TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 33

       *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718



*_33_*




.........Mommy ce ta shigo falon tare da aunty Iklima, batare data lura da halin da Fadwa ke ciki ba tafara magana cikin raba hankalinta biyu. “Fadwa a fiddo gift ɗin nan dan yanzu nake son ku wuce gidan wankin amarya ɗin nan ke da Bintu kafin sauran su biyoku a baya”.

      “Mommy inaga sai dai aunty Bintun tayi gaba. Dr Jamal ne yay kirana asibiti”.

    “Asibiti kuma? Mi ake acan ɗin?”.

“Inagafa jikin Soulmate ne, dan nata kiransa dama ɗazun bai ɗagamin ba sai nai tunanin baƙin ran nasa ne bai gama sauka ba”. Ganin tana tafiya tana magana Mommy ta riƙota da sauri. Kafin tace komai Fadwa ta rigata magana da ƙoƙarin yin gaba. “Mommy wlhy hankalina a tashe yake idan na dawo mayi magana”. Sakin nata Mommy tayi, Fadwa ta ƙarasa fita da sauri. Cikin sa'a ta samu napep data ajiye wasu mata.


        Azalzalar mai Napep data dingayi yay gudu ya sakasu isowa da wuri, ta miƙa masa dubu, yana mata maganar ga canjinta bama ta sauraresa ba tai gaba dan a rikice take. Tana tafiya tana kiran Dr Jamal, cikin sa'a ya ɗaga ya sanar mata inda zata samesa, sai dai bata gane ba. Dan haka ya turo mata Nurse ta shiga da ita. 

       Yana kwance samɓal Dr Jamal na gyara masa ledar ƙarin ruwan da ake masa. Ta ƙarasa cikin sassarfa gaban gadon, idanunsa a lumshe suke alamar barci, yayi wani fayau da shi saboda ramar da yayi sosai, wadda ita sai ma yanzu ta sake ganinta a bayyane garesa.... Dr Jamal da gaba ɗaya yake cike da haushinta ya juyo yana kallonsa babu walwala tare da shi. “Fadwa yanzu kinyi dai-dai kenan? Mijinki na a cikin irin wannan halin amma kika tsallake kika tafi gidan biki kika barsa?. Badan ALLAH ya kai Khaleel gidan ba kin san kuwa komai zai iya faruwa?”.

      Kukan da take rikewa ta saki, ta kai duƙe gaban gadon tana kamo hanunsa da babu ƙarin ruwan. “Doctor ni ban san jikinsa yayi tsanani hakaba wlhy, duk ta inda na ɓullo dan nasan damuwarsa ya kasa bani damar hakan..”

           “Amma sai ki sanar a gida tunda ke yaƙi ya sanar miki....”

    Shigowar su Abba ya hanata bashi amsa. Khaleel dake gaba ya watsa mata harara ya ɗauke kansa. Taga harar tasa amma sai ta ɗauke kanta, tare da zare hanunta daga cikin na Shareff. Abba da Abie dai sai maimaita sunayen ALLAH suke a bakunansu, dan yanda Shareff ɗin yay fayau na rama a ƙanƙanin lokaci ya basu tsoto. Dr Jamal ya gaidasu, tare da kwantar musu da hankali akan su masa addu'a dan jikin nasa da sauƙi. Addu'ar fatan ƙara samun sauƙin sukai masa, tare da jajanta al'amarin. Abie ya kalli Fadwa dake gefe tsaye, faɗa ya fara mata akan miyasa bata sanar da kowa Shareff ɗin baida lafiya ba. Shiru tai taƙi tankawa, sai ma fuska data ɗaure tamau dan kamanin Anam data gani tattare da dattijon ya bata tabbacin shine baban Anam ɗin kuma ƙanin Mamansu da suke uba ɗaya. Duk da cikin taushin murya da sauƙaƙawa yake mata faɗan sai ta murguɗa baki, babu wanda ya lura da abinda tayi sai Abie. Maimakon yaji haushi amma sai yay Murmushi kawai. 

