TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

👬🏻 TAGWAYE 👭🏻 10 & 11

    Episode Ten: Brave and Selfless


Last free Episode


"Please, help me. Dan Allah, ki taimaka min" Sai kuma ya cika ta a hankali ya bi jikin katangar ya fadi kasa.


Sai data ja numfashi sosai ta dawo cikin hayyacin ta sannan ta juyo tana kallonsa daga tsayen da take a kansa, sai kuma ta sunkuyo sosai tana kare masa kallo, he looked dirty and terrible. Ta kuma lura da ciwon da uake fitar da jini a wuyansa. But there is something about him, something da yake ta fincikar zuciyarta zuwa gare shi ta kuma kasa fahimtar menene, ta durkusa tana karewa fuskarsa kallo ko zata fahimci ko ta sanshi somewhere amma taga cewa bata taba ganin wannan fuskar ba. But something a zuciyarta keeps screaming "money" ta kuma rasa a ina money din yake. 


Tayi analysing situation din. Ta tuno da sautukan da suka ji a daki masu kama dana harbin bindiga, ta kuma tuno da mutanen da taji sun wuce ta kusa da gidan su kuma da alama wani suke nema, ta kalli Hassan tana tabbatar wa da kanta cewa shi ne wanda suke nema, kuma sune suka ji masa ciwon jikinsa. Amma me yasa? Waye shi su kuma su waye? Zata iya yiwuwa shi mugu ne su kuma police, za kuma ta iya yiwuwa sune mugaye shi kuma victim dinsu. " A kidnapped victim" zuciyarta ta gaya mata. Ta kalli kayan jikinsa, duk da cukurkudewar su amma ta fahimci masu tsada ne, meaning shi din mai kudi ne. 


Ta girgiza kanta tana son ta saita tunanin ta. "Uwar biyu an sace yaron nan, yaron da yayi mana interview wai ana tunanin masu garkuwa da mutane ne suka dauke shi" ta tuno da maganar Baba tun last week, dazu da yamma ma sai da taji yayi maganar "yaron nan har yanzu ba'a ganshi ba uwar biyu, dogo ne baki mai matsakaiciyar kiba da kyakkyawar fuska. Har yanzu ina ganinsa a idona. Allah ya bayyana shi" 


Ta sake kallon Hassan, he fits the description. Akwai kyakkyawar fuska kam babu laifi. She might be wrong but she is going to help him, tasan in taci nasara zata samu reward mai kyau. Bata san ta yadda zata taimaka masa ita kadai ba kuma bata son taso mutanen gidan su saboda tana son ya san ita kadai ta taimaka masa saboda yafi ganin kokarin ta sosai dan tafi samun reward mai kyau. Abinda zata yi din yana da hatsari but she is going to do it. Ruqayyah ce fa, Ruqayyah kuma bata jin tsoro.


Ta tattaba fuskarsa, ya dan bude ido yana kallon fuskarta ta cikin hasken farin wata kamar yadda itama take kallon tasa fuskar tace "zan taimaka maka. Bansan ko waye kai ba za kuma ka iya cuta ta na sani amma na fahimci kana bukatar taimako dan haka zan taimaka maka dan Allah ba dan komai ba".


Ta cire dankwalin kanta ta yaga shi gida biyu ta ninke part daya ta dora a ciwon wuyansa sannan ta daure wuyan da dayan part din. Ta taba jikinsa taji ya dauki zafi alamar zazzaɓi ya fara saukar masa. Ta rafa lissafin abin yi. A lokacin taji maganganun mutanen sun kuma dawo wa farkon layin daya yana cewa "police might be on their way. Wani zai iya reporting harbin" dayan yace "not Nigerian police. Am not leaving unguwar nan sai na mayar dashi gawa. Gida gida zamu bi. Am sure na ganshi ya shigo layin nan na tabbatar he is hiding a cikin wani gidan. Ta nan farkon layin zamu fara" ya fada yana knocking kofar gidan da yake opposite nasu da karfi yace "open this door ko mu fasa ta".


Hassan ya kamo Ruqayyah jikinsa, idonsa yana kokarin juyewa, jini yana dibansa ya sake cewa "help me please. Ki kai ni gurin Hussain" dusu dusu yake ganin ta. Ta cire hannun sa daga jikinta tana jin wani iri, ita tun da take namiji bai taba taba ta ba, ko brothers dinsu basa irin wannan wasan saboda sun samu tarbiyya mai kyau a gurin Inna ade da Baba. Ta rada masa. "Ka kwanta anan, kar kaje ko'ina. Kar kayi motsi. Ina zuwa" sai ta mike zuciyarta tana yi mata plan na abinda zata yi. Ba tare da tsoro ko shayi ko kokwanto ko kuma tunanin komai ba ta zagaya ta daya side din toilet din ta taka bucket ta kama katanga ta haura, Hassan ya bi katangar da kallo sannan ya mayar da idonsa ya rufe yana jin tunanin sa yana barin kwakwalwar sa.


Ruqayyah ta dira a bayan gidan su, tana jin kafarta tana amsawa ta dan jima har taji kafar ta saki, tana jin maganganun mutanen a daya side din gidan daga dukkan alamu an bude musu kofar gidan sun shiga. Ta ja dogon numfashi sannan ta fita a guje tamkar yar tseren gudu, dogayen ƙafafuwan ta suna taimaka mata gurin covering distance mai yawa cikin lokaci kankani taje karshen layin bayansu sannan ta zagayo kan layin su gaban gidan dayake karshe, ta durkusa tana mayar da numfashi sannan ta mike tsaye tayi gyaran murya ta bude muryarta da dukkanin karfinta ta fara ihu "wayyo Allah jama'a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah gardi a dakina. Jama'a ku taimaka min jini ne a jikinsa"! 


