TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya hakima page 11_12

 πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»

         *GIMBIYA HAKIMA* 

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»




 *🌎MANAZARTA* 

 *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–Š️


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»``` 

________________________________




  _STORY AND WRITING_ _BY_ 


    _Jameelah jameey πŸ–‹_ 


    *(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*  


   





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*



 _Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


 ```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




11&12






Washe gari bayan Yarima Hakim ya tashi daga bacci yayi wanka sannan ya yayi addu'ar fita, ya fita sannan ya wuce shashen Fulani.. 




"Fulani ina kwana, "lafiya Lau Hakim ka tashi lafiya? "Lafiya lau Alhmdulh.. 



"Fulani ni zan wuce office,"to Hakim, Allah ya tsare ya baka sa'a, "Amin Fulani.. 



"Hakim ka biya shashen Gimbiya Zulaha da Gimbiya Bilkisu ka gaishesu kaji? 




"Fulani kin san matan nan ba son mu suke ba, mai zanje nayi wajen su.. 



"Kaje ku gaisa Hakim ai kafi su har gun Allah,dan haka ka wuce ku gaisa.. 



"To shikenan ni na wuce dan yau inada lectures, "to Allah ya baku sa'a.. 



Nan Yarima Hakim ya fara shiga shashen Gimbiya Zulaha, nan yasa akayi mashi iso sannan ya shigo.. 



"Antashi lafiya? Lafiya, wani abu ka shigo man waje tunda safe? Dan nema.. 


Dan Gimbiya Zulaha Tayi mamakin ganin Yarima Hakim, ai ita ta tashi da niyar ganin gawar Hakim, to wai shi Hakim wani kalar mutun ne wannan, mutun yaci guba amman ya tashi lafiya lau kamar kowa, tana cikin maganar zuci taji yace... 




"Kwantar da hankalinki matar sarki, kema kin san bin umarni ya kawo ni wajenki, ba dan haka ba ba abunda zani yi a wajenki.. 




Gimbiya Zulaha taji zafin maganar da Yarima Hakim yayi mata, amman sai ta daure bata nuna mashi komai ba tace.




"Ai daman ana san yaro mai biyaiya ga iyaye kayi kokari sosai  Hakim.. 



Haka Yarima Hakim da Gimbiya Zulaha suka kama gaya ma juna magana a fakaice sannan ya taso ya wuce Shashen Gimbiya Kilishi.. 



"Antashi lafiya Aunty? "Lafiya lau Hakim, ana nan anata kokari ko? 



"Alhmdulh Aunty ni zan wuce na barki lafiya,"to shikenan.. 




Haka ya fita yana mamakin halin Gimbiya Kilishi, ita bata nuna ma mutun tana jin haushin shi ba kamar Gimbiya Zulaha ba da bata iya boye kishinta ba, bayan tare suke duk wani tungu acikin gidan.. 




Haka Yarima Hakim ya tafiyarshi gun aiki yana mamakin halin mutanan gidan su, na bala'in son mulki su dai su gaji sarauta.. 



"Ranki yadade Gimbiya Kilishi tana san shigowa, "je kice mata ta shigo, nan Gimbiya Kilishi ta shigo tace.. 



"Gimbiya Zulaha ya naga haka? "Hmm! Abun ya bani mamaki Kilishi, wait shi Hakim wani kalar mutun ne? 




"Nima abunda nike tunani kenna, Amman anya da gaske Mino tasa ma Hakim magani? anya dan gaskiya ina kokonto Gimbiya Zulaha.. 




"Wallahi Kilishi a gaban idon Lanto Mino tasa maganin, Kawai dai ina tunanin shi Hakim din wani kalar Mutun ne? 




"To rabu dasu, in sun san wata ai basu san wata ba, wannan aikin kawai ki barshi a hannuna Gimbiya Zulaha.. 




"Aa Kilashi wannan aikin dole mu duka biyu zamuyi wannan aikin dan naga alama ba aikin mutun daya bane.. 




"Gaskiya hakane kin kawo shawara mai kyau kema Zulaha, to ni zan wuce Humad na can yana jirana zamuyi magana da shi... 




"To shikenan, ai da safe shi Humad din ya shigo gaidani, "ni kwana biyu kenan banga Hamid ba.. 



"Eh jiya ai gida ya wuni, kenan baije ya gaidaki ba? "Eh banganshi ba, "to wani uzurin ne ya hana shi zuwa wajenki na sani, "hakane ni na wuce.. 




"Humad, "Naam Ma'ma barka da shigowa, "yauwa Humad sannu da hutawa sarki mai jiran gado... 




"Haba Ma'ma sau nawa zani gaya maki akan ni bani san wanann mulkin da kike neman tusaman, kuma ga sarki can mai jiran gado Yaya Hakim, Amman sai zaki cema wa.. 





"Humad anya kuwa kasha Nono na? Anya Humad kaine Humad nifa na haifeka, Amman ace baka biyo halina ba, Ina bata yuyuwa.. 




"Nidai gaskiya Ma'ma ya kamata ki duba wannan maganar da wannan kudin da kike kashewa a banza wajen sabon Allah ai gwara ki gina massallaci da kudin duk wanda yayi sallah zaa baki Lada.. 



