi da baƙin da tayi babu inda sukaje,Abban Sa'eeda ma yayita jigilar zuwa asibitin tare da bada abinda ya sawwaƙa daga aljihunsa.


Haka suka tattaro zuwa gida,kullum cikin siyan pampers suke gashi da shegen tsada saboda ba ko'ina ake samu ba,taimakonsu ɗaya ne,shagunan da marigayi musa ya siya ne suke samun kuɗi daga shagunan if not da abubuwa sun ƙara rincaɓe musu,kullun cikin nasiha Iklima da Maman Jummalo suke ma Umma Kande akan ishara ce Allah ya nuna mata,ba sauraransu take ba hasalima cewa tayi maƙiyanta ne suka jefeta da ƴaranta wai don sunga suna da rufin asiri,sunyi-sunyi  Maman Jummalo akan da dawo hanyar Allah da ma'aikinsa amma inaa,ta riga da tayi nisa batajin kira.





*TUNATARWA*



*Ƙalubali ga iyaye mata masu rashin kula da tarbiyyar yaransu tare da son abin duniya,kusani kiwo ne Allah ya baku,dole ne ku kula da cinsu,shansu,lafiyarsu,tufafinsu,wurin kwanansu sai uwa-uba Tarbiyyarsu  da daɗi ace ai wacce  yarinyarta ƴar kirki ce ga tarbiyya da kamewa,haka kuma babu daɗi ace ai wacce yarinyarta ƴar isaka ce,bata da kunya,ga shegen bin maza kamar akuya,idan kika kula da tarbiyyar ƴarki wallahi rige-rige mazan ƙwarai suyi wurin neman auranta domin kuwa kowani namiji yana buƙatar mahaɗin rayuwarsa da gari wacca itama zata tarbiyyantar da yaransa,kinga kuwa idan baki ba ƴarki tarbiyya mai kyau ba taya mutumin ƙware zai nemi auranta???*


 

*Ƴan uwana iyaye mata a kula da tarbiyyar yara,kunga dai yadda Umma Kande ta ƙare da yaranta duk don rashin tarbiyyar da suka samu ne a hunnunta suka faɗa halaka musamman Nusaiba, Allah ya tsaremu ya tsare ƴaƴanmu da zuri'armu baki ɗaya*


Haka su Umma Kande sukayi ta jigilan siyan pampers ɗin Nusaiba har Allah yasa ta samu lafiya jikinta ya murmuro duk da ba barin siyan pampers ɗin zasuyi ba tunda ta dinga amfani dashi ne har ƙarshan rayuwarta.Wannan kenan




       @@@@@@@@@@@@@@



*ABUJA*



Karnuka ne bila adadin suka biyo Haj. Zulfa'u a ta ɓangaren hagu,ga wasu mutane su biyu mace da namiji hannun a tsarƙafe dana juna suna binta,gudu take a cikin duhun daji tama rasa ina zata bi saboda hagu da dama bibiyarta ake,cigaba da gudun tayi saboda karnukan sun kusa taddota,sai can tayi tuntuɓe da dutse lokaci guda ta faɗi ƙasa,haba karnukan nan kanta suka yo tare da cizonta ta a ko'ina suna haushi,ita kuma babu abinda take inda ihu da neman agaji ba,tana wannan ihun ne saiga wa'innan macan da namiji suma sunzo gunta suna nunata suna dariya,mai cikin nan ne da yara maza guda biyu tana riƙe dasu ta bayyana agabamta kamar walkiya,dariya ta tintsire dashi,suma ƴan biyu maza dariya suke tayi,sai kuma da tsagaita dariya tare da fara magana cikin muryarta mai firgitarwa


"Zulfa'u ƙarshanki ya kusa!!! Bazaki taɓa guje mana ba!!! Dole yarana su ɗau fansa!!! Kinga yadda ƙarshanki zai kasance tare da karnuka !!! "


Haj.Zulfa'u da duk tayi jina-jina saboda cizon da karnukan suke mata babu ƙakƙauwa kota ina a ilahirin jikinta,cikin muryarta wacca bata fitowa ta fara magana


"Karku zo!!! Kubarni da rayuwata!!! Kubarni "


Haka tayita maimaitawa su kuma mutanan sai dariya suke mata,can kuma suka ɓace Dif!  kamar walƙiya.


