TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 7_8

 πŸ€¦πŸ½‍♀🀦🏽‍♀🀦🏽‍♀🀦🏽‍♀🀦🏽‍♀🀦🏽‍♀🀦🏽‍♀🀦🏽‍♀🀦🏽‍♀



*STORY & WRITTEN*



     *BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*







*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*✍🏽





*Wannan shafin na ku ne*


*Batul Adam jattako*

*Marubuciyar* (Dama ta) πŸ’”πŸ’”πŸ’”


*Ina jin dad’in shawarar da kike bani da kuma kulawar ki gare ni, ba abin da zan ce miki sai godiya*.






*Ban manta daku ba*


*Mrs Mansoor*

*Marubuciyar* (Munafukin miji)

πŸ’–πŸ’–πŸ’–


*Da*


*Memcy Ata*

*Marubuciyar* (Ni da yaya Farooq)πŸ’žπŸ’žπŸ’ž


*Ina jin dad’in yadda kuke son wannan novel d’in*


*Ana tare*.🀝🏽





*QUESTION OF THE DAY*


Wani sahabi ne yake fad’in Magana tazo daidai da saukar wa a cikin Alkur’ani mai girma?






7&8


Murmushin mugunta yayi ya ce "by the count of three ku fara up & down"

K’irgawa ya fara yi da 1…2….kafin yakai 3 har mun fara. 


Mun d’au kusan 15 min muna up & down amma yaya Faruk bai da alamar dakatar damu.


Juyawa nayi na kalli Anisa da ta dage ba ta ko tsayawa, zufa sai zubo mata take yi ga k’afar ta sai rawar awilo take yi saboda gajiya.


Duk da nima a gajiye nake amma hakan bai hana ni tausaya mata ba kasancewar yadda ba ta son purnishment.


Rawar da k’afar ta taci gaba da yi ne yasa na kasa danne dariyar da take ci na, fashewa da dariya nayi ba tare da nasan dariyar zata fito ba.


Mamaki ne ya kama yaya Faruk ganin dariyar da nayi amma bai ce min komai ba illah mik’ewar da yayi ya nufi inda chargers wire d’in mu suke ya zaro d’aya daga ciki ya nufi inda muke.


Anisa ce ta fara kuka tana cewa "yaya Faruk don Allah kayi hakuri kar ka dake mu baza mu sake ba"


Wuce ta yayi ya k’araso guri na ya zuba min d’aya a jiki, ina jin saukar bulalan na daka tsalle na hau kan kujera amma haka yaya Faruk ya biyo ni ya k’ara zuba min.


Rawar a sosa mata na fara yi domin ko ta ina sosa jiki na nake yi, ji nake yi kamar an zuba min k’aik’ayi a jiki na.


Rok’on shi na fara yi ina cewa "yaya dan girman Allah da darajar su momi da daddy da kuma darajar matar da zaka aura da kuma girman kakin sojan da kake sa wa kayi hakuri"

Duk da ba ko wani lokaci yaya Faruk ke dariya ba amma a lokacin sai da yayi dariya sannan a lokaci d’aya ya d’aure fuska kamar bashi ba ne yayi dariya.


Kallo na yayi kamar bazai yi magana ba can ya ce "uban wa kike wa dariya? ko kin ga mahaukaci ne a gurin nan"


"ni ba da kai nake yi ba, Anisa nake ma dariya" na fad’a da alamar tsoro. 


1-sitter ya samu ya zauna ya d’aura k’afar shi d’aya akan d’aya yana fuskantar mu.


d’akin ya d’au shiru kamar ba mutane a ciki, sai da ya gama mulkin sa sannan ya kalle mu ya ce "zan tausaya muku na laifin da kuka yi, yanzu sai purnishment d’inku na surutun da kuka sa ni, saboda kun san surutu bai dame ni ba, ni ba irin ku bane in ta zuba kamar parrot"


kuka muka fara yi muna bashi hak’uri saboda yadda k’afar mu ta gaji amma ko alamar tausaya mana bai yi ba illa juyowa da yayi ya ce "kuyi kneel down & raise your hand up, ku rufe idon ku, by the count of 2 ku fara"


ai kafin ya fara k’irgawa muka yi kneel down, gwiwa ta kuwa ji nake kamar ba jiki na take ba saboda tsamin da tayi.


Haka muka d’aga hannun mu muka rufe idon mu, a raina kuwa ban san sau nawa na ma yaya Faruk Allah ya isa ba saboda duk yadda ka ke neman mugu in kazo gurin shi, zance ya k’are.


Duk da ido na a rufe yake hakan bai hana hawaye zubowa a ido na ba saboda rabon da a bamu irin wannan purnishment d’in ko a school har na manta.


Mun d’au kusan 7 min a haka sannan muka ji sallamar yaya Khaleel, wani dad’i ne ya kama ni saboda nasan Allah ya kawo mai ceton mu saboda shi yaya Khaleel duk ya fisu hak’uri da wasa don in muna hira dashi kamar wani mate d’in mu muka maida shi.


Yaya Faruk ne ya amsa mai sallamar da yayi, nufo inda yaya Faruk yake ya mik’a mishi hannu suka yi musabaha kana ya nemi kusa da kujerar da yake ya zauna


"yaya sannu da gida? Yaya Khaleel ya fad’a.


Ya amsa mai da "yawwa Khaleel, ya school d’in?


