TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 18

 *_Mamuhgee18_*

Fusgar iska yayi ya sake ficewa Yana hura hanci duk da cikin ransa yaji Dan dama dama na ganin gararda zai fara kwasa a kwanakin musamman ma da idanuwansa Suka qyallo masa kiret din kwai da doya da dankalin turawa jiyayi wata Yar dariya na neman subuce masa ya dauke Kai tareda tamke fuska ya fice Yana cewa"


Wannan Yar baqin cikin batason naci wannan kayan ai wlh Saidai kowa ya rasa muguwar tsohuwa.


Cikin dakin Suka shigarda abincin suka jera inda yace a ajiye Suka fice.


Harta rufo dakin zata shiga cikin gida Nanu yadawo riqeda wata ledar ya miqa Mata yace"


Sarki yace kiyi abinci.


Karba tayi tayo cikin gida zainab tayi saurin karbar ledar tareda budewa ta zaro ido ganin Naman kajine masu qanqara da kayan Miya.


Wata gudar jin dadi iya talatu tasaki tareda miqewa ta sauke tukunyar tuwon gari datayi niyar dafawa tana cewa"


Yau dau allah yayi wahalata taqare zanfaraci daga Zaki Kuma daga 'yaya.


Itadai Nadiya Babu wani dogon farin ciki ko murna atareda ita sbd tsoron karta dafa tayi masa ba daidaiba dukda dai ta iya girki sosai tunda itakeyi na gidan tun batai hakaba.


Jiki sanyaye tafara wanke kayan miyar da Naman

 zainab kuma ta hada rishon tazuba kalanzir da aka kawo dashi cikeda galan.


Iya talatu daki tashiga ta dauko Mata tukunyoyinta guda biyu sabbi data siya Mata na aurenta da Bello dabaayiba ta miqa Mata tareda kula Mai guda uku da plate biyu sai Kofi uku da cokali biyar duka sabbi Saidai bawai masu tsada bane kawai dai Babu laifi.


Zainab ba wata gwanar aiki bace Saidai fira datake taya nadiyar dashi harta gama abincin,


Tuwo tayi na shinkafa da miyar busashen ku6ewa dataji Naman kajin gidan har wani qamshi yakeyi har maqota 

Dattiya daya fesawa idi Suka kasa Suka tsare a majalisarsu ta dattijan anguwa suna jiran dare yayi suje suci banza Dan kuwa shima idi cewa yayi wlh daga yau tareda dattiyan zasu riqa ci tunda ai tare sukeshan wuyarsa idan yatashi Rashin mutuncinsa akansu.


A sabuwar kula zainab ta dibarwa zakin komai aka goge aka Kai masa daki tareda plates din da sabbin cups dinta.


Iya talatu harna dumame ta Diba a qaton kwanonta tashigewarta daki.


Babansu ma cika masa wata tsohuwar kula sukayi kafin Suka zauna sukaci nasu zainab tabar gurin

Itakuma ta dauki rushon tashigar tsohon dakinta tareda galan din keron ta fito ta tattara gurin ta share gidan tas Takoma ta sharo dakinsu tazo tadibi ruwa tashiga wanka.


Tana fitowa tayi alwala ta nufi daki.


Komai Bata shafaba bayan spray dinda ya siyo Mata Wanda shima yakusa qarewa ta saka bra saita maida zaninta iya qugu tafara neman rigarda zata saka sai kawai taji shigowarsa gashi akwai nepa.


A rikice ta miqe tsaye jikinta na rawa sbd tsananin kunya da fargabar yanda take din.


Aka bra dinta data 'dan yi Mata kadan qirjinta sun fito ta gaban idanuwansa Suka sauka atake ya dauke Kai Yana daure fuska musamman dayaji maqoshinsa yawu na neman qin wucewa.


Hijab ta fizga da sauri tasaka tareda durqusawa ta dauki rigar dake Daman kayanta kawai tafara qoqarin zurawa.


Zama yayi bakin katifata tareda kunna wayarsa Yana latsawa sai kawai yaga yama rasa Mai zaiyi ya miqe tareda sakin tsaki yayi wurgi da wayar Yana cewa"


Ke bani abinci.


Aje hijabinta tayi bayan tagama saka doguwar rigar bacci har qasa Mai kauri ta nufi kulolin takawo gabansa tareda plate da spoon.


Koda yaga tuwo ne bai wani damuba Dan dama shi bazai iya tuna yaushe rabanda yaci tuwaba arayuwarsa tun bayan rasuwar mahaifiyarsa.


Sanin baya mugun ci yasa tazuma masa daidai yanda tasaba ta miqa masa.


Ba laifi yaji dadin abincin Saidai Sam bayason yaji ko kadan can qasan maqoshi yace"


Karki Kara saka yaji abinci wuwuyar yarinya kawai.


