TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 17

 💫 SANYI DA ZAFI 💫

 ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣7️⃣

Tana shiga gıda Mamag tace “ke kuma an ina kika tsaya?” Ahankali tace “waje” kawai tashiga ciki zata kwaso kayan abinci dan daura girki Mama tace “kibar girki inada abincin da Riyad yakawomin har yanzu da zafinsu a kula shi zanci, kizo kije school daganan ki wuce aiki, Riyad yace kidawo” dasauri tafito daga dakin ta kalli Mama tace “Mama nifa yau na dauki permission bazanje school ba” saikuma ta taho ta zauna wajen Mama tace “Mama wai kinsan mutumin chan ne”? Mama na kallon kwayar idanunta tace “wani mutumin”? Cikeda mugun hali tace “shi wannan mutumin daya kawomu naga kunatayi kaman daman kunsan juna ne tun chan” dan murmushi kadan Mama tayi tace “a’a amman kawai zuciyata ya natsu dashi kaman na sanshi daga wani wuri, kema kinsan dawuya nake natsuwa da mutane amman shi kawai yayi fuce araina, mutumin arziki ne mutunci da dattaku, yanada halaye da dama nagari, bantaba gani a idanunshi yamin kallon mai wata cuta ba, gakuma yanda yabiya kudin asibiti akamin komi, wanda yamaka Akhairi kasoshi” ranta adan bace tace “Mama ni na tsaneshi” baki Mama tasaki tana kallonta ganin da gaske take, yunkurawa tayi tace “kuma konawa ya kashe miki a asibiti saina biyashi alkawari ne ko zanyi shekara dari ina neman kudin” dan dariya Mama tayi tace “zo ki juye abinciccikan ki wanke kulolin nidai fitina’u” wucewa tayi ta kwasa batai musu ba haka dai tai aikin komi Baba Liman ma yashigo gaida Mama wuraren 1 ta shirya ta tafi aikin sabida yanda Mama tace “saitaje” ga mamakinta ko kallon banza Madam bata mata ba hakama sauran ma’aikatan dudda bataga Hussy ba, kin zuwa office na Riyad tayi tadaiyi duka ayyukanta idan tana gaban desk aka kira ana neman cleaner a so so room ta taje, harta tashi by 6 bata ganshi ba bakaramin dadi tajiba ta tafi gida.


