TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 38_39

EPISODE 38

Bude kofan dakin da suka sata ciki Ammi tayi tai shiru tana kallon Rashida da sai bayan su Riyad sun fada mata waye ita saita fara ganin yanayinta da mahaifinta Mujitappa dudda bawai tana kama dashine gabaki daya bane dan tana kama da mahaifiyarta but wlh tayo yanayin Mahaifinta sosai, gakuma kama na jini Allahu Akbar! Ammi saita fara tuna sanda mahaifiyarta ke kuka sosai tana cewa bata taba fasikanci arayuwanta ba, duk alokacin cikinsu babu mai iko ko wanda ya isa yaja damai Martaba a fada hakan yasa kowa yayi shiru, ijiyan zuciya Ammi ta dauka ta shiga dakin ahankali ta zauna bakin gadon tana kallon fuskan Rashidan da hawaye ke bin idanunta hannunta Ammi takai ahankali tadaura saman wuyanta wani irin sanyi ni’ima Rashida taji yasauka ajikinta kalan wanda takeji idan Mama ta tabata hakan yasa tabude idanunta ahankali batare data juyoba, ahankali Ammi tace “Rashida” tunda Rashida take arayuwa bata tabajin murya daya mata kusan shige dana Mamanta akunne ba saiyau hakan yasa tajuyo da jajayen idanunta ahankali takalli Ammi kaman yanda Ammi ke kallonta dudda yanda take cikin bakin ciki but saida taga kamannin matan da Riyad hakan yasa tagane mahaifiyar Riyad ce, ahankali Ammi tanuna kanta tace “sunana Ammi, I’m your new Mama take me as one kinji Allah jikan mahaifiyarki” hawaye taga sun taru sosai a idanun Rashida dayasa ahankali Ammi tasa hannunta tadagota takawota jikinta kankameta Rashida tayi kawai saita fashe da kuka sosai, Ammi bata hanata kukaba sai bayanta datake bugawa tace “Rashida bana fata wata rana na mutu yarana su kasamin addu’a sai kuka, burin kowace uwa shine yaranta suyita mata addu’a kidena kuka I know it’s painful but Mama tafi bukatar addu’a awajenki kinji” gyadamata kai Rashida tayi ita kadai tasan metakeji Ammi tace “gashi jikinki zafi tashi muje kiyi wanka I will call Dr tazo tadubaki” dagata tayi zuwa bayin dake dakin tabude ta shigar da ita itama ta shiga hannu tasa abayan zip na riganta taja mata shi kasa tace “bari nakawo miki soap da brush” fita tayi bata jimaba takawo soap brush sannan tafita ta tsaya bakin kofa tace “imaxa ina jiranki” tawuce tabude wardrobe na dakin taciro mata wasu simple black-shirt da skirt har kasa English shima mai slit ta back kafan ta ijiye mata akan gadon sannan takoma jikin bayin tace “imaza gani nan fa” ruwa Ammi taji na zuba hakan yasa ta tsaya almost 5min sannan tadan bude kofan kadan ganinta tayi tsaye gaban shower ruwan na dukanta da rigan da komi da sauri Ammi tashigo tana kashe shower tana kallon yanda take kuka kafin ahankali taja towel saida tafara kara mata sannan taja rigan kasa tadago ta kulla mata towel din ata gefen armpit sannan tadauki karamin towel tasa mata asaman gashinta daya jike sharkan ta kwashe takamota suka fito zaunar da ita tayi abakin gado takai hannunta tana share mata fuska tace “ya isa” tadauki rigan tasamata takai saida tagama samata sannan tasauke towel din zuwa waist nata skirt din shima takama kafanta tasa aciki tadagata taja skirt din har waist nata kafin taja towel din na saman kanta ma ta tsani kan kafin taja towel din tawuce takai bayi tadaga riganta dake bayin tasa a washing machine sannan tafito sauka tayi tana kiran Dr nata tashiga kitchen Ammi nada son girke girke da kanta dudda tanada masu aiki lafiyayyen tuwo ta debo mata da miyan kuka da man shanu tahayo sama inda ta barta anan tasameta Ammi tace “you will have to eat koba yawa okay” hannunta tasa ta gutsuro tuwon takai bakinta ahankali Rashida ta kalli hannun Ammi dake miko tuwon bakinta kawai saita fashe da kuka tana bude bakinta emotionally Ammi tai murmushi kadan tasamata sabida tagane Mamanta ta tuna mata sosai taci tuwon tana kallon fuskan Ammi, Ammi tabata ruwa tasha sannan takaita bayi tayo alwala ta daurata kan dadduma tace “yi salla bari nashigo da Dr” fita tayi daga dakin bata wani jimaba ta shigo tareda wata Dr zama sukayi saida Rashida ta idar Dr tace “sannu” dan dudduba Rashida tayi tace “bari namata allura da magani” allura tafara mata sannan aka bata maganin tasha zama kusada ita Ammi tayi takama kanta tasa ajikinta wannan dumin uwa dataji daga jikin Ammi



