TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 44

   *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718



*_44_*



...........Banza yay mata kamar baiji ba, sai ma ƙoƙarin mikewa yake bayan ya latse remote tv ya mutu. Ganin zai bar wajen tai saurin riƙo hanunsa dan in har ta bari ya wuce bazata iya kai kanta ko nan da ƙofar fita ba saboda da gaske bata gani da ƙyau a cikin duhu sai da taimakon glass ɗin.

    “Yaya Please ka bani”.

Hanun nata ya kalla tare da ƙoƙarin juyowa, da sauri ta janye nata a yanayin jin kunyar aikatawa. Kafeta yay da idanu yana ƙarema fuskarta kallo kai tsaye, yayinda ita kuma ta kasa ɗagowa ta kallesan. A cikin ransa  yake faɗin, (Fitsararriya ashe kinada kunya?). A zahiri kam babu alamar wasa tare da shi yace, “Muje ki kwanta”.

      “Ina ɗin?”.

Ta faɗa cikin waro makantattun idanunta da mai kallo a haka bazai taɓa tunanin rauninsu ba saboda girma da hasken dake cikinsu tamkar wadda ke iya hango abinda ke faruwa a kilomita huɗu na gabanta. Gab da ita ya matso har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskarta. Cikin magana tamkar mai raɗa “A inda kike?”.

       Baya taso jan jikinta bugun ƙirjinta na daɗuwa amma sai ya hana hakan ta hanyar tokare hanun kujerar da take jiki da hanunsa. Duk sai ta daburce. Ture hanunsa tai da ƙarfi, tai gaba da nufin guduwa ƙafarsa ta nema taɗeta tai gaba zata faɗi ya riƙota, ɗan fisgota yay ta faɗo jikinsa, baima jira tako maida numfashi ba ya ɗauketa cakk ɗinta yay hanyar bedroom ɗinsa dan ya gaji shima kwanciya yake buƙata. Inko ya biye mata sai dai su raba hali. Watsal-watsal take da son ƙwace jikinta tana faɗin, “Ni wlhy ka saukeni bana so, bana son haka Yaya MM, ALLAH zan cijekaaa!!”. Ta ƙare faɗa da ɗan ƙarfin sautin daya sakashi direta a saman gadonsa da sauri. 

      “Kina da hankali kuwa? Fasan kunne zakiyi?”.

   Mikewa tai cikin sauri da nufin barin masa ɗakin dan ita kam dai bazata taɓa yarda ta kwana a ɗakinsa ba, gidan nasa ma domin yin biyayya da iyayenta ne da son cimma burinta cikin sauƙi zaisa ta zauna har zuwa lokacin data ƙayyadewa shirinta. Bai hanata ba dan tuni ya zare keys ɗin ɗakin, sai ma toilet daya nufa cikin halin ko'in kula. Jin ƙofar a kulle ya sata juyowa da sauri duk da ba fes take iya ganin komai ba amma kasancewar da fitila tana gani fiye da acikin duhu. Sosai hankalinta fa ya tashi, dan abu ɗaya zuciyarta ta iya bijiro mata zaisa yay mata hakan, a gareta kuma shine abu na ƙarshe da bazata iya mallaka masa ba koda a yau zaice zai mata dukan da shine kawai abinda take shakka da tsoro tattare da shi. Haɗiye duk wani fargabanta tai tai tsayuwar sojan badakkare a jikin ƙofar tana dakon fitowarsa. Tsahon mintuna 6 sannan ya fito duk tana lissafa ta hanyar kallon agogon dake bangon ɗakin. Yi yay tamkar bai ganta ba ya hau zame jallabiyar jikinsa. Bayyanarsa a zahirinsa da ga shi sai boxer ya sata juya masa baya da sauri tana ambaton sunan ALLAH. Kayan barci ya ɗakko a wadrobe ya saka harda fesa turare kamarma bai ganta ba. Ya haye gadonsa yana faɗin, “Baƙya buƙatar kwanciyar ne?”.

      Maimakon amsa sai ta fashe masa da kukan ƙarya. “Yaya dan ALLAH ka bani key da glass ɗina na wuce barci nake ji, ALLAH haka babu ƙyau, kuma kaina zai iya yin ciwo”.

    “Idan kin so hakan kenan”.

