TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 20

 *_Mamuhgee20_*

Baban dashi aka yini asibiti Dan kuwa sosai zuciyarsa tayi rauni da ganin halinda 'yarsa ke ciki shidai allah yasani duk duniya Babu abinda dai yake so kamar nadiya shiyasama duk wani Abu daya danganceta yake zarewa yayita masifa tuburan akanta.,


Akaro na farko dayaji jikinsa yayi sanyi daga alamarin aurenta da Zaki musamman ma dayaga asibitin daya kawota gashi komai tsada ga kudi dayake kashewa sosai akanta da duk lalurar asibitin,


Tunda ta farfado itama kowa ke lallabata tsakanin zainab da baban hakama iya talatu idan tazo,

Yaya dahiru da amaryarsama kullum saisunzo da daddare dubata,


Taji jiki sosai Saidai alhmdllh cikin kwana biyar sauqi yafara zuwar Mata sosai Saidai qafafuwanta datakejin azabar takawa Dan kullum saisun warware bandage din sunwanke qafar sun canza Mata wani.


Zainab ce take kwana agurinta shiyasa take Dan sakewa Amma idan yazo zainab guduwa gida takeyi ta Dan huta.


Tsakaninsu dai Yanda nan yanda suke banbancin shine yanxu Yana zuba mata fararen idanuwansa dake dawo da zazzabinta musamman da yanzu kayanta daya siyo Mata na jinyar kusan dogayen riguna ne Amma marasa wani nauyi sai lafewa ajiki gashi Sam sallah kawai ke hadata da hijib zainab daukewa takeyi.


Yauma dagashi zai itane a dakin zainab ta gudu.


Gashinta daya tarar zainab na gyara Mata ya kalla yaga yanda yakeda tsawo andaure Mata da band gashi sosai tayi wani irin haske na alamar tana jinya ya sake kallon dogon wuyanta zuwa qirjinta dake sama Yana qasa sbd numfashinta.


Dauke Kai ganin tanata wani mutsu nutsu alamar wani Abu ya gyara tsayuwa tareda zuba hannuwansa a aljihun wandonsa fuska ba sakewa yace"


Kinyi sallah???


Girgiza Kai tayi tana sunkuyar dakai.


Ya Dade shiru cikin takaicin zainab data tafi batareda ta tsaya yin abinda yakamata dinba gashi yanzu baisan uwarda zai musu ba.


Ganinsa kawai tayi a gabanta tayi saurin dagowa idanuwansu suka shiga na juna tayi saurin sunke idanuwanta tana matse hannuwanta.


Hannu ya miqa Mata batareda ya kalletaba Yana sake tamke fuskarsa.


Kallon hannun nasa tayi tareda dagowa da sauri ta kallesa taga ba alamar sauqi daga fuskarsa take taji jikinta na rawa sbd duk lokacinda jikinsu ya hadu jitake jikinta na vibration.


Ahankali ta dago hannunta Yana rawa ta Dora a nasan kusan atare Suka rintse idanuwansu Dan abinda yakeji idan jikinsu ya hadu kusan yafi wanda takejin.


Ahankali ta miqe Suka nufi toilet din dakin Yana riqeda ita tana dingisawa ahankali sbd qafar.


Suna kaiwa bakin qofar toilet din Suka tsaya shi ya sauke Kai Yana sake daure fuska ita Kuma tayi qasa dakai Dan kuwa zainab ce ke taimaka Mata gurin alwalar.


Daddafawa tayi tashiga bayin tareda turo qofa ahankali tana rintse ido.


Daqyar da dubara tayo alwalar Saidai duk ta jiqa bandage din qafar tana juyowa wani mugun santsi ya kwasheta ta bugu da madubin gurin atake ta zube agurin goshinta na fitarda jini.



Shiru shiru Bata fitoba tun Yana basarwa harya maida hankali kan qofar yaji yadainajin motsin ruwa daga ciki.


Yana zaunen zainab tashigo kusan tareda nurse da Dr sayyid dasuka Saba sosai dashi.


Atare Suka kallesa Dr na cewa"


Sarki Ina patient Dina ne bangantaba??


Zainab yayiwa wani kallo yace"


Jeki ciki ki dubota.


Toilet din ta nufa ta bude Kai tsaye zata rufo qofar ta hangota some tsakiyar bayin wani razanannen ihu tasaki tareda qarasawa da sauri tana kiran sunanta.


