TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya hakima page 7_8

 πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»

         *GIMBIYA HAKIMA* 

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»




 *🌎MANAZARTA* 

 *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–Š️


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»``` 

________________________________




  _STORY AND WRITING_ _BY_ 

    _Jameelah jameey πŸ–‹_ 






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*



 _Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


 ```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




07&08




"Ni wallahi Hakim kina bani mamaki, "mamaki name kenan Aliyu? 



"Kai dai rayuwarka haka kake ba ruwanka kamar ba dan sarki ba.  



"Hmmm Aliyu kenan to muye dan ina dan Sarki? Ai duk daya muke a wurin Allah banbancinmu shine wanda yafi bauta mashi.. 



"Hakane amman duk da haka maganar gaskiya kana bani mamaki ace dan sarki kamar kai dan Sarkin ma na Zaria amman  kana rayuwa cikin tallakawa gaskiya ina mamaki ko ni da nike dan waziri ai bani kallar wannan sai dawowarka nike shiga cikin su... 




"Kenan da baka shiga cikin tallakawa? "Gaskiya bani shiga ai sai su renani.. 



"Kaga niko ina shiga cikin tallakawana dan nasan mai suke bukata, sanann nasan maiye rayuwa, kasan ko saboda mai nake yin lectured a A. B. U? 




"Aa nidai nayi mamaki ace kamar ka kake wani lectured a wata A. B. U, da daman ina san nayi maka maganar kawai fuskace ban gani ba... 



"To na zabe yin lectured saboda nasan wani hali al'ummar kasar Zaria ke ciki, san nasan wani hali tallakawa ke ciki, mai suke bukata ayi masu, mai ake yi masu wanda basu jin dadinshi, sai kuma ina kara yin expressed akan halin mutane.. 




"Kaji dalili, Alhmdulh naji ance ankusa koma wa hutun Season kaga za'a kawo new inters student kuma ni zan dauki yan Chemistry.. 





"Gaskiya kaji dadi halinka yana bugerni, wanda bai san halinka ba sai yace baka da tausayi balle imani.. 



"Amman Hakim maiyasa baka dariya cikin tallakawa? Kuma kana san shiga cikin su dan kaga matsalarsu.. 



"Dan ina shiga cikin su shine zai sa nayi masu dariya ko sakin fuska sosai, ko ka manta nidain Yarima ne? 




"ai naga tunda kana ma'amula dasu sosai ya dace ka zama mai sakin fuska garesu sosai.. 




"Hmmm! Ai ni kai kasani haka Allah ya hallicine ban cika magana ba, ko da ko ina gaban Gimbiya Fulani, dan haka ba laifina bane yin Allah ne.. 




Hmmmm! YARIMA HAKIM kenan, dan sarkin Zaria matashi maiji da samartaka ga kuma haiba da kyau  da jinin sarauta dake yawo jikinshi.. 




Yarima Hakim, missikiline na ajin karshe dan bada kowa yake magana ba, inka ga maganar shi to shida mutun uku ne, daga Fulani mahaifiyarshi kenan sai kuma Maimartaba sannan abokinshi tun na yarinta Aliyu haidar, da wannan mutanan biyu suke ganin maganar shi mai tsawo, ko kannanshi  Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya basu ganin maganar shi balle dariyarshi abunda ke hadasu shine kawai su gaisa, ba wai wulakanci ke sashi haka ba Aa halinshi daga Allah ne wannan kenan.... 




________________________________




Washe gari tun da asuba Kuyangan Gimbiya Hakima suka fara aiki, kamar yanda ta bukata.. 



