TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 47

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718



*_47_*




..........“Wayyo kaga kasa tayi fushi da abincin fa Soulmate”.

    “Ita ta sani”.

Ya faɗa cikin halin ko'in kula da cigaba da cin nasa. Fadwa zata cigaba da masa magiyar ya bita itama ya balla mata hararar. “Malama idan zaki ci naki kici bana son damuwa”. Shiru tai cikin kama baki kar kuma ƙaiƙayi ya koma kan masheƙiya. Har suka kammala breakfast ɗin babu wanda ya sake magana a cikinsu, sai dai cikin nishaɗi ta cigaba da cin nata a yanzu, amma a zahiri tayi kalar damuwa dan karya ramfota. 


        ★★★


   Acan rijiyar zaki kam zaman lafiya yaƙi tabbata tsakanin Daddy da Mommy. Duk yanda kowa ke tausarta cikin ƴan uwanta akan ta nutsu abi komai a hankali amma fir ta nuna taƙi fahimta. Ita dai burinta kawai Shareff ya saki Anam. Babu kalar tujarar da su Mamie basa gani daga gareta, sai dai babu mai nuna yama san tanayi su dai fatansu zaman lafiya ga yarinyarsu. Babban abinda ke sake wutar tashin hankali a zuciyar Mommy shine rashin zuwan Shareff gidan, dan kuwa Daddy ya haramta masa sake zuwa gidan a yanzu har sai komai ya daidaita, kowa yasan yayi ne saboda Mommy ɗin. Gwaggo kuwa tunda ta nunama Mommy cewar ta kwantar da hankalinta zata nemo mafita, amma Mommyn ta murje idonta taima Gwaggo tas akan ita bata buƙatar wata mafitarta sai Gwaggo ta koma gefe ta naɗe hannu tai shiru, tayi tamkar ma bata gidan bata san borin da Mommy ɗin ke zubawa ba.

     Ba bori da tujarar Mommy bace kawai ke wanzuwa a gidan, harda Gwaggo Halima dake ganin ƴan uwan nata sunma ɗiyarta gudan jininta rashin adalcin raɓata kishi da ɗiyar ɗan uba. Itama dai bata da burin daya wuce ta ɗakko Fadwa ta dawo gida har sai Shareff ya saki Anaam sannan ta koma, sai dai baban Fadwa ɗin yay mata katanga da hakan. Hasalima ya bata sharaɗin ko gate ɗin gidansa ta taɓa da nufin fita a bakin aurenta da babu dawowa har abada. Dan shi mutum ne da dama baida wasa sam, badan haka ba da ya jima da zama mijin hajiya a gidansa saboda azabar Gwaggo Halima. Hatta da yaransa suna matuƙar shakkarsa, kuskuren da aka samu kawai shine siyasa ta kwashe kaso mafi yawa na hankalinsa har takai a yanzu bai iya saka idanu a kansu. Gwaggo Halima ta nutsu a gidanta cikin matuƙar tashin hankali da baƙin ciki, tasan ko giyar wake tasha bazata taɓa gangancin rabuwa da uban ƴaƴanta ba, domin yin hakan a gareta ba ƙaramin nakasu bane, shiyyasa ta nutsu a gida zuciyarta na mata zafi da raɗaɗi musamman naƙin jin Fadwa har a waya dan Abbansu yayi seizing wayar tata duk dan kar suyi waya, ya kuma hana har ƙanenta zuwa gidan Fadwan wannan shine dalilin da yasa a ƴan gidan su babu kowa a kusa da ita sai su aunty Malika dake matsayin ƙanne ga Abban nata.


        Yau ma dai kamar kullum tun bayan kai Anaam gidan Shareff da tujarar Mommy aka tashi gidan. Sai dai babu wanda ya kulata sai Gwaggo ce da tazo wuya ta fito tai mata tatas a tsakar gidan saboda ita kam dai haukar Mommy ɗin ya fara kaita maƙura. Tun Mommy na ƙoƙarin son nunama Gwaggo irin ɗaci da zafin da takeji a zuciyarta har tayi shiru ta koma kuka...

