TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 13

 *_Mamuhgee13_*

Rintse idanuwansa yayi ya bude cikin wani irin zafi yace"


Kinfi kowa sanin abinda nake iyayi da Wanda zan iya yiwa kowa akan harkar dukiya,meyasa kikeson batamin ayyuka so da dama?


mezakiyi da JJ dakika sa akace ya rasu???

Wat are you planning this time zeell?


Yafada cikin daga murya da bacin rai,



Wat Eva u're planning karki sake ki batamin aiki sbd Zaki is one of the  precious abunda bana Wasa dashi Dan kuwa Ina hango wa kaina taskokin nasara da ikon mulki dazanyi amfani dashi nasamu so be very very careful with me.


Daukar wayarsa yayi tareda juyowa ya kalli am dake cikin takaicin abinda ke faruwa Rai bace yace"


Nasan kasan inda takai JJ kuyi gaggawar kashesa ku maida gawar inda take tunda anriga ance ya mutu

Bazan dauki ganganci irin nakuba.


Ficewa palon yayi zuwa samansa Yana sake jin haushin abinda zeel din tayi duk da dai yasan tanada dalilin yin hakan Amma Koma meyene dalilin bayason rasa Zaki yanxu batareda yasamu cimma burikansa akansaba.


Acikin daren am yakira wasu yaransa dake boyayyen gurinda Babu Wanda yasani cikin asibitin yace su shaqawa JJ din phamialiasinon shida 'dayan likita dinda yatayasu aikin sace JJ din su mutu su jefarda gawarsu ko Ina suka samu ciki asibitin su gudu.


Hakan kuwa akayi suna shaqa masa Basu tsaya duba koya mutum ba Suka Shaqawa dr shima atake ya mutu Suka fito tareda cinnawa gurin wuta suka tafiyarsu Saidai suna fitowa yaran Zaki sunga fitarsu Suka bisu nan Suka gudu dayake da baqar mota suke atake suka guje musu.


Ahankali wutar tafara yin yawa hartanayi sama nan aka lurada gobara a dayan bangaren asibitin da ba'a zuwa sbd ko gamasa ba'ayiba.


Atake aka fara Kiran fire Bridget sbd ganin wutar naci sosai.


Koda su nano Suka dawo Suka sanarda Zaki take yagane gawar JJ ce agurin nan hankalinsa yatashi Suka fara kashe wutar yanajin kamar yashiga ciki ya fiddo gawar JJ.


Qurmus wutar ta cinye gurin ba'a samu ciro gawar JJ ba sai asuba inda gawar ta cinye ba'a ganesa gabaki daya ya canxa.


Gawa 'daya Suka gani Suka tabbatar JJ ne kawai kenan aciki suka kunna wutar.


Sabon kukan baqin ciki na zuci Zaki yayi zuciyarsa na daukar radadin Rashin JJ,

Kallon qonanniyar gawar JJ yayi ya rintse idanuwansa dasukai jajir yanajin zafin zuciya Dan kuwa ya tabbatarda wannan kisar wulaqanci ce akayiwa JJ Dan kuwa Dole akwai abinda ke boye tunda aka dauko gawar aka kawo nan aka qona.


Ido jajir yadago yakalli su nanu murya can qasan maqoshi yace"


Ku shigoda mota asa gawar muje da safen nan zamuyi jana'izarsa

Asibitin kuwa duk securitynsu da ma'aikatan dake cikinta ku sauya musu kamanni.


Dan kuwa suka Suka rufe ido Suka hau duka da fasa duk wani Abu dake asibitin Wanda yasa jama'a Suka fara guduwa Dan tsira da rayukansu Dan kuwa tuni gurin ya kaure da ihun sare sare da duka.


Shikuwa haka Suka dawo gida da gawar lokacin har gari yayi haske sosai,


Duk Wanda yaga gawar JJ Saida Imani yasake kamasa nan 'yan anguwa Suka dinga hallara cikin jimami da tausayi tareda yimasa kyakkyawar addua Dan kuwa kowa ya kadu da faruwar wannan alamari musamman Zaki daya kasa kuka sai jajir da idanuwansa Sukayi sai jijiyoyin qarfin jikinsa dasuka firfito a damtsen hannuwansa da kansa sbd tsananin nauyi da 'dacinda zuciyarsa ke masa.


Ayau duk wani Mai tashen iskanci yashiga taitayinsa Dan kuwa kada qaddara da tsautsayi takaika kutsawa huruminsa.


Cikin gidanma sosai Suka tausayawa JJ musamman Nadia dake kuka sosai sbd JJ shine mutum mafi kusa da ita mai yaye Mata kewar kadaici da damuwa Dan kuwa shine yafi kowa Bata kulawa,


Shine mai zaunawa yayita yimata fira duk da Bata iya basa amsa Amma sunajin dadin firarsu.,


Shine take yiwa kallon 'dan uwa mafi kusa data bawa mahimmanci arayuwarta bayan babanta da zaki Saidai ayau tayi rashinsa adaidai lokacinda take buqatarsa kodan yanda zata fuskanci wannan aure da aka hada da Wanda batako cikin duniyar gabansa.


