TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 11

 #MAMUH.*_BURI DAYA Yana cikin Zafafa2020 na siyarwane  ba free ba idan baki biyaba ki nemi wainnan numbers din kibiya ki karanta cikin amincin allah._*


07067124863

08030811300



*_Mamuhgee11_*

Qarfe goma Sha 'daya su JJ da Suka fito kowane 'dan daba ranar dai manyan Kaya sukaita sawa wani suyi masa kyau wani kamar irin mutanen 9s dinnan sbd tarin sumar kansu gashi ranar Zaki yabada umarnin kowa ya aje makaminsa Babu ta'addanci yau tunda ranar auren magajinsa ce,


JJ kuwa wata farar shadda ce ajikinsa wadda Zaki ya dinka masa ba laifi tanada 'yar tsada Dan kuwa dubu ashirin yasiye ta yadi goma goma  guda biyu shi tasa sky-blue ta jj din fara.


Tuni qofar gidan da layin yafara cika da mutanensu Amma sai 'yan anguwa dasuka fara halartowa 

shidai dattiya kallon kowa yakeyi zuciyarsa ba dadi ga cikin gida ma Nadiya jikinta sai rawa yakeyi sbd tashin hankalin data samu kanta aciki ga zazzabi tanaji ga Rashin sukunin da zuciyarta ke ciki.


Lokacinda yafito cikin sky-blue din shaddarsa 'yar ciki da babbar riga ga hularsa Yana daura agogo yafito daki daidai fitowarta daga daki zataje Kiran iya talatu cak ta tsaya tareda juyowa ahankali daidai ya kallo gefen Suka hada ido.


Wasu irin hawaye ne Suka ciko idanuwanta sanin daga yau idan ta auri Bello bazata sake rayuwa a inda yakeba.


Dauke Kai yayi Yana sake hade fuska ya fito waje.


Wani irin annuri da haiba ke fita a fuskarsa sbd tsananin kyawun da yayi tamkar shine angon musamman izzarsa dake qara masa burgewa da kyau.


Nufosa JJ yayi cikin tsananin farin ciki ya miqa masa hannu sukai musabaha batareda ya saki hannunsa ba yace"


ALEEYU HAIDAR Ina cikin farin cikin ganin kana taredani a yau ranar aurena Rana mafi farin ciki agareni Saidai Ina roqon wani Abu daga gareka.


Wani irin murmushi yayi Yana basarwa yakalli JJ din ganin yanda yayi wani iri sai habarsa ta dakesa atake yaji tsananin qaunar JJ din nasake shigarsa Dan kuwa shikadai yasan irin son dayakewa JJ Wanda yasa yake danne ciwon dayakeji a qirjinsa ganin JJ na farin ciki da auren.


Cikin kulawa yace"


Kafadamin abinda kakeso agurina zan baka kodan tarihin wannan Rana agareni.


Murmushi JJ yayi yace"


_*NADIA*_ nakeson tasamu dukkanin farin ciki da walwala tareda kulawa da qauna data rasa tun rasuwar umma,


Kallonsa yayi tareda dauke Kai Yana zame hannunsa daga nasa fuska a daure yace"


Wannan duk zaka Bata bayan aur.....


Bai qarasaba ya juya zai wuce

JJ yace"


Nayi Mata alqawarin nema Mata lafiyarta matuqar Ina raye da lafiyata,

Saidai bansaniba kozan iya,

Roqona anan shine Ina roqonka da a duk lokacinda na gaza cika wannan alqawarin to cikaminshi koda inanan ko banan.....


Juyowa zakin yayi Saidai kafin yayi magana ya hango kb tafe cikin mutane ya rufe fuskarsa Yana boye wani Abu cikin riga.


Janye JJ yayi da sauri zai tare kb din Saidai jj na juyowa yaga sharbebiyar wuqarda ke hannun kb wadda asalinta bakin lace ne da Ida kamar tafiyar maciji idan aka sokeka da ita yanada wuya ta fito Bata yanko hanjinkaba shiyasa ba'a tsallaketa.


 Kb na daga wuqar JJ ya tare atake ta shige cikinsa gaba dayanta kafin kb ya fizgota da qarfi yanda zatafi yimasa illa.


Wani irin numfashin wahala JJ yasaki tareda zubewa qasa kb na ganin hakan ya gudu musamman da Babu Wanda ya Ankara da abinda ke faruwa


Zaki zabura yayi ya damqo hannun kb JJ yayi saurin riqe nasa a wahalce yace"


Ina buqatar kusa Dan Allah.


Cikin karaji yacewasu nano subi kb su kamosa karsu Bari ya gudu.


Atake guri ya kaure da hayaniya sbd ganin abinda ya faru jini gabaki daya ya Bata farar shaddar jikin JJ har qasa.