      “Gwaggo baki san irin zafin da nake ji bane a zuciyata wlhy, ji nake kamar na tsinema Shareff na huta. Ni yaron nan zai wulaƙanta a idon duniya ya nuna ubansa ne ya isa da shi bani ba!!”.

      “Ai taimakonki yay, saboda yin biyayya ga mahaifin nasa ne ya janyowa igiyoyin aurenki cigaba da wanzu har yanzu a gidan nan shi da Usman. Ban san mike damun kankiba Nafisa, ina wayonki ina hankalinki ne? Kinbi kin ruɗa kanki akan ɗan abu ƙanƙani da maganinsa ke'a hanunki cikin sauƙi.....”

          “Gwaggo taya zakice cikin sauƙi? Da'a sauƙine Shareff zai kai iyanzu bai saki yarinyar nan ba har zuciyata ta cigaba da ƙuna?”.

   “Kinbi hanyar da bazai saketa ɗinneba ai. Idan kin shirya cin nasara akan ɗanki sai ki nutsu ki dawo hayyacinki” ta ƙare maganar da miƙewa ta fice tabar Mommy da binta da kallo cikin rashin fahimtar kalamanta........


_________________________________


         Gaba ɗaya yau bashi da ra'ayin fita ko'ina, sai dai hakan bai hanashi yin wasu ƴan ayyuka ba ta cikin system ɗinsa. Zuwa yanzu babu kowa a sashen nasa, itama Fadwa tunda ta fita bata dawo ba. Shi kuma bai nema kowaccensu ba yanata harkokin gabansa har akai kiran sallar zuhur. Shigarsa bedroom ɗinsa domin ɗauro alwala ya sashi jan tsaki, dan yana nan a yanda suka tashi barci suka barshi. Har cikin rai abin ya sosa masa zuciya, yana da mace har biyu a cikin gida amma sashensa ya gagara samun shara. Ba yau ya saba ganin hakan ba, sai dai bazai yarda itama Anaam ta zama haka ɗin ba tunda yaga Fadwa ta fara gyara nata halayen itakuma. Jiya itace tai masa gyara, bazai yuwu kuma yau tayi ba bayan ba itace ta kwana a ɗakin ba.

      Koda ya fito sai da ya leƙa sashin Fadwa dan tabbatar data tashi yin salla kamar yanda musulinci ya koyar da duk magidanci na ƙwarai. Da mai-aikinta data dawo ya fara cin karo a falo, ta zube har ƙasa tana gaidashi. Hannu kawai ya ɗaga mata ya nufi bedroom ɗin Fadwa ɗin. Kwance ya sameta tana ramuwar barcin data hana kanta yi daren jiya, ya ɗan kafeta da ido na wasu sakanni kafin ya tasheta. Ɗagowa tai da ƙyar tana kallonsa cikin rufewar idon barci..

     “Tashi kiyi salla sai ki koma ki kwanta”.

   Da ƙyar ta iya amsa masa da to, yasan kaɗan daga aikinta yana fita ta koma, dan haka ya cigaba da tsaiwa a kanta har sai da ta tashi ta shiga toilet sannan ya fito. Sashen Anaam ya nufa, itama dai bai sameta a falo ba sai bedroom, saɓanin Fadwa ita kwancen kawai take amma ba barci take ba. Taji shigowar tasa amma taƙi ɗagowa ko sau ɗaya balle ta nuna tasan da wanzuwarsa. Tun a kallo ɗaya ya fahimci ba barci take ba, sai dai idanunta sun nuna taci kuka duk da suna a rufe dan ta cire glass ɗin. 

      “Ki tashi kiyi salla”.