Ya amsata yana jan bargo cikin halin ko'in kula. Kukan ƙaryar tata ta dakatar zuciyarta na mata zafi, sai dai hango keys ɗin a bedside drawer ɗin inda yake ya saka mata jin sauƙi, cigaba tai da tsaiwa a wajen har kusan minti ɗaya kafin ta nufi wajen cikin sanɗa da tunanin yayi shammatarsa ta warto. Tana gab da isa ya fiddo hanunsa dake cikin duvet ya ɗauke, rigarsa ya ɗaga ya ɗaura saman cikinsa ya maida bargon ya rufe. Ganin ta dakata daga yunƙurin tahowar ya ɗan buɗe ido yana kallonta a sigar da ita bata fahimci haka ba musamman saboda matsalar nata ido. 

     “Gashi anan ki ɗauka” 

  Kanta ta ɗauke idonta na ciko da ƙwalla na gaske a yanzun. Dan tsaf ta fahimci tarko ne ya kafa mata. Hannu tasa ta share hawayenta, sai kuma ta taka da baya-baya ta koma saman kujerar dake a bedroom ɗin ta zauna..........


        ★Tun barowarta sashen nasa ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai faman kaikawo take hawaye masu zafi na kishin mijinta na ragargazar zuciyarta tamka irin kowacce macen da aka kawowa abokiyar zama, ba ita kaɗai ba, irinta da yawa sukan azaftu matuƙa da rashin barci da ƙunci a irin waɗan nan kwanakin bakwai da amarya takan samu matsayin na amarcinta. Kai wasu ma borinsu har yakan zarta natan, ga masu ƙarancin imani ma kwana suke shiryama zukatansu munanan abubuwa harma da masu aikatawa. To ita dai Fadwa saita kasance a jerin masu azaftuwar ƙuntatama kai da ƙiyasta abubuwa da dama da bai dace zuciya ta ƙiyasta ɗin ba ta kasance duk da su Aunty Wasila sun bata tabbacin hakan bamai faruwa bane ta kasa nutsuwa, sai dai babu tunanin mugunta ko shirka a ciki, ita dai kawai mijinta take hangowa da wata a yanayin da ita kaɗai ta sanshi.

     Tsahon lokaci ta ɓata tsaye jikin window tana kuka da dakon kallon hanyar tsumayen fitowar Anam da mijinta, amma sai saɓanin hakan ne ya biyo baya, domin kuwa shi kaɗai taga ya fito zuwa sashen Anam ɗin, bai kuma ɗauki tsahon lokaci ba ya fito ya sake komawa nasa sashen. Neman zubewa tai ƙasa kuka mai cin rai na kufce mata dajin tsananin tsanar su Daddy da take ganin sun ƙulla wannan aurenne saboda basa ƙaunarta ita da mahaifiyarta dalilin asiri da Abie da Mamie da aunty Mimi sukai na raba kansu tamkar yanda a koda yaushe Gwaggo ke faɗa. (karku ga laifin Fadwa, a haka aka raini zuciyarta, a haka ta girma da ƙiyayyar waɗanda bata da wani tabbataccen laifinsu a zahirin rayuwarta, da yawa iyaye na kuskuren wajen ƙoƙarin fidda matsalarsu da ƴan uwansu ga ƴaƴansu, sun kasa gane hakan yanada matuƙar tasiri ga zukatan ƴaƴan, dan in har akai wasa su ƴaƴan zasu tashine da ƙiyayya mafi muni da tsauri ta waɗan nan ƴan uwan nasu koda ace su daga baya sun haƙura sun yafema juna ne. Shiyyasa mafi yawan zuminci ke ƙara lalacewa da taɓarɓarewa a zukatan kowacce zuria fiye da ƙyamatar kafurci. Tasirinsa ne a tsakanin *_Anam da Fadwa_* duk da suna amsa sunan jini ɗaya, amma tunda ba uwa ɗaya ta haifi iyayensu ba, sun ɗauki hakan babbar tazara da bazata iya basu wata ƙyaƙyƙyawar jituwaba sai ƙyara da hantarar juna kawai. Sai kuma ga *KISHI* ya ratsa, wanda yake zamtowa linzami na rasa imanin *MATA* da yawa a dalilin zafafawa, ko da sunada tabbacin bazasu iya canja ƙaddara ba).