Ta ringa fada tana maimaita wa, daga can ta hango mutanen sun fito da sauri daga gidan da suka shiga suna hasko inda take da fitila, sai kuma taga sun taho a guje zuwa wajenta. Daya da touchlight a hannun sa dayan kuma da bindiga.


Ta yi saurin shigewa cikin wani kango yadda ba zasu ganta ba sai dai suji sautin muryarta. Tana jin sun kusa zuwa tayi shiru, taji sunzo gidan karshe suna buga kofar da karfi, mai bindigar ya ture dayan ya saka bindiga ya harbi lock din gidan, karar bindigar yana amsa amo a cikin shirun daren.



Tun harbin farko inna ade ta bude idonta, ita dama bata fiya yin nauyin bacci ba. Ta jima kwance tana tunanin anya kuwa da gaske karar bindiga taji? A lokacin ta sake jin ta biyun. Ta mike zaune tana salati, abinda da uwa, yayan ta ne suka fara fado mata a rai, matan suna cikin gida kuma dakin da suke ciki na kasa ne, an ce kuma bullet baya iya wuce katangar kasa, samarin ne take jiwa tsoro, sune suke kwana a shagon gidan makotansu tate da samari da yawa kuma ginin siminti ne kar fa bullet ya same su. 


Daga nan ne kuma taji ana bubbuga kofar gidan daya ke kallon nasu. "Open this door ko mu fasa ta" taji an fada da murya mai karfi. Ta fara jijjiga Baban biyu tana salati "baban biyu ka tashi barayi sun shigo unguwar nan, gasu can suna buga gidan Maman Minal" ya mike zaune yana salati shima yana mitstsika idonsa. A lokacin ne suka ji karar dirar mutum daga katanga. Kuma kamar katangar toilet dinsu ta baya, ko dai an hauro katangar an shigo gidan ko kuma an haura an fita. Inna ade ta mike "yan biyu na!" Ta fada cikin tashin hankali "baban biyu an shigo mana gida kar a shiga dakin yaran nan ayi musu wani abu na shiga uku" ta fada tana laluben hanyar fita daga dakin. Dama fitilar su daya a gidan kuma yaran suke bawa su su kwanta a haka. 


Baban biyu ya rike ta "tsaya anan kar ki fita, bara ni inje gurinsu" ba tare daya jira abinda xata ce ba ya wuce ta ya bude kofar dakin ya fita. A bakin kofar dakin yaga Sumayya a tsaye, idanuwanta a waje, da touchlight a hannunta amma kuma a kashe. Cikin rawar murya da karkarwar jiki tace cikin rada "Baba naji an hauro gidan nan ta bandaki kuma Ruqayyah tana bandakin" bai jira karashen maganar tata ba ya karbi fitilar hannunta ya tafi bandakin cikin sauri. Inna ade itama da kunnuwanta suka jiyo mata kalaman Sumayya ta fito da sauri daga dakin tabi bayan mijinta zuciyarta kamar zata bar kirjinta. Sumayya, ganin an barta ita kadai yasa itama ta bisu da sassarfa.


Yana shiga toilet din ya kunna fitilar hannunsa, haske ya karade bandakin tare da bayyanar masa da jinin da yake malale a gurin, yayi kokarin kare Inna ade kar ta gani, a lokacin ne kuma ya ga Hassan a kwance a kasan katanga yana numfashi da kyar. Wannan ya tabbatar masa da cewa jinin bana Ruqayyah bane ba na wannan mutumin ne. Amma ina Ruqayyah?


A lokacin ne suka jiyo ihu


"wayyo Allah jama'a ku taimaka min ga wani ya shigo min daki. Wayyo Allah gardi a dakina. Jama'a ku taimaka min jini ne a jikinsa"!


Ko daga bacci aka tashe su sun san muryar Ruqayyah ce. Inna Ade tace "Ruqayyah! Baban biyu wannan ai muryar Ruqayyah ce. Daga ina take wannan ihu? Yaushe ta fita daga gidan nan?" Baban biyu ya shige ciki yana tallafo fuskar Hassan, kallo daya yayi masa ya gane shi, ya kuma gane dankwalin Ruqayyah da yake daure a wuyansa. A take ya fara guessing abinda yake faruwa. Amma kuma hankalin sa ya tashi saboda fahimtar hadarin da Ruqayyah take ciki. 


Hassan ya bude ido a hankali yana kallon baban biyu, cikin magagin ciwo yace "Hussain? Ku kaini gurin Hussain" shima kuma yaji muryar da take ihun daya cika gabaki dayan unguwar. Yaji kamar yasan muryar, kamar muryar wacce tace zata taimaka masa, wacce ta haura katanga saboda shi, saboda Allah tace zata taimaka masa ba dan komai ba. Ya fahimci mai take cewa a ihun nata kuma ya gane mai take yi, tana kiran mutanen da suke nemansa ne away from him and toward her, tana jawo danger away from him and unto herself. So selfless, so brave. 


A lokacin suka ji mutanen da suka shiga makota suna nemansa sun fito da gudu sun tafi inda take ihun. Hassan ya runtse idonsa, Inna Ade ta saka kuka "wayyo Allah na, wayyo 'yata". Sai suka ji ta daina ihun, sannan kuma suka ji karar harbin bindiga, karar data cika unguwar baki daya. 


