TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 20

 💫 SANYI DA ZAFI 💫

✍🏻M SHAKUR


EPISODE 2️⃣0️⃣


Mama na duke a tsakiyan anguwa tana kuka sosai ana kallonta an taru Hajiya Jummai tazo inda take tsugunnawa tayi takai bakinta saitin kunnen Mama tace “mission accomplished! Now watch how I will ruin rayuwar yarki this is just the 1st step, watch and see how zanyi feeding yarki to those hungry police officers, I will make sure sunyi kacha kacha da duk wani abu daya maidata diya mace, barima kiji Amarya na aikamusu yau akwai biki” tawani kwashe da dariya, juyo da kanta Mama tayi ta kalleta irin kallon nan na bakomi akwai Allah sannan tace “nabaki raina ki dauka Jummai, yau kidauki wuka ki sakamin aciki na mutu na yarda, kome kikeso kiyi dani kiyi amman spare yarinya na, she’s a small girl, meta miki? Mijinki dama tun tana ciki yace ba tasa bace haryau ko fuskanta baitaba ganiba to meta miki? She’s not a threat, she’s a small child kulleta a police station will ruin her life, Hajiya Jummai banda kowa sai ita, kiyafema Rashida ni kisa a kulleni” murmushi tayi tace “kinga I hate you with every blood na jikina saisa I want to end you using abinda kikafi komi so, wlh wlh ko kudina zasu kare yau saina tabbatar an yaga yarki a cell, wlh sainasa sun maidata nama, saina tabbatar sun halakar da rayuwanta tass, maybe then na hakura nasa afito da ita kokuma na aikata prison she need to be taught a lesson, ke I will cook her up bazata fito daga cell anytime soon ba, this is for auren Mijina dakikayi!” Tana maganan ta tashi tawuce wajen mota ahankali Mama tajuyo da rinannun idanunta ta kalleta ga mamakin Mama saitaga yan matan sun taso fess da kafansu sun fito sun shiga mota direba sun yatada motan sun tafi, Ahankali Mama ta tashi wani kalan bubbugawa zuciyanta keyi dabai taba mata arayuwanta ba, yan layin sai kallonta suke mata an lalleko daga gida tanaji ana kananun magana ana dama maraji makomarsa kenan anzo baku abinci mu makota mun shaida but yarki tazo tana dukan mutanen arziki ai gashinan tahadu da daidai da ita, gida Mama ta shiga ta tattaro duka kudin dasuke dashi tasan belin mutum da kudi akeyi sunada 80k agida a account din Rashida kuma akwai 100k da aka mata salary na hotel just jiya 50k ake biyanta but sallan nan sai aka basu 100k, sakawa tayi a lalita tasa takalmi tafito ta kulle gidan ta shiga tafiya bama tasan wani police station aka kaita ba, tafiya take a anguwa wasu nacemata Allah kiyaye gaba wasu na Binta da kallo Adamu me chemist ne yafito hangota dayayi dan shi yana mutunci dasu yace “Mama Allah kiyaye gaba ina zaki yanzu”? Bama ta iya magana sai hawaye bakin hijabinta tasa tace “bansani ba duk police station dana gani zan shiga” dasauri yace “ina ganin kije head quarter dan naga babban police car suka zo dashi sabida local street police post ba’a ijiye musu manyan motoci haka, Allah kiyaye gaba”  gyadamai kai tayi ta wuce ta tare keke ta shiga 500 aka kaita headquarters.