Washegari da sassafe ta tafi hospital nasu yau pediatric surgery departmant zasu to watch not to do itada team dinta zasu, direct tawuce inda suke ijiye bags nasu ta ijiye aka dan musu lectures kadan sannan tawuce tashiga shirye shiryen shiga surgery tsayawa tayi tana wanke hannunta wata tazo itama ta tsaya kusada ita tai murmushi tace “Hi” saikuma ta kalli Labcoat nata tace “Rashida I’m Maimuna but Maimoon ake cemin, tun ranan monday nake noticing naki, can we be friends pls”? Dan tsayawa Rashida tayi tana kallonta like a weirdo dasauri Maimoon tace “please” dan lumshe ido Rashida tayi yarinyar seems very cool and calm ahankali tace “I don’t know yanda ake friendship gaskiya” murmushi sosai Maimoon tamata tace “I know and I will teach you, let’s go” shiga cikin operation room din sukayi duk hannayensu a sama aka sassaka musu handglove ga yaron da za’ama operation din da baifi shekara biyar ba anyi sedating nashi shigowa surgeon din yayi wanda Babba ne bawai yaro ba aka samai nashi handglove din yawuce surgical table din student Doctors din dasuke su bakwai duk suka tsaya a gefe, Dr yace “yaron nan dake kan table din nan nada hydrocele wazai gayamin procedure da zanbi in this surgery, and ya sunan surgery din”? Maimoon ce tafara daga hannu tabata amsa yace “wrong” almost dukansu saida suka bada amsa yace “wrong” yakalli Rashida dabatai magana ba dan ita bata show off ko a aji, yace “make attempt miss” dan ijiyan zuciya ta sauke Rashida confidently cikin turencinta that is good muryanta kuma makes it sweet a kunne tace “zamuyi Hydrocelectomy surgery to remove the hydrocele daga scrotum din, zamuyi making incision anan…..” tafara bayanin procedure din da sai kawai Dr ya tsaya yana kallonta exactly abinda zaiyi tafadi kaman ta tabayi, hannu yamikama head nurse yace “scalpel” samai wuka akayi a hannu yarike yadauki marker yamikama Rashida yace “come close” ahankali ta matso kusada surgeon din gabanta nadan faduwa yabata marker yace “draw the line” karba tayi ahankali taja, to her biggest shock yace “make the cut” dasauri ta kalleshi, confidently yace “I’m here you won’t make a mistake so go ahead” dan tsayawa tayi Dr yace “we all start ahaka, go for it, I’m right here ina kallonki” bismillah tayi ahankali ta karba tana kokarin kallon fuskan yaron yace “don’t look at his face” ijiyan zuciya ta sauke tareda rufe ido what is her biggest motivation da inspiration na son zama likita? Ahankali tace “Mama! I want to become the best Doctor for Mama! I want to make research nagano yanda ake curing HIV for Mama! I want to make Mama better, I want to be the best Dr in Nigeria da kewaye da al umma zasuyi alfahari dasun samu” daidainan tabude idanunta kawai tashiga cutting Dr na tsaye kusa da ita yace “suction” aka kwashe jinin, wasa wasa da shi da Rashida sukai surgery din nan tass yasake barinta tai stitching yaron up, her stitching style kadai saida ya kalleta almost 10yrs yana aiki in this surgery student Doctors daban daban interns but baitaba ganin skilled yar baiwan Dr like this girl ba ita kanta for now bama tasan wacece itaba imagine abinda take iyayi in year5, sallaman su yayi yakalli Rashida yace “makesure you become a surgeon Doctor R” dan sunnar da kanta tayi batare datai murnushi ba cus she hardly smile outside tawuce tafita Maimoon tabiyota tace “wowwww you are amazing Rash kai! I can never do that” ahankali tace “thanks” dasauri Maimoon tace “let’s go grab some drinks” wayanta Rash taciro daga jaka taga 2:30 tace “ohh no I have to go to work” taciro log book dinta da sauri tawuce taje aka mata signing tajuyo takalli Maimoon tace “gobe” bata jira amsanta ba tajuya dasauri Maimoon ta tsaya awajen tai shiru tana kallonta, tace “she’s unique, Bilal you loose a rare gem”.  Wajajen 3 takai hotel din dan saida ta tsaya tai salla tana shiga tawuce changing room tafito kenan saiga Madam tace “yanzu ne lokacin zuwa aiki i will deduct 5k from salary naki” sauke kanta tayi kasa tawuce tashiga aiki thank God yau Friday gobe ba aikin, tass tagama aikace aikacen ta wuraren 5 Madam ta kirasu hall duk suka wuce, abinci tagani an kakkasa buhun shinkafa, jarkan mai, indomie, madara da milo sugar sai gero da taliya tace “kowa ya tafi da abincin azuminshi gida courtesy of  Oga” sai murna ake, tunda tafara aiki dasu da Ramadan ana basu abinci last year an bata is not new thing amman saitakeji yanzu kaman karta dauka sabida Riyad but kuma idan bata dauka ba za’ayita surutu daman ance tanada girman kai, Madam tace “zansa security su taya kowa fita da nashi sai kuje ku kira keke, Happy Ramadan to everyone” ihu duk sukayi ana shouting thank you Ma sannan ta sallamesu wucewa tayi ta chanza kaya ta goya jakanta tafito taje ta taho da keke tana zuwa security suka tayata lodawa abayan keken ta tafi.


