TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 8

 #MAMUH.*_Buri daya_*

*_Mamuhgee8_*

'Dagata yayi cak tana buge buge yakwantarda ita qasa tareda danneta Yana neman wuyar rigarta inda zai zura hannunsa.,


Sake lalubar kofin silverta tayi hankalinta a matuqar tashe ganin rabata da mutuncinta zaiyi Dan kuwa tuni ya farka rigarta dataqi Bari hannunsa yahau kan qirjinta da kyau.


Wani irin kuka takeyi mai qarfi Saidai ba sauti,


Hannunta ne ya sauka akan kofinta ta wuwuri kofin ta jefa saitin qofa da qarfi gashi qofar itama langa langa ce.


Sautin qarar sai akan kunnen Zaki sbd hakanan yau yakasa bacci Wanda JJ ma ganin hakan yakasa bacci.


Dattiya ma yaji ya miqe yataso da fitilarsa Yana fitowa tsakiyar gidan gabansa yayi mummunan faduwa jin motsi mai qarfi Yana fitowa dakin nadiyar.


Sbd tashin hankali sakin fitilarsa yayi ya banka dakin da qarfi Yana kiran sunanta hankali tashe.


ba zato yaji mugun bugu a bakinsa a gigice ya dago cikin duhun ya riqo hannun Nadiya Yana qoqarin qwaceta ban qaton ya haushi da bugu.


Tun lokacinda kawun yakira sunan Nadia ya rufe idanuwansa ahankali sbd jin jikinsa nafara rawa.


JJ ne yayi saurin miqewa daga kwance yadauki fitila da wata sharbebiyar kakkaifar Adda yafito ya nufi tsakar gidan.


Bayan fitars JJ sake rintse ido yayi wannan karon numfashinsa yaji Yana shaqewa kamar  mai asthma.



JJ na isa yaga abinda ke faruwa nadiyarma kamar ta suma ga kawun yariqeta yaqi sakarwa shegen shikuwa dukan hannun kawun yakeyi Yana janta.


Cikin tsananin tashin hankali da baqin ciki jj yakaiwa kb din wani mugun naushi a fuska Saida yasaki wani razanannen ihun daya tayarda sauran mutanen gidan duk Suka fito.


Sunan Nadia da kawun yasake Kira da qarfi yasa iya talatu kallon kayanta dasuke yage tafara salati tana tsinewa kb.


Shaqosa JJ yayi a fusace ya daga hannu zai Kai masa mugun duka kb din ya daga hannu zai tare sai ganin hannun sukayi a qasa jini na wani irin tsirtawa wani guntun fitsari iya talatu tasaki zainab kuwa gabaki daya tasaki nata fitsarin sbd Basu taba ganin wannan tashin hankalin ba.


Dukkaninsu juyowa sukayi sukaga Zaki riqeda addar da JJ ya ajiye.  


Atake kb yafadi Yana ihu da qarfi sbd ganin hannunsa a qasa ga Zaki ya sare,


JJ ne kawai baiji tsoron ganin jini da abinda Zaki yayiba tunda sun Saba gani aikinsu ne,


Shaqo kb din yayi Zaki ya hanasa tareda jawo kb ko gani bayayi sbd tsananin halinda yake ciki yau idan bai raba kb da duniyaba bayajin abinda yakeji zai fada masa,


Rintse ido yayi ya hangota kwance some jikin kawu kayanta dake babbarke ne suke neman haukata qwaqwalwarsa.


Wata sharbebiyar wuqa ya fizgo a jikin jj ya yaga wandon kb din da ita ya daga da qarfi zai sare masa gabansa JJ dasu nano dasuka firfito daga dakin qofar gidan Suka riqesa suna Allah ya huci zuciyarka sarki Amma karka masa wannan hukuncin,


Cikin hasala jj yace"


Neyo kabarmu dashi,

Yataba hurumin da ba'a tabawa zamuji dashi.


Wurgi yayi da wuqar Yana yamutsa kansa jin yake kamar ya cinnawa kansa wuta sbd zafin da zuciyarsa keyi,

Jiyake abinda ya tokare masa a qirji kamar zai kashesha,

Da qarfi yace"


Ku sauyamin kamanninsa yanda ko uwar data haifesa koya warke bazata ganesa ba,

Ku karya sauran dayan hannunsa daya taba suturar dake jikinta,

Ku karyamin qafafunsa,

Ku kasheminshi,


Ruwa JJ yayi saurin kawo masa yayi wurgi dasu Yana cewa"


Zuciyata zata saukane idan nagansa kwance cikin mummunan yanayi.


Aikuwa wani irin duka su JJ dasu Nanu sukai masa duk da dare ne atake gurin yacika Dole aka Kira police ganin zasu kashesa.