Sauka tayi tashiga ciki ta tafi chan gaban kanta yan sanda dake wajen sukace “lafiya Hajiya” baki Mama tabude zatai magana sai kuka matar tace “Hajiya dan Allah kifita ki gama kukan saiki dawo” dasauri dayan dan sandan yace “mehaka Grace? Mama lafiya calm down meya faru fadamana”? Da kyar ta tsagaita kukan tace “y’ata wasu yan sanda suka kama kusan minti talatin kenan bansan inda aka kaitaba yan anguwan mu since nazo nan headquarter” mutumin yace “ya sunan diyar taki”? Ahankali tace “Rashida Almustapha” log book dake gabansu yaduba yaga sunanta kafin yayi magana Grace tace “banan aka kawota ba kije wani police station din” kallon Matan Mama tayi saikuma ta kalli wanda ke attending to her ahankali yace “Mama je waje ki zauna ina zuwa” fita waje Mama tayi tasami waje ta zauna, kirjinta bugawa yake like never before ga azumi abakinta wlh kusan 2hrs tai spending awajen dan har 5 tayi sannan yafito yazo wajenta yace “zo gefe Mama” Dasauri Mama tabishi ahankali yace “Mama bansanki ba amman kin bani tausayi wlh tuntuni sai bin office daban daban nake ama barki kiga diyarki sunki, wai yaran data daka suna ICU, sannan she attacked officer mu wata and abuse her” cikeda tashin hankali Mama tace “wlh wlh karyane sherine agabana yaran suna shiga mota da kafansu basa ICU, kuma wlh Rashida bata taba police dinba” ahankali yace “to yanzu dai  bani dubu goma zan taimakeki da kyau koda yarki zata kwana zansa ido akanta kar acutar da ita” fashewa da kuka Mama tayi tana tura hannu alalita ta kirgo 10k tabashi ya karba yace “bari kiji Mama the truth is powerful mutane sukasa aka kulle miki yarinya dan haka yanzu dai idan kinada wani babba haka kije kitaho dashi ko za’a miki alfarma abaki belinta inba hakaba wlh bazama kisan yarki na nan ba ninedai nafada miki” yanda Mama ke kuka sai yataba zuciyanka tace “wanake dashi? Banda kowa sai Allah ni” dan sandan yace “nidai nayi miki iya nawa kije ko waye kisamo, suna ganin kalan kudi ajikinsa zasu badata, bari nakoma ciki kada anemeni” wucewa yayi yakoma ciki yabar Mama wajen tsaye shiru Mama tayi saikuma ta daga idanunta takalli sama irin kallon Ya Allah kana ganin komeke faruwa sannan tasa bakin hijabinta tashiga tafiya tawuce gate kafanta yayi butu butu da hijabinta ma sabida zaman kasa datayi sai tunani take ina zata shagon Mama miwa tane tunda tanada kudi but tace baruwanta da police station bata zuwa, Rashida tafada mata tace taji ance Riyad na Umara saisa batai tunaninsa ba.