A gigice ta farka tana cewa


"Boka Burumbuɗu ka taimakeni!!! Zasu dawo!!! Zasu kasheni!!! Wayyo!!! Wayyo ni Zulfa'u!!! "


Mai aikinta ce ta shigo ɗakin da gudu kasancewar da yamma ne bayan Asr,tayi baccin tare da yin wannan mummun nan mafarkin mai tsoratarwa tare da firgitarwa,cikin tashin hankali mai aikin ta ce


"Hajiya lafiya? Ko a kira miki likita ne ko kuma Haj. Amina tazo"


"A'a karki kira kowa!!! Tafi!! Tafi!! Kawai!!"


Mai aikin zata sake magana Haj. Zulfa'u ta daka mata tsawa da cewa


"Ki tafi nacee!!! Bana buƙatar kowa yanzu!!! "


Jiki na rawa haka mai aikin tabar ɗakin saboda tsawan da Haj. Zulfa'u tayi mata,abinda tunda take da ita bata taɓa mata kenan tsawa,zancen zuci ta fara 'Anya Hajiya ƙalau take kuwa kwanan nan,kullum cikin firgici take da tsoro,ko abincin kirki ta daina ci,fita ma yanzu ta daina,gashi ta hana baƙi zuwa gidan,ko miye dalili oho! ' haka tayi ta zancen zucinta har ta sauka daga matattakan benan zuwa kitchen daman girkin dare take sai taji ihun uwar ɗakinta shiyasa tazo da gudu don jin ko lafiya.


Haj.Zulfa'u duk hankalinta ya tashi matuƙa ainun,gashi bokanta ba yanzu zai bayyana gareta ba sai nan da wani ɗan lokaci,tunani take wai shin meke shirin faruwa da ita ne a kwanan nan,mai yasa take yawan mugayan mafarkai da miƙiyiyarya ne,wayyo boka kayi sauri kazo ina neman agajinka da gaggawa,haka tayita tunaninta har akayi sallar magrib daman ita ba sallar take ba,ta riga ta sallamawa boka Burumbuɗu komai nata.(Ya Salam🤔🤔🤔, Allah ka tsare mana imaninmu)


Tun daga ranar kuma sai bata sake mugayan mafarkai ba,ita a tunaninta bokanta yaji da wannan ɓamgaren wato tsareta da ahalinta na daga abin cutarwa da ya mata alƙawari a baya saboda sharudɗan da take bi nasu.Wannan Kenan



         @@@@@@@@@@@@@



*KEBBI*


Cin nasara su Sa'eeda suka kammala exams tare da tahowa ƙwansu da ƙwarƙwatarsu zuwa Birnin Kebbi don halartar ƙwarya-ƙwaryar walimar da za'a gudanar a family house ɗinsu wanda har ƴan uwa na nesa sun fara zuwa,tun daga wasu maƙota jahohin har ƴan ƙasar waje,irin su Sadiya second born ɗin Momin Sadam dama wasu ƴan uwansu da suke da matansu a ƙasar waje duk sun hallara a family house wato asalin gidan *Alhaji Kabir Dikko* .


Su Umman Sa'eeda da Momin Sadam sun dawo daga Umra tun a satin daya gabata,Umman Sa'eeda tayi ƴar ƙiba,ga fatarta ta murje tayi haske sosai kasancewar daman wahala ce ta saka yin duhu,sanda suka dawo direct daga airport aka wuce da ita zuwa family house,murna iya murna domin Umman Sa'eeda taga ƴan uwanta,kowa sai murnar bayyanarta suke,musammam tsoho mai ran ƙarfe wato Baba Garba,ji yake kamar ƙanwarshi Maimuna ce ta dawo garesa,har da kuka yayi saboda farin ciki,masauki mai kyau part guda aka ware ma Umman Sa'eeda daman ita Momin Sadam daga airport ta wuce gida kasancewar Daddyn Sadam shima gobe zai dawo daga tafiyar da yayi.


Family house ɗin babba ne in fact layi guda ne,kuma duk cike yake da ƴan uwa,ginin zamani ne,akwai masallaci da makarantar islamiya a ciki,ga tangameman gate mai shegen kyau,part-part ne gidan kuma painting su iri ɗaya ne babu bambamci,ga inter-lock a ko'ina na gidan,harda wurin wasan yara,da kuma babban hall wanda a ciki ne ake duk family meeting tare da shagulgulan sallah,hall ɗin babba ne gashi yasha decoration gwanin ban sha'awa.Haka Family house ɗin ya cika maƙi da ƴan uwa na kusa dana nesa,yaransu da manya,order abinci aka ba wani hotel don yin walimar.