Sumayya ta kwalla kara "Hassana!!!" Hassan ya maimaita a hankali "Hassana!" Yaji sunan ya zarce zuciyarsa ya zauna a gurin da wani abu bai taba zama ba. Sunan mahaifiyarsa ne, sannan kuma female version of his own name. Ya tuno fuskarta sanda ta durkusa tama daure masa ciwonsa. So Young, so beautiful, so brave, so selfless. Sai yaji a ransa cewa zai iya bayar da tasa rayuwar saboda ita, me yasa ya gudu har ya shigo gidan nan ya saka yarinyar nan in danger? Me yasa bai tsaya kawai mutanen can sun harbe shi kowa ya huta ba? Ya fara addu'a a hankali "ya Allah indai wani zai mutu Allah ka dauki raina ka bar yarinyar nan. Allah ya bani dama da kuma ikon kwatanta sakawa yarinyar nan da kwatankwacin abinda tayi gare ni. Allah ka .........." 


A lokacin suka ji jiniyar police ta cika unguwar, sai kuma harbe harben bindiga ya biyo baya. Sannan kuma shiru. Shiru except for kukan Sumayya da Inna. Sai kuma kamar daga sama suka ganta ta durgo daga katanga. Duk suka juya suna kallonta ita ma tana kallonsu. "Hassana?" Baban ya fada. "Hassana" Hassan ya maimaita yana mika mata hannunsa kamar mai kiranta zuwa gare shi. Ta taho straight ta durkusa a gabansa tace "it is okay, yan sanda sun kama su. It is over"


*************************************************************************************************


Hassan ya sauke idonsa daga kallon agogon daya kafawa ido kusan mintina ashirin da suka wuce, ya gaji da kallon kofar ya koma kallon agogo kuma zuciyarsa tana bugawa tare da kowanne bugu na hannun agogon. It is already after 3am. Tun 1am yake zaune a guri daya yana jiran shigowar Hassan kamar yadda kidnappers din suka yi mishi alkawari "zai zo gida da ƙafafuwan sa" they said, but he was a fool to believe them. Ta ya akayi ma ya yarda da maganar barayi? Barayin ma na mutane.


Ya cire hular sa ya ajiye a gefe, duk ta dame shi ciwo take sakawa kansa yana yi. Ya cire agogon hannun sa shima yayi jifa dashi, ji yake komai ya fita daga ransa dan uwansa yake so ya gani, gabansa faduwa yake yi, ji yake kamar ya dora hannu aka yayi ta rusa kuka amma kuma sai ya tuna da cewa shi fa Hussain ne. Jarumi ne shi.


Sanyi yaji ya fara ratsa shi, irin sanyin da yake kadawa idan assuba ta gabato. Ya lumshe idonsa sai yaji wani ruwa ya zubo daga idon nasa zuwa kan kuncinsa. Yayi sauri ya goge. Ba zai iya tuna ranar da ya taba yin kuka ba. But he can't take it anymore. He just can't allow himself to think, baya son yayi imagining wani abu ya faru da danuwansa, yayi komai da suke bukata ya cire police ya kai musu kudi shi kadai yayi isolating kansa duk a banza? For the first time in his life da yayi abu with care kuma shine zaiyi failing?


Wayarsa tayi kara a gefensa, ya juya slowly yana kallon screen din "commissioner of police" ya gani. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ya fada ya sake fada, sai da kiran ya katse wani ya sake shigowa sannan ya dauka. Bai iya yin magana ba. Commissioner yace "yalllabai albishir nazo dashi. Mun samo Hassan" ya fada muryar sa cike da farin ciki. 


Wani sanyi ne ya taso daga kafafuwan sa ya dire har kansa. Sannan kuma wani dumi mai dadi ya ratsa zuciyarsa da kwakwalwar sa ya fara saisaita masa tunanin sa. Ya mike tsaye "a ina? Yana ina? Lafiyar sa kalau? Is he okay?" Ya jera tambayoyin da suka saka commissioner din yin murmushi sannan yace cikin kwantacciyar murya "dan uwanka yana raye, kuma alhamdulillah mun samu nasarar kama barayinsa, sannan mun karbo maka kudinka daga hannun su" cikin zakuwa Hussain yace "bar maganar barayi da kudi, ina Hassan yake?" Commissioner yace "muna asibiti yanzu tare dashi. An shiga dashi theater room" Hussain yace "asibiti kuma, wani abin ya same shi ne?" Commissioner yace "a'a, kawai dai ya danji ciwo ne kadan, but it is not that serious. Na kira kane saboda nasan zaka so a fito dashi kana gurin, shima kuma nasan zai so yana fitowa ya ganka" Hussain yayi murmushi, rabon da yayi murmushi tun sayi daya daya wuce "na gane. Nagode. Gani nan zuwa". 


Ya ajiye wayar yayi kamar zai je dakinsa sai kuma ya fasa ya koma dakin Hassan ya dauko key din mota ya fito ya dauki hularsa ya fita da sauri, har yaje gaban mota kuma sai ya koma cikin gidan da sauri ya hau saman Aunty yana bin kofofin kannensa yana knocking cikin sigar kida, kudan duk a tare suka fito tunda ba wani dogon bacci suke samun yi ba. Fuskarsa kawai suka kalla suka rude da ihun murna, gabaki daya suka rungume shi shima ya bisu daya bayan daya yana rungume wa. 


Aunty ta fito tana kallonsu, sannan ta daga hannunta sama tace "alhamdulillah. Allah mun gode maka".


Sanda aka fito da Hassan, duk family dinsa suna bakin kofa suna jira amma shi bacci yake saboda allurar baccin da akayi masa. Wuyansa a nade da bandage, kafarsa ma haka. Aunty ta fara sharar hawaye, Hussain yana kallon doctor yace "akace min minor ne ciwon, menene haka?" Doctor yayi murmushi yace "ba wani abu yallabai, bawai ciwon bane yasa kuka ganshi haka wahalarda yasa ne, daya kwana biyu zai warware, harbinsa akayi a wuya amma bullet din bai shiga ba gogar gurin kawai yayi. Kafarsa kuma targade ne sai kuma ciwo da yaji a kafar itama. Duk it has all been taken care of".