Bari taje ta gwada yima manager magana kozata taimaketa gashi Baba Liman yaje kauyensu shima duba gona, adaidaita tasake shiga ta tafi hotel din hanyar shiga taje yauma wasu security daban ne dana ranan suna ganinta sukace “ina zaki”? Arude Mama tace “manager zan gani” wani kallo suka mata daga sama har kasa sannan sukace jira anan daya yashiga ciki yama manager magana tafito daga office nata hango Mama tayi daga glass door tace “I don’t know her, please send her away yau banda lokacin all this beggars I’m very busy” takoma office security yafita yaje inda Mama take tsaye yace “batanan” tsayawa Mama tayi tana kallonshi yanda taji kaman jiri na neman dibanta batasan sanda ta duka ba saitahau kiran sunan Allah. “Allahumma ajirni fi musibati……Innalillahi wa innailaihi raji’un, Ya Allah kadubi yarinyana dake cikin cell kar awani abu yasameta please karsu cimma burinsu” tashi tayi tana taba bango kawai kaman kanta ya kwance takeji cus batada hope kuma yanzu sai magana take ita kadai. “Rashida na is scared, yarinyana bata taba zuwa police station bama, yanzu tanachan locked up a cell an ciremata slippers, an karbe komi nata, hala ana azabtar da itama, idan suka batama mata rayuwa fa, wat if they rape her? My poor baby must be so scared yanzu, yarinyana batada kowa aduniya sai ni, wat are they doing to my child right now……….” Diiiiiiiiiiiiii! Taji karan ana daddanna mata car horn dayasa kawai ta birkice hannunuwanta tadaura saman kunne ta kulle idanunta kawai tahau juwajuwa akan titi go slow kawai yahadu bama tasan meke faruwa ba,  “Mamaa!” Taji an kira sunanta da karfi dasauri tabude idanunta dasukai jazur, Riyad tagani tsaye agabanta yana sanye da farin shadda datasha aiki kanshi da kula ganinshi kawai saita fashe da kuka sosai ahankali yasa hannunshi yasauke hannayenta daga saman kunne ganin she’s not herself yakama hannuwanta duka biyun sukabar tsakiyan titi zuwa motanshi yabude baya yasata shima yashiga bayan wani bodyguard dake tukanshi yaja motan suka gangara gefen hanya yayi parking, Riyad dake kallonta yace “Mama menene? Why are you in the middle of road”? Bakinta rawa yake ta birkice kawai tace “Riyad…….Riyad…….Riyad” hannunta yakama ahankali yace “get me water” fita direban yayi anatse Riyad yace “Mama calm down I’m here now, calm down everything will be fine, calm down Mama kinji” bakinta is still calling name nashi, ahankali yace kice “Innalillahi Wa Innailaihi Raji’un” ahankali Mama tace “Innalillahi wa innailaihi raji’un” dan natsuwa tasamu kadan daidai lokacin an kawo ruwan budewa yayi yabata tasha kadan sannan yace “wat happen Mama”? Fashewa da kuka tayi tace “tasa an kamamin yarinya an kulle a police station” anatse yace “wace”? “Kishiyata wacce mukai zaman aure tare kafin mijinmu ya koreni”? “Wat happened Mama”? Labari Mama tabashi tundaga time datazo gidan da time da Rashida ta shigo, da all abinda yafaru da duka abinda tagayama Mama na zatai feeding Rashida to yan sanda” jiyayi ranshi yayi tsananin baci, “drive” yafadi ahankali yama Munir text dan daga gidansu zuwa head quarter is even closer than daga nan hotel zuwa wajen.