Ruwa daya ta dauko takawo masa ta tayarda sallar magriba da akayi tun dazu.


Tana Gama sallah ta tattara gurin ta fita da kayan takai tsohon dakinta inda ta ajiye risho.


Kodata dawo Yana kwance ya rufe idanuwansa kamar mai bacci sai kawai ta zauna itama tana shafawa qafafuwanta Mai sbd akwai sanyi sosai.


Su dattiya kuwa koda Suka zauna cin abinci Babu Wanda Wai washe dukkanin haqoran da Allah yayi masaba shida mal idi sbd farin ciki mal idi yace"


Yaushe rabo"""" 


Cinyar kaza dattiya yakai baki Yana cewa"


Eh ai wahalarmu ce zamu rage anan tunda Allah ne kawai yasan iya hasarar daya goga Mana.


Mal idi da kunnuwansa sukai wata rawar da'din miyar da Naman yace"


Wlh mudai wannan Abu gwara da akayi,

Wata gararma sai Abu yayi nisa qilamafa ayi maka sarkin maroqa kaga ni Kuma mataimakinka ko.


Wani murmushin Jin dadi dattiyan yayi Yana cewa"


Hmm ranarda akamin wannan sarautar ai kaima kasan Banda wani mataimaki bayai Kai.


Iya talatu dake jinsu a tsakar gidan tace"


Allah dai ya shirya wainnan masu mutuwar zuciyar.



Washe gari tunda wuri ta tashi tahau aikin gidan tadora ruwan zafi ta cika masa flask tadawo tahau aikin yimasa breakfast lokacin Yana ciki Yana motsa jikin daya Saba.


Doya ta soya masa da kwai Wanda zainab ce take qara nuna Mata yanda akeyi harsuka Gama ta adibar masa nasa takai masa lokacin Yana gurin wanka tana cikin gyaran dakin yashigo tana gamawa ta fice Dan zuwa wanke wanke.


Yana gama cin abinci ya fita.


Sai bayan azahar tsamu ayyuka suka rage Mata tayi wanka tayi sallah ko hutawa batayiba iya talatu takirata suka hau wani aikin.


Da daddare kodata kwanta jikinta har wani ciwo yakeyi sbd wahala Dan aiki Kam yayi Mata yawa fiyeda da can.


Duniya sabuwa aka bude a cikin gidan sbd cima Kam yanzu ansamu safe Rana dare Kuma lafiyayyan abinci sukeci wani lokacin saiyanajin takaicin yanda tun farko baya Basu abinci tunda yanada halin hakan wata qilama hakan da tuni yasa kawun ya daina yawon ta zubar dinsa.


Dattiya kuwa yanzu da aka bude Jin dadi sabo duk inda yake lokacin cin abinci nayi to Yana gida Dan kuwa yanxu wani lokacin idan yaci yaji yayi nas har wata kasalar futa yawon maula yakeji saiyayi zamansa Yana Shan iska Yana sakatar haqori cikin wata irin Isa Yana hura hanci.


Zainab ma ba laifi ta 'dan rage yawo sbd ganin kusan abinda takewa yawon yanzu suna samu a gidansu Dan dama yunwa ce kesata yawon batanan batacan.


Nadiya kuwa yanxu Kam tafara zama abin tausayi sbd duk wata wahala tana cikinta Dan kaf gidan aikinsu suci su qoshi ne kawai duk wata wahala ta gidan ita keyi,


Ko cokali Babu Mai iya dagawa sai itace keyi gashi sanyi yashigo sosai sai abin yafara tabata Dan kuwa kumburi tafarayi sbd sanyi dayayi Mata mummunan kamu yatsar qafafuwanta har wani yankewa sukayi sbd aikin ruwa da sanyi.


Gashi bikin Yaya dahiru yazo sosai ake hidimar biki a gidan sai abun ya ninkar Mata ko zama batayi idan gari ya waye sai dare idan ta kwanta tayita juye juye sbd ciwon jiki da qirji.


Yana lureda ita duk baqar wahalarda takesha idan tazo da dare tanata murqususu sai abin ya ringa qular dashi Amma dai ya qyale yaqi Mata magana.


Abinda yabawa kowa mamaki shine kayanda ya dinka Mata a dinkensu masu 'yar tsada har kala biyar Wainda aka dinko daidai jikinta har zainab na tsokanarta da cewa"


Lallai Yaya Zaki har hannuwansa sun haddace girman komai na jikinki..


Rintse ido tayi da sauri tareda barin gurin zainba din tana saka kayan cikin kayanta Suka fito tana cigaba da tsokanarta.


Ranarda akayi biki aranar da daddare kasa bacci tayi tafara juye juye dafe da qirjinta tana hawaye cikin tsananin azaba ga tarinda takeyi mai tsananin zafi a maqoshinta Wanda shiyasa tafara Yi kamar zata fice hayyacinta.




Post a Comment

0 Comments