TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 17

*_Mamuhgee17_*

Cikin farin ciki zainab din tadauki daya takai baki tana cewa"


Shikenan wlh Nadiya cikin wata daya Zaki canxa ki baje abunki hankalin baba yasake tashi.


Girgiza Kai kawai nadiyar tayi Dan itama tayi mamakin wannan cimar tsawon rayuwarta Bata taba cin dadi irin wannan ba har gwara kaza iya talatu wani lokacin idan taso cin dadi takan yanka cikin kajinta ta soya su ci.


Cikin gida suka koma da abincin acan sukaci tareda iya talatu dake faman zuba sanyin dadin hantar.


Lemun exotic dinda ke ciki ma dayake babba ne shiya qarasa cika cikinsu.


Suna cikin hakan dattiya yashigo ya waro ido ganin abinda ke gabansu 

Butarda ke gabansa yayi shuri da ita zai wuce

Iya talatu ta kalli zainab tace"


Kinga daukemin buta ta ba ita ta kar zomon ba.


Nadiya kuwa ganin irin kallon dayake watso Mata yasa ta miqe ta wanke hannu tahau aikin gidan.


Dayake tanason gamawa da taje ta gyaro dakinsa shiyasa take aikin da sauri harta gama ta nufi dakin tafara da gyare katifar tsaf ta goge komai tayi shara tareda fesa turaren dakin data gani ajiye takoma cikin gida Dan wanke kayanta.


Sai azahar ta Gama wankin Dan hardana iya talatu dama itake Mata wankin kayanta.


Tana gamawa tayo wanka tasanya doguwar rigar atamta cikin kayan da JJ yayi Mata na biki wancan lokacin ta fesa spray kawai tayi sallah ta kwanta a gurin sbd can cikin gidan tsit yake zainab batanan baba kuwa antafi sana'ar iya talatu ma ta fita dama haka rayuwar gidan take so da dama ita kaidaice ke yini gidan.


Tana kwancen taji buga qofa ta miqe da sauri Dan tasan qila shine yadawo.


Jin an Kuma bugawa yasa ta taso ta bude taga Nanu ne yanxuma.


Wata ledar yakuma miqa Mata tareda babbar ledar ruwan pure water ya wuce Dan sauri yakeyi daga gani.


Karba tayi tadawo cikin dakin ta zauna bayan ta ginginar da ledar ruwan,


Ta Dade zaune kafin ta bude ledar wani take away din ne

Tabude taga shinkaface soyayya da cabbage sai nama daga gefe sai spoon din roba.


Plate din dakin ta dauko ta zuba abincin kadan aciki ta rufe sauran tafaraci sbd Sam batada wani cin abinci sakamakon hanjinta yunwa tagama nade matasu tuntuni Dan bako yaushe ake abinci agidan ba.


Tana gamawa ta fita da plate din ta wanke tadawo dashi taje ta kwaso shanyar kayanta tareda yin alwalar la'asar da akayi tanacin abinci.


Saidatayi sallah tagama kafin tafara nade kayanta ta saka cikin jaka tasake share dakin tayi cikin gida sbd lokacin iya tadawo.


Siyayyar kayan hadin su tsimi da garintane na Mata nan Suka hau aikinsu iya na kallonta tana mamakin Wai a kwana daya da yini daya harta fara ganin kamar nadiyar ta 'dan canza sbd wani nustuwa dataga kamar tasake shigarta ita sai yanzumane take Mata kama da amaren.


Suna cikin aiki maraice sosai saigashi yashigo cikin gidan da alama yadan Jima da dawowa Bata saniba.


Towel da basket din wankansa datagani a hannunsa yasa tasan wanka zaiyi dayake ta Saba da wannan tun da can sai bataji komaiba ta miqe taje ta dauki bokiti ta Debi ruwa taje takai masa har cikin bayin tana fitowa zai shigo ta rabe harya shigo saitayi saurin ficewa.


Dawowa tayi Suka cigaba da aikinsu tana qara sauri sbd magriba da aka kusa Kira.


Sai bayan anma fito sallar magriba Suka gama bayan tasake kakkamta tsakar gidan tawuce tayo wanka tareda alwala tasaka wata doguwar rigar plain yadi Mara nauyi ta fesa spray ta tayarda sallah.


Tana cikin sallar yashigo daukeda qatuwar ledar kayan tea da bread sai wata ledar takeaway din na indomie da soyayyan kwai sai yoghurts.