Tun safe kowa ya fara shiri,Sa'eeda na a part ɗin da aka ware ma Ummanta,acan ta shirya cikin tsadaddun lace wanda Momin Sadam ne tasa a ɗinki mata tare da Ummanta,sunsha kyau sosai,sai walwali suke,ga wani haɗadɗan takalmi half cover da jakarsa ta saka ita da Ummanta iri ɗaya saidai colour ɗin ne ya bambamta,wooow kawai zan iya furtawa saboda kyauwun da sukayi,haka suka fito ita Ummanta zuwa ɗakin taron kowa ya hallara har da goganku Sadam shida amininsa Kamal,a saman hall ɗin akwai kujera two seater acan aka umurce su da su zauna,babu musu suka je wurin suka zauna.


"Wooooow!!! What a precious angel from paradise!!! " cewa Kamal


Sadam da hankalinsa ke akan waya ya ɗago don ganin abin abokinsa yake dabo haka,dummmmm!!! Haka zuciyarsa ta bada,ganin Sa'eeda cikin wannan shiga ta alfarma,a gaskiya duk tafiye-tafiyan da yake tare da hulɗa da mutane maza da mata  bai taɓa ganin mace mai kyau irin Sa'eeda ba,gashi kayan da ta saka ya mata mugun kyau sai kace amarya duk da ba wata kwalliya tayi ba,tunina ya lula yana ayyana abubuwa da yawa na game da ita,shifa tunda yabar Kaduna yake tunanin Sa'eeda tare da girkinta,muryarta yake ƙara tariyowa a sanda tace mishi shi mutum ne ko aljan,harda shirman da tayita yi lokacin da ta shigo ɗakin ba tare da tasan akwai mutum ba,katse mishi tunani Kamal yayi da cewa


"A gaskiya yarinya Allah ya mata baiwar kyau da sura"


Ai tuni wani malolon abu ya tasoma Sadam tare da tsaya mishi a wuya,wani irin haushi Kamal ya bashi,tsaki yayi tare da cewa


"Kaifa daɗina da kai shegen son mata,wannan yarinyar kake yabo haka,mtws! "


"Yarinya fa kace,tabb da sauranka wallahi,yoy never know what is called hot babe Man!"


"Kaga malam ba abinda ya kawoni nan bane,kacika surutun jaraba,haba kabari idan kaje gidan radio sai kayi mana! "


Dariya Kamal yayi wato shidai mai hali baya barin halinsa kenan,Sadam da miskilanci.Uncle hassan ne ya buɗe taron da adduar dayake jiya shima ya iso ƙasar,addu'a sosai akayi sai daga baya kowa  ya fara gabatar da kansa gasu Umman Sa'eeda, bayan kowa ya gabatar da kansa sai aka miƙama tsoho mai ran ƙarfe wato Baba Garba micro phone  don ya bada tarihi,cikin muryarsa wacca bata fita sosai saboda tsufan da ya fara bama su Umman Sa'eeda tarihi kasancewar bata taso a cikin suba,ya fara da cewa




*TARIHI* ( *tare da wasu ɓangare na abubuwan da suka faru shekaru aru-aru* )



Sunan mahaifinmu Alhaji Kabir Dikko matarsa ɗaya wato mahaifiyarmu mai Suna Hajiya Suwaiba,mahaifinmu asalin dan Zamfara ne a ƙaramar Hukumar Gora dake a jahar Zamfara,kasuwanci ne ya kawo mahaifinmu Kebbi State har Allah ya ɗaukakashi tare sama kasuwancinsa albarkha,ƙannan mahaifinmu biyar ne duk maza wanda suma sun dawo Kebbi wurin mahaifinmu da zama kasancewar shi ne babba a ɗakinsu kuma iyayansu sun daɗe da rasuwa,haka har Allah ya bama mahaifinmu ikon siyan layin nan complete saboda a zamaninsu yana ɗaya daga cikin sharararrun ƴan kasuwa masu kuɗin gaske.


