TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 11_12

 *QUESTION OF THE DAY*


Wani sahabi ne ya sadaukar da dukiyar shi da rak’uman shi a lokacin da manzon Allah (s.a.w) yake cewa "wa zai ba Allah rance, ya biya sa ranar tsayuwa?






11&12


Washe gari mun so mu makara kasancewar har yau ba mu wartsake gajiyar purnishment d’in da yaya Faruk ya sa mu ba. Yaya Khalil ne zai sauke mu a makaranta daga nan shi ma ya wuce School saboda yace akwai wani assignment da zasu yi submitting da safe.

A hanyar tafiyar mu, yaya Khalil ne ke ta mana nasiha akan mu dinga kiyaye abin da zamu dinga ja ana bamu purnishment ko a dake mu saboda yanzu mun girma.

Yaya Khalil ne ya kalli Anisa yana cewa "Anisa yau in zan dawo sai in tawo da mai gyaran targad’en dan na ga ma ‘kafar kamar tayi sauk’i"

Dariya muka yi gaba d’aya saboda mun san yaya Khalil tsokanar ta yake yi.

Cikin shagwa’ba tace "haba yaya Khalil! Har da kai ake tsokana ta, bari in na koma gida sai na fad’a ma momi saboda tace ya daina bamu irin wannan purnishment d’in…."


Yaya Khalil ne ya katse ta da cewa "A’ah sister, ka da ki fad’a ma momi, yaya Faruk yana yin hakan ne dan taimakon ku da inganta ku, ba za ku gane haka ba sai nan gaba, kuma lesson d’in waec da neco da kuke gani, yana da matuk’ar mahimmanci a lokacin jarabawa, mutane ne basu gane ba"

Amsa masa muka yi da "insha Allahu zamu kiyaye yaya Khalil"

A raina kuwa addu’a nake yi Allah in ya tashi bani miji ya ba ni irin yaya Khalil saboda saukin halin shi dan duk matar da ta samu mai hali irn na yaya Khalil ta ji dad’i ba irin yaya Faruk ba, in ban da miskilanci da mugunta ba abin da ya ajiye.

Har ya ajiye mu a school muna hira cikin farin ciki da nishad’i kamar kar mu rabu.




Yau ma kamar kullum, in dai aka tashi break a school, ko ni in je class d’in su Anisa ko ita tazo class d’in mu. Yau ma hakan take saboda ni ce yau naje class d’in su.

Samun ta nayi tana rubutu na zauna kusa da ita ina cewa "ke kuma me kike rubutawa ne tun d’azun gashi har an fita break baki gama ba"

Amsa min tayi da "malamin maths ne ya ba mu classwork yace muyi mishi submitting kafin ayi closing, kin san shi da sa purnishment kamar yaya Faruk, na ma kusa gama wa"

Kallon ta nayi cikin zolaya na ce "sister wata shawara na kawo mana, mai zai hana yau kar muyi lesson mu tafi gidan ku tun da nasan momi baza ta bari ya dake mu ba ko ya samu purnishment tun da kinga bayan lesson d’in school muna zuwa ran weekend, ba sai mu dinga d’an hutawa ba…."

Ban k’arasa Magana ta ba Anisa ta zaro ido tana cewa "in kin ganni a lahira kai ni a kayi, ba inda zani, kina gani har yanzu k’afa ta ba ta daina min ciwo ba"

Hararar ta nayi ina cewa "ke wani sa’in ba kiyi ba, kin cika tsoro, idan muna nuna muna tsoron shi haka zai dinga mana, kin ga gwara mu nuna mishi mun girma ba kamar yadda yake mana kallon yara ba"


Anisa tace "ni fa ba inda zani, in kin ga na k’ara guduwa daga extra lesson to anyi closing d’in lesson d’in ne kuma kina dai ji Ummu da yaya Khalil suka mana fad’a akan haka shine zaki ce mu tafi kuma ai gaskiyar yaya Faruk ne da yake cewa ba mu girma ba, ni kam ban girma ba"

Ai ban san lokacin da na fara dariya ba ina cewa "ke ce dai ba ki girma ba amma ni kam na girma, kina gani zamu yi graduation d’in gama secondary school, yanzu ai mun zama big girls" na ci gaba da dariya ta.


Anisa ce ta harare ni cikin wasa ta ce "ke matsalar ki ba kya raina abin abin dariya (A raina nace kamar Fauxia mb ta Kainuwa writers) yanzu miye abin dariya, ai duk cikin girman ne, da yaya Faruk ya zuba miki wire a jikinki ki kace yaya Faruk dan girman Allah kayi hakuri, dan darajar momi da dadi da kuma darajar matar da zaka aura da kuma darajar kakin da kake sa wa"


Dariya muka fara yi saboda ni sai a lokacin ne maganar ma ta ban dariya, cikin zolaya na ce ai gwara ni k’afa ta ba tayi rawar awilo ba kuma ni ba a tashe ni a barci na ce dan Allah yaya Faruk kayi hak’uri ba za mu sake ba"


Dariya muka sake fashewa da ita tare da tafawa yayin da Anisa ke cewa "in k’afar ki ba tayi rawar awilo ba amma ai kinyi a sosa mata san da ya zuba miki bulala"


 dariya muka k’ara yi muna maida abin da ya faru jiya.


