TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 15

*_Mamuhgee15_*

Butarda baban yabari bayan alwalarsa ta qarasa ahankali ta dauka har lokacin hawaye take zubarwa


Ruwa ta qarasa jikin durum ta Diba tazo tashige bayi har lokacin idon iya talatu na kanta tana Mata kallon qurulla zuciyarta fal farin ciki Dan kuwa ganin take tafi kowa matsuwa da nadiyar tasamu ciki ko zakin zai shiryu su samu yanci itada tattalin arzikinta.


Itadai alwalarta takeyi cikin tsananin damuwa da tsoron yanda zatayi rayuwa a daki daya dashi.


Tana gamawa ta nufi dakinsu itada zainab tashiga tana qoqarin tayarda sallah baban yashigo gidan Yana qwala Kiran sunanta.


Saurin tayarda sallar tayi cikeda tsoron karyazo ya daketa duk da duka   ba dabiarsa bace iyakacinsa cika baki Saidai ganin yanda yau yaketa fada yasa takejin tsoron karya daketan.



Ta Jima tana sallar kodata sallame qin fitowa tayi tana qoqarin gyara zama zainab tashigo dakin rataye da jaka ta ajiye tana kallonta tace"


Kije baba nakira yau fada yakeji Dan Nima yanzu yagama zubamin akan zuwa gidan anty nafisa.


Hawayentane ke qoqarin dawowa ta kalli bakin qofar tana sako hawayen kafin ta miqe jiki ba qwari ta fito tana share hawayenta.


Tun kafin ta iso gabansa yace"


Koma ki dauko jakar kayanki kixo ki fice gobe zansa asa muku hanjin gado da katifar Dana siya Miki ta aure.


Qoqarin durqusawa take gabansa alamar roqonsa ya daka Mata tsawa Yana cewa"


Maza wuce tun kafin na karya Miki qafafu Mara kunya,

Kinsan bakyason zama dakin nasa kika biye masa kuka gama nunamin iyakata dazu,


Dama nasan ni shikenan Banda sa'a tunda duniya babu Wanda yagama rainani sai mijin 'yata gashi yanzu kema rainanin zakiyi saura dabancin yarage yakoya Miki saiki hau gyarawa talatu zama kema Kinga zuwa gaba gidan zamu bar muku Dan kungama riqa a harkar ta'addancin,,,


Zaki miqe ki wuce ko saina mangare ki agurin.


Miqewa tayi jiki sanyaye ta juya ta nufi dakinsu,


Zainab da sai yanzu taji abinda ke faruwa tayi saurin jawota cikin dakin tareda 'dan mintsineta a gefen ciki tana 'yar dariya tace"


Iyye Nadiya Ashe yau tarewa za'ayi shine ko kifadamin nabada gudun mawar gyarawa Yaya Zaki amaryarsa.


Gudu hawayenta Suka qara tana qoqarin sunkuyar dakai zainab din tayi saurin tallafota tana cewa"


Ke meyene Kuma abin kuka anan?

Bari kiji wlh damace kika samu kiyi rayuwar dakikeso ta jin dadi 

Yanzufa kowa shakkarki zai riqaji amarya guda a gurin sarki Zaki....


Kallonta nadiyar tayi tareda harara tana 'dan turo baki zata juya ta dauko jakarta.


Sake riqota zainab tayi tana cewa"


Ke tsaya Mana kiji kokuwa duk matsuwar tarewarce bazaki tsaya kiji darasin riqe miji ba tunda iya talatu takasa baki Ni basaina bakiba..


Kinga Dan allah karkije kina masa wannan kwana da hijabin wlh shegen duka zai Miki ya qarasa kunnuwanki dakeji Dan kuwa lokacin JJ yace Sam Babu abinda Zaki ya tsana kamar dunkun dunkun mace..


Kallonta nadiyar tayi da sauri zuciyarta na harbawa..


Dariyar qeta zainab tayi ganin nadiyar tafara yarda da zancenta duk da qarya takeyi sai kawai tasake gyara tsayuwa tacigaba da cewa"


Yes Kuma Yaya Zaki ya tsani taurin Kai wannan ai kema kinsani basai na fada mikiba Dan kuwa kinfi kowa sanin ya sautin Marin Yaya Zaki yake...


Boye dariyarta tayi ganin tsoro qarara na bayyana tattareda nadiyar taci gaba da cewa"


Sai one last thing shine Yaya Zaki ya tsani qazanta duk da dai nasan ba laifi ke ba qazama bace Amma Dole Zaki ninka tsaftarki akan tada tunda kina gani wanka biyu ko uku Yaya Zaki keyi a yini Dan haka kina qazanta kinsan Babu Mai cetonki tunda kowa tsoronsa yakeyi har baba kina gani.,


Dan haka nidai Ina sonki 'yar uwata banason rasaki Dan allah ki kiyaye abinda nafada Miki wlh idan kika mutu rayuwarmu lalacewa zatayi...


Cikin sabon tsoro Nadiya ta fashe da wani sabon kukan tausayin kanta akan abubuwan da zainab tafada Mata wlh itama batason ta mutu yanxu.


A boye zainab tasaki dariyarta ganin ta Dora nadiyar sosai saita daga hannuwanta tana share Mata hawaye tace"


Daina kuka kinji nadiyata idan kin kiyaye Babu abinda zai faru Barima nabaki turare har biyu Wanda Zaki ringa sawa idan kikayi wanka hakan zai qara tabbatarda tsaftarki gurinsa.


Jakarta ta bude ta dauko spray din smart collection na Lacoste tabata da madarar turaren lamsa Mai Dan yawa kadan.