"Yi man shiru, Humad na gaji da sauraran bakin ciki, to tsaya kaji ko kana so ko baka so dole sai kayi sarkin Zaria, kafi kowa cancanta kayi sarki ba Hamid da Hakim ba, dan haka tashi kaban waje shashasha marar zuciya, wanda yayi Amai kare ya lashe.. 




"Allah ya huci zuciyarki, na barki lafiya, nan Yarima Humad  ya tafi ya bar mahaifiyarshi da bakin ciki, tana bakin cikin yanda Humad baki daya baya kwadayin Mulki ko kadan, "anya Humad ba asiri aka yi mashi ba, Gimbiya Kilishi ta fada tana mamakin wannan abun... 


________________________________



Bayan Gimbiya Hakima ta tashi bacci, su Lantana suka shirya yata yanda take bukata, sannan ta fito ta zagaya cikin gida sanann ta dawo taci abinci.. 



"Lantana! 



"Allah ya taimaki Gimbiya, "dauko man alkarbata zamu shiga kasuwa zamuyi sayaiyar makaranta.. 



"An gama ranki ya dade,  nan Lantana ta dauko ma Gimbiya alkaiba, sanann suka wuce kasuwa.. 




Gimbiya sayaiyar Makaranta tayi a kasuwa sai da ta saya komai sannan suka wuce gida bayan sun dawo gida, nan Lantana ta shiryama Gimbiya kayan ta dan gobe zata wuce... 



Bayan Lantana ta gama shirya ma Gimbiya kaya, sannan ta wuce itama  ta hada kayanta ita da Bilkisu da Azima dan dasu za'ayi tafiya Sai da suka gama hada kayan su sannan suka kwanta bacci... 


Washe gari da wuri su Lantana suka tashi suka ida hada duk abunda basu hada ba, sannan kuta hada ma Gimbiya Hakima ruwan wanka, sannan suka fita suna jiran ta tashi daga bacci sai ta shiga wankan... 




"Ba'ba Bilkisu, "Naam Azima, wani abu naga kamar kina cikin damuwa? 



"Wallahi tsoro nike ji sosai, da Ina murna Gimbiya Hakima Zata tafi makaranta zamu hutu har sai ta dawo sannan zamu cigaba da bauta, amman ina cikin wanda Gimbiya Hakima ta zaba zata tafi dasu karatu.. 



"To ya zakiyi Azima, ai ni daman nasan dani Gimbiya Hakima zata tafi zaria wannan karatun nida Lantana, dan baki bani bashin rantsuwa ko gidan miji damu Gimbiya Hakima zata tafi saboda ta saba da aikinmu Azima.. 



"Niko gaskiya banji dadin wannan abu ba, na gaji da wannan bautar dan kawai ba yanda zaniyi.. 



"Aiko kima saba, keda kika fara yima Gimbiya Hakima hidima daga baya, ni nan nida Lantana tun Hakima tana yar'shekara biyar muke yi mata hidima har yanzun maganar da nike yi maki.. 




"Wai gaskiya sannun ku, kunyi kokari amman duk da haka Gimbiya Hakima bata raga maku, balle mu.. 




"Ai haka halin Gimbiya Hakima yake sai dai hakuri, "to Allah ya bamu hakurin zama daita tunda mudai yanzun muka fara, ko taya zamuyi zama da ita a Zaria? "Wannan ansar sai munje zaria zamu ganta.



"Ku taso ga Gimbiya Hakima nan ta fito ku, nan suka tashi suka marama Gimbiya Hakima baya zuwa shashen Maimartaba, suna zuwa nan ta tadda Fulani da Yakumbo... 




"Barkanku da hutawa, "barka Daughter har kin shirya ko? "Eh na shirya Momy... 




"To Daughter kiji tsoran Allah, indan mu bamu ganinki, to kisani Allahn da ya halliceki yana nan yana kallonki ko da karkashen kasa kika shige kika boye... 



"Sannan kiji tsoran Allah kiji tausayin bayin da zaki tafi dasu Daughter, dan Allah karki cucesu kamar yanda kike yi masu, kinga yanzun karatu zaki tafi.. 




"Insha Allah Momy, zan kiyaye, "yauwa Allah ya yi maki albarka, "Amin Momy... 




Bayan Yakumbo ta gama yi ma Gimbiya Hakima wa'azi nan Fulani da Maimartaba suka yi mata fatan alkhari, sannna maimartaba yace... 



"Na baki direba, sannan kin zabe kungangai gudu uku, na baki masu gadi guda hudu, dan haka Mamana akiyaye, in kinje kiyi abunda ya kawoki.. 




"To shikenan insha Allah Baffah, nan dai suka gama yi mata wa'azi sannan aka sa kayan Gimbiya Hakima cikin mota nan suka dauki hanyar Zaria, da mota hudu akayi ma Gimbiya Hakima rakiya dan harda Gimbiya Yakumbo sai da ta raka Gimbiya Hakima makaranta... 




Bayan sun sunka gidan da aka kama mata, sannan suka dawo gida.. 



Gidane flat house, babban parlour ne da bedroom guda uku, sannan boys coters, nan masu gadi da direba zasu ringa kwana, Gimbiya Hakima da su Lantana kuma zasu ringa kwana cikin gida, amman bedroom din Gimbiya Hakima daban... 




 _By jameelah JameeyπŸ–‹_ 




Post a Comment

0 Comments