TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 53

 EPISODE 53

Cikin wani kalan izza da kamala Riyad yace "already gidan sarauta yayi suna ganinmu ake like wicked people, masu bakar zuciya, masu neman dukiya da power at all cost, wayanda can do anything to get abinda sukeso harda kisan kai, masu danne wanda sukaso su danne, i want to be a king that will make a change na nunama duniya cewa good people exit agidan sarauta! Masu purest of heart, marasa ill intention" cikin kakkausan murya yace "ayau zan kafa sabuwan doka agidan nan Sarkin Gida" Sarkin Gida yashigo da gudu da sauran fadawa zasu gaida Riyad ya daga musu hannu irin baiso yace "ku saurara ku rubuta acikin littafin dookoki Masarautan Kano cewa duk wanda aka kama dawani hali na makirci, kona sheri, kona mugunta, ko cutar da wasu mahalukin, dan Adam ko babba ko karami, kowa waye masarautan nan zata kori mutumin mu yanke alaka dashi!" Dasauri Jummai takama wandon Muji tana "dan Allah dan Allah kayakuri Mijina, kasa baki" kowa kallon Riyad ake kusan duka family basu taba ganin this brave angry Riyad ba, today is the first day dasuke ganin Riyad as king, idanunsu ada suna ganinshi as just Riyad ne but yau Riyad yazama real Sarki a idanunsu, Juyowa yayi yakalli Jummai yace "wannan matar mai suna Jummai an kamata da sherin kazafi! Sheri.takurama bayin Allah, musguna musu, makirci and duka lokacin datake aikata ayyukan nan tana nuna eh daga masarauta na tafito bawai ta boye identity nata bane dan haka zan aikata gidan alkatau na nan gidan saurauta dazatai aiki na sharan masarautan nan ko'ina na tsawon wata daya kafin bayan wata dayan akoreta tabar gidan har abada!" Dasauri Jummai tamike tsaye tana kallon Riyad da mijinta dakuma fadawa dataga suna zuwa kanta zasu kamata ganindai da gaske ta kwana ciki yasa ta kalli Mom dataga taki kallonta daidai fadawan sunzo sunwani jata kaman jaka ihu tayi Jummai tace "inhar zaka hukuntani haka Mai Martaba kasan cewa harda uwarka yakamata kahada" dasauri Mom tace

"kujata kufita da ita mana ta ishe mutane da surutu" fadawa suka wani jata Mom Riyad yakalla kafin adake yace "wait!" Tsayawa fadawan sukayi dasauri Mom tace "Riyad mehaka? Kabari atafi da ita mana" Murmushi Jummai tayi Riyad yace "wace mahaifiyata kike magana?" Tana kallonshi tace

"wacce harta tsargu tafara magana" dasauri Mom tace "nikuma zakima sheri makira irinki is capable of doing anything" ihu Riyad yama Mom yace

"quiet! Mom don't speak again idan bance kiyiba" yakalli Jummai yace "idan kika kuskura kikama mamana sheri bazakizo abinda zan miki ba Jummai" dasauri tace "bazan tabama mamanka sheri ba cus inada evidence ga wayata nan tsakar falo dauka kabude kaje call log zakaga nakirata last night itama takirani i record call namu play it" daukan wayan bafade yayi yabama Riyad ya karba, Playing voice din Riyad yayi kawai sai jikin Mom yahau rawa kaman kasa ya tsage tashiga ciki takeji, tunda yafarajin maganan su akakai inda Jummai ke cewa Mom was behind HIV Mama kawai wayan yafice daga hannun Riyad yafadi akasa yanda Riyad ya shiga shock na Muji was even was even worst, saida Hambali yarikeshi Mom kawai ta dafe kanta  kunya ya shigeta but deep down bata wani damuba sabida Babanta is attorney general kuma ai is a plan she suggested not executed.

Jummai ganinsu yanda kowa ke cikin shock yasa takwashe da dariya tace "yes yes yes! Na tsani Zainab sabida tashigo gidana ta daukemin farin ciki, shekaranmu nawa muna neman haihuwa ita tazo ta samu mijina ya manta dani, nadawo banda amfani da amaryansa yake naje na sami Maryam nagaya mata tace min idan inaso na maida soyayyan da Muji kema Zainab zuwa kiyayya tanada plan!