Aisha k'awar mu ce ta nufo inda muke tana cewa "kuna jin dad’in ku, wannan hira haka da dariya fa"

Murmushi nayi na ce "ko ke kika ji abin da ya faru sai kin yi dariya" nan na zayyane mata yanda muka yi da yaya Faruk, ita ma dariyar tayi inda muka ci gaba da hirar mu har aka buga k’ararrawa na koma wa class.




Tun da yaya Faruk ya dawo ba ni da sukuni domin a takure nake, d’an chat d’innan da nake yi ba dama sai dai in yi shi a ‘boye, gashi ni ba inda nake zuwa, in dai yana gidan mu to ni ina d’aki saboda kiyaye abin da zai tanka min, ga wata tsurfa da ya fito da ita, in dai yana gidan sai ya tashe ni na dafa mai abinci ko yace wanda aka yi ba shi yake marmari ba ko yasa ni had’a drink.

Wannan hutun yaya Faruk d’in ya zaman min bak’in hutu saboda ya hana ni sakat da jin dad’in rayuwa ta.



Yau Allah ya amsa addu’a ta saboda jiya muna hira a falo naji Abbu yana fad’a ma Ummu yau yaya Faruk zi koma Abuja, dad’in da naji bai misaltuwa saboda nasan zan samu sauk’i na takurawar da ya min.




Ina zaune a falo ina kalllan philliphine series film na (endless love), wani scene da aka nuno shi ya d’auki hankali na inda aka nuno jenny kwance a jikin johnny san da suka yi aure inda a asibiti aka tabbatar tana d’auke da blood cancer, yanda jenny yake lallashin ta yana kwantar mata da hankali yayin da ita kuma take kuka, wani scene aka k’ara nuna wa suna zauna a k’ark’ashin bishiya inda jenny ke kwance a jikin johnny yana ba ta caring duk saboda blood cancer da take d’auke dashi gashi likita ya tabbatar musu ta kusa mutuwa.A gaskiya film d’in ya d’auki hankali na ga tausayi kamar in yi kuka dan sai da naji k’walla ta tarun min a ido, don haka ne ko motsi ba na so nayi.

Mai da hankali na nayi gun allon tv inda aka nuno jenny ta mutu a jikin johnny yana rungume da ita, hawaye ne yake zubo mai a idanun sa saboda kan ta mutu tace ya mata alk’awarin ba zai yi kuka ba.

Saboda tausayin johnny da ya kama ni ban san lokacin da na fara kuka ba saboda ganin ya rabu da masoyiyar shi ta gaskiya wanda suka sadaukar ma junan su da soyayya tun suna yara har kawo yanzu da suka girma.

Duk da ban san dad’in soyayya ba saboda ba na yin ta amma sai da naji wani feeling a raina saboda wannan shine soyayyar gaskiya, lallai wannan film d’in yaci sunan shi (endless love)

Soyayyar yahudawa kenan ma bare a je ga wadda Annabin mu Muhammad (s.a.w) ya koyar damu.

A raina na ce nima Allah ka bani wanda zai so ni tsakani da Allah da nuna mun caring da soyayya.

K’amshi da ya cika d’akin ne yasa nayi saurin d’ago kaina don ganin wanda yake sanye da wannan turaren.

Yaya Faruk ne cikin kakin shi na soja, fuskar nan a murtuke kamar bai san wata kalma wai ita dariya ba. kallo na yake yi kamar bai t’aba gani na ba, ganin abin nashi ba sauk’i yasa na sunkuyar da kaina k’asa.

"Teemah" naji ya kira suna na.

Cikin sanyin murya na amsa da "na’am yaya Faruk ina wuni"

bai amsa gaisuwar ba illah ce min da yayi "me yasa ki kuka"

shiru nayi saboda ban san amsar da zan bashi ba

tsawa ya daka min mai firgitarwa yace "ba tambayar ki nake yi ba ko sai kin ji a jikin ki"

"ba komai yaya Faruk" na fad’a cikin marairaicewar murya.

Takowa yayi ya zauna kusa dani har muna jin numfashin junan mu, shiru falon ya d’auka kamar ba mutane a ciki, can ya kalle ni yace "Teemah kina soyayya ne? 

Tambayar shi ta ban mamaki saboda nasan ba na soyayya amma saboda kar in yi laifi sai na girgiza mishi kai alamar a’ah

Ci gaba yayi da ce min "idan ba kya soyayya mai ya baki tausayi a wannan film d’in har ki ke masa kuka? tun d’azun na shigo amma ba ki lura da ni ba, kinyi concentrating akan film d’in, if you are not in love, why will you worry yourself in this movie at your age?

Shiru na mishi saboda ni dai nasan ba na soyayya kuma nasan Abbu ma bazai bar ni ba har sai na shiga jami’a.

Yaya Faruk kuwa duk da film d’in ya burge shi kuma ya tayar mai da tsohon mikin da ke cikin ranshi amma bai nuna ba illa wani sabon lamari da ya shiga ranshi.ci gaba da nazari yayi a cikin ran sa yana wani tunani na daban, ko da yake nesa ta zo kusa, ba ya son yin sake, yana bin komai ne a sannu.




Post a Comment

0 Comments