Wani irin runguma Zaki yamasa Yana cewa"


JJ Dan Allah karka rufe idonka zamuje asibiti zaka warke yanxu muxo a daura maka aure,

Karka manta Kaine kuzarina da ganina,

Kaine magajina,

Karka rufe idonka Dan Allah JJ......


Cikin tsananin karaji yace akawo masa mota.


Hankali tashe da ganin jininda ke zuba Suka sakashi mota a gigice Zaki ke tuqin hannunsa daya na damqe dana JJ da tuni idanuwansa Suka rufe.


Duk yanda su dattiya ke cikin 6acin Rai hankalinsu yatashi matuqa da abinda yafarun Dan kuwa tabbas kowa yasan JJ shine abunda Zaki yafi so,shine komai na Zaki.


Zancen na shiga kunnen Nadiya ta sulale qasa tana tsiyayo hawaye da idanuwanta dasuka gama kumbura dayin jajir.


Suma sauran mutan gidan sun firgita sosai da jin zancen musamman da aketa cewa JJ yariga ai yarasu.



A asibiti kuwa suna zuwa 'yan sandan da ale dikko yaturo musu suna isa nan aka karbesa a gagauce akai cikin theatre dashi.


Kasa zama Zaki yayi tareda yamutsa sumarsa yanajin zuciyarsa kaman tana qonewa sbd tsananin tashin hankali da baqin cikin dayake ciki.


Su nano tuni Suka iso asibitin sbd dai kb ya gudu Amma dai aisunsan bazai guje musu ba idan hankali ya kwanta.


Sosai suke cikin tsananin tashin hankali da fargabar abinda zai faru,


Asibiti kuwa atake kowa yasan yau su sarki na asibitin Dan kuwa tuni kowa ya dauko makansa.


Minti goma Sha hudu da shiga dashiga dashi likitoci biyu Suka fito fuskarsu ba dadi Kai tsaye 'dayan yace"


Sai hakuri Allah yamasa rasuwa..


Akaro na farko arayuwarsa da hawaye Suka sauko idanuwansa yayi baya tareda zubewa a kujera Yana dafe kansa dazai tsage sbd wani irin sarawa da jijiyoyin kan sukeyi.


Su Nanu kuwa tuni duk Suka saki makamansu kowanne na sunkuyar dakai cikeda baqin cikin rasa 'dan uwansu,aminsu mai qaunar dukkaninsu.


Sosai Dr aminu da Dr faruk Suka tausayawa halinda Zaki yashiga musamman dasuka lura kansa yake ruqewa sunsan illar dake cikin hakan sukai saurin sa nurses maza su kamosa ashigo ciki dashi Yana buqatar kwanta suyi masa allurar minti goma.


Miqewa yayi da kansa yashiga kodan yaga gawar JJ 'dinsa Saidai suna shiga yaga gawar JJ din rufe har Kai da qafa 

Atake yaji zuciyarsa na neman tarwatsewa itama ya isa bakin gadon yayi shiru Yana tuno maganganunsu na qarshe.


Ya dade Yana kallon gawar kafin ya juyo baiko tsaya sauraron Kiran da Dr kemasa amasa allura ba yafito atake yaransa Suka Mara masa baya musamman dasukaga fuskarnan ba rahama ko daya.


Cikin motarsu Suka figeta sai qofar gida lokacin Sha biyu saura minti ashirin gashi mutane na nesa basusan da abinda ke faruwaba tuni aka sake cike gurin taf da 'yan zuwa daurin aure.


Dan kuwa tuni akayi shimfidu anata gaishe gaishen barka da zuwa.


Suna sauka Kai tsaye gurin kawun ya nufa shima yana ganinsa yayiwa idi ido nan aka fara shelar za'a daura auren.


Take kowa ya zazzauna aka fara.


Yana isowa ganin mutane da yawa yasa yazo har kusada kawun ya zauna Kai tsaye yace"


Zanyi magana dakai kar a daura sbd JJ ya....


Cikin nutsuwa kawu yace"


Kabari agama daura auren muyi magana yanxudai ka nutsu auren 'yatane bana son matsala.


Miqewa yayi yabar gurin ya hargitse kansa yake.


Cikin nutsuwa dattiya ya fitarda dubu goma a miqawa liman yace"


Ga sadakin 'dana nan.

 

Karba akayi aka miqawa mal idi dashine yayi waliyin Nadiya.


Yakai mota zai shiga subar gurin yaji ana cewa"



*_AN DAURA AUREN ALIYU HAIDAR DA NADIYA DATTIYA AKAN SADAKI NAIRA DUBU GOMA LAQADAN BA AJALAN BA ALLAH YASA WANNAN AURE SAI MUTUWA_*


Aminnnnnn jama'a Suka karba anata miqawa dattiya hannu ana tayasa murna nan guri ya kaure da hayaniyar Taya murna.




Post a Comment

0 Comments