Wani 6angaren kuwa Zaki take yiwa kukan sbd tasan yanacikin qunci mai yawa na Rashin JJ tunda tasan waye JJ agurinsa,Bata taba ganin abinda Zaki yafito yanuwa duniya tsananin qauna da son dayake masaba bayan JJ Dan haka tasan yau yayi babban rashinda zai ringa quntata zuciyarsa.



Qarfe Tara akayi jana'izar data Tara 'dibbin mutane harda dikko Dilla da 'dansa tareda 'dibbin securities dinsa  aka watse.


Babu wani zaman gaisuwa da zakin yayi duk Wanda yayi gaisuwa wucewa yakeyi sbd zakin ko qofar gidan bai zaunaba Yana cikin dakinsa sbd tsananin ciwon Kai dayake fama dashi ko hayaniya bayaso shiyasa yau ko iya talatu Bata saki dabbobinta ba sbd ma karsu damesa da kukan akuyoyi yanxu ayi Mata waje dasu.


Kawun nema Suka zauna a qofar gidan shida su mal idi suna karbar gaisuwa duk da yawanci ire iren mutanensu ne masu masu wando a sabule da dinkin sare sare fuska sune masu zuwa gaisuwar Kuma duk Wanda yazo yayi saiya miqe sbd Rashin ganin sarki agurin.


Nadia har dare bata hangi fitowarsa daga dakinsa ba saitaqara jin zuciyarta na nauyi musamman tunowa da dah JJ nanan bazai barsa da damuwaba da yanxu yabisa yaji lafiyarsa ko Kai masa abinci.


Tana bakin gurin wanke wanke tsakar gidan tana alwalar ishai taji motsin fitowarsa daga dakin sbd qofar dakin datajiyo qarar anbude

Zuciyarta tafara bugawa da sauri 

Take hannuwanta suka Dan fara rawa takasa motsawa tana jiran jin Ina yayo sbd so take ta tashi tabar gurin tun kafin yaqaraso ya rage zafi akanta.


Cikin gidan yayo jikinsa sanye da three quarter da vest black sai towel a hannunsa da kwandon kayan wankansa da fitila kasancewar Babu nepa.


Tana dainajin takunsa ta hadiye miyan fargaba tareda miqewa tsaye tana qoqarin daidaita numfashinta dake fita da sauri ta juyo kanta aqasa batareda ta kalli fuskarsaba ta nufi bucket dake gefen durum na ruwa tafara zuba masa hannuwanta na rawa sbd tasan abinda yake nufi da tsayuwar dama ta Saba ko ita ko JJ ne masu masa wannan aikin.


Tana gama zubawa ta 'dauka takai har cikin bayin ta ajiye zata fito shikuma zai shiga tayi saurin matsawa gefe daga ciki.


Dattiya ne yashigo gidan da fitilarsa dataji sabbin batir sbd haske ya hango abinda ke faruwa ya zare ido da qarfi  take yaji hankalinsa na neman tashi Sam yama manta da cewar Nadia matar zakin ce yanxu a diririce ya qarawa fitilarsa haske murya a zabure Yana cewa"


Ke Nadia me kikeyi agurin???

maza baro gurin nan zo nan ki wuce daki kafin na karya Miki qafafu.


Yanda yayi maganar yasa Zaki juyowa ya kallesa sbd sosai sautin tsoron haduwar tasu ta fita a muryarsa dakuma rudewa wadda baitaba ganinsa da itaba.


Batareda ta dagoba Sum sum ta fito ta wuce ta gaban baban ta shige daki qafafuwanta na cigaba da rawa.


Baban yabita da harara Yanajin wani irin takaicin ganinsu a keben...

Shidai wlh yaga takansa da Zaki arayuwarsa..


Kota kansu baibi daga ita har uban nata yarufo bayin Yana zare vest dinsa.



Washe gari tunda safe tahau ayukan gidan kamar yanda tasaba harta gama tafara wanke wanke tana gab da gamawa taji motsin fitowarsa daga dakinsa take tafara daburcewa tana qoqarin cigaba da aikin Saidai jin muryarsa a bayanta Yana waya da alee dikko yasa ta qarasa rikicewa har batasan lokacinda ta 'dora hannunta da qarfiba kan wuqa ta caketa take jini yafara fita tayi saurin dafe gurin har lokacin hannuwanta rawa sukeyi.


Rintse idanuwansa yayi cikin takaicinta tareda datse wayar cikin tsawa yace"


Tashi kibar nan kafin na taka wuyanki wuwuyar yarinya.


