TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 31

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718



*_31_*




.........Sai ƙarfe goma da wani abu Fadwa ta baro sashen Shareff, dan tun a daren jiya ta lallashi abunta ya sakko duk da dai yaƙi sakin fuska har yanzun. Amma da yake maza su babu ta ido wani lokacin duk da tsuke-tsuken fuskar tasa hakan bai hanashi ya biye mata ba ya sake murjeta san ransa a daren da safiya ma. Duk kewar kwanakin da sukai ba tare da juna ba sai da ya fanshe kayansa da fatan ALLAH yasa ya samar da madadin abinda ya rasa na tayin cikinsa. A gefe kuma magungunan mata da tasha su Mamah suka ɗura mata sumane suka sake susutar da shi ya kasa kauda mata ido.

       Ta samu mai-aikinta harta kammaa gyara ko'ina, almajirin ma dake zuwa ya share tsakar gidan har yayi ya gama abinsa ya tafi, dama da sassafe yake zuwa shi. Ɗan motsin da taji a kitchen ya sakata leƙawa. Mai aiki ce keta gyaran kitchen ɗin. Cikin girmamawa ta gaisheta, ta amsa mata sama-sama da tambayarta mita musu na kalaci.

       “Hajiya ai baki faɗi komi za'ayiba, shiyyasa sai na dafa shayi kawai na soya ƙwai”.

   Tsaki taja da buɗe kular da ƙwan ke ciki. Sai kuma ta juyo tana kallon mai aiki. “Wannan ai shirme ne, Soulmate bazaici ƙwai kawai ba. Ita Ayshan yau wani saban salo ne ya hanata fitowa kuyi breakfast ɗin tare?”.

        “Wlhy hajiya ban saniba, badai ta fito ba har yanzu. Itama waccan ɗin yau banga fitowarta ba”.

   Ɗan tsaki taja ta wuce store. Ta ƙwala mata kira da sauri ta sameta, “Ki soya Irish, kuma ban san shirme karki cika masa gishiri. Sai ki ɗumama farfesun jiya dabai ciba zanje nayi wanka”. 

     “To hajiya”.

Fita tai batare data tanka mata ba. Itako ta bita da harara tana ƙunƙuni duk da kuwa ta girmi Fadwa nesa ba kusa ba. Shigewarta babu jimawa Aysha ta fito, kitchen ta nufa kanta tsaye mamakin da gaske Anam ta wuce gida na cinta, dan yanzu tai kiran wayarta Husnah ta ɗaga tace barci takeyi. Suka gaisa da iya cikin girmama juna. 

      “Maman Abu yau duk mun makara kenan ba'ai breakfast da wuri ba ko?”.

    “A'a tun ɗazun na dafa shayi aka soya ƙwai, amma hajiya tace a sauyawa Alhaji bazaici ba”. Cikin ɗan waro ido waje Aysha tace, “Kina nufin Yaya bai karyaba har yanzu? Sha ɗaya saura fa”.

    “Eh ai yanzu hajiyar ta dawo daga wajensa ma”.      

   “Lallai ma Aunty Fadwa, shine ita bazata zauna ta haɗa masaba kuma ta bar miki. Na kula har yanzu bata gama sanin wanene Yaya ba.”

          “Maman Abu dai batace komai ba, dan ita kanta yau ta jinjina wautar Fadwa ɗin duk da tun jiya take mamaki akan duk abinda ya faru. A yanda ta santa da soyayyar Shareff tun suna gida batai zaton zatazo gidan aure tai sakaci haka ba, tunda dai komai na mace Fadwa ta iya nan kuma mahaifiyarsu (Gwaggo Halima) batai sakaciba gaskiya musamman ma akan Fadwa data kasance mace babba. Fatan dai ba raye-raye a wayar nan dake ɗauke mata hankali tazo ta cigaba dayi anan ɗin ba, dan tara ƙawayen data saba tun acan taga har anan kullum cikin zarya suke.

        Da taimakon Aysha aikin ya kammala yanda tasan Shareff zaici a kwanciyar hankali. Suka ɗiba nasu ta shirya na Shareff ɗin da Fadwa. Tana ƙoƙarin fita Fadwa ta fito cikin kwalliya sai zabga ƙamshi takeyi. Gaisheta Aysha tayi. Ta amsa cikin raba hankalinta biyu tana buɗe abincin. Da murmushi ta kalli Aysha. Aysha ta mayar mata batare da tace komai ba. “ALLAH ya kaini ran aurenki shatu. Dama inata zullumi nakai abincin nan ya gane banice nayi ba”. Ita dai Aysha dariya tayi kawai. Fadwa zata ɗauka tray ta amsa da cewa. “Bara na ɗauka sai na gaishesa daga nan”.