EPISODE 39

yasa within seconds tai bacci Dr tama Ammi sallama ta tafi Ammi tadade tana kallonta yarinyar ko Masha Allah she’s very young and so pretty daga yanayin jikinta kasan kamilan yarinya ne maza basu taba tabata ba boobs dinta kaman balbalam acike, gyaramata kwanciya Ammi tayi taja bargo tarufa mata sannan takashe wutan dakin ta tashi tafita tana rufo kofa, dakinta ta shiga taciro wayanta Babanta takira ringing daya yadaga yace “Yar Budurwan Babanta” murmushi sosai Ammi tayi tace “Buba mesa zaka biyewa shirmen su Riyad kaje ka karbamai aure batare da yan uwan mahaifinsa sun sani ba” anatse yace “Riyad namiji ne dayasan meyake arayuwa yasan inda yakemai ciwo, idan baiso yafadi agida yanada dalilansa dakuma hujjojin sa, ba yaro bane kuma ba aurensa na farko bane, jikana bai taba neman abu daga gareni ba the only time dayayi kuma bazan taba kinmai ba”. DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFI BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA Dan shiru Ammi tayi sai chan tace “Buba sun fada maka usulin mutanen”? Anatse yace “a’a” fadamai komi Ammi tayi tace “Buba banson matsala bayan mijinmu yarasu nasamu Sa’ida da fitinan matansa, banson wani matsala kuma wlh” anatse Buba yace “babu matsalan dazaki shiga shi Allah ba azzalim kowa bane sannan Allah yanada hanyoyi da dama nayin abubuwa, ba wayon Riyad bane yasa yafara haduwa da yarinyar nan tun lokacin rasuwan mahaifinshi ta ceci rayuwar sa ba, ba wayansa bane kuma yasa yakara haduwa da ita bayan shekara daya tana aiki a hotel dinsa ba, kome kikaga yafaru Yar budurwa haka Allah yaso yafaru kuma yanada dalilin dayasa komi yafaru ahakan wanda idan akai walkiya zamuga abinda ke cikin duhun inamai tabbatar miki idan sherima akama mahaifiyar yarinyar nan aka sama ciwon nan da gangan komi yakusan bayyana, abinda nakeso gareki shine ki rike yarinyar amana be a mother to her, batariga tasanmu ba tunda Riyad bai sanar dasu ba tukunna Allah kadai yasan yanda zataji idan taso tasanni until then just take care of her sannan tazauna dake a sirri sai bayan ta warware kafin gidan susan da ita kar hayaniya yasa zuciyanta ya buga kinajina” ahankali Ammi tace “to Buba” yace “akullum addu’a na tana kanki da jikokina Allah zai tsareku duka babu wanda ya isa yacutar daku wlh saidai idan Allah ne yaso hakan yafaru ban barku hakanan ba addu’a da saukan Al Qur’ani kullum cikin yinsa nake so calm down Allah na tareda mai gaskiya” gyadama Buba kai tayi tace “toh Buba nagode” katse wayan yayi tawuce tadauki kasa.