Mu uku ne wurin Mahaifinmu babbar yayarmu sunanta Mariya ta haifi yara uku amma Ruƙayya,Salima sai Mubarsk amma biyu sun rasu saura Rukayya(Momin Sadam),sai kuma ni mai suna Abubakar,ina da yara hudu,Kabir mai sunan Mahaifinmu, Suwaiba mai sunan Mahaifiyarmu,Maryam sai Nabila (Dr.Nabila),sai Mahaifiyarki mai suna Maimuna,ita ce autarmu ta haifi ƴan biyu maza amma suna da shekara uku a duniya dukkaninsu lokaci guda suka rasu,sai ku kuma,iyayenmu sun bamu ilimin boko dana zamani,shiyasa a duk ahalinmu babu wanda baiyi karatu ba.



Hussaina haƙiƙa ƙaddara ta faɗama mahaifiyarku a lokacin tana tsohon ciki,kasancewar abokina ne ta aura wato *Alhaji Sani Mai Gado* shahararran ɗan kasuwa ne kuma ɗan boko,matarsa ɗaya Zulfa'u,ya auri Maimunatu ne saboda bayajin daɗin zama da matarsa saboda munanan halayanta,sai kuma Allah yayi nufinsa da auran Maimuna wacca ta haifa mishi yara har huɗu amma biyu sun rasu (Twins)sai tsohon cikin dake jikinta.



Ban mantawa ana gab da ɓatan Maimuna abokina Alhaji Sani ya kirani akan yanaso ya kai ƙaddarorinsa kotu sai bayan yaransa sun girma idan ya mutu sai a raba musu gado,dalili na tambayeshi akan hakan,bai ɓoyemin abinda ya gani da idonsa ba da daddare ya tashi sallar dare yaga matarsa Zulfa'u tana surkulle tana faɗin sunan Maimuna da yaranta harda shi kansa,dalilin hakan ne da safe ya kirani,ni kuma babu ɓata lokaci nazo har Abuja inda suke mukaje kotu akai cike komai tare da ƙaddamar da ƙadaddorinsa har ma na ƙasar waje, bayan dawowana Kebbi ne Alhaji ya kwanta ciwo sai kuma a lokacin muka nemi Maimuna da yaranta muka rasa,babu inda ba'ayi cigiya ba amma shiru,sai kuma bayan wata ɗaya naje Kaduna wurin wani abokani na kaɓe Hassan da motana a rashin sani wanda shi ne asalin ganin Hassan da mukayi,a kullum ina zargin Zulfa'u da ɓatan Maimuna saboda abinda Alhaji Sani ya faɗamin game da ita,ban ɗau mataki a wannan lokacin ba saboda ɓatan Maimuna amma yanzu komai zaizo ƙarshe da izinin Allah,sai munga ƙarshan Zulfa'u in sha Allah.




*Cikin Labari*



Haka Baba Garba kammala bada tarihi babu wanda a cikin ɗakin taron bai zubda ƙwalla ba tuno da abinda ya faru a baya,Umman Sa'eeda kuka take harda shassheƙa ashe kishiya ce sanadin tarwatse ahalinsu,kishiya ce ta hallaka Mamanta da ƴan uwanta,kishiya ce ta saka musu ƙunci da damuwa a zukatansu wayyo duniya ina zaki damu,itama Sa'eeda saida tayi hawaye jin tarihin asalinta da kuma abinda ya faru shekaru da dama,amma kuwa anyi azzalumar mata,sheɗaniya,in sha Allahu ƙarshanta yazo,miƙama Umman Sa'eeda microphone ɗin akayi,itama ta bada tarihin rayuwarsu tun daga rayuwarsu a ƙauyen Damari har auran da tayi, irin ƙalukalen tare da wahahalun da tasha duk saida ta bada labarinsu,babu sauyin da kake ji a ɗakin taron saidai sautin kuka da fa ce majina,saboda akwai tausayi a labarin rayuwar Umman Sa'eeda,Uncle  Hassan yayi kuka iya kuka jin yadda ƴar uwarsa ta rayu cikin wahala,dole ne ya faranta mata,lokacin jin daɗin ta yazo ita da ƴarta,walimar cin abinci aka fara,ma'aikatan hotel ɗin suke bin kowani table da abinci kala-kala tare da abubuwan sha iri-iri suma.