Yau sunday tana so taje kasuwa tadan yo musu yan kananun cefenen azumi tunda batada aiki yau, atampa tasaka green shima ya kwana biyu tadau wani black hijabi ta daura asama mai hula ya tsaya mata a knee aiko yamata kyau tafito falo inda Mama ke zaune tana kirga kudinsu, zuwa tayi kusada Mama ta zauna Mama tace “yauwa kin shirya”? Gyadama Mama kai tayi, kudin da Mama takasa agabanta kashi biyu ta dauki me yawan tabata tace “ga wannan kudin dubu talatin ne nakine kisai dan atampa da takalmi da yan kayan kwalliya da turare kema kiyi kyau da salla kuka dawo sai akai dinki ko” dasauri ta maidama Mama kudin tace “Mama bana bukatan kayan salla, kayan danake dasu zan iya sawa da salla, Mama we have important things to do, drugs dinki, abinci, school fees dina dakuma kudin da mutumin chan ya kashe na asibiti ni sai na biyashi” kallonta Mama take tace “shiyace miki kibiyashi “? Girgizama Mama kai tayi tace “Mama you’re my responsibility ni kadai don’t others, banson wani ya taimakeni wajen kula da mahaifiyata, inda bekaiki asibitin masu kudin nan nasu ba dana iya biya amman yakama kaman an sashi ya kaiki asibitin kudi” tai maganan tana batarai tsayawa kawai Mama tayi tana kallonta tun Rashida na yarinya tanada wani irin kishi dasai ka san halinta ne zakasan kishine itafa batason kowa na raban Maman ta, yana daga cikin abinda yasa takejin haushin Riyad dakuma so tabiyashi kudinshi sabida yanda taga yana nan nan da ita bataso taga Mama na kula wasu with a smile, maida kudin kawai Mama tayi hannunta ta danne tace “listen to me umarni nabaki kisai kayan salla inaso nima naga yarinyana tayi kyau takuma fito da salla kinji” shiru tayi tana kallon Mama taki magana hade fuska Mama tayi tace “bazaki amsaba?” Ahankali tace “naji toh” dan murmushi tayi tabata 20k tace “wannan sai kiyo su cefene su maggi da nama da kayan miya tunda mun sami kayan abinci” gyadama Mama kai tayi ahankali ta tashi Mama tace “adawo lpy ki duba titi kafin ki tsallaka kinji” toh ta amsa tawuce tasa takalminta tafita abinta Mama tai murmushi.


Kusan 3hrs tabata a kasuwa, tasayo atampa mai kyau da gyale da takalmi tadansai bra da pant guda biyu sai pad dan tanaji cikinta na ciwo sannan tayo cefene tashigo keke tabar kasuwan.

Abakin titi aka saukesu hakan yasa ta dandaro cikin anguwansu da kafa, tun kafin takai gidansu ta hango wata arniyan karaman mota baka pake a kofar gidansu motan waye wannan? Hakan yasa ta kara sauri tana zuwa tabude kofar gidansu da sauri ta shiga saura kadan tayi karo da Riyad azaure yadan koma baya kadan tsayawa itama tayi gabanta kawai yafadi ta zubamai ido, yana sanye da wani milk soft yard dake kyalli yabi jikinshi kaman magic, kafanshi kafanshi sanye da Jordaan leather loafers brown, hannunshi daure da agogon Audemars Piguet, dayan hannunshi rike da waya samsung galaxy fold, ba hula gashin kanshi ya kwanta yana sheki sai kamshi yake zubawa, dauke kai tayi da sauri daga kallonshi dan he’s so clean wlh ko datti ko stain ko tabo guda daya babu ajikin kayanshi, haka kayan a goge babu squeezing ko daya, shima tundaga kan kafafunta dake sanye dawani black takalmi flat da duk an dinke ya kalla dudda fararen kafanta are shinning ga long fararen nails na kafanta da babu lalli ko daya akai zuwa ataman dake jikinta da hijabin da ledoji biyun dake hannunta bakake data rike sannan yazubama fuskanta idanu she looks tired, she’s even sweating a goshi dan duk gashi ya kwanta a goshin nata, ga lips dinta sun bushe kaman she’s a bit sick. “Kallon fa”? Tai maganan cikeda rashin kunya dayasa ya daidaita kwayar idanunshi cikin nata dasauri ta janye idanunta hakanan taji takasa kallonshi but tsabagen karfin hali tace “kadena zuwa gidanmu banso” cikeda isa kaman anyi forcing nashi yayi maganan awulakance yace “are you angry ba wajenki nake zuwa ba”? Wani dum! Taji saukan maganan da sauri ta kalleshi tsaf shima yake kallonta mene mutumin nan yace? Mema ya dauketa? Taji haushi dan ba wajenta yake zuwa ba on wat ground? Kokarin hado martanin dazata bashi take dan she was a bit speechless but yarigata wani kallon raini yamata calmly yace “bakida matsayin dazan zo nemanki” yana maganan yabi ta gefenta yafice wlh takai 1 good minute fassara maganan shi take akanta taji ranta na kumfa dasauri tajuyo tafito kofar gida daidai yaja motanshi tabishi da kallo yana wani saka bakin glass a idanunshi ko inda take bai kallo ba yawuce abinshi kaman zata hadiye zuciya tamutu tace “nima ka isa kazo wajena ne aka gayamaka? Sai ji dakai kaman wani dan shugaban kasa sabida yana takama da dan hotel din dayake dashi I will leave your company soon zan nemi wani hotel din wlh kuwa” tana maganan tajuya tana saisaita bacin ranta takoma cikin gidan kaya tagani cikin gidansu harda su indomie da kwalin kwai kudan 5 crete gasu manta manyan roban madara Milo oat, wlh shopping data gani zube a compound yakai na 300k ga bandir na kudi kuma ijiye kasa na yan 1k guda biyu dasauri ta shiga ta tsaya gaban kayan ranta abace tace “Mama waya kawo mana abubuwan nan”?