Da kyar Hussain ya iya sakin hannun Hassan yaje yayi sallah, yana dawowa ya koma ya zauna ya cigaba da rikon hannun. Sauran yanuwan a zagaye dasu. A haka Hassan ya farka ya gansu. 


Daya bayan daya yake binsu da kallo, duk suma suna kallon sa da murmushi a fuskokin su har ya iso kan Hussain. Ya lira da yadda yayi baki ya rame, ya danyi masa murmushi yace "hello bro" Hussain yace "hi bro. Welcome back" Hassan yace "na dawo gida, amma kafin in dawo na samo matar aure a inda naje" duk suka bude ido suna kallonsa cikin mamaki. Hussain yace "matar aure kuma?" Safiyyah tace "tare aka kama ku?" Khadijah tace "a ina take?" Nafisa tace "ya kamannin ta suke" Zulaihat tace "yaya sunanta?" 


Yayi murmushi yana kokarin mike wa zaune yace "no ba tare aka kama mu ba, a can dai unguwar take, she is the most beautiful, brave, and selfless person I have ever met" ya juya yana kallon Hussain yace "sunanta Hassana and she saved my life".



Anan muka kawo karshen free Episodes na littafin tagwaye. Anan ne kuma muka fara labarin. Wannan tafiyar ba irin sauran ba ce ba, wannan tafiyar da zafi muka debo ta.


Ga dai Hassan da hassanar sa (Ruqayyah, Rukee) ga kuma Hussain da gimbiyar sa, sannan ga Sumayya a gefe. 

Shin yaya wannan tafiyar zata kasance?

Shin cikin wadannan su wanene iyayen Amir?

Shin menene ya faru har Amir ya samu kansa a yashe a kofar gidan marayu?

Wacece matar data kira Amir zata bashi labarin iyayensa kuma menene alakar sa da ita?

Yaya zata kare tsakanin su?


Zaku samu amsar wadannan tambayoyin in kuka turo kudinku ₦300 ta account 

First Bank

Account Name : Alhassan Musa Sadiq

Account Number : 3189669587 


Sai su turo shaidar transaction din ta hanyar WhatsApp zuwa wannan layin

09135803002 


Wadanda basu da account zasu turo katin MTN na ₦300 zuwa wannan layin

09135803002 


Nagode, sai na jiku.



Episode Eleven : The two sides of a coin


Hussain ya kama Hassan yana mayar da shi kwance, yana cewa "wannan Hassana ba dan sunan ta ba da na fara kishi da ita tun yanzu" Hassan ya runtse idanunsa cikin nuna jin zafin ciwon wuyansa yace "ba zata kula ka ba, komai neman maganar ka ba zata kula ka ba. Ita kamilalliyar yarinya ce" Hassan ya nade hannayensa a kirjinsa yana bata rai yace "me kake nufi da kamilalliyar yarinya ce? To waye kuma ba kamilallen ba?" Aunty ta matso tana dariya tace "zaku fara ko? Hussain sai kace ba kai bane mai kuka kana neman Hassan ba shine daga dawowarsa zaku fara musu. Ni na dauka in ya dawo ba zaku kara rigima ba" duk suka yi murmushi Hussain yace "ban fa yi kuka ba Aunty, kar ki sa ya raina ni mana. Kawai dai ina mamakin yadda mutum zai shiga irin halin da ya shiga sannan the very first thing da zai fada bayan ya dawo hayyacin sa shine wai ya samu mata" ya karasa maganar yana rike baki "mata fa? Hassan din? Ni na dauka duk macen da Hassan zai kira da mata sai tayi passing through different stages na gwaji. Ko guda daya ta fadi kuwa to an cire ta a list amma wannan cikin dare daya har tayi passing? Ni nafi tunanin zafin ciwo ne ya saka shi wannan maganar" Hassan yana daga kwance ya harare shi yace "ko kakan zafin ciwo ba. Nasan abinda nake yi kuma nasan duk mutumin da zai saka rayuwarsa on the line to save someone da bai taba gani ba a rayuwarsa to kuwa tabbas dole a kira shi dukkanin suna na gari da yake available. Like I said, she saved me. Nasan Allah ne mai raya wa kuma na yarda Allah ne yasa ka zan ga yau, zan ganku, amma through Hassana taimakon Allah yazo min. Don't you think this means something?" 


Aunty tayi replacing kujerar da Hussain ya tashi daga kai tace "ban san yarinyar da kake magana akanta ba, amma na san ka Hassan, nasan kuma duk abinda ka zaba kuma har ka yaba dashi to kuwa abu ne mai kyau. Dan haka bani da kokwanto cewa duk sanda naga yarinyar nan nima zan yaba da ita"


Hussain ya kalli agogon sa yace "don't stress yourself da tunani, rest, ka koma baccinka. Ni zan je gurin police suna ta jirana tun dazu suna so suyi briefing dina akan case din. In ma dawo kuma zan samu doctor muyi maganar fitar da kai waje dan kafi samun cikakkiyar kulawa" daga haka ya bar dakin. Zuciyarsa tana cike da farin cikin dawowar danuwansa amma kuma bai san dalilin da yasa yaji hankalin sa bai kwant da maganar da dan'uwan nasa ya dawo da ita ba.