"Ladi, "Naam Larai.. 



"A gaskiya Ladi muna bautuwa a gidan nan, muna yi ma Gimbiya Hakima bauta amman bata gani, yanzun ji yanda muke ta wanann wahalar tun da asuba muke abu daya yanzun har bakwai tayi kuma tace kafin karfe takwas mun gama komai.. 



"To ya zamuyi Larai tunda munfito a bayi? Ai hakuri ya zama dolenmu, kuma ai daga wannan mopping din mugama sai mu jira fitowarta ta bamu umirnin mu tafiyarmu.. 



"Aiko dai Ladi, ai mu mungode Allah da ta fidda mu a madafa da Jiya mu zata wanka ma mari taci mana mutunci kamar yanda ta saba... 



"Eh mana, da man su A'bu basu cika haduwa da itaba tunda gyaran gida kawai suke suna gamawa kuma inta gani zasu kama gabansu ba kamar muba dasu Inna Lantana da ba mu rabuwa sai dare, kinga ai munfisu shan wahalarta.. 



"Sosai ma, su daga Jiya kawai fa har sun fara koke-koke sun bani su ya zasuyi basu iyawa da aikin madafa, shine nace masu muma haka muka sha wuya har Allah yasa ta chanza mana aiki... 



"Ku ina fatan kun gama ga maigirma Gimbiya Hakima nan fitowa, "mun  gama yanzun muka gama, sai yanzun kenan Allah yayi zata fito yar-mulkin! 



"Ke Larai ba ruwa, ki gyara kalamanki yanzun indan tajiki kiyi ya? 


"Sai tasa a hukuntani, kuma hukunci na nawa ne bangani ba indai na Gimbiya Hakima ne.. 



"Nidai ba ruwana kunga tafiya wajen masu madafa naga har yanzun basu fara fito da abincin ba ga shi har Gimbiya Hakima ta tashi na niyar fitowa ma... 




"To Ba'ba Bilkisu a dawo lafiya, "Allah yasa Ladi ni na barku lafiya.. 





"Ku yan madafa Ina fatan kungama dai ko? 


"Eh mun gama yanzun muke shirin kai abincin wajen cin shi.. 



"To barkan ku, kutaso mu tafi kawo na taya ku dauka A'bu.. 



"To Ba'ba Bilkisu mungode, ni tunda dazun rabon da naga Inna Lantana, "kin san aikin Gimbiya Hakima ba karewa yake ba, tana can ta shafa mata mai.. 




"Allah sarki Inna Lantana, duk dai sannunmu da bauta, "yauwa kunga har mun iso, nan suka jera abinci a bisa dining table bayan duk kowace ta gama abunda  take suka zauna zaman jiran fitowar Gimbiya Hakima... 



Gimbiya Hakima itace bata fito ba sai karfe goma, bayan su kuma tun karfe takwas kowace ta gama aikinta... 




"Takawarki lafiya yar'masu gida, Gimbiya Hakima uwar marayu, tar sarki jikar sarki.. 



"Bilkisu! "Naam Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima anfito lafiya? 



Gimbiya Hakima bata ansa ba sai da tayi kusan ten minutes sannan tace "Lau, Ina fatan kowa ya gama aikin shi? 



"Eh Alhmdulh duk sungama umirnin Gimbiya kawai suke jira ta aiwatar a garesu.. 



Sai da ta mula tasha iska sannan ta tashi Bilkisu da Lantana suna biye da ita suka duba masu shara, sai dai suka gama zagaye sannan suka dawo ta zauna wajen abinci.. 



"Ace ma masu Shara su tafi su ban waje, "angama Uwargijiyata, nan Ba'ba Bilkisu ta fito main parlour inda suke tsugune tace.. 



"Ku su Larai, Gimbiya Hakima tace ku tashi ku tafi aikin ku yayi kyau, "godiya muke, nan suka tashi suka tafi suna Alhmdala cikin zuciyarsu sun rabu da Gimbiya Hakima lafiya ba tare da ta ci masu mutunci ba... 



"Lantana! "Naam uwar marayu, "Uhmm, abunda Gimbiya Hakima tace kenan Amman har Inna Lantana ta gane abunda take nufi🧐