Wajajen magrib sukakai police headquarter ya kalli Mama yace “Mama ki zauna anan zan fito da ita kinji” gyadamai kai Mama tayi ya kalli security yace “make sure she stays in the car she’s not feeling well” “yes sir” ya amsa yana fita yaga Munir yafito daga tashi motar ga sauran bodyguard nashi yayi gaba kawai Munir da guards nashi na binshi abaya, all eyes yadawo on them ko kallon yan sandan wajen baiyiba yawuce sama direct zuwa office  na inspector cus yasanshi sosai yana kawo gaisuwa fada dudda bai sanshi babu rawani ba, kai tsaye yabude kofan ba knocking babu komi Inspector na zaune yana dube duba, da zafi sosai an anger kan muryan Riyad yace “I will sue you and I will sue the entire police headquarters for rashin adalci for tauye hakkin talaka, for rashin yin investigation, I will make sure anyi sacking all of you anyi replacing naku with better and eloquent officers dasuka shirya yin aikinsu yanda yakamata” from yanda yake magana kadai yasa gaban Inspector yashiga faduwa yama kasa magana, Munir yace “you must be confuse kana magana da Mai Martaba SARKI RIYAD! Sarki mai adalci, sarkin talakawa” wani kalan tashi inspector yace “an gaida Mai Martaba Allah huci zuciya ka, tub……” hannu Riyad yadagamai yace “release Miss Rashida Almustapha, and nabaka 24hrs kuyi realeasing evidence cewa yaran data daka suna ICU with Doctors report and everything, and again inaso kuyi proving cewa she’s really a killer, banda haka I want to know wat right that officer takedashi to slap and hit Miss Rashida, and again wanda aka bishi har gida shine akaje neman tsokana, prove all this ba set up bane inba hakaba” Munir yace “zaku hadu da bacin ran Mai Martaba” baki Inspector yabude zaiyi magana Riyad yadagamai hannu for the second time yadakamai tsawa sabida yanda ranshi yake abace yace “release her now!!!!” Shi kanshi Munir saida ya kalli Riyad rabon dayaga dan uwanshi yayi fushi haka harya manta, da wuya Riyad yayi fushi, jikinshi har rawa Inspector yake yafita dasauri shi baimasan case din ba duk suka bishi yawuce kasa Riyad na biyedashi yadauki key na kofan da ake budewa a shiga bangaren cell nasu yabude kofan da sauri ya shiga saikuma ya juyo yace “Allah taimaki ranka shi dade ban santa ba ita yarinyar” wuceshi Riyad yayi kawai yashiga ciki mutumin ya bishi abaya cell cell ne daban daban, na mata daban na maza daban but duka ajere suke, ga mutane kukkule amman baiga Rashida ba in any of cell na mata dasuka wuce ba,  zagawa dashi Inspector yayi zuwa cell masu kama dana kaji ana kiran dakunan NO SS CELL wato no sitting no standing cell, wanda shi na punishment ne bazaka iya tsayuwa ba bazaka iya zama ba kana duke kawai idan anaso a azabtar dakai ake kaika wajen, hangota Riyad yayi ita kadai an rufeta a cell dayakenan kaman cell din dan buri alalo alalo gwanin ban tausayi she looks very very miserable and terrible ko kadan bata kallo inda suke ba danta dauka matarce tadawo, ahankali Inspector da gabanshi ke faduwa ganin ita kadai ce abarayin NO SS yace “itace naga kana kallonta”? Juyo da kanta Rasheeda tayi jin datayi anyi magana tunda ta shigo wajen sai yanzu taga haske hasken Riyad dake tsaye yana kallonta idanunshi sun chanza launi kallo yake mata dabazaka iya tantance na menene ba, ahankali yake kallonta even though she’s not crying but kasan she’s very very scared, she’s terrified, she’s lonely, she’s afraid, dauke kanta tayi daga kallonshi da sauri tashiga wasa da fingers nata, bude kofan Inspector yayi yace “fito” kokarin motsi tayi da kafa amman takasa sabida yanda kafafunta suka sankare suka rike sai kawai Riyad yaji zuciyanshi ta tsinke awani irin hankali yafara tafiya dudda bata kallonshi but every step nashi tana jinshi har a bangon zuciyanta, ahankali azo gaban cell din ya tsaya chak still taki dago da kanta, yakai wajen 10secs yana kallonta kafin awani irin hankali yaciro hannunshi daga aljihu yamika mata cikin wani irin murya mai masifan taushi yace “Rasheedah!” Har kasan zuciyanta taji yanda yakirata hakan yasa tadago kanta takalleshi sannan takalli hannunshi dayake mika mata batare data karbi hannunba, ahankali yace “come Mama is waiting” dasauri ta kalli fuskanshi kafin awani irin hankali takai hannunta tadaura gently kaman mai tsoro cikin nashi, atare dukansu sukaji shock amman yadaure yakamata sannan ya fizgota tashi daya tafado kirjinshi making deep sound mara kara sosai dazai nuna how hurt she’s, kafafun na mata ciwo sosai amman sabida dauriya da taurin rai taki nunawa but takasa motsi tana kirjinshi, dan sauke kai Inspector yayi aranshi yace “budurwan mai martaba muka kulle dama? Suwaye keson sani a bala’i” takai one minute a kirjinshi batare daya taba bayanta ba banda hannunta daya rike but ita takasa motsa kafan tafita daga kirjinshi, in a very caring tone dabama tasan yanada shi ba yace “can you walk now”? Duk yanda taso karta kalleshi kasawa tayi tana kirjinshi tadaga fuskanta takalleshi hada idanu sukayi cikeda tsananin kulawa yace “can you walk yanzu?” Very soft itama ta gyadamai kai tana yunkurin fita daga kirjinshi, saitai baya zata fadi dasauri yakai hannunshi daya yakama waist nata sai kawai adake yakama hannunta daya yakai ta bayan kanshi ya ijiye yayi supporting nata dakyau kafin yace “let’s go” she’s scared internally, she’s shaking bamata da karfin wani abu so she just followed him tana dan dingishi suka fito ahaka.