       A tare suka nufi sashen nasa, sun samesa a falo zaune yana waya. Aysha da tasan bai cika damuwa da zaman dining cin abinci ba sai ta dire tray ɗin saman centre table. Fadwa kam gefensa takai zaune dan haka ya ɗan kalleta idanu ƙasa-ƙasa dan kwalliya na ɗaukar hankalinsa matuƙa ga mace, Fadwa kuwa gwanace wajen iya tsarawa nan ɓangaren ta ciri tuta dan batajin ganda kamar girki da sauran ayyuka da latsa waya ke hanata nutsuwar yinsu yanda ya dace. Ya ajiye wayar daya kammala yana kallonta da ƙyau, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Aysha dake gaishesa.

       “Kin tashi lfy?”.

    “Lafiya lau Yaya, ya gajiyar tafiya?”.

“Alhmdllhi”.

Ya faɗa a taƙaice. Harta yunƙura zata tashi ya dakatar da ita. “Ku har kun karya ne?”.

      “Yanzu zanje na karya Yaya”.

Ɗan jimm yay kamar bazaice komai ba. Dan har ya ɗauke idonsa a kanta sai kuma ya sake juyowa.

“Har yanzu tana kwance ne?”. 

     Ta fahimci Anam yake nufi. Dan haka ta girgiza kanta. “Tun ɗazun ta tashi ta wuce gida”.

     Fadwa da sai yanzu ta saka musu baki, tace, “Gida kuma? Rijiyar zaki wai?”.

   “Eh aunty, tana idar da sallar asuba kusan 6:30 nama zata da wasa take na shareta sai dana tashi naga da gaske ta tafi shine na kirata Husna tace min tanama barci”.

       Daɗine ya sauka har cikin ƙasan zuciyar Fadwa, ko banza shirinta na jiya yayi aiki tunda Anam ta bar mata gida a kan gaɓa. Amma saboda mazuran da yay jiya sai ta nuna rashin jin daɗinta a yanzu har hakan ya bama Aysha mamaki dan tasan dai ba shiri suke da Anam ba. Zaman nan da akai tare dan ya zama dolene kawai. Shiko mai gayya komai bai ce ba. Sai ma umarni ya bata akan ta tashi ta bashi abinci. Cikin shauƙin farin cikin tafiyar Anam ta miƙe ta fara haɗa masa tea. Aysha kuma ta miƙe ta fice ta basu waje.

     Kusan itace ma ta basa abincin a baki tana zuba masa hirar wahalar da taci lokacin da ta samu miscarriage. A ransa yana jin rashin daɗin rasa ɗan tayinsa, amma ya barma ALLAH tunda dama shine ya bashi bada wayonsa ba. A fuska kam tausayintane sosai sai dai baice komaiba. Rashin maganar tasa yasa ta sake yarda da maganar su Sima lallai da gaske baya buƙatar cikin a yanzu daman. Ta godema ALLAH data farga da wuri ta ɗauka mataki gashi yanzu farin cikin dake neman kufce mata na dawowa gareta.

        Basufi awa ɗaya da yin breakfast ɗin ba ya miƙe ya shiga bedroom, babu jimawa ya fito cikin shirin fita. Kallonsa take da mamaki. “Soulmate badai fita ba ko?”. Yi yay kamar baijita ba, ya kai zaune da ɗaukar wayarsa ɗaya, danne-dannensa yay yakai kunne alamar kira, hakan ya sata yin shiru tana kallonsa har ya kammala. Sake dubansa tai a shagwaɓe. “Dan ALLAH Soulmate fita zakai wai?”. Wayar daya gama ya ajiye gefensa, batare daya kalleta ba ya bata amsa. “Dama munyi dake bazan fita ba?”. Baki ta tura da dawowa kusa da shi ta zauna ta narke masa a jiki. Zata fara shagwaɓa sallamar Khaleel ta dakatar da ita. Kai tsaye ya bashi umarnin ya shigo, maimakon ta tashi a jikin nasa saita sake narkewa har Khaleel ya shigo. Kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa tunda indai taɓarar Fadwa ce ba yau ya fara gani ba. 