Karba tayi hannuwanta na rawa kafin ta jawo jakar kayanta tasaka 

Zainab din ta daukar Mata jakar Suka fito sum sum kamar munafuka tabi bayan zainab din har qofar dakinsa Suka shiga sbd sanin baya nan.


Wata muguwar harara dattiya yabi bayansu da ita har Suka shige yanajin kamar yace yafasa tadawo tunda ai ba lallaine kebewarsu so daya ace tasamu cikiba.


Ciki mamakinsa da 'dan takaici iya talatu data sallame sallah tace"


Todai karkace tadawo Naga kanata kallon qofar soron kamar kaga kudi agurin 

Kariga kace ta tafi to wlh idan kace tadawo shiyasa Sam bakada qima a idon zakin baida marainin wayo kamarka.


Tsoki yaja cikin quluwa yace"


Wai ke talatu kullum bakya iya zama baki gasamin baqar magana ba,

Yanzu 'dan kanwar tawa kike cewa Banda qima a idonsa saikace wasu 'yan bariki.


Au dama kanada qima a idonsa shiyasa yake sakar maka karensa ko yaransa suna neman zauta rayuwarka.


Eh naji koma meyamin Ina ruwanki inace kece kika qarasa zugani na Hana auren ruqayya da neyo hartaje garin dangin oduduwa tasamo Mana wannan din.


Zatai magana ya miqe ya fice Yana baza babbar rigarsa ransa duk jagule.



Sukuwa suna shiga dakin zainab da Bata taba shigowaba tahau kallon dakin tsaf dashi kamar baa cikin gidansuba,


Qatuwar katifa ce Mai tudu sosai adakin sai 'yar wardrobe qarama ta kayan sawarsa Dana JJ sai takalmansa a jere gefe sai wata cupboard dake cike jereda makamai su adda,wuqaqe da gariyo masu matuqar ha'dari da kaifi.


Tsakiyar dakin kuwa dama carpet ce ash shimfide.


Komai na dakin fes yake kamar dai JJ nanan.


Jikin wardrobe zainab ta ajiye jakar kayan nadiyar tana kallon dakin tanajin Ina itace zata dawo nan wlh dataji dadi gashi harda standing rechargable fan a dakin.


Bakin katifar taje ta zauna tana latsawa tace"


Wayyo Nadiya wlh karki Bari kiyi laifinda Yaya sarki zai koreki daga dakin nan.


Dauke Kai Nadiya tayi idanuwanta na sake cikowa da hawaye

Zainab tayi saurin tasowa tana cewa"


Karkima fara wannan hawayen sbd baba yagama Miki gata yarinya.


Yanzu dai muje muci abincin dare saikiyo wanka kidawo ki kwanta cikin wannan qatuwar lafiyayyar katifar wayyo allah inama nice gefe daya ga Yaya Zaki da wannan lafiyayyan jikin nasa daga gani zaiyi laushi......


Saurin matsawa Nadiya tayi daga gefenta tana girgiza Kai cikin tsananin kunya da tsoron zancen na zainab.


Itakuwa dariya tayi Kuma har cikin ranta take wannan zancen tasan wlh Yaya Zaki ba qaramin iya soyayya zaiyiba sbd wannan Jan ajin nasa da kwarjinsa.


Bude jakar sukayi suka cire kayan dau'da sukayi cikin gida dasu da niyar gobe tayi wankinsu.


Indomin da zainab tashigo da ita guda biyu super pack ita zainab din ta dafa sukaci sbd Babu wani abincin dare da akayi ko na ranama ba ayiba sauran biredin da zainab tarage da safe dama taci da ranar.


Bata wani ci indomin ba sbd gabaki daya a tsorace take ga wani irin bugawa da kirjinta keyi na yanda yau din zata kasance Mata duk da tasan ko kallon tsiya bazai bita dashiba bare na arziki.


Suna gamawa ta rafka sabon tagumi batada alamar tashi 

Zainab ta takurata ta hanyar Bata tsoro da zantukan qarya harta sata tayi wanka ta saka doguwar jallabiyarta ta bacci ta saka hijabinta taje har daki tayiwa iya talatu Saida safe a matuqar kunyace.


Wani Abu iya ta miqowa zainba tace"


Ungo Bata wannan kice tashanyefa yanzu agabanki.....


Cikin fushi dattiya daya kawo ya miqa hannu ya karbe tareda watsawa zainab mugun kallo yace"


Bar nan kafin na fasa Miki Kai.


Da sauri ta fito tana dariyarsa sbd ganin yanda fushi bayawa baban nasu kyau ko kadan.


Ita kadai takoma dakin tashiga kamar munafuka tana sunkuyar dakai duk da har lokacin baidawoba.


Qasa ta zauna bayan tayi sallar ishai da akayi tun suna cin indomie,


Shiru tayi tana qanqame jikinta dake tsananin rawa sbd fargaba da tsoron karyazo yamata dukan ganinta a dakinsa.


Ahankali lokaci yaja harta fara gyangyadi daga zaunen saitaji motsin ana rufe qofar gidan.


Wani mugun zufan tsoro da fargaba ne ya karyo mata ta sake qanqame jikinta tareda cusa Kai cikin qafafunta.


Yana waya da wani officer akan wasu yaransa da aka kama a wani gari yashigo da wata irin sallama can qasan maqoshinsa.


Tsakiyar dakin ya tsaya tareda yimata kallo daya ya dauke Kai sbd shaf ya manta ma da zancenta.

#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*



 

Post a Comment

0 Comments