Da gudu Dr sayyid da nurse sukayo bayin cikin tashin hankali suna tambayar meye.


Ganinta kwance zainab nason dagota takasa yasa arikice Dr sayyid ya qaraso Yana cewa su matsa ya Kai hannuwa zai daukota yaji anriqe hannunsa riqewa irin wadda yasan ya riqu.


Da sauri ya dago abinda yagani a idon zakin yasashi matsawa gefe batareda ya furta ko kalma dayaba.


Hannu biyu zakin yasa ya daukota cak ya fito bayin da ita Suka biyosa zainab na Dan fidda sautin kuka ahankali sbd ganin yanayin zakin tasan Idan tayi hauka itace za'a bawa gado a dakin kusa dana nadiyar.


Cikin fada Dr ke dubata Yana cewa meyasa zasu barta tashiga toilet din ita kadai.


Fitowa yasa sukayi kafin yayi Mata dressing goshinta tareda Mata wasu allurorin Yana saka Mata wasu allurai a ruwa ta bude idanuwanta ahankali hawayen azaba suka gangaro Mata.


Sannu"Dr sayyid yace Mata cikeda tausayinta shidai Allah yasani yanajinta cikin zuciyarsa Kuma sosai ya lurada tana fama da maraici arayuwarta sbd Sam yanda Bata iya sakewa da danginta koyaushe cikin sanyi take kanta a sunkuye.


Zama yayi kan kujera bayan yagama Yana rubutu cikin file dinta Yana cewa"


Nadiya please ki ringa kula kina kiyayewa da duk abinda zai tab lafiyarki.


Wasu sabbin hawaye ne Suka gangaro Mata ta juyarda kanta dayan gefen.


Shiru yayi Yana kallonta kafin ya miqe ya fice.


Zaki baisake shigowa dakinba ya wuce gida Dan Yana tsananin buqatar maganin ciwon qirjinsa kafin aga ya buga a gurin.


Zainab ce ta zauna tana Mata sannu cikin sanyin murya tana dafa goshinta dake nade da bandage cikin tausayin 'yar uwarta.


Kwana biyu tashin shima yayi sauqi tasake warwarewa Saidai wasu irin qaidojinda Dr sayyid ya shimfida akan lafiyarta kafin ya sallamesu Suka koma gida cikeda kewarsa sbd sosai yake bawa Nadiya kulawa Kuma sosai hakan yayi tasiri a zuciyar dukkaninsu musamman dattiya dahar wani sabo sukayi Dan duk zai koma gida idan yazo sai Dr yabasa dubu guda yace yahau acaba.


Iya talatu ma girman dayake Bata Wanda Sam Bata samuba daga yayanta daga Nadiya saishi yasa take jinsa matuqa.


Zainab kuwa dama tuni takamu Dan baqaramin burgeta Dr sayyid yagamayiba.


Zainab ce tayi musu gyaran dakinsu tashare ta goge komai tareda fesa turare takaiwa nadiyar ruwa har bayi taje tayo wanka.


Tana cikin shafa Mai yashigo dakin idanuwansa Suka sauka kan daurin qirjinta datake qoqarin saka hijabi da sauri har jikinta na rawa. 


Qarasowa yayi ya nufi bakin wardrobe ya zare rigarsa ya dauki towel dinsa ya fice.


Miqewa tayi ta dauki rigarta ta bacci Mai tsantsi doguwa har qasa tasaka bayan ta fesa spray.

Har safar qafa tasaka sbd sanyi ta sanya baqar wula ta rufe kanta tareda cusa gashinta ciki Dan tunda zainab tasa Mata relaxer gashinta yayi tsayi sosai sbd miqewar dayayi.


Sallar ishai tayi tayi kwanciyarta agurin tareda qudundunewa cikin hijabinta sbd yau sanyi Sosai takeji sbd asibiti kullum dakin datake dumi  Dr sayyid ke saka masa shiyasa yanzu har cikin qashin bayanta takejin sanyin har gabobinta na fara Mata ciwo.


Yana shigowa dakin yaga yanda ta dunqule waje daya saiyaji kamar hankalinsa zai tashi Amma ya basar yayi duk abinda zaiyi yaje ya rufe gida  yashigo ya rufe dakin ya kashe wuta ya nufi katifa saiya kasa Hawa ya tsaya Yana jujjuyo zancen Dr sayyid akan sanyin daya kamata gashi yanda yake Jin fitar numfashinta yanxu yasan ciwon ne yakeson tashi tunda dr yace ko kadan daga yanxu kar abari sanyi na shigarta.