       Shareff daya fahimta bata da alamar tashi ɗin, ya dubeta yana ɗan tsuke fuska. “Gyara mana”.

   Baki ta ƙara tura masa, sai kuma ta tashi fuska a murtuke tabar falon ko amsa gaisuwar Khaleel batai ba dan har yanzu haushinsa na jiya na ranta ya mata addu'ar kishiya. Baibi takanta ba shi dai ya gaida Yayansa. Suka mike a tare suka fice dan motarsa Khaleel ɗin ya amso wajen wanki da yakai tun sassafe. Khaleel ne ke driving ɗin, yana gefensa suna hira da gaba ɗaya ma akan company ne. Sai ɗai-ɗai data shafi zamansa a gidansa wanda duk shine ke masa tambaya akan wasu abubuwan.

      Sun fara shiga sashen Daddy inda suka sami iyayen nasu uku zaune suna shan hira. Dan in har Abie na gari to bazaka taɓa rabasu ba sai dai in sun fita aiki, yau kuma babu aikin shiyyasa har breakfast tare sukayi. Bayan ya gaisheasu su duka suke masa fatan alkairi akan abinda yaje yayo cikin kulawa. Yaji daɗin addu'oin iyayen nasa dan su duka yana matuƙar jinsu a ransa. Ya ɗan jima anan tare da su suna hira har Khaleel ya fice ya barsu, sai da aka kira sallar zuhur suka fito suka nufi massallaci. A lokacin Anam nacan cike da farin ciki. Dan bata jima da tashi a barci ba Fawwaz ke sanar mata su Mamie sunzo. Da farko bata yarda ba su Husna harda Mom nata mata dariya. Ganin haka yasa ta mike ta nufi gidansu, tun a gate maigadi ya sanar mata, aiko da gudu ta shiga tana ƙwala kiran Mamie!! Abie!!. A lokacin Abie na can tare da su Shareff zasuje massallaci.

     Bayan an idar da salla koda ya shigo gidan sashin Mom ya fara shiga, suka gaisa har da ƙannensa sannan ya shiga wajen aunty Amarya. Daga can sai sashen Gwaggo data tsaresa yaci birabisko data dafa. Baici ba, amma yace ta saka masa a kula zaije dashi gida yaci. Taji daɗin hakan har cikin ranta, ya fito yana murmushin tsokanarsa da take. Sashen Mommynsa ya nufa inda anan ne ya zauna sukasha hirarsu har take kawo masa ƙarar Maheer da yay biris kamar ba shirin aurensa ake ba. Haƙuri ya bata da tabbatar mata zai kira Maheer ɗin a satin nan zai taho gida insha ALLAH. Taji daɗin hakan har a ranta. Yay mata sallama akan zaije gida sai zuwa dare zai sake leƙowa.

       Daga nan gidan su Anam ya shiga. Inda ya sameta nanuƙe da Mamie da Abie tana zuba surutu tana cin abinci. Suko sun biye mata sai dariya suke cike da farin cikin kasancewa da abarsu. Shigowarsa baisa ta daina surutunta ba. Sai dai taƙi yarda ta kallesa ko sau ɗaya dan tunda taji sallamarsa tai gefe da kanta. Shima kallo guda yay mata ya ɗauke kansa, ya maida hankalinsa gasu Abie. Tayin abinci Mamie ta masa babu musu yace zaici. Kasa haƙuri Anam tai sai da ta kallesa. Ya wulla mata harara ta tura masa baki da ƙyaƙyƙyafta idanu. Fuska ya sake tsukewa cike da gargaɗi a gareta ta taɓe baki. Duk abinda suke Abie na lure da su sai dai yayi kamar baya gani har Mamie ta dawo da abincin. Mace ce da sam bata da son jiki, yau da safe suka iso ƙasar amma bata zauna jiran wani ya basu abincin rana ba bayan na safe da suka samu Mom ta shirya musu. Tayi girkinta kodan farin cikin Anam, dan abinda tafi sone ta girka. Abincin ya faraci a nutse suna hirar China da su Mamie, itako ta daina hirar tana cin abincinta a shiririce tana saurarensu, sai dai sai balla ma Shareff harara take ta gefen ido.

        Sai da aka kira la'asar suka fita da Abie massallaci. daga can ya wuce gida dan tun ɗazun yake ganin kiran Fadwa na shigo masa yaƙi ya ɗaga, saima wayar da yasa a silent.........✍



Post a Comment

0 Comments