    Abbah da jin bata amsawa Abie ɗinba ya dubeta shima ransa a ɓace, baida faɗa amma in aka kuresa shima ɗan babu sauki ne. Aiko ya balbaleta da masifa yana zaginta akan shiru dataima Abie ɗin. Haƙuri Abie ya fara bashi amma yaƙi saurarensa, sai da yayi mai isarsa har Fadwa ta fara share hawaye sannan ya ƙyaleta dalilin dawowar Dr Jamal ɗakin.


      Cikin ƙanƙanin lokaci rashin lafiyar Shareff ɗin ta shiga kunnen kowa. Waɗan da basu riga sun wuce wajen kamu ba sai suka zarto asibitin dubasa. Babu wanda aka bari ya shiga wajensa dan ba'ason masa hayaniya. Sai Mommy data matsa ita da Gwaggo suka leƙasa. Har dare anata shigowa asibitin duba san, dan wandama sukaje gidan kamu daga can nan suka dinga zartowa. Hakan sai ya tabbatarma da jama'a mara lafiyan ɗan dangi ne. Har sha biyu bai farka ba, anata ma ƙara masa ruwa har lokacin, dole kowa ya tattara ya tafi aka bar Khaleel da Maheer a wajensa duk da Fadwa harda kukanta itace zata zauna da shi.  A can gida ma Anam tana kwance rijif da zazzaɓi duk da doctor yazo ya dubata bayan na ido. Haka dai aka kwana zukatan mutane da yawa babu daɗi. 


       Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure duk da rashin daɗin da ake ciki akan ciwon Shareff dan na Anam ba kowa ya sani ba. Da sassafe Fadwa ta wuce asibiti ita da Mommy data zillema mutane da ƙyar. Sun samu ya farka har Maheer ya taimaka masa zuwa bayi yayo alwala. Yana cikin yin sallar daya makara ne suka shigo. Sun ɗanji sanyi a ransu. Suna zaune harya idar, suka shiga jera masa sannu yana amsa musu da kai dan sam baya son yin magana. A dai-dai lokacin suma su Abba suka shigo harda Daddy, kamashi su Khaleel sukai ya koma saman gado, cikin magana ƙasa-ƙasa da bata fita da ƙyau ya gaida su. Cikin kulawa duk suke amsa masa da tambayar ƙarfin jikinsa. Ya amsa musu “Da sauƙi” akan laɓɓansa. Abba ya fara masa faɗa akan ya akai ya zauna da ciwo haka babu wanda ya sani? Sai kace wanda baida kowa?.

       Ɗan murmushin ƙarfin hali yayi na yaƙe, murya ƙasa-ƙasa yace, “Abba zazzaɓine kawai shiyyasa. Kuma naji sauƙi Alhamdulillahi”.

     Abie ya girgiza kansa yana mai dubansa da tausayawa. “Wannan yafi ƙarfin zazzaɓi kawai my son. Kaga kuwa yanda ka rame? Sannan a kwanakin nan gaba ɗaya babu mai ganinka, mu duk mun zata aikine ya maka yawa shiyyasa”.

          Ɗan murmushin yake ya kumayi sai dai baice komaiba anan ma. Idanunsa da sukai wani irin kaɗawa jazur ya lumshe da jingina a jikin filon da Khaleel ya saka masa. Ya buɗesu a hankali ya saci kallon Mommy da Fadwa dake zaune kowa ya zuba tagumi. A hankali ya furta “Mommy inajin yunwa”.

        Kai Mommy ta jinjina masa, tare da taɓa Fadwa datai zurfi a duniyar tunani. Numfashi ta kawo mai haɗe da ajiyar zuciya ta kalli Mommyn. “Kira su Bintu muji wai ba'a kammala abincin bane gashi yace yunwa yake ji”. Da to ta amsa. Tana shirin kiran waya sai ga sallamar Mom da Mamie. Su Abba ne kawai suka amsa da Khaleel. Suka shigo Maheer biye da su ɗauke da basket, sai Mubarak da carton na ruwa. Daga Mom har Mamie fuskokinsu sun kasa ɓoye damuwarsu akan yanayin Shareff ɗin, suka shiga masa sannu da jera masa addu'a su Daddy na amsawa da amin. Mommy da Fadwa dai sunyi kamarma basu san da zuwansu ba. Abba ne ya bada umarnin Maheer ya zuba masa abincin dasu Mom ɗin suka kawo tunda yace yunwa yakeji daman...