Kowa kallonta yake tace "nasan zata iya karyatani amman kun ganni nan kap rayuwana bansan wani me HIV ba ita ke gayamin cikin bayin da aka kawo mata daga wani yaki lokacin akwai wata daketa ciwo takaita asibiti akama yarinyar gwaji akace HIV ne inhar zaku tuna cikin bayi da aka rarraba lokacin wata mai suna Safara'u Mamanka akaba" Gwaggo tace "kwarai natuna Safara'u idan naje dakin

Maryam ina cewa ke bakicin abinci ne amman daga baya nadena ganinta, Jummai tace "bayan tagano tanada HIV ta sallami yarinyar a boye tabata kudi takula da kanta shine take gayamin zata iya kiran yarinyar awaya mu mata allura mu debi jininta musan yanda zamuyi mu sama Zainab jinin ajiki" Kowa kallon Jummai yake adakin tace haka takira yarinyar ita oo baniba tasa hannu tadauki sirinji taja jinin yarinyar tabani natafi dashi lokacin Zainab batada lafiya cus cikin na wata guda mugun laulayi take, ana ma kara mata ruwa ne tana bacci kuma tanada nauyin bacci, lokacin yayi daidai da lokacin da babu kowa adakin, Muji yafita aiki naje na zare karin ruwan kaman vanda ake dura maka allura ta wajen yashiga jijiya haka na kafa gindin sirinjin a ramin na fesa jinin ina kallo ina murmushi cikin bacci tadanyi motsi ta tashi da sauri naja ruwan ina maidamata nace yacirene ruwan koma baccin ki, takoma bacci natashi natafi naje na jefa syringe din abola. Nadinga cewa zaiyi kuwa Mrayam nacemin ai zaiyi menene menene ahaka data fara ciwo awata na shida akace HIV n...." wani irin fizge kanshi Muji yayi yay wajen Jummai yafara dukanta tana ihu saida aka rikeshi tahau dariya kaman mahaukaciya tace "ku kasheni to me yarage narasaka Muji I've lost komi, kome nayi aduniya sabida kaine dan haka tafashe kawai guess wat har asibiti na bita nabata guba ta mutu! Yes i poisoned her" Innalillahi yanda kirjin Riyad ke bugawa yakusa barewa so Mrs Bugaje was right data kirashi just last night harya fara bacci tace tana suspecting poisoning Mama akayi cus bakinta was green datana mata wanka tagani but tanakan investigation.

Wannan karan wani kalan zubewa Muji yayi akasa yana kallon Jummai dake kallonshi tace "I was a good wife babu abinda bana maka, kusan bautamaka nakeyi, after Allah da shine ubangijina wanda nake bautamawa you were the next person in my life, ka kama kayimin kishiya ka manta dani da duk abubuwan dana maka, wata ta dauke maka hankali dare daya, nikuma nai alkawari saina rabaku har abada!" Runtse idanu Riyad yayi duk yanda yaso yadaure saiga hawaye sun zubo daga idanunshi, ko shine Rashida bazaiso yayi zaman aure da wanda members of his family are like this ba. Fuskanshi ya share yamike tsaye tareda juyawa yace "ku kulle both Maryam and Jummai and call the police they will both pay for crime nasu, Mama will get justice" dasauri Mom tace "Riyad riyad wani ihu yayi yace "take this two women out of this room now!" Fita dasu fadawa sukayi shikuma Riyad yawuce sama da gudu.

Hatta Maman Kabeer saida jikinta yayi sanyi tasan da sunso su kashe Riyad but bayan yazo yazama sarki sun hakura ganin be wani iyaba sunsan zaiyi making mistake daga baya, or da kanshi ma yace yasauka, wickedness din Jummai da Mom bazata taba iyawaba, haba HIV fa ina mata zasu da kishi, itada mijinta yayi mata hudu curr da kwarakwari fa tace me? Ina mata zasu da kishi? What is this?

Infect innocent woman da HIV Ya Allah, jitayi jikinta yayi sanyi wani tuba da tsoron Allah na shiganta, remembering yanda Mama ke kuka alokacin tana cewa ita ba fasika bace Allahu Akbar! Allahu Akbar!

Inama tana raye! Wayyo Allah.

Ahankali Ammi tabar yan falon na lallashi Muji dat is completely heartbroken filled with regrets da danasani, tawuce sama dakinta tabude ahankali akasa taga Riyad yazauna ya kife kanshi kan kafa Munir na gefenshi yadafashi, wucewa tayi inda yake gently ta daura hannunshi saman kanshi dago kanshi yayi idanunshi sunyi jajir ganin Ammi yasa yakasa hadiyewa yakasa daurewa sai hawaye masu zafi yace "Ammi how can I even look at Rashida na gayamata yan gidanmu killed her Mother? How Ammi? Ammi tayaya zan gayamata poison akaba Mama eh?" huci yayi me zafi yace "Ammi if I were in Rashida shoe ni kaina bazan taba zaman aure da mutum daya fito daga gida filled with evil killers menene menene ba, Ammi we wronged Rashida da yawa, how can I look at her nagaya mata all this I can not do it Ammi I can't, I can't Ammi, Ammi she will hates me more, Ammi wat do I do now?

Yazanyi, Ammi why do I have to come from this kind of family???". 




Post a Comment

0 Comments