Hannu yasa yabude kofa mutanen data gani awajan da yawa gasu police gawasu kaman bodyguard ga Munir datake gani a hotel nasu ga yan sanda maza biyu na dazu bataga macen ba yasa tadan yunkura cikeda karfin hali zata fita daga jikinshi kaman daga sama taji saukan hannunshi akan waist nata yamaidata side nashi da kyau dawani irin sauri tadan juyo da kanta ta kalleshi but fuskanshi is looking straight bayako kallonta yacigaba da tafiya da ita hakan yasa ahankali ta maida kanta kasa daidai sunzo kofan fita saiga yar sandan dazu tana shigowa itama suka hada ido wani abu Rashida taji yazo mata wuya ya tsaya duk kalan ciwon da kafanta ke mata amman saida taji tasami karfin daga kafan kawai takai ta kwasheta within a blink of an eye jikake tippptipp! Officer tai wani mummunan faduwa danko ita bata lura da kafan da Rashida tasamata ba dan fuskan Rashidan take kallo dana Riyad datagani tareda ita, da all the people dake wajen,  yan sandan sukai kanta ganin kalan faduwan datayi ana “lafiya kika fadi haka sannu me kike kallo haka” dan babu wanda ya lura da abinda Rashida tayi dagowa officer tayi hancinta na jini ta kallo kofan hada ido tayi da Rashida dake mata kallon munyi settling score dake, tsayawa shima Riyad yayi yana kallon Rashidan cus he saw wat she did saikuma kawai yacigaba da tafiya da ita suka fice har wajen motan shi su Munir suka biyosu baya yabude baya Mama idanunta harsun kumbura na zaune taganshi da Rashida dataga har yar rama tayi, sai kawai Mama tafashe da kuka jikin Rashida yayi mugun sanyi da taimakonshi ta shiga bayan motan sai kawai ta rungume Mama dan jim yayi yana kallonsu kafin ya maida kofan bayan yarufe yajuyo yadan taka zuwa wajensu Munir dake kallonshi kallon what is going on, anatse yace “I will see you at home bari na kaisu gida” bai jira amsan Munir ba yajuya yawuce saiya shiga gaba direban yatada motan yaja har lokacin Mama kuka take wlh takasa magana ma, hakuri take ta bama Mama amman yana shigowa tayi shiru kawai dai ta rungumeta agaban wani pharmacy yasa aka tsaya yafita yashiga yakai kusan 10min aciki yafito rikeda leda yadawo ciki ya zauna aka tada motan har zuwa anguwan su parking yayi yabude gaban motan yafito yabude bangaren Mama ahankali Rashida tasaketa goge fuskanta tayi ta sauko sannan ta mikama Rashidan hannu tace “taho muje” cike da karfin hali ganin yana wajen yasa tace “ni zan iya fita dakaina” tsayawa Mama tayi tana kallonta irin kallon wani irin taurin kai da karfin hali Rashida kedashi ne, shima Riyad folding hannunshi yayi a kirji ya tsaya kawai suna kallonta jan jiki tayi har tazo bakin kofan ahankali ta daga kafa daya tafito hakama dayan sannan ta yunkura ta tashi dudda she’s not showing the pain a fuskanta but wlh kasan da kyar take komi takawa tashigayi ahankali sai kawai tawuce tai zaure da dafa bango ta shige cikin gida, Mama tabiyota abaya tana shiga rabin buhun shinkafar taci karo dashi a tsakar gidan nasu jitayi zuciyanta kawai yarikice ranta yabaci tama manta tanada ciwo kawai tai wajen shinkafan azuciye ta daga shinkafan zata mike kafanta yayi wani irin kara da duk dauriyanta saida tai ihu daidai lokacin Riyad ya shigo gidan azuciye yayi wajen yasa hannu ya fizge buhun shinkafan yayi ihu yace “what is your problem?” Kallonshi tayi ido cikin ido tace “mezamuyi da shinkafarsu? Zubarwa zany…….” “Quiet!” Riyad ya daka mata tsawa da saida taji jikinta yayi rawa, cikin tsananin fushi ya nuna Mama datake rabe a bangon zaure kawai ta tsaya chak tana kallon yarinyar tata gwanin ban tausayi, irin kallon yaya zanyi da wannan yarinyar ya Allah, yace “can you give your Mom just a minute of peace?” Kallon Mama tayi saikuma ta kalleshi zata bude baki authoritatively Riyad yace “I said quiet!” Cikin kwayar idanunshi ta kalla the anger datake gani da fushi kawai saitaji takasa magana wani bai taba shutting nata up in her life ba sai yau, cikeda tsananin bacin rai yace “kina tunanin komi arayuwan nan you settle it da fada da duka you think is by fighting?” Yasake shiru saikuma ya lumshe idanu tareda fuzar da iska yasake kallonta yace “every action have consequences do you for once sit down kiyi tunanin waye ke suffering consequences na action naki?” Yadan mata ihu kadan still kallonshi take da manyan idanun nan nata, saiya sake nuna Mama dake tsaye looking at them tana goge hawaye da bayan hijabi yace “do you have slight idea of abinda Mamanki went through today? Did you even know an ina naganta?” Yasakeyin shiru saikuma a sanyaye yet da tsaurin harshe yace “do you even love your mother?” Wani kallo datamai har saida idanunta sukahau sparking sabida anger kaman zata rufeshi da duka, cikin fushi tace “kai waye dazaka tambayeni ko inason mahaifiyata, waye kai”? Cikin tsatsauran murya Mama tace “tamaka rashin kunya ka yanka mata mari Riyad!”.




Post a Comment

0 Comments