Ahankali Mama tace “Riyad yakawo” kaman zata fashe sabida bacin rai tace “Mama shine zaki karba?” Kallonta Mama tayi tace “babu yanda banyi dashi ba amman yaki yarda wai ni mahaifiyar sa ce kodan darajan azumi na amsa, kinga uban kudin daya ijiye dane naki amsa da kyar na zari yasake daura daya, haka ya ijiye komi anan dan ni naki karba” cikeda bakin ciki harda abinda yamata a zaure tace “Mama shine baki kira yara kinsa sun maidamai da kayan mota ba”? Kaman wacce aka daka kawai saita fashe da kuka sosai ta ijiye kayan data shigo dasu daga kasuwa nan kasa ta tsallaka tashiga daki kawai tahau kuka idanunta sunyi jajir tashi Mama tayi tabiyota ciki cikeda damuwa tace “Rashida mekuma haka da kuka? Duk mai imani yadaga ido yaga rayuwanmu dole yaji tausayinmu, na karba badan komi ba saidai naga yaron kirki ne hakanan zuciyana ya natsu dashi kuma bawai saurayi bane ya gayamin yanada mata so mutum ne mai hankali ba yaro ba, saikuma dalili nabiyu shine karbansu zai saukaka miki kema at least daganan zuwa 2month zamu manta da siyan Kayan abinci albashin dazaki samu saimu hada da wayan nan kudin ki biya kudin school fees ragowan mu rike na asibiti, you think I’m happy da rayuwan wahalan dakikeyi? Understand me it’s Ramadan kyaututuka haka is normal ko na yan anguwan man sabida baki karba ne da yanzu an kawo mana, it’s okay ya isa stop crying” Mama tajawota cikeda lallashi rabon datai kuka haka tun ranan da aka kwantar da ita a asibiti cikin kuka tace “Mama stop collecting abu daga hannun kowa, I’m enough for you, Mama bazan taba bari ki kwana da yunwa ba, I will never” hawaye taji yaciko idanunta saikuma tai murmushi ta danne takai hannunta ta share mata fuska tace “I know y’ata will never allow me to go hungry, natuba to bazan kara karban komi daga hannun kowa ba, Rashida na is enough for me, the best daughter aduk duniyan nan, come here” Mama kawai ta rungumeta tana murmushi she’s lucky Allah ya azurtata da y’a dake sonta haka, sun dade ahaka sannan Mama ta dagota takai hannu ta yaye hijabin jikinta ta tana taba wuyanta tace “jikinki da zafi baki da lafiya ne”? Ahankali tace “cikina ke ciwo kadan gobe naje asibiti zan karbi magani” cikeda so Mama tace “sannu kinji, zauna kihuta ni zan miki girki” dasauri tace “zanyi Mama” tashi zatayi Mama takama hannunta bawasa kan fuskanta tace “zauna kihuta” zama tayi Mama ta tashi atampanta tafara dubawa ta yaba sannan tashiga daura musu abinci itakuma anan bacci yayi awon gaba da ita.