Wai ashe tace nufin ta tashi ta zuba abinci ta fara ba su A'bu suci sannan ta ci itama wai Gimbiya Hakima ba dai masifa ba😁



"Ranki yadade angama zubawa, kallonta kawai Gimbiya tayi, nan take Inna Lantana ta shiga taitayinta.. 




"Murja bissimilla ga abinci, "to Inna Lantana, nan suka ansa suka ci sai da kowace tayi three spoon sannan suka ajiye.. 



Sai dai Gimbiya Hakima ta mula tasha iska sannan ta yi ma Lantana nuni da hannu.. 



"Gashi ranki yadade, nan Gimbiya ta fara cin abinci cikin natsuwa da kwanciyar hankali, sai da tayi two spoon sannan tace, "ku tashi ku tafi ku bani waje, "godiya muke Gimbiya Hakima... 



Bayan Gimbiya Hakima ta gama cin abinci ta aika sako wajen jakkadiya tana san yin magana da Maimartaba.. 



________________________


"Hakim! "Naam Ranki yadade, "nifa Hakim ina mamakin yanda ka makale sai kayi wannan koyawar a jami'a.. 



"Fulani ya kamata ace yanzun kinyi hakura da wanann maganar dan Allah ki saman albarka cikin lamarin.. 



"Shikenan naji Allah yayi albarka, "Amin Fulani godiya nike, ni zan wuce massalaci, "to adawo lafiya...




Nan ya fitowa shashen Gimbiya Fulani dogarawa suka goya mashi baya sunata yi mashi kirari nan suka shiga massalaci sukayi sallah bayan sun fito yaga sun kara biyo shi nan ya tsaya. 



"Wai dan Allah bana ce maku kubar yi man wannan abun kamar wani abu.. 



"Allah yaja da ran Yarima dan sarki jikan sarki, ka hanamu binka cikin gari nan ma kana cewa mubar binka, ai wannan shine aikinmu kare lafiyar Yarima sarkin gaba.. 



"To naji, amman ai ni nace na hutar daku ko? "Eh ranka dade, "to dan haka ku wucewarku nagode. 



Haka suka tafi suna mamakin saukin hali irin na Yarima Hakim shi dai bai damu da mulki ba.. 



"Wai Kilishi ya ina maki magana kinyi shuru, tunanin mai kike? 



"Hmmm! Kedai bari Zulaha, ina tunanin yanda zamu kauda wanann dan iskan yaron kullun da abun nike Kwana muke tashi, duk hanyar da muka bi bata bulewa, kullun sai fi yaran mu yake.. 



"Wannan abun nima yana damuna Kilishi, ban ki na bude idona naga Hakim baya numfashi a doran kasa... 



"Baki daya Yaro shida uwarshi kallon banza suke ma kowa cikin gida, wato dan sun samu boka wanda yafi namu aiki shiyasa, sun mallake gida kina ga Maimartaba baya jin maganar kowa cikin gidan nan sai ta uwarshi.. 



"Kuma muma mun haifa cikin gidan nan fa, kuma nice babba cikin gidan nan, dan kawai an rigani haihuwa sai a daukeni sakara cikin gida ko magana ta ba'atsayawa a saurara.. 




"Karki damu Gimbiya Zulaha zan san abun yi, dole YARIMA HAMID zai gaji mulkin Maimartaba ba YARIMA HAKIM ba, dan Yarima Hakim da wata hudu ya girma Yarima Hamid kinga ko ya zama dole mulki ya fito dakin matar farko ba ta biyu ba.. 




"Aiko dai Gimbiya Kilishi, shiyasa nike sonki, dan kina gane gaskiya.. 



Haka sukai ta tautaunawa yanda zasu samu su kawarda Yarima Hakim a duniya duk saboda mulki.. 



______________________________



"Ranki yadade Jakadiya ta aiko da sako, "mai tace Bilkisu? 



"Cewa tayi Maimartaba yana san ganinki.. 



"To ace mata gani nan zuwa, "angama Uwargijiyata.. 



"Uwani kije kice tace gata nan zuwa, "to shikenan Lantana.. 



Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi.. 




Post a Comment

0 Comments