Ajewa yayi tareda zama bakin katifa Yana waya kamar cikin izza.


Tana gamawa ta lanqwashe qafafunta tareda yin qasa da Kai tana kallon yatsun qafarta tana qoqarin Dan rage rawar da jkinta keyi.


Batareda ya kashe wayarba yace"


Ke zubamin abinci a plate dincan.


Tashi tayi a natse ta dauko plate din da spoon tadawo gabansa hannunta na Dan rawa ta bude takeaway daya ta zuba masa indomin tareda aje masa agabansa.


Saukowa yayi Yana cigaba da wayar yafara cin abincin hankalinsa kwance kamar wani wani sarki.


Sauran wadda Bata zuba masa ba ta zauna tafara ci ahankali itama batareda ta bude wani takeaway dinba sbd kota bude bazata iya cinyewaba.


Harya Gama waya yakeyi akan wata motar dikko da aka kama da yaransa aciki.


Tana gamawa ta dauki plate din da takeaway din ta fice dasu.


Dakin iya talatu ta nufa sbd tana jiyo muryoyinsu acan Dan akwai nepa.


Take away din indomin dabata fasaba ta miqawa zainab ta fito tareda wanke plate din Takoma.


Ajewa tayi tareda sake tattare gurin ta dauke ledar kayan tea din ta ajiye gefenda taga ana jere kayan tea.


Zaman shiru tayi har akayi Kiran ishai ya fice.


Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikeda tausayin kanta da irin rayuwar dazatayi ta kadaici sabo.


Tanayin sallar ishai gayi kwanciyarta a gurin Bata wani jimaba bacci ya dauketa.


Koda yashigo qarfe goma takusa ko inda take bai kallaba ya tube ya kwanta Dan dama shi baya kwanciya da riga damunsa takeyi.


Da asuba daya tashi yana miqewa yaji mutum a gabansa da sauri itama tayi saurin tashi zaune hartana buge qafarsa dayake bai tsaya daidaiba saiya fado kanta gabaki daya.


Wani irin zaburowa tayi hakan yasa qirjinta ya hadu sosai da nasa Wanda yasa numfashinsa tsayawa na wucin gadi yayi jarumtar miqewa da sauri Yana qoqarin tamke fuskarsa cikin duhun ya kunna wutar dakin sbd har asubar akwai nepa.


Haske na gauraye dakin tafara gyara rigarta da sauri tana saka hijabinta.


Fuska a tamke ya fice batareda ko sake kallonta ba.


Yauma Ras ya tararda kawun a tsakar gida riqeda buta yama kasa alwalar.


Ta gabansa yashige bayin sbd qara manna masa hauka tundaga cikin bayin yayo alwala danma kawun ya dauka wanka yayo.


Yana fitowa yawuce baice masa qalaba.


Itama fitowa tayi tayi alwala lokacin kawu yafice masallaci shima.


Kodata idarda sallah kwantawa tayi agurin tana karatun alqur'ani cikin ranta ahaka bacci yasake dauketa.


Shima Yana dawowa komawa yayi ya kwanta sbd Yana buqatar hutu yau.


Sosai sukayi bacci harsaida goma ta gota ita tafara farkawa tayi saurin miqewa sbd buga daki da akayi.


Gyara hijab dinta tayi ta nufi qofar zata bude kamar daga sama cikin muryarsa data qara girma sbd bacci taji yace"


Idan kika bude qofar nan saina karya hannuwanki.


Juyowa tayi da sauri sbd atunaninta bacci yakeyi.


Still idanunwansa a rufe suke tayi baya ahankali tadawo Saidai Bata zaunaba.


Tashi yayi ya sauko ya nufi qofar ya bude.


Nanu ne ya gaidasa cikeda basa girma ya miqa masa Dan madaidaicin flask na ruwan zafi Yana cewa"


Sarki yau Dan Tani zubawa ruwan shayinsa suka kafin a amso ammasa afuwa sbd mantawa yayi shine fa Saida aka Kira ya dafa maka wannan Mara sugan.


Karba yayi tareda bude baki yace"


Ka Debi yara kuje ku tarbi motocin alee dikko dazasu shigo ta dajin bayan gari karku Bari jami'ai su San dashigowar motocin yau Ina hutu kafadawa Wainda za'a Bari banason hayaniya Kuma akwai wani Dan kasuwa dake barraj shago na shida jiya daya sakarwa su kawu kare daga sunje gurinsa kafin ku wuce kuje kuyiwa arzikinsa kariyarda gyaranta sai Allah. 