Da sauri ta miqe jikinta na qara daukar rawa ta nufi daki ta shige da sauri tana sakin hawayen datake riqewa na azaba dakuma tsoronsa.



Dattiya da tunda yaji muryar zakin yataso da qarfi daga kwancen dayake ya labe Yana kallon abinda ke faruwa Dan gabaki daya yanxu yarasa nutsuwar zuciya idan Zaki na kusada Nadia Sam har cikin ransa bayason su kebe ko yayane Dan kar Zaki yakaisa yabaro.


Zaki na luredashi yaja qaramin tsaki tareda fasa dibar ruwan brush dinda zaiyi ya fice sbd haushi da takaicin dattiyan da Kuma nadiyar

Da JJ nanan da yanxu baishigo yaga wannan abin takaicinba.




***


Kwana bakwai kenan da rasuwar JJ tuni aka fara mantawa dashi aka hau harkoki Saidai Zaki da mutuwar take zaune daram cikin ransa Dan kuwa haryanzu Yana son gano abinda yafaru musamman da alee dikko baice komaiba gameda muguwar barnarda akayiwa asibitinsa saima sake qarfafa masa dayakeyi gameda alamarin.



NADIA kuwa tuni duk wani kyalli da lallen amarci ya goge aka cigaba daga inda aka tsaya na rayuwar gidan,


Tananan ayanda take da yin duk wani aikin gidan na iya talatu,

Saidai yanxu da aikin suka dan qarar Mata sbd abubuwa da dama da JJ keyiwa zakin itace keyi yanxu kamar Kai masa ruwan brush har qofar dakinsa kullum da safe sai zuwa fitoda plate ko kular abinci idan a gidan yaci abinci shi dama aikin Kai ruwan wanka tasaba tuntuni tun ummansu nanan.



Dattiya kuwa tuni abun duniya ya ishesa sosai yasaka musu ido duk yanda yaga ta nufi dakin Kai wani Abu yake zuwa daga bakin soron ya tsaya Yana wayar qarya da 'yar Tecno dinsa da keys duk sun goge harsai yaga ta fito kokuma ya azalzaleta da Kira,


Idan Kuma zakin ne yashigo haka zai dinga Ware ido akansu harsai yaga yafice

Har wani yamutsewa yayi sbd daga hankalinsa da yayi Wanda kullum saiya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin Zaki Dan kuwa badan balainsu ba da yanxu tana gidan mijinta Bello baida wannan fargabar.


Cikin takaici iya talatu dake zuba 'dan gum din gyaran takalmi a cikin matsin datake hadawa na kayan matanta tace"


Wannan halin daka dauka gwarama ka ajiyesa Dan Banga dalilin wani kasawa da tsarewaba,

Kasan bakason su kebe ka daura musu aure

To nidai kar gurin 'bare 'barenka ka fadamin kan saqe saqen Dana Shanya nayin tsimi.


Katseta yayi da cewa"


So kike insaka ido ya fake da aure tun yanxu ya lalatamin yarinya......


Laaaaaahhhhh haaa ilahh,dattiya daga maula Kuma sai saninka duk ya bace,

Ni talatu yau mezanji daga bakinka?

To kaga tun wuri ka aje wannan maganar Dan kuwa idan Zaki yagama warwarewa daga jimamin Rashin jabeeru yagano wannan abinda kake saqawa aransa game dashi to fa zaku komawa halin ne,


Shi baya ragar maka kaikuma baka riqe tsufanka

Amma Ina maganar an daura aure Kuma wata maganar bakason kebewarsu na fitowa.


Kallon takaici yamata cikin ciwon ran dabaisan yazaiyi dashiba yace"


Wlh nidai ancuceni,

To wlh bazan yarda na xuba ido inaji Ina gani nagama guje gujen gujewa hada iri da 'yan ta'adda ba nazo na qare da jika daga tsotson sarkin Yan ta'addanba,

Idan shi sarkine a dabancin me kike tunanin zaa haifarmin??sai Wanda zai rabani da qafafuwana Kinga ya qarasa aikinda ubansa bai qarasaba.


Kallon uku kwata ta masa tana qarawa 'dan matsinta gum tace"


Saika raba auren tunda bakason samun jika karkaxo ka ishemu da wannan leqe leqen.


Miqewa yayi Yana cewa"


Kibar zancen nan karna Kuma jinsa aure Kam dama ai rabasa zanyi Dana samo Mata mijinda baida tsoro ba kamar wancen lusarinba Bello.


Ficewa yayi daidai lokacinda zakin yafito bayi daga wanka Kuma dukkanin zancensu yaji ya girgiza Kai sbd takaicin zancen Wai shine zai tsaya lalata 'ya.


Qaramin tsaki yaja Yana ficewa daidai tana fitowa zata wanke hannu Babu ko dankwali akanta.


Cikin idanuwansa nata idanun Suka sauka ba zato.



Post a Comment

0 Comments