          A jiya kasancewar su Aunty Malika tattare da ita ya sama zuciyarta salama da ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta, musamman da zuciyarta ta dinga ayyana mata Shareff a sashensa ya kwana. Amma yau ganin zahiri ya hanata nutsuwa balle fahimtar kanta da kanta a matsayin abinda bazai iya canjawa ba ko samuwar ikon hanawa tamkar kowacce mace irinta. Kuka taci bana wasa ba, wanda ya jata lokaci mai tsayi har kusan ƙarshen dare sannan barci ɓarawo ya fara rinjayarta. A hankali ta sulale akan gadon ƙirjinta cike da nauyi tamkar yanda idanunta ke tattare da nauyin barci. (Koma dai miye ta bani tausayi, mu ƙiyasta kammu a matsayinta bisa adalci na rayuwa. ALLAH ka bamu kishi mai sauƙi da bazai sakamu a nadama ba🙏🏻😣).


    

          ★A lokacin da Fadwa ke can tana kuka da tunanin kasancewarsu a tsakkiyar lambun fure mafi girman daraja a garesu ba hakan baneba. Anam ta jima zaune akan sofa barci na rinjayarta tsoro na fisgota, sai dai bata da wata mafita ko ƙwarin gwiwa saboda babu ɓarawo mafi iya sata kamarsa. Kujerar 1sitter ce guda biyu, hakan yasa bata samu gamsuwar kwanciyarba duk da ta naɗe dukan jikinta a kanta. Daga inda yake kwance yaka hango yanda take mutsu-mutsu tamkar magen data sha matsa a hanun mafarauta. Guntun murmushi kawai ya saki, akan laɓɓansa ya furta “Azababbiyar yarinya”. Yana lumshe idanunsa dake cike da barci. Kusan mintuna goma ya bata domin barcinta ya ƙara nauyi sannan ya miƙe a hankali ya taka gareta. Cikin dabara ya ɗagata gaba ɗayanta yakai saman gadon ya kwantar yana danne dariya. Shi baima taɓa tunanin tanada nauyin barci hakaba, hijjab ɗin ya zare mata sannan yaja mata bargo shima ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Tsakanin Anam da Fadwa bai san wanene yafi wani daru ba. Itama yaso zuwa sashenta yay mata sai da safe amma tsoron abinda zai tarar ya sakashi haƙura. Bai taɓa tunanin da gaske *MAZA* najin shakkar matansu a irin wannan lokacin ba, dan duk yanda yake jin kansa da mazantakarsa da ƙin ɗaukar shirme sai nauyi da kunyar Fadwa ke zagaye da jininsa duk da auren nasa yazo a cikin wani kashine da yasha banban dana sauran maza mafi yawa irinsa.

     Numfashi ya furzar a hankali da juyowa gaba ɗayansa yana facing ɗinta, kallon fuskarta yake a cikin wani irin yanayi mai sanyi da zungurar zuciya, ya matsar da fuskarsa gab da tata tare da saƙala hanunsa saman jikinta ya rungumota a nasa jikin sosai, kamar wadda aka isarwa da saƙo ta buɗe ido, sai dai rashin ganinsa da ƙyau ya sata jan numfashi ta haɗiye tare da nasa da yake busa mata saman fuska. Jan jikinta tasoyi baya ya ƙara matseta. 

      “Yay......”

Kalmar ta kasa ƙarasuwa a zahiri tamkar yanda taso furtawa sai a cikin bakinsa, ba ƙaramin bugawa zuciyar Anaam tayi ba, duk da abinda takema tsoro kenan tun farko dama hakan bai hanata jin mamaki da shiga bazata ba. Bata da wani ƙarfin ƙwatar kanta, sai ma ƙoƙarin zare mata duk wani kuzarinta da razani yake ta hanyar cigaba da sarrafata a wani salo mai kashe jiki da ruguza dukkan alwashi na duk ɗiya mace mai lafiya. Tun tana iya cijewa harta fara amsar salon nasa dan takai shekarun da gangar jikinta ke a matuƙar buƙatar fiye da hakan ma. Sosai ya fitar da ita daga hayyacinta tamkar yanda shima nashi hankalin ya barranta da gangar jikinsa da zahirin rayuwarsa..........✍




Post a Comment

0 Comments