A gurin police ne ya kuma samu wani shock din, shock din ganin Salisu a zaune a kasa duk rigarsa jini, kafadarsa daya a nannade da bandage. Yana ganinsa yace "Salisu? Me kake yi anan? Ciwon menene kaji haka a hannunka? Salisu ya sunkuyar da kansa kasaya kasa dago kai su haɗa ido. Hussain ya kalli dan sandan da yake wajen yace "me yake yi anan gurin ga kuma ciwo nan a jikinsa? accident yayi? A kaishi asibiti mana" police din ya saka kafa ya daki Salisu a bayansa yace "juya ka bashi labarin a inda kaji ciwon jikinka?" Salisu ya sake dunkule wa guri daya sam ya kasa dago kansa. Hussain ya rike dan sandan da sauri "ya zaka dake shi, ga ciwo a jikinsa ga kuma duka? Wanne irin police ne kai?" A lokacin commissioner ya fito, suka zazzauna shi da Hussain suka gaisa ya kuma taya Hussain murnar warwarewar lamura sannan yace "ka san wancan yaron?" Ya fada yana nuna Salisu, Hussain ya hadiye abinda yaki tafiya a makwogwaron sa saboda fara fahimtar inda maganar ta dosada yayi. Yace "yaron mune, a gidan mu aka haife shi a gidan mu ya taso, a hannun mu yayi karatunsa, a yanzu haka mahaifiyar sa tana cikin gidan mu tana shirya mana abinda zamu bukata in muka koma gida" commissioner ya girgiza kansa yace "am sorry to inform you cewa shine mastermind na wannan kidnapping din" Hussain ya mike da sauri kamar wanda aka yi wa allura, Salisu ya fara kuka yana rarrafe ya rike kafar Hussain "oga Hussain dan Allah kayi min rai kayi hakuri, wallahi sharrin shaidan ne oga Hussain, nayi nadama ba zan sake ba. Ba hali na bane ba ka sani sharrin shaidan ne" Hussain ya saka kafa ya doke shi tare da ja da baya kamar wanda yake gudun ya sake taba shi yace "sharrin shaidan? Salisu? Wannan shine sakayyar soyayyar da muke yi maka ni da danuwana? Wannan itace muguntar da zaka saka alkhairin mu da shi? Dama yanzu duniya har ta kai wannan lalacewar Salisu? Dama yanzu har dan Adam bai mayar da saka alkhairi da mugunta komai ba a duniya? Dama yanzu duniya ta zama babu wanda zaka yarda dashi komai kuwa kyautatawar ka gare shi? Shikenan komai dan adam ya aikata sai ya kira shi da sharrin shaidan. To auzubillahi minash shaidanir rajim. A yanzu mutane sune shaidanun kansu basa bukatar taimakon wani shaidan wajen aikata ta'asa" commissioner ya jashi ya zaunar dashi a kujera yana bashi hakuri. Hussain ya sake cewa "Hassan fa, rayuwar Hassan yayi wasada ita, har harbin Hassan fa akayi ba dan yana da sauran kwana ba da yanzu mun dawo daga sutturar sa" Salisu yace "wallahi oga Hussain bansan zasu cutar dashi ba. Alkawari suka yi min cewaba zasu cutar dashi ba. Nayi kokarin hana su cutar dashi shine suka harbe ni su suka yi min wannan harbin sannan suka bishi" commissioner yace "kadan ma kenan, dama ai karshen irinku kenan. Wadannan mutanen sun saba kashe mutane akan kudin da bai kai wannan yawa ba ma. Ko ba dan ka shiga tsakaninsu da Hassan ba dama kashe ka zasuyi su raba kuɗin a tsakanin su. Kai da tunani kake xasu baka? Kuma su barka da raj ayi tracing dinka ka tona musu asiri? Ai anyi irinka da yawa kuma basu kai labari ba" Hussain ya mike yana cewa "babu hannuna a cikin case dinka Salisu, ban sanka ba daga yau, danuwana ma bai san ka ba. Ko an sallame ka kar kabi koda hanyar gidan mu ce. Babu mu babu kai har abada" Salisu ya fara kuka wiwi yana bada hakuri, commissioner yace "ballantana ma ba za'a sake shi din ba, za'a hada shi da sauran a tura su court a yanke musu hukunci dai dai da laifin su".


Da wannan Hussain ya bar Salisu. Bayan cike ciken takardu da yayi da kuma sauran abubuwa sai ga kudinsa an dawo masa dasu cif ko kwandala bata yi ciwo ba. A ciki ya fitar ya bawa police kaso mai tsokar da yasa duk sai da suka ji sun kasa rufe bakunansu saboda murna, sannan kuma yayi alƙawarin biyan hospital bill din police guda daya daya samu rauni.


A hanyarsa ta komawa asibiti ya kira gimbiya ya gaya mata duk halin da ake ciki, tun daga muryarta ya fahimci cewa tana cikin farin ciki sosai. Shima sai yaji duk damuwar da take ransa tana wucewa tana tafiya tare da sautin dariyarta. Yayi dariyar shima. Tace "kasan wani abu? This is the first time da naji kayi dariya tun ranar da aka dauki Hassan. Lallai ba karamin so kake yiwa Hassan ba, Allah ya bani, ko ince ya bamu ni da matar da Hassan zai aura ikon cigaba da karfafa kaunar da take tsakanin ku" sai yace "kinsan kuwa daga farkawar sa har ya fara xancen aure? Wai ya hadu da wata yarinya ta taimaka masa kuma wai ita zai aura" Fatima tayi dariya tace "anya kuwa Hassan din mu ne ba'ayi mana chanji a can ba? This is something that you would do, not him" yayi dariya yace "nima abinda nace masa kenan. Mr Careful is now not being careful" tace "amma nasan ai ba wai direct kawai za'ayi auren ba. Nasan zasu samu time together su dan fahimci junan su kadan. Hey! Why not a haɗa da namu kawai ayi tare?" Ya danyi tsaki yace "ke ma kin fara biye masa kenan ko? Ni kuma na rasa dalili nine yau nake zama Careful din akan maganar" tace "what happened to the Hussain I know, the Hussain that just go with the beating of the drum, relax and chill" 