Koda police sukazo kb kawai Suka dauka sukai asibiti dashi tareda gundulen hannunsa a leda.


Cikin gidan kuwa ruwa zainab ta debo qafafunta da hannuwata na rawa taba baban ya kelayawa Nadia


Atake ta farfado a firgice cikin tsananin tsoro jikinta na rawa 

Zainab tayi saurin rungumeta tana hawaye itama sbd kaf dinsu gidan suna tsananin son junansu Saidai halayensu ne kesa ka dauka basason junansu.


Baban kuwa miqewa yayi yace suje dakin zainab su kwanta tare.


A Daren Kam kowa bai koma bacciba musamman Zaki da dattiya daya qara gama yanke shawarar aurar da ita cikin qanqanin lokaci.


Washe gari duk wasu yaran Zaki Saida sukai baqin cikin wannan Rana sbd sarki dai ranar ko qofar gida bai fitoba ataqaice dai Saida ale dikko ya Aiko masa da babban likitansa ya dubasa sbd ko miqewa tsaye daidai ciwon kirji mai qarfi yaqi Bari yayi.


Kb Kuwa ba'a mutuba Amma anci wuya Dan kuwa gabaki daya a kumbure yake ga jini daya zubar sosai sai qara masa akeyi gashidai yanxu baida hannu daya Kuma hukuma nagani tayi biris yanajin sauki aka sallamesa yayi alwashin saiya Rama abinda sarki yayi masa shida yaransa Dan kuwa shima baya tafiya.



Bayan kwana biyu duk tasake zama wata iri da ita sbd sanyi data qarayi sosai gabaki daya rayuwarta mutum biyune rayuwarta,BABANTA da YAYA ZAKI tunda abin nan yafaru Zaki ya daukewa 'yan gidan wuta gabaki daya sai shakkarsa taqara shigarsu sai kaffa kaffa sukeyi musamman ma ita.


Baba kuwa tuni yasamu mal zailani da maganar auren da 'dansa bello yace yanaso na Nadia.


Babu wani dogon qunbiya qunbiya Suka gama maganarsu tunda kowa yasan kowa tare sukai samartakarsu.


Bayan mal zailani yayi magana da bello kan maganar shima yace a shirye yake asa Rana kawai.


Har gida mal zailani yasamu dattiya shida wani yayansa da abokinsa

Shima dattiya yakirawo mal idi

 Suka sake magana akai neman aure Suka bada kudin nema dubu goma.


Washe baki dattiya yayi ganin 'yan dubu dubu Yana cewa aransa""Ankwana biyu baa haduba"


Karba sukayi aka yanke ranar aure wata biyu masu zuwa insha Allah.


Suna tafiya dattiya yasake qirga kudin Yana murmushi yaciro dubu biyu ya miqawa mal idi ya zuba saura aljihu Suka fita.


Lokacinda ya sanarda iya talatu maganar kallonsa tayi cikeda haushi tace"


Kai yanxu Dan Allah shine ka karbi kudin gaisuwar zuqeqiyar yarinya kamar Nadia a dubu goma??


Kunna radio dinsa yayi Yana kamo gidan fm yace"


Eh ko dubu biyar ne dai na bayar

Lokacinda wani shegen zai sake shigowa ya asarani kinacan kina baccin wahala ko dubu 'daya bazatayiba.


Tsuke fuska tayi tana hararar qafafunsa dasukai 'yar banzar qura tace"


To nidai karka doramin wainnan qafafun masu dau'da a tabarmar sallah ta tunda Nima koda nahada kudin gumina nasiyeta kanacan kana yawon ta zubar a gari.


A kufule ya kalleta yace"


To ko natashi ma akai gaba daya?

Talatu kin renani waike bakisan darajar miji bane koyaushe bakimin 'daa sai gasa baqaqen maganganu.


Tabe baki tayi tana cigaba da hada garin matarta data gama zubawa 'yar fulawa.


Miqewa yayi Yana masifa ya zari babbar rigarsa ya fice koba komai yau basuje sana'ar ba gwara ko ita yaje yasamo ko dubu biyu ko 'daya yamaga ana taro acan gaba.


Da harara tabi bayansa tana cewa"


Kadaiji dashi

Lokacinda jarababben mai mulkin gidannan zaiji ka karbi kudin gaisuwar nan ai lokacin ne zanbaka tabarmar jinyar kanka.


Zainab dake fitowa cikin daki tasaki dariya sbd tana jinsu sbd itama tasan daga baban har bellon na ruwa tsundum.


NADIA kuwa yitayi kamar batasan abinda ke faruwa tacigaba da sha'ainin rayuwarta.




Post a Comment

0 Comments