Shiru yayi kansa na daukar zafi haryaji tana fidda wani irin Nishi alamar dai ciwon ya dawo Mata.


Cikin duhun Kai tsaye ya sunkuceta gabaki dayanta ya kwantar kuryar katifar tareda zare Mata hijabinta ya kwanta tareda bude musu jibgegen bargonsa Mai laushi.


Rawa jikinta keyi sosai na sanyin dake ratsa qashin jikinta ganajinsa kusada ita sosai gashi dama baya kwana da riga ajikinsa.


Jin rawar jikin nata yayi yawa da nishinta yasa ya jawota cikin jikinsa ya rungume tareda zagayeta ya rufe a qaqqarfan jikinsa ga dumin bargo


Baa wani jimaba sanyin jikinta yafara raguwa 'dumi na shigarta sosai ahankali tafara dawowa normal Saidai yanayin yanda qirjinta ke manne da nasa yasa takasa motsi sbd kunya da tsoro ahaka bacci ya dauketa Dan dama akwai maganin bacci sosai acikin magunanta Dan harda hutu Dr sayyid yakeson tasamu.


Bai bacci ba shiru yayi da ita cikin jikinsa akaro na farko yakejin kamar rayuwarsa tasamu nutsuwar datake buqata,

Wani irin sanyin Hali yaji na shigarsa sbd yanda dukkanin gabobin jikinsa suke karbar baquntar jikinta a nasa.


Da asuba koda ya farka bacci takeyi sosai wannan karon hannuwanta zagaye suke da qugunsa hularta ta zame ya qurawa fuskarta ido sbd nepa daya farka yaga akwai. 


Zameta yayi ahankali tareda gyara Mata bargon ya sauko ya nufi electronic cattle dinda ke dakin ya zuba pure water hudu ciki ya jona ya fice zuwa alwala.


Kusan tareda kawun Suka fito sallah sbd sallar asubar yanxu tashiga kawun batareda yasaniba ta hanyar saka idonsa akansu.


Harya dawo bacci takeyi ya juye ruwan a flask yasake zuba wasu yazo bakin katifar ya zauna tareda Dan buga pillow ahankali.


Cikin yanayin bacci dake cinta ta bude idanuwanta tareda mayarwa ta rufe 

Saura kadan zuciyarsa ta fado da hakan datayi Dan kuwa har wani tari ya miqe Yanayi sbd sarqewar numfashi daya kamasa.


Kyaleta yayi ya hawo katifar ya kwanta tareda rufe rabin jikinsa kawai Yana 'dan qara gyara muryarsa kadan sbd yawun dasuka sarqesa sbd qafafuwansu dasuka hadu cikin bargon.


Lumshe idanuwansa yayi ya rufe yanajin yanda dumin numfashinta ke sauka a wuyansa yana dumama dukkanin jikinsa har numfashinsa na slow.


Kamar Wasa sai baccin dabai wani yiba cikin Daren ya daukesa ahakan.


Qarfe bakwai maganin yadan saketa ta bude idanuwanta ahankali tana sake gyara kwanciyarta cikin jikinsa.


Da sauri ta qarasa bude idanuwanta baccin na sakinta gabaki daya tayi saurin matsawa baya tana kallon fuskarsa datayi wani irin kyau dayana baccin,


Bakinsa dayayi wani Dan ja kadan ta kalla zuwa dogon hancinsa da gashin girarsa dake kwance kamar na mace,


Tabbas farine sosai dayake sirke da 'dan yellow na asalin mutan Igbon asali Saidai shi Sam baya wani tara sumar Kai saita gemu Wanda yake bana ustazanciba saina tsabar qwarewa a ta'addanci.


Karo na farko data saki murmushi bayan qare masa kallo.


Ahankali ta sauko tana qoqarin daukar hijab taji yace"


Ki juye ruwan cattle din kiyi amfani dasu idan kika taba ruwan sanyi wlh saina karya dogon wuyankin nan.


A matuqar tsorace da kunyace ta juyo ta kallesa taga har lokacin idanuwansa a rufe suke kenan duk Yana saneda abinda takeyi tun tashinta.


Cikin tsananin kunya da rawar jiki ta dauki cattle din ta fice tana rufe jikinta da hijib sbd sanyi.




Post a Comment

0 Comments