"School lafiya lau" sannan ya juya ya kalle mu wanda duk mun galabaita saboda izayar da yaya Fauk ya mana kana ya juyo da kallon shi ga yaya Faruk yaci gaba da cewa "yaya Faruk ina neman alfarma a gurinka ka tausaya ma sisters duk da ban san laifin da suka yi ba na tabbata ba za su sake ba, ko saboda Anisa yaya ba ta jurar purnishment"


Juyo wa yayi ya kalle shi yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai da ya gama shan k’amshin sa sannan ya ce "Anisa kawai ka sani da zaka ce ba ta son purnishment ko ita Fatima an fad’a maka ba ta gaji ba"

Da mamaki Yaya Kalil ya kalle shi amma bai ce mai komai ba.


"Stop" abin da yaya Faruk ya ce mana kenan.

Kamar jira muke yi muka sauke hannun mu yayin da muka fara kuka.


Ummu ce ta fito daga side d’inta ta nufo main parlour inda take jiyo kukan mu.


Guri ta samu ta zauna ta kalli yaya Faruk inda take cewa "babban yaya kai da k’annen naka ne? hala wani laifin su ka yi"


Ta juyo da kallon ta zuwa gare mu tana cewa "ku kuma ku rufe wa mutane baki, kun cika ma na gida da kukan ku"


Yaya Faruk ne ya sanar da ita abin da muka yi.


Mik’ewa tayi ta na ce wa "Anisa da Fatima ai kusan halin su d’aya, ga rawar kai da ya musu yawa, gwara da ka hukunta su, gobe ba za su sake ba" ta mik’e ta koma side d’in ta. 


Kallon mu yayi da wannanan murmushin na shi da ba ka cika gane me yake nufi ba sannan ya ce "zaku iya tafiya amma ku sani bayan sallar isha’i zan maku tambaya a note book d’in ku, idan ku ka kasa amsa wa, hmmm ya girgiza kai, ya ce ba sai na fa’da muku ba, ku ‘bace min daga nan"


Tashi muka yi muka nufi d’aki, inda na mik’e da k’yar na shiga band’aki na d’auro alwala na shimfid’a sallaya kana na kalli Anisa wacce ta kwanta akan gado sai lumshe ido take yi alamar gajiya da kuma bacci da yake son d’aukar ta,

"Anisa" na kira sunan ta.


D’agowa tayi ta kalle ni ba tare da ta amsa ba illah idon ta da yayi ja.


Cikin tausaya wa na ce ‘ki daure ki tashi kiyi sallah kin ga ma an kusa sallar magrib"


Wani irin kuka ta fashe dashi mai ban tausayi tana cewa

 "Fatima bazan iya tashi ba, k’afa ta ciwo take min, pls ki kira min yaya Khaleel ya nemo mai gyaran targad’e"


Duk da nima daure wa nake yi amma hakan bai hana ni yi dariya ba na ce "wane irin targad’e a na zaune k’alau, kawai tsabar up & down ne ya yi aiki a kan mu"


Da k’yar na samu ta tashi ta d’auro alwala ni kuma na ta da sallah, ban san nima k’afa ta na ciwo ba sai da nazo yin ruku’u da sujada nan na gane ban da wayau.


Bayan mun idar da sallah ne na d'akko ma na man zafi muka shafa a k’afar mu amma duk da haka ba mu daina jin ciwon k’afar ba.


Yaya Khaleel ne ya shigo yana mana dariya yana cewa "wasu yau sun sha hukunci, wannan ko a barrack ne ai sai haka" ya sake fashe wa da dariya.


Ganin yanayin da muke ciki yasa ya tsagaita da dariyar cikin tausaya wa ya ce "serious na tausaya muku amma ku ma kun san hali kuka k’i yin extra lesson bayan kun san yana gari, kuma ku ka dawo gida kuna gulmar su shi da yaya Aminu, pls ku dinga kiyaye abin da za a muku hukunci kun ji sisters"


Da ma bai san haushin shi nake ji ba, ya ce wai yaya Faruk ya k’yale mu saboda Anisa, ni na zama on my own kenan, ba mai tausaya min.


Hararar shi na dinga yi, in naga zamu had’a ido sai in wayance, ashe ya lura da abin da nake yi, don haka yayi murmushi ya ce


 "Fateemah kenan! na san fushi kike yi da ni saboda na ce a tausaya muku saboda Anisa, ko da ba na gurin ku ka yi deciding d’in dawo wa gida, nasan ke kika kawo shawarar"


Shiru na mai saboda ni a yanzu abin da na fi buk’ata shine in ci abinci kuma in gasa k’afa ta da nake jin kamar ba a jiki na take ba.


Anisa ce ta kalli yaya Khalil cikin galabaita tace "yaya Khalil pls kaje kace iya talatu ta kawo mana ruwan zafi a bowl da tsumma mu gasa k’afar mu ta tawo mana da abinci"


Tausayin ta ne ya kama shi saboda yasan Fatima tafi ta dauriya da kuma tsiwa don haka ya mik’e ya nufi kitchen da kanshi ya d’aura ruwan a electric kettle sannan ya juyo ruwan a cikin d’an bowl da tsumma a hannun shi ya nufi d’akin.

*MAKAUNIYAR SOYAYYA*πŸ’–πŸ’πŸ’•




Post a Comment

0 Comments