EPISODE 35

Misalin 9 ta turo kofan dakinshi tashiga da sallama takai hannu tana kunna wutan dakin, wani irin lafiyayen bedroom ne dayaji komi gawani ubansun royal bed da Muji ke kwance akai yana sanye da farin jallabiya, hasken daya gani yasa yadan bude idanunshi kadan ya kalli kofa ganin wacce ta shigo yasa ya maida idanun yarufe maida kofan tayi tarufe ta taso har zuwa bakin gadon ta zauna tace “na gaida mijina Namijin Muji! Gaisuwan girma dakuma kasaitacciyar asuba tagari gareka Mujitappa na” dan bude idanunshi kadan yayi yamaida yarufe yace “da fatan kin tashi lpy?” Gyadamai tayi tana dan murmushi tace “najika shiru tunda kadawo daga asuba kashige daki, hope lafiyanka kalau?” Dan bude idanunshi kadan yayi saikuma ya maida yarufe hakan yasa ahnakali ta mika hannu ta shafa kanshi tace “menene ke damunka eh Mijina? Nasha gayamaka matsalanka matsalata ce, farin cikin ka farin ciki nane, damuwarka damuwata ce, I’m your best friend tell me menene” dan shiru yayi saikuma yadan yunkuro hakan yasa dasauri ta dauki pillow takai bayanshi tasamai ya zauna da kyau tareda dan sakin mata murmushi yace “thank you Jummai” gyadamai kai tayi tace “bawan nan ba idan baka sanar dani abinda ke damunka ba bazan tabajin farin ciki ba, dan Allah kagayamin” ahankali yace “Jummai ni kaina bansan meke damuna ba, natashi kalau naje masallaci kalau, amman dazun nan kawai najini inajin kaina wani iri, I’m just feeling so lonely and so empty wani iri zuciyana yakemin kaman wani abu nawa dana dade ina nema yana kusadani yanzu” yadanyi shiru saikuma yasake kallonta yace “nasan munriga munyi alkawari nida ke mun rufe chapter nan tunda yan uwanki suka bamu yara har uku tun suna jarirai mu muka rainesu sun dawo namu amman yau kawai natashi inajin ni haihuwa nakeso!” Wani irin mummunan faduwa gaban Jummai yayi tacigaba da kallon mijin nata ahankali cikeda damuwa Muji yace “I want my own flesh and blood Jummai!” Yasake shiru yace “I’m 65yrs banso na mutu ban kawo d’ana dubiya ba, kina ganin ba gwara na kaara aure naga ko Allah zaisa mudace ko zamu sami baby”? Yayi maganan yana kallon Jummai data hadiye wani abu da kyar awuyanta tace “kasan duk abinda kakeso arayuwan nan inasonshi, nariga na manyanta dazanji kishi ko wani abu, nasan Samha, Badariya da Musa duk sun bamu yara tun suna jarirai ma mun karba mun raina amman hakan bai kore cewa mijina baida yaro na jininsa da tsokansa har yanzu ba, dan haka na yarda kayi auren muga abinda Allah zaiyi, kanaso na samo maka wacce zaka aura ne kona barka kasamo ko kanada wacce kakeso?” Dan yatsine fuska yayi ahankali yace “banda kowa amman akwai wata baiwa dakika taba aikowa office takawomin abinci na yaba da natsuwan ta ki aika gidansu ko ki tambayamin ita muji” murmushin yake tayi aranta tace “wato kaga yar fara yar fulani shikenan ita kakeso mayen fararen mata to da bakar mace zakai rayuwa harka mutu” azahiri tayi mutmishi tace “anjima kadan zanje dakaina na ganta namata magana, yanzu tashi to kai wanka ka warware kaji ko kanaso ni namaka da kaina?” Dan kallonta yayi saikuma yataso da kanshi yadaura akafadanta ahankali yace “ina alfahari dake Jummai, dakowani namiji zai sami mata tagari irinki da alokacin zai tabbatar lallai aure nada dimbin ni’ima, thank you Jummai for always supporting me, akwai wasu kudi a akwatina konawa kikeso ki dauka harda dollars” murmushi tayi tace “to godiya nake mai gidana, tashi kagani muje na wankeka subul” dagashi tayi tawuce dashi bayi tsaf ta wankoshi suka fito ta shafamai ta shiryashi sai hira takemai suka fito breakfast sukai tare bayi sai kaikomo suke, Jummai takalli wata baiwa tace “je sama ki taso Maryam tazo ta gaida Babanta”suna zaune awajen wata yar budurwa dazatayi sa’an Rashida ta sauko tana sanye da rigan bacci iya guiwa tana goge idanu tazo dinning din, tabaya ta rungume Muji tace “morning Dad” tasakeshi tawuce wajen Jummai ta rungumeta tace “good morning Mommy” washe baki Jummai tayi tace “sai yanzu aka tashi sabida anzo hutu daga school ko, Allah kaimu next month ki koma Istanbul zamuga karyan iskanci” Muji dake binta da kallo idanunshi suka sauka kan Nail polish dake kumbunan




Post a Comment

0 Comments