Da kyar Mama ta tadata around 4 na asuba sabida suyi sahur, tariga tasan bata azumi wucewa tayi tama Mama abincin sahur sannan tawuce bayi yau da hot water tai wanka dan zazzabi takeji da ciwon mara but she feels she can manage dan is not that serious tana dawowa takaima Mama itama nata ruwan zafin tashigo daki tace “muje Mama” idanunta Mama ta kalla tace “dan Allah kina zuwa clinic kisha magana kar zazzabin nan yarufeki da kyau kinji” gyadamata kai tayi Mama tace “barshi zan iya zuwa bayin da kaina jeki kimtsa” batai musu ba ciki tawuce tashiga kimtsawa tasa black abaya tahada jakanta na baya saikuma ta kara kwanciya yawanci a rashin karfi ne kafi gane Rashida is sick dan baka ganewa a baki da fuska sabida masifa da fada, shigowa Mama tayi ganinta a kwance yasa Mama tace “namiki shayi”? Girgizama Mama kai tace “idan naje school zanci abinci Mama karki damu” da dan damuwa Mama tadauko mai tana shafawa hartai salla tana kwance wajen saima lumshe ido data farayi sai kawai Mama ta barta zuwa 7 ta tabata tace “tashi kitafi school” tashi tayi ganin Mama tafara damuwa yasa tace “laaaa Mama kinga najini garau maybe dama baccin danake ji yakara karamin zazzabi” 200k na jiya Mama takawo da 100k nasu tasa asama tabata tace “gashi ki biya kudin makaranta kisai yan littafan da baza’a rasa ba” kallon kudin tayi zatai magana Mama tace “ni Maman ki aka bama kudin nan, nikuma nabaki, kaman yanda Hajiyan nan taraba mana 20k a clinic naje na siyamiki crocs consider wannan kudin haka, go and pay school fees naki and buy textbooks dakike bukata” ayanda fuskanta kadai yayi kasan bataso ba but ganin yanda Mama tayi yasa tasa hannu ta karba kawai tasa kudin ajaka ta goya, taja black gyale tashiga rolling tai kyau kaman balarabiya dudda bakomi akan fuskanta sannan tace “Mama natafi” 5k takara cirowa cikin kudinsu dabaifi 50k ba Mama tabata tace “dan Allah kihau keke yau, kici abinci mai kyau a school kinji” gyadama Mama kai tayi tace “natafi Mama thank you” “adawo lpy Allah bada sa’a” fita tayi tana kaiwa junction ta shiga cafe tai printing ramita, sannan tafito tashiga keke sai bank taje tafara biyan school fees nata sannan tafito tashiga keke again sai asibitin su, sauka tayi wuraren 9:30 taga student nasu Maimoon na hangota ta taho wajenta dagudu tace “anyi releasing namu yau, kaman za’ayi manyan baki ne dai ance mu student mutafi wlh” ahankali tace “really, bari na karbi magani to natafi” dasauri Maimoon tace “meke damunki”? Dan yatsine fuska tayi tana tafiya tace “I think I’m coming down with Maleria saikuma cramps” Maimoon tace “oh no sorry” office nasu tashiga tabude locker ana ijiye musu magani haka tadauki na Maleria da cramps suka fito yawance Maimoon ke hiran, ahankali tace “I want to buy food da water dazansha magani dashi” dasauri Maimoon tace “muje cafeteria” Jellof rice tasaya da beef 800, tasai ruwa daya ganin tana bude jaka yasa Maimoon tace “mu zauna anan kici mana” girgiza kai tayi tace “kema kawai na gayamiki ne only Mama na ke sani idan bana azumi I don’t want people knowing kunya yake sani” dan murmushi Maimoon tayi tana kallonta yanda take arranging abincin ajaka tana maganan she looks so cute and adorable maida jakan bayanta tayi ta goya tace “bari naje to sai gobe” Gyadamata Kai Maimoon tayi suka fito tana kaiwa titi tashiga keke, is just around 10 yanzu gwara ta tafi hotel tamusu aiki saita sami free evening har gaban hotel din aka kaita ta sauka tabiya kudi tashiga ciki, direct changing room nasu taje, saida tafara chanza kaya sannan tadan fito ganin kowa na aikinshi yan morning sun riga sunzo tun dazu so kafin wani yadawo dakin nan cikinsu kuma probably sai idan yan afternoon sunzo kuma, hakan yasa tadawo ta maida kofan tarufe batare data saka sakata ba takoma ta zauna taciro rice daga bag da water dakuma maganinta ta ijiye kan long bench dake wajen itama ta sauna ahankali sannan ta dauki abincin tabude tasa spoon tafara ci ahankali bayamata dadi ma abincin sabida zazzabi.