A asibiti ya tarar Hassan ya kuma tashi, har Aunty ta na bashi abinci a baki yana ci. Ya leka bowl din hannunta yaga fruit salad ne yace "kai da zaka ci abincin da zai saka ka ciko ka mayar da jikinka ina kai ina fruits?" Aunty tace "a yanzu ai lafiya yake nema ba wai kiba ba, yana bukatar alot of vitamin c" Hussain ya shafa kafadar Hassan da fatar duk ta fara yamushe wa yace "and alot of meat. Me suke baka ne a wajen?" Hassan ya doke hannunsa yana hararar sa yace "what I need is a deep bath, in na gaya maka rabona da wanka sai kayi dariya dan haka ba zan gaya maka ba" Hussain ya toshe hanci yace "shi yasa atmosphere din dakin take chocking mutane".


Hussain da kansa ya hada wa Hassan ruwan wanka sannan kuma ya taimaka masa yayi wankan yadda ruwa ba zai taba sannan suka fito ya kuma taimaka masa gurin shiryawa a tsanake ya saka kayan da Safiyya taje gida ta dauko masa. Sannan suka kuma saka shi ya sake cin abinci duk da cewa da kyar yake hadiya saboda yuwansa yana yi masa ciwo sosai. 


Hassan yace "ina fita daga nan zan fara shirya mana tafiya waje, gwara muje can a duba ka sosai" Hassan yace "ni da zaka bi ta tawa da ka bar maganar tafiyar nan. Babu abinda doctors din mu nan nan ba zasu iya bafa, wadansu daga cikin su fa su suke aiki a can din" Hussain yayi murmushi cikin rada yace "ai ba dan asibiti nake so mu fita ba, dan ka samu ka huta ne sosai. Anan yan dubiya da yan jaje ba zasu barka ka huta ba" Aunty ta dago kai daga zubawa Khadijah abinci tace "me kake cewa?" Ya shafa kansa Yace "babu komai Aunty, cewa nayi abincin yayi dadi sosai".


Daga baya ne Hassan ya basu labarin duk yadda lamarin ya kasance, briefly ya gaya musu irin zaman da yayi a hannun kidnappers din da kuma yadda suka yi jiya. Hankalin Aunty ya tashi jin Salisu ne a ciki, yammatan suka fara masifar sai sunci ubansa, Hussain yace "wanne uban nasa zaku ci bayan ubansa yana lahira? Shi kuma yana police station daga can za'a kai sji court sannan a wuce dashi prison, me zakuyi masa wanda Allah bai riga yayi masa ba? Daga nan Hassan ya basu labarin haduwarsu da Ruqayyah da yadda ta saka rayuwarta a cikin hatsari dan ta taimaka masa. Duk jikinsu yayi sanyi sosai, suka kuma jinjinawa kokarin ta. Aunty tace "tabbas alamu sun nuna cewa yarinyar ta kirki ce, tunda bata san ko kai waye ba, zata iya kasancewa kai mugu ne da zaka iya cutar da ita ko ahalin gidansu. Wannan shine taimako na gaskiya, ka taimaka wa wanda baka da tabbas din shi zai taimaka maka" Hassan ya gyada kai yace "tabbas, tunda ba sani na tayi ba ballantana muce tayi ne dan ta samu wani abu a gurin mu" duk sauran suka amince amma banda Hussain, har yanzu maganar bata kwanta masa na, yace "tunda naji kace talakawa ne sosai ina ganin abinda za'a yi in mun dawo sai a kira babanta a samu wani abu mai kyau a bashi, yadda zai samu jari, ko kuma ita a bata scholarship tayi karatu" Hassan ya girgiza kansa yace "ba haka za'a yi ba, aurenta zanyi, sometimes money is not always the solution, kudi in muka basu zasu iya karewa amma aure, hada jini, babu yadda za'a dawo dashi baya" 


Hussain yace "exactly my point, babu yadda za'a yi undoing aure, ko an rabu tambarin yana nan, shi yasa ya kamata ayi dogon tunani da dogon nazari kafin ayi shi. What if suna da wani aibu, wani ciwo ko wani tambari marar goguwa? What if da akwai wani hidding halinta ko na iyayenta wanda ba'a sani ba? What if a cikin rescue mission din nata akwai wata hidding agenda da bamu sani ba?"


Hassan yace "shi yasa nace zan aureta, ni Hassan, bance Hussain ya aure ta na. Ko ma menene a tare da ita it will be my burden not yours" 


Suka tsaya suna kallon kallo


Aunty tayi tagumi tace "zaku tsaya in yi magana ne ko kuma ba kwa bukatar jin ta bakina? Yanzu ku shirya ku tafi inda zaku je ku huta din kar a dame ku. Kafin ku dawo zan nemi gidan inje da kaina inyi musu godiya daga nan zan ga yarinyar zan kuma ga iyayenta, sannan zan san abinda za'a yi musu" ta juya tana kallon Hussain tace "su kuma wadanda baka son su zo su dami dan uwanka yanzu zanyi musu yawa su zo su ganshi, tunda ya bata suke garin nan kuma babu yadda za'a yi ace an ganshi kuma har ya bar kasar ba tare da sun ganshi ba. Daga nan ta dauki waya ta fara sanar wa da jama'a, kafin laasar Asibitin ya cika da yan dubiya da jaje.