        Shigowar Doctor ta sakasu duk suka fito, Daddy ya dubi agogo, ganin lokaci yaja gashi yau juma'a ga ɗaurin aure yace su ai gara su wuce gida ma Khaleel da Fadwa sai su zauna a waje sa, dan dama acan gida sune suka hana kowa zuwa har Gwaggo. Cema mutane akai kawai an ma sallamesa dan haka kowa ya dakata da yunƙurin zuwa aka maida hankali ga shagalin biki. Fadwa da Khaleel aka bar masa, su kuma gaba ɗayansu suka wuce gida, sai dai Maheer bai so hakaba, soyay shima a barsa anan basai yaje ɗaurin auren ba. Amma babu yanda zaiyi su Abba suka korashi, ga Mommy sai zabga masa harara takeyi.....


       ★★ 


  Gidajen biyu duk sun gama cika da jama'a, bakajin komai sai hayaniya da al'ada irin ta biki. Maza duk sun wuce massallaci domin halartar sallar juma'a da ɗaurin aure. Yayinda amarya Anam ke ƙudundune har yanzu taci kuka harta godema ALLAH, zazzaɓi ne mai tsananin zafi tattare da ita. Haushin kowa takeji a gidan, har shi Muzzaffar ɗin da rabonta da shi a zahiri tun randa Shareff ya dawo, saita waya jefi-jefi yake kiranta daga gaisuwa kuma sai yace mata yana da uzuri. badan bata son sa ba take jin haushinsa, kauce-kaucen da yake mata ne yafi komai mata zafi, musamman a kwanakin matsowar bikin. Su Abie sun isa da itane shiyyasa take danne komai saboda farin cikinsu, ko sai bayan sun ɗaura mata aure suka gaya mata bazata taɓa jayayya da su ba saboda matuƙar girma da darajar da suke da shi a gareta. Amma shi mizaisa ya dinga mata kauce-kauce kamar dole akai masa ya aureta bashi yazo yace yana sonta ba?, ya kuma ɗauke ƙafa da zuwa inda take ma sai kace zasuyi auren ƙiyayya?. Hawaye ne suka cigaba da silalo mata a hankali dan bata da ƙarfin yin kuka, a wannan yanayin barci ya saceta saboda allurar barci da doctor ya mata.


         ★Tun bayan barin su Daddy asibitin yaƙi ya sake magana da kowa, Fadwa da Khaleel ma cayay su bashi waje yana buƙatar kaɗaici. Ran Fadwa ya ɓaci sosai har ta kasa shanyewa ta dubesa zatai magana Dr Jamal ya ɗan girgiza mata kai da mata alamar roƙo kar tace komai. Harara ta watsama Shareff tai fitowarta. Shiko Khaleel biyota yay fuskarsa ɗauke da murmushi, yayi tunanin ma asibitin zata bari gaba ɗaya, amma sai ya sameta a waje zaune tana danna waya alamar kira take ƙoƙarin yi. Baice mata komai ba ya kai zaune a kujerar dake kallonta, waya ya ɗauka shima, yana jinta tana faman jan tsaki da alama wanda take kiran bai ɗauka ba. Suna a wajen zaune Dr Jamal ya fito, Fadwa ya kalla dake cika tana batsewa. Yay murmushi da girgiza kansa. “Madam kiyi haƙuri kar kiji zafinsa da yawa, shi mai ciwo haƙuri ake da shi dan bakomai ake masa yaga an masa daidai ba. Zaki iya komaa yanzun ya samu barci, amma ba'a buƙatar motsi mai ƙarfi dan barcin nasa bazaiyi nauyi sosai ba”.

      “Amma Doctor dan mutum na ciwo sai ya dinga dizga mutane kuma. Shi baya ganin ƙoƙarin mu ne?”. “Bawai baya gani bane, yanayin da yake ciki ɗinne sai anyi haƙuri da shi Please. Ki ƙara haƙuri ki koma ciki mu zamuje massallaci ne”. Bata sake cewa komai ba ta tashi ta shiga, su kuma suka fice shi da Khaleel da yaƙi saka baki a maganar tasu dan ƴan miskilancin na kusa..........✍



Post a Comment

0 Comments