Kawu daya kawo yaji abinda yafada ko kallonsu baiyiba ya wuce ciki Yana cewa"


Shi wannan duk qarfinsa bai ishesaba sai yahada Dana Rashin Shan suga Dan kawai ya kashemin 'ya nayi mgana yace zaiyi magani na,


Shikuma alhajin kwatano yau zaisan ya tabo dangin Zaki indai zakine hasararda zai goga masa saiya gwammace baizo cirani Nigeria ba Dan dama tun Yana yaro ba'a taba 'yan gidan shikadai yafiso yayita cin uwarsu basuda maceci sai allah.


Koda yashigo aje flask din yayi yafice yayi brush yadawo yadauki kayan wankansa ya fice.


Ita taje takai masa ruwan wanka tadawo tafara gyaran dakin.


Fes tagyara koina ta gyare shimfidarsa tayi shara.


Yana shigowa ta fita taje tahau gyaran tsakar gidan tadawo ta tararda yasha tea harya koma ya kwanta.


Sauran Wanda yabari Tasha ta tattare gurin tafito Dan taya zainab wankin dataga ta fitar tanayi.


Sai azahar Suka gama tayo wanka a dakin zainab ta shirya zainab harda shafa Mata jambaki daqyar ta iya zuwa tadauki kayan sawa tadawo cikin dakin zainab ta shirya Takoma can tayi sallah lokacin yafita sallah azahar masallaci.



Da abincin Rana yashigo Mata wannan karon sakwara ce da Miya anan ta zauna taci sbd sanin bayason dogon iyayi shiyasa taketa taka tsantsan kartayi laifi ya kakkaryata kamar yanda yake fada.


Da daddare ma yau indomi sukaci Suka kwanta Amma saidata Dade gurin zainba ta rage dare kafin tashigo ta kwanta.



Ahankali lokacin yafara ja yanzu kusan satinta cikin na uku da tarewa dakin tuni harta Saba da rayuwar shirun dasukeyi sai Kuma hakan yasa fargabarta ta ragu sosai Saidai tsoronsa dayake daram cikin ranta.


Cinta da shanta ya canza gabaki daya sbd cimar datake ci yanzu safe Rana dare harya zamto yanzuma itace ke kawo musu abinci cikin gidan Dan kuwa sosai su iya talatu ke Jan gararsu 

Babanma dayaga dai cutar yawa zatai masa idan ankawo wani lokacin shike karbewa ya cinye ya hanasu Yana cewa ai kullum suke ci yaudai rabonsa ne shikadai.


Lurada Bata iyaci Bata bawa babanta ba yasa kawai yayo siyayyar abinci jibgi guda yasiyo da gaton risho yasa su Nanu Suka kawo.


Buhun shinkafa 'daya da katon din macaroni da spaghetti sai galan na mangyada da manja saisu tarkacen magi dasu ashana harma dadu omo da sabulai.


Sosai iya talatu ta bude baki da hanci tana kallon kayan abincin lokacinda ake shiga dasu dakinsa ta sake numfashi Mai shegen qarfi tana kallon dattiya dake shigowa gidan Yana waiwayen soron gidan da ake shigoda kayan saura kadan yafada cikin durum din ruwa Saida talatu ta riqo rigarsa tana cewa"


Yi ahankali karka karye mu cinye kayan kana kwance.


Fixge rigarsa yayi Yana Mata mugun kallo yace"


Ke Kuma shine baqin cikinki kar aci kayan Dani,

To inagadai ai badan niba da bazaki ciba kema tunda dabanyi masa aurenba zaisiyone yakawo harkici din ke me bakin cin.


Au yanxu Kuma alfaharin auren kakeyi sbd ganin buhun 'yar gote.,

To mudai Kam ai dama munsan arziki yanxu zamu fara cinsa duk uwar dukuyarda dikko ke loda masa yanxu Kam ci zamuyi musamman Ni.....


Ke banason zaqewa talatu wlh ki kiyaye ni.


Kallonsu zainab tayi cikin takaici tace"


Dan Allah baba karku fara fada tun yanxu akan arzikinda ko samunsa baayiba tukuna.



 

Post a Comment

0 Comments