Washegari gimbiya tazo da safe, bayan ta duba Hassan ta kuma zuba masa lafiyayyen girkin data shiryo masa tun daga kano wanda duk masu ruwa ruwa ne yadda zai ji dadin hadiya, duk kamewar Hassan sai daya yaba mata da girkinta sannan yayi mata godiya. Daga nan sai suka fita ita da Hussain tana tayashi shirye-shiryen tafiyar su shida Hassan. Sai da suka gama komai sannan ya kaita airport shi kuma ya koma gida.



Two Day's Later


Ranar Monday, kwana daya da tafiyar Hassan da Hussain India inda Hassan zai ga likita kuma zai samu ya huta sosai. A ranar ne su kuma su Ruqayyah bayan sun taso daga makaranta as usual Ruqayyah ta fito daga taxin tana mita. "Allah kaɗai ne yasan irin gajiyar da nayi wallahi. Yunwar da nake ji kuwa ina jin zan iya cinye abincin da akayi a gidan mu gabaki daya" Sumayya ta fara kokarin fitowa tana kuma zaro Naira dari a aljihun rigarta. Ta juya tana mikawa drivern sai taji yace "ki bata, ta sayi awara ta kara akan abincin dan ya ishe ta" tayi dariya yayin da Ruqayyah ta juyo da niyyar juye wa mai maganar kwandon bala'i, suka yi ido huɗu da drivern ranar nan. Ta bude ido tare da cewa "kutumelesi! Dama motar ka muka shigo?" Ya daga kafada kawai yana murmushi, ta juya gurin Sumayya da take dariya tace "da haɗin bakin ki muka shigo motar sa ko? Ya akayi ban gani ba?" Sumayya tace "nima sai da muka shiga sannan naga shine, nayi kokarin nuna miki ke kuma kina can kina yiwa yarinyar data taka miki kafa bala'i dan haka na rabu dake kawai" Ruqayyah ta kalle shi taga har yanzu murmushi yake yi sai taji tamkar ta kama kyakkyawar fuskarsa ta goga ta akan kwalta. Ta juya ta bar gurin tana maganganu kanana kanana. 


Adam yace da Sumayya "sister dinki drama queen ce" ta gyada kai tace "sosai. But she is not as bad as she always acts" yace "Allah yasa, dan nasan ke kullum tare mata zaki ke yi, kullum kina side dinta ko?" Ta sake gyada kai tace "yes, bayan Inna da Baba bani da wanda ya kaita. Komai zafinta dole ita din tawa ce, she is a side of me that I can never get rid of. In babu ita to babu ni kuma ba zan........." Ya daga mata hannu "bla bla bla. Naji, amma nasan kinsan cewa bata da kirki, wannan side of her din kinsan dashi fiye da kowa" ta fito daga mitar tana kara mika masa kuɗin hannunta "ga kudin ka Adam. Mun gode" ya jefa mata murmushi "ki siya wa sister dinki awara, tunda ta riga ta gama debe wa abincin gidan ku albarka ko zata cinye ba zata ko shi ba" ta rufe masa kofar sannan ta jefa masa kuɗin ta window ta juya tabi bayan Ruqayyah ba tare data kuma cewa komai ba. Ta sani, tabbas tasan Ruqayyah bata da kirki amma kuma it hurts her in taji wani ya fada, kullum tana wa Ruqayyah addu'a, kuma bata taba barin tayi wani abu marar kyau ba tare data yi kokarin gyara mata ba. Kuma sosai tana ganin gyaran, gashi nan ta fara chanzawa, gashi nan ranar nan har ta kusa rasa rayuwarta saboda taimakon wani Allah. 


Ta tarar da Ruqayyah tana kokarin shan kwana, har yanzu mita take yi amma kuma daga dukkan alamu ba wai mitar mai taxi take yi ba kuma, mitar wani abun ne na daban.


"Mutane yanzu basu san a kyautata musu ba, shi yasa taimako yake da wahala, in ka taimaka ma babu abinda zaka samu" Sumayya ta kalle ta tana girgiza kant cikin takaici tace "shi taimako in dai kayi shi dan Allah ai baka bukatar komai daga gurin wanda ka taimaka wa" Ruqayyah tace "ko godiya? At least dai ai yazo yace min thank you for saving my life ko?" Sumayya tace "Rukee kenan. Kina kallon dai yadda aka fitar dashi daga gidan mu cikin jini, na tabbatar asibiti za'a wuce dashi kuma na tabbatar har yanzu yana asibitin, bai kamata ace har kin fara mita ba, kuma ai yayi miki godiya tun kafin ya bar gidan mu" Ruqayyah tace "wacce godiya yayi min? Ni me yace min ma in banda kira kamar tsohon makaho, 'Hassana" ta fada cikin kwaikwayon muryar Hassan, Sumayya tayi dariya ita kuma tayi tsaki, "bai san yadda na tsani a ce min Hassana ba, Baba ne kawai yake fada shima kuma dan babu yadda zanyi dashi ne".


A lokacin suka sha kwanar gidan nasu, abinda suka gani a kofar gidan ya saka su taka burki cikin mamaki, suka rike hannun juna, Sumayya ta rada wa Ruqayyah "ga mutumin naki nan yazo godiyar" Ruqayyah tace "ni Companyn sa nake so ya bani daya".


Manyan motoci ne guda biyu a kofar gidan, irin motocin da ba a kan kowanne titi su Ruqayyah suke ganin irin su ba. Ga kuma wadansu bakaken mutane masu bakaken kaya da bakaken tabarau a tsaye a gaban motocin, twins din suka rakube suka wuce su suka shiga gidan suna masu hada baki gurin yin sallama.