Fitsari ne ya matse Sa'eeda kasa haƙuri tayi ta miƙe don ta zaga,har taje tayi fitsarin wurin dawowa bata sani ba tana kalle-kalle kanta ya bige a ƙirjin mutum,ji kaki ƙus! Ai ba shiri ta ɗago kanta don kallon wanda ta bige,Ras! Ƙirjinta ya bada ganin wanda ta bige,shima kallonta yake babu ko ƙyaftawa,suna a haka sai can ta taɓe baki tare da fuskar kuka tana cewa



"Kawai kawai ka bige mutum amma ka kasa bashi haƙuri"



Mamaki maganarta ta bashi,au shima ya bigeta ce yake wurin kalle-kalle yana waya bata sani ba bige shima zai bata haƙuri,tabb! Ai kuwa tana ruwa,uffan bai ce mata ba sai ma kira daya shigo wayarsa zai ɗauka ya ce ta ce 


"Mugu kawai,mai tsorata mutum"



"Nine mugu? "



Kusa da ita ya ƙaraso yana tambaya tare da kashe kira,ai ba shiri Sa'eeda tace *ƙafa mai naci ban baki ba* ita a tunaninta dukan ta zaiyi,saida tayi nisa da wurin da yake ta juya ta ce



"Eh ɗin,Eh din,Nace mugu,mugu mugu Sadam"



Murguɗa masa baki tayi tare da ƙarasawa cikin ɗakin taron da gudu,tsayawa yayi yana kallon gun da tabi,komai nata birgeshi yake,wanka ma kansa mari yayi tare da cewa



"Wake up Man,what's wrong with you"



Haka aka kammala walimar kowa ya wuce gidansa,na nesa kuma suka wuce ɗakin baƙi,Su Umman Sa'eeda da Dr Nabila gidan Momin Sadam suka nufa saboda tace tanaso Umman Sa'eeda ta kwana biyu wurinta,haka suka ɗunguma zuwa gidansu  Momin Sadam har da su Aunty Sadiya da Aunty Sakina wato yayyin Sadam.



Sun isa gidan wurin 5:45pm na yamma,wani sabon girkin aka ɗora na dare saboda karuwan family da aka samu,sai bayan Isha'i aka zauna cikin abinci harda Kamal kasancewar ya zama ɗan gida,sai faman satan kallon Sa'eeda yake yana cin abinci,Sadam dai yana ankare da abinda Kamal yake,shi ya rasa mai yasa ya damu da Sa'eeda haka da baya ko so wani ɗa namiji ya kalle ta,haka dai suka kammala cin abin,dai suka dugunzuma zuwa falo tare da fara hirar yaushe gamo,harda Daddyn Sadam yana wurin ana hirar dashi,sai can Kamal ya kasa hakuri ya ce



"Ammm Dad nifa nayi kamu a gidan nan,Ina son Sa'eeda da aure,Dad a taimaka a bani ita"



Darammm!!! Dammm!!! Dammmm!!! Haka ƙirjin Sadam ya bada, baisan sanda ya ɗaga muryarsa cikin fushi  kowa yana jinsa yace



"Ayi mata miji!!!................... "






*Mu haɗu a pages na gama my Esteem fans🙃🙃🙃🙃✍️✍️✍️🌹🌹🌼🌼💖💖*




*To waye ne mijin da Sadam yace anyiwa Sa'eeda??? Mai yasa yake jin abu a game da Sa'eeda???*......





*To ta yaya su Baba Garba, Uncle Hassan da Umman Sa'eeda zasu fuskanci Haj. Zulfa'u jin ashe ita ce tayi sanadin ɓatan kakar Sa'eeda???*......




*Wani mataki Haj.Zulfa'u zata ɗauka ,shin zata bari su haɗu kuwa???*....



*Nusaiba dai an koma baby ana yawo da pampers,shin Umma Kande zata saduda ko kuwa har yanzu tana akan bakanta????*.....




*Kai! Kai! Kai! Abubuwa da yawa🙃🙃🙃,amsoshinku na nan tafe a pages masu zuwa,kudai  ku cigaba da zubo ruwa comments da reactions🌹🌹💖💖🌼🌼💘💘,ni kuma bazan gaji ba wurin suburbuɗo muku new updates zafafa* 🌹🌹🙃🙃💖💖🌼🌼💘💘😂🔥🔥🔥🔥🔥





*Ina ƙaunarku My Esteem Fans Lodi Lodi* 🌼🌼💖💖🌹🌹🙃🙃💘💘




Post a Comment

0 Comments