  Bata tanka masa ba, kuma bata motsaba ya juya yay ficewarsa. Idanunta ta buɗe ta raka bayansa da harara tana laɓe baki. Sai da yaja kusan mintuna uku da fita sannan ta tashi domin gabatar da sallar, a ranta tana addu'ar zuwan jininta a nan kusa.

        Bayan ta idar da sallar saman sallayar ta cigaba da zama tana sharar hawaye, buƙatar kasancewarta da iyayenta ce ke damunta. Abinda Shareff ɗin yay mata ɗazun a dalilin makircin Fadwa har yanzu yana cizon mata rai. Ta san tun farko dama ya tsaneta, taya bazai goya bayan matar son sa ba koda ace itace mai gaskiya. Itako ta ɗauka alwashin baza'ai nisa ba balle har su sami galabar ƙuntata shi da matarsa, a yau ɗin nan za'ayi mai yuwuwa ita ba shashasha bace...

      Yawaitar ƙamshin turarensa a ɗakin ya tabbatar mata shigowarsa, amma sai tai kamar bata jiba duk da taji sallamar da yayi ciki-ciki. Ta gabanta yazo ya gitta ya zauna a bakin gado ta kusa da ita kaɗan, dan ƙafarsa ɗaya ma akan sallayar take. Ido ya ɗan tsura mata na wasu sakanni, tayi kicin-kicin da fuska tamkar bata san da shigowarsa ba...

     “K kina ganin ba'a isa ace miki kinyi ba daidaiba kenan? To bari na faɗa miki matata ba abin rainawarki bace, a baya kunyi abinda kuke so k da ita, amma a yanzu bazan ɗauka raina juna daga kowaccenku ba. Dole ne duk mai buƙatar son zama lafiya da ni ta zauna da ƴar uwarta lafiya a gidan nan kuma cikin girmamawa da daraja juna!”.

     Yanda yay maganar a kausashe ya sata jin zuciyarta a wuya, hawaye ne suka shiga rige-rige sakko mata saman fuska, “Ni bance ina buƙatar zaman gidan ba ai, balle naima wata ƴar iska biyayy.....”

    Bummm ya buge mata baki da bayan hannu. Ba ƙaramin zafi ne ya ratsata ba, ta dafe bakin tana kallonsa da idanunta da sukai jazur ta cikin glass, sai dai babu hawaye yanzu a cikinsu sai tsantsar baƙin ciki da ƙunar zuciya. Ya miƙe tsaye yana nunata da yatsa. “Idan kin isa mara kunya a gidan nan ki sake yima matata ko kallon banza kiga yanda zanyi dake mara kunyar banza” 

       Hawayen da take riƙewa suka ɓalle mata, ganin zai fice bata amayar dana cikintaba ta miƙe zumbur, “Idan na zauna kenan har za'ayi yadda za'ayin dani, inda kun kwantar da hankalinku ni dama banzo wannan gidan naku da niyyar zama ba, matar taka kuma wlhy tasa a ranta bashi taci, dan ni naci uwarta iya wasan data ɗau layin muyi, dan bata kai matsayin mace ba a wajena. Itace jaka da har take tunanin mijin nata wani abin a SO ne, ni baka cikin irin mazan dazan iya SO Yaya balle muradin zama a shi gidan, ƙaddara ce ta kawoni nan badan rasa masoya ba. Zan kuma barsa a yanzun nan bari na har abada, dan ALLAH kuyi kwaɗon juna ku cinye......”

         A wani irin mugun fusace ya juyo gareta, dan har ya saka kafarsa ɗaya zai fice a ɗakin batare daya kulata ba, sai dai kalamanta na ƙarshe-ƙarshe sun masa saukar mashi ne a tsakkiyar ƙirji. Ko ɗar bataji da yanayin nasa ba dan itama zuciyar tata irin tasance kuma a wuya take fiye da tasan. Kallonta yake da jajayen idanunsa da suke neman wargaza duk wani ƙwarin gwiwar ta amma ta dake.........✍     




Post a Comment

0 Comments