Babbar tabarma ce wadda Ruqayyah ta tabbatar aro wa aka yi daga gidan su Minal a shimfide a tsakar gidan, akan ta akwai wata mata wadda idan gaskiya za'a bi zata iya girmar Inna ade amma a kamanni zata iya cewa Inna ade ta haife ta. Kana ganinta kasan cewa naira ta zauna mata. A tare da ita akwai yammata, su biyar reras, wadansu farare wasu bakake. A gaban su da tray shima da aka aro a gidan su Minal aka siyo pure water mai sanyi guda goma aka zuba akai. 


Daga gefen su karamar tabarma ce wadda tasu ce ta gida, akanta Baba ne tare da Inna Ade fuskokin su dauke da faffadan murmushi. Gabaki daya jama'ar gurin suka amsa musu sallamar. Inna Ade tace "yauwa, gasu nan ma sun dawo" Aunty tana kallon yan biyun da suke karasa shigowa tsakar gidan tace "tubarkallah masha Allah, ashe suma yan biyu ne?" Inna Ade ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Hassana tace "Kai! Amma fa kyawawa ne, wacece takwarar tawa?" Inna Ade ta dago tana kallon ta tace "kuma yan biyu ne?" Hassana tace "a'a, ni suna kawai naci, yayyen mu maza ne dai yan biyun. Shi wanda kuka taimaka shine Hassan, akwai hussainin sa".


Daga dan nesa su Ruqayyah suka durkusa suna gaishe da bakin. Duk suka amsa da fara'ar su. Aunty ta miko hannunta, ku zo kusa dani ku zauna kunji yayan albarka? Wacece hassanar a cikin ku?" Da sauri Sumayya ta nuna Ruqayyah itama Ruqayyah ta nuna Sumayya. Duk aka kwashe da dariya. Inna Ade tace "Ruqayyah ki amsa mana anayi miki magana" Ruqayyah ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da tsinke a kasa tace "na'am" Aunty ta taso da kanta tazo har gabanta ta ruko hannunta tace "zuwa nayi har gida inyi miki godiya Ruqayyah. Nagode Nagode Nagode, Allah ya biya ki da gidan aljanna" duk sukace ameen banda Ruqayyah da take murmushi kasa kasa tana boye fuskarta.


Aunty tace "Allah yasa wannan abu daya faru ya zama silar zumunci a tsakanin mu daku zumunci na har abada. Dan mu kam abinda kukayi mana ba zamu iya biyan ku ba, bamu da kudin da zamu iya biyan ku fatan da zamuyi kawai shine mu hada jini daku idan kun amince. Shine kadai sakayya".


Bayan baƙin sun tafi, Inna da Baba sun tafi rakasu mota su kuma su Ruqayyah sun shiga daki suna cire uniform dinsu sai Ruqayyah ta daga labule tana leken waje tace "ni banga ana shigo da kwalayen ba" Sumayya ta ce "wadanna kwalaye kuma?" Ruqayyah tace "kina nufin wai hannu rabbana suka zo mana gida? Sai pure water din mu da suka shanye?" Sumayya tace "ho! Rukee. Wai duk bayanin matar nan baki fahimta ba?" Ruqayyah ta saki labulen tana kallon ta tace "wanne bayani fa? Ni ban fiye gane dogon bayani ba nafi son in ga aiki a aikace" Sumayya tazo ta kama hannun ta tace "ni abinda na fahimta daga bayanin ta shine kamar tana neman aure ne a gidan nan. Kamar tana nema wa wannan mutumin da naji sun kira da Hassan auren ki".


Ruqayyah ta saki hannunta tana kallonta dalala da baki cikin mamaki, she never thought it possible, ta dauka yana da aure sannan da jerin manyan yammatan da suke rushing a kansa, bata taba tunanin mutane irin su zasu nemi hada zuri'a da irinta ba shi yasa dam bata gane bayanin ba. Ita jira kawai take taga an miko.


Sai ta kama rawa tana juyi a dan karamin dakin nasu, Sumayya tana dariya cikin taya yaruwarta farin ciki. Har sai da hajijiy ata kama Ruqayyah ta fada kan katifar su tana birgima. Sumayya tazo tana janye kayan shanyar su data debo tana cewa "ni daga mana kaya kar kiyi masu squeezing ki kara min wahalar guga" Ruqayyah ta jawo ta ta fado jikinta tana cewa "ke ta guga kike yi? Yar uwarki zata zama matar CEO na H and H amm kina damun kanki da guga?" Sumayya ta mike zaune tana dariya tace "zata zama kika ce, ba wai ta zama ba. In banyi gugar ba ai ba zaki samu kayan sakawa ba in CEO din yazo ganin ki" Ruqayyah ta mike tsaye tana kallon kanta, ta dauko mudubi ta kalli fuskarta sannan ta ajiye tana cewa "farko aiki zan saka shi ya fara bawa Baba, Babban aiki irin wanda hatta yan Zariya sai sun san yarsa tayi babban kamu. Sannan sai in saka ya rushe gidan nan ya gina mana wani, irin gidan Alhaji Kabiru sabon kudi wanda aka saka tiles har a jikin bango. Kuma ginin hawa uku nake so, kasa su Zunnur ne zasu zauna tare da abokansu da suke kwana tare a shagon Bala, hawana biyu kuma inna ade da Baba, hawa na uku ni da Sumayya, sai im saka ayi min personal balcony a can sama inda zan ke hawa ni kadai ina kallon kowa a kasa na, ina kallon duk unguwar nan a kasa na, ina kallon kaduna a kasa na. And that, will only be the beginning"

Post a Comment

0 Comments