Ahankali yake tafiya da shi da Munir dawasu ma’aikata guda biyu dake biyedashi abaya, akwai some changes dayakeso ayi abinda ma yakawo shi hotel din kenan this morning, duk ya gama nuna musu saura changing room na ma’aikatan shi corridor suka shigo suna biyeda shi yasa hannu yabude kofan yasakai ciki yana magana yace “the lockers nakes…….” Shiru yayi ganin yanda Rashida tawani yarda takeaway jellof rice din da ruwan yashiga tittila akasa ta tashi tsaye da sauri daidai su Munir zasu biyoshi su shigo ciki yace “wait!” Duk kallonshi sukayi suna tsaye bakin kofan batare da sun shigo ba strictly yace “kuje lobby” yanayinshi kawai yasa Munir yace “okay” yajuya ma’aikatan ma suka bishi yajuyo yazuba mata ido tana kallonshi cikeda fada baki tabude zatai magana dan akwai abinci abakinta sai kawai tai wani wawan kwarewa sai tari, maida kofan yayi yarufe ya kalleta ganin yanda take tari kaman zata mutu yasa gently yaduka yadauki bottle water nata daya fadi yadan zube yamike tsaye yasake kallonta tsabagen tarin datakeyi tama kasa tsayuwa ta tsugunna idanunta sunyi jajir ga rice guda daya fito daga hancinta alamun ba karamin kwarewa tayi ba, dasauri yataka zuwa inda take ahankali ya tsugunna yamika mata bottle water batare dayayi magana ba yana kallon fuskanta, tsabagen azaba sabida ga yaji a abinci ga kearewa mai kyau batasan lokacin data daura duka hannayenta biyu saman kan nashi ba takama both hannunshi da goran takai bakinta hakanan jiyayi jinin jikinshi ya tsaya chak jin saukan hannayenta biyu kan nashi, ahankali yadaura idanunshi kan hannunta dake saman nashi sannan yakai idanunshi kan fuskanta da yanda takeshan ruwan kaman yaki, tass ta shanye ruwan sannan tacire bakinta daga goran har lokacin tana rikeda hannunshi dabatasan tayiba tana sauke ijiyan zuciya kaman wacce tagudo daga hanyan mutuwa idanunta sunyi jaa, kusan 1min tayi tana sauke ijiyan zuciya sannan ahankali kaman mara gaskiya tadan dago kanta tadaura idanunta akan nashi yanda yake duke dab da ita kamshin turarenshi ya bade wajen da sauri ta maida idanunta kasa still bata sakeshi ba, yana kallon fuskanta baya ko kyafta ido yace “can you let go off my hand now”? Dawani irin sauri ta kalleshi saikuma ta kalli goran ruwan data rike ganin yanda ta kama hannunshi da duka hannuwanta biyu saida taji kaman ta kurma ihu sabida kunya dawani irin sauri tasakeshi hakan yasa ya mike tsaye ya kalli magungunan ta dake kan bench na wajen sannan yawuce kofa haryasa hannu yabude kofan ya tsaya batare daya juyoba yace “kifito amaidaki gida, kafin ki mutu in my building” dasauri ta kalleshi kaman wata damusa dan juyo da kanshi yayi but bai kalleta ba yace “take days off when you feel better you can resume” yasa kafa yafita saikuma ya tsaya yace “someone will clean the place you don’t have to, kifito akaiki gida!” Yana maganan yawuce yafita takai almost 2min aduke a inda yabarta saikuma ta daga hannuwanta ta kalla yanda tarikeshi saikawai taji kunya da haushin kanta sai abin yasa taji mugun zazzabi ya rufeta tanama jin sanyi, ahankali ta lallaba ta mike tadauki jakanta ta goya abaya batare data chanza uniform nata ta maida abayanta ba kafin wani ya sake shigowa yaganta tana chanza kaya she will not take the risk, tadauki magungunanta tarike a hannu tafito tana tafiya ahankali hakanan kawai sanyi taji tanaji barinma a hannuwanta dasuke abude dan uniform nasu short hands ne, gashi small farin baby hijab ne jikinta that covers her chest only, ahankali take tafiya is as if every step datai taking yana kara mata zazzabi harta fito lobby kadan kadan take tafita tana jin sanyi kaman akwai kankara awajen, hakan yasa bakinta yahau kakkarwa irin na me jin sanyi din nan kaman an sata a cold room, idanunta na rawa rawa suna kukkullewa kadan kadan take bude idanunta tasan ta hango mutane zazzaune da suit a lobby daganan kuma batasan meya sake faruwa ba dipp kaman an dauke wuta ta zube awajen.




Post a Comment

0 Comments