TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 7

#MAMUH*_Buri daya_*

*_Mamuhgee7_*

Ana tashi taron nan maroqa Suka hau aikinsu aka dinga musu barin kudi suna godia 

Kawu Dattiya ji yayi yau ranar datafi kowace Rana sa'a ce Dan kuwa tuni kudinsa Suka Kai dubu takwas ya tura aljihun wandonsa tareda qara gyara zama yayi Yana cewa"


To Ashe musakan nan sunfimu samun kudi aikuwa yau Nima cikinku zan lafe tunda qiris yarage tantirin can bai maidani musakinba.


Sake lanqwashe qafa yayi kamar musakin gaske yayi kalar tausayi.


Saida duk baqi Suka watse kafin ale dikko yafito tareda Zaki sake da Amaan 'dansa.


Kallon tarin mabaratan yayi ransa na baci shi arayuwarsa ya tsani mabaratan nan da son banza yayi musu yawa wato su sai mutum ya Nemo zuso karban banxa.


Yanayin yanda ya dauke Kai daga kallonsu yasa ran Zaki ya baci sbd duk lalacewar kawunsa Babu Wanda ya isa ya wulaqanta masashi,

Shi shikadai ne yakeda ikon masa Abu bawai Kuma Dan Baya sonsaba saidan yanasone yaji wuya ya canxa wata sana'ar.


Kallonsu yayi yakalli security yace"


A sallamesu abar musakai su kadai za'ayiwa sadaka.


Idi najin haka yayi saurin nade qafarsa shima Dan kuwa baza'ai babushiba,


Kallon baqin ciki dattiya yayi masa Yana hadiye yawun fargaba sbd yasan Dole akwai balainda yake Shirin qulla musu shine shikuma tsohon banxan nan idi ya nade baisan balain dake cikeda kallondq zaki ke musuba.


Aikuwa duk aka watse aka barsu su tara musakai nan dikko ya kalli Zaki yace"


Lion yaya hakane?


Batareda yakalli dikkon ba yace"


Ale sadaka zakayi musu ta musamman sbd banaso su manta wannan ranar.


Ba musu ale dikko yafito da maqudan kudi bunch guda na dubu 'daya 'daya 

Atake Suka hau zare idanuwa kamar sunga aljanna idi har wani qaiqayi hannuwansa ke masa.


Kallon JJ Zaki yayi atake ya dauko wani buhu Dan qarami yafara walwalewa.


Zaki na kallonsu ya karbi rafar kudin ya miqawa nano yace"


Ka Raba musu ita Amma bayan munga waye musakin gaske.


JJ kuwa Yana gama warware buhun ya cillo musu abunda ke ciki.,


Wani sharbeben baqin dogon maciji ne aciki yafado tsakiyarsu..,


Wani irin juyin waina dattiya yayi tareda miqewa yayi gabas aguje rigarsa na cika da isa yana dingisa qafarsa datai tsami sbd lanqwasawa,


Idi kuwa duk abinda yasamu yayi watsi dashi yanka a guje hularsa datai masa yawa tana faduwa,


Sauranma atake Suka kwasa aguje suna tsinewa Zaki.


Mutum biyune musakan gaske Wainda aka Bari Basu iya gudu su dinma qoqarin guduwar sukeyi da Jan gindi.


Kallonsu Zaki yayi ya girgiza Kai kafin ya kalli Nanu dake dariya yace raba musu rabonsu ne sukadai.


JJ kuwa mataccen macijin ya dauka Wanda bamai cewa matacce ne sbd bada jimawaba yaransa Suka kashesa agurin taron.


Mota Suka nufa dikko na 'yar dariyar jin dadin abinda Zaki yayi musu.


Bude masa mota drivern sa yayi yashiga Suka wuce Yana jaddadawa Zaki gobe qarfe goma na safe zasuje wani guri.


Bayan tafiyarsa shima shida yaransa Suka shiga motocinsu Suka bar gurin.



Dattiya yariga idi isowa gida duk da qafarsa tuni tadau wani irin zogi musamman yanda ta kumbura tu da yashigo gida ya zauna qofar dakinsa kan shimfidar tabarma yakalli talatu dataqi tambayarsa ya akayi yadawo yau ko sauran takalmin Babu a qafarsa.


Numfashin 6acin Rai yasauke cikeda baqin ciki yace"


Wlh yau nayi baqin ciki da Dana sanin Rashin tambayar ruqayya waye uban wannan nan yaron harta rasu tabarmin ajalina.,


Sai alokacin talatu takallesa tana zubawa tsiminta ruwan magananin 'dan kanoma sbd yayi Dan bauri anfi cewa yaji magani tace"


Idan dai qashi nada tauri to kare baida aikin komai,

Bazaka kama kankaba Zaki bazai daina wahalarda rayuwarkaba.


Qwafa yayi yace"


Kinkuwa San yau Wai Ni Zaki zai jefowa baqin kumurcin maciji dabanda qafafu yau dakin shiga taqaba.,

Wlh cikin tsananin rashin Imani yasa JJ ya jefo manashi 

Ni yanxuma idi nakeji idan ba akansa iftila'in yafada ba.


Sallamar idi ce ta katsesa fuskarnan murtuk Babu alamar rahama sbd shi komaima nasa ya zubar acan har 'yan dubunsa bakwai da 'dari hudu duk ya watsar wannan wace irin masifa ce,


Cikin tsananin zafin Rai da baqin ciki yace"


Allah ya tsinewa ubanda yayiwa ruqayya cikin balai.


Amin dattiya da iya talatu Suka fada atare sbd tsananin matsen dasuke da zakin.


Dattiya dake jin tsananin zugin qafarsa data fara kumburi yace"


Allah yaji qanki ruqayya ya saka Miki da duk Wanda yayi Miki wannan ta'asar Dan kuwa yaci amanar marainiya baiwar Allah ta tafi ta huta da ganin wannan balai.......


Shigowar JJ ce tasa dukkaninsu yin tsit suna matse fuska da bacin rai sbd sunsan Zaki na kusa tunda sukaga JJ.


Nadiya dake zaune gefen talatu tana mata aiki tana dago Kai Yana shigowa 

Kyakkyawar fuskarnan tasa a tamke Saidai wani sirrin kwarjininsa dake Hana ayi masa kallon qwaf yasