TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 9

 #MAMUH.*_Buri daya_*

*_Mamuhgee9_*

Bayan sati biyu da magana ranar jumaa da yamma Bello yazo qofar gidan tareda abokinsa nuhu dukkaninsu sunyi adonsu cikin yadin wagambari na leda sai qyalli yakeyi na gugar dayaji,


Dattiya dake tareda idi a bakin masallacin layin suna magana Yana hangosu ya washe baki cikin jin dadi sbd yanzu yagama adduar Allah yakawo masa hanyar samun ko dubu 'dayace.


Atareda mal idin Suka fito sarari dansu hangosu aikuwa suna hangosu gurinsu Suka nufo har qasa Suka durqusa Suka gaidasu 

Dattiya sai saka musu albarka yakeyi Yana washe baki kafin yayi gaba Yana cewa"


Bismillah ku qaraso ciki aikaima Bello yanzu kazama 'dan gida tunda zaka auri NADIYA.


Wasu ruwa da JJ yasaka abaki Suka mugun dawo masa da qarfi sbd jin maganar qarshe da kawun yafada,


Tari yafara mai qarfi sbd sosai ruwan Suka sarqesa,

Kallon qofar dakin sarki yayi sbd yabarsa Yana bacci yakumasan qila yatashi.


Saurin juyawa yayi yashiga dakin yagansa Yana motsin tashi Kuma ya tabbatarda baijiba.


Juyowa yayi yafito zuciyarsa na jujjuya zancen to kodai shine baiji daidai ba Amma Kuma su bellon yanda suke wani sassauke Kai yatabbarda akwai wani abin.


Kasa zama yayi yakoma dakin yaga yatashi Yana zaune bakin katifa Yana waya cikin basarwa yagane da ale dikko ne yake wayar,


Sake juyawa yayi ya fice duk hankalinsa ba'a kwance ba sbd bayason sarkin ya fito.


Bai gama tunaniba yagansa ya fito fresh skin dinsa mai haske Yana zufa alamar zafine yafito dashi koba komai lokacin wankan maraicensa ne.


Bai kalli qofar gidanba idan su JJ da sauran yaransa suke yayi cikin gida Dan yin wanka da threequater dinsa da armless riga dama sai tawul rataye a wuyansa fuskarnan tamke kamar ko yaushe.


Zainab ce tafara hangosa ta miqe tareda daukar wayarta dake gefenta tareda takalmanta data gama wankewa ta nufi dakinsu tana cewa"


To Bello sai anjima nizan shiga na Dan yi waya.


Cikeda jin dadi bellon yace"


Yauwa zainab to nagode.


Cikin 'daga murya iya talatu tace"


Ke Nadiya bazakiyi sauri kifito bane kinbarsu sun gaji da tsugunawar qafafuwansu harsun fara rawa.


Batareda dattiya yasan da zuwansa ba yace"


Shashanci me kika tsayayi haka za'ayi auren kije kina masa sanyin jiki?


Baice musu qala sai ita daya kalla lokacinda tafito sanyeda sabon hijabi zainab ta sanyo mata Hoda harda janbaki maroon dayayi mata kyau sosai kasancewar Bata taba saka janbaki mai kalaba iyakacinta Vaseline abaki.


Wani mugun kallo ya watsa mata atake ta rikice tana neman juyawa cikin muryarsa mai saka shiga taitayinta yace"


Bani ruwan wanka.


Da sauri nuhu abokin Bello ya miqe Yana cewa"


Sarki Bari na debo maka da kaina ma...


Wani kallo sarkin yayi masa dayashi saurin sakin bokitin...


Gyaran murya dattiya yayi tareda hararar gefen zakin yasaki yaqen Dole yace"


Nuhu Aida kabarshi ta Diba tabashi saiku koma daga soron gidan zaima fi muku nutsuwa can din.


Aikuwa kamar jira suke Suka miqe Suka koma soron gidan Dan dama dukkaninsu a tsarge suke da ganin Zaki na gida sun dauka bayanan.


Aikuwa tana Kai masa ruwan tadawo ta nufi soron gidan tanajin ba dadi cikin ranta sbd ganin wani kallo dayayi mata lokacinda ta aje masa ruwan.


Suna ganinta Bello yahau washe baki sai alokacin Suka saki jiki Suka fara gaisawa itadai tana rakube a gefe.


Nuhu ne ya zaqe yanata jawo musu fira sbd yafi bellon rawar Kai da iyayi shikuwa bellon sai kallonta yake Yana murmushi Dan kuwa shi harya farajin sati biyar dinda Suka rage sun masa nisa.


Qamshin sabulun wankansa na imperial L da ita kadai tasani yasata sake rabewa tareda sunkuyar dakanta 


Bello kuwa harda qara Ware idanuwansa da kyau Yana sake mata kallon qurulla 

Ga nuhu sai kawo musu zancen soyayya da yanda Bello kesonta  yakeyi Yana qarawa.


Tsaf fararen idonsa Suka shiga cikin nata atake jikinta yadau rawa taji hawaye na ciko idanuwanta.


Yana shigowa soron JJ yataso daga qofar gida yashigo 

Kallo daya yayiwa Zaki yaga ba fuskar masa magana harya shige dakinsa shikuma yajuyo gurinsu Bello fuska a hade yace"


Kai ku Ware daga nan bamason hayaniya,


Wuqa ya fitar mai shegen kaifi da qyalli ya Dora saitin wandon Bello da jikinsa yafara mazari yace"


Duk Randa nasake ganinka gidan nan saina maka zanen gobirawa anan""yaqarasa fada Yana zungurin wandon da wuqar.


Nuhu tuni yayi muryar sanyi yace"


Zamu kikyaye oga JJ.


Qofa ya nuna musu tuni Suka wuce da sauri wani na tunkudar wani musamman sauran yaran neyon dake cikeda qofar gida duk sun mimmiqe.


Kamar Bello zai fashe da kuka haka ya isa gida ya tube yasaka riga da wandonsa na aiki ya nufi shago Yana fushi Dan kuwa wlh JJ yacucesa daya korosu Dan kuwa so yayi yau ya dasa soyayyarsa a zuciyar nadiyarsa.



JJ kuwa bayan fitarsu mayarda wuqarsa yayi ya juyo gurinta fuskarsa a sake sosai Dan dama dashi kadaine take dadewa Yana Mana fira.


Fira yadinga mata wani lokacin har murmushi takeyi tana rufe fuska sbd rabi duk tsokanarta ne yakeyi da maganar soyayya.


Ahaka har kusan magriba kafin yabarta tashiga gida tana murmushi shikuma yayi waje Dan kuwa yasan sarki baison kusancin kowa ayanxu.


Dattiya dake jiran shigowarta ya qurawa hannunta dake cikin hijabi ido 

Cikin sanyi take qarasowa tana murmushinda itama Bata saniba 


Ahasale dattiya yace"


Wai meyene haka kike tafiya kamar Mara ruwan jiki???bazaki cire hannunki daga hijabin bane saikace matar alaramma.


Fitarda hannuwanta tayi yaga Babu komai a hannun ya tsuke fuska yace"


Ruwan alwala kikazo dibar musu???


Girgiza Kai tayi tareda masa alamar sun wuce.


Cikin yayi da qananun idanuwansa tareda miqewa ya dauki buta baisake cewa kowa qala ba yashige bayi tun acan ma yayo alwalarsa Yana fitowa butar kawai ya aje ya fice.


A masallaci ma koda yaje kusada Zaki da JJ yasamu sahu nan yasake tsuke fuska musamman dayaga JJ namasa wani ladabi yasan cutarsa zasuyi Saidai ganin fuskar JJ a tamke tam Babu Wasa yasa yasake tsuke tasa shima Dan ko gaisuwa baiso.


Ana gama sallah yafito JJ yabiyo bayansa suna fitowa yaja ya tsaya yace"


Lafiya zaka bini?


Murmushi JJ yayi Yana Sosa Kai cikin 'dan ladabi zaiyi magana kawun ya katsesa da cewa"


Wannan ladabun mai amsheka ba sam,

Kafitomin a zallar yanda kake kamun magana idan ma itace kakeda ita.


To kawu dama inson Nadiya ne shine nakeson sanarda Kai Kuma Nima aurenta nakeson yi......


Wani kallon takaici kawun yamasa kafin cikin bacin Rai yace"


'yar tawa zanbawa magajin dake jiran gado a dabanci,ta'addanci,da Sara Suka?

Wato gani dattiyan mahaukata tunda kaga Ina sake muku fus....


Ido hudu yayida Zaki dake bayansu saiya qarasa maganarsa da cewa"


Kaga jabiru kabarni da wannan maganar nariga nabawasu Bello saura sati biyar bikin ma.


Juyawa JJ yayi sbd jin yanda kawun yayi magana cikin lalama sabanin farko daya fara masa Rashin arziki

 saiyaga Zaki yasaki murmushi kenan ganinsa yasa kawun sassauta harshensa.



Ahankali yaqaraso yau kyawunsa duk yasake bayyana sbd jallabiyace yasako ash data fito da farin fatarsa ta asalin Igbo.


Kallon kawu yayi yace"


Muje gida kawu.


niba gida zani ba inada abinyi.


Juyawa sukayi Suka barsa 

Sanin akwai abinda ke Shirin faruwa yasa yabiyo bayansu Yana zuba masifarsa suna jinsa sukai banxa dashi.


Har tsakar gida Suka shiga Zaki ya kalli kawun yace"


JJ nason auren waccan yarinyar

Meyasa baza'a bashiba?????


Kallon JJ kawu yayi yace'


Sbd Ni ubanta namata miji.


Kallonsa Zaki yayi yace"


Shikenan????


Eh"kawun yada Kai tsaye sbd shima yau Rashin arzikin yakeji.


Juyawa yayi ya wuce JJ yabi bayansa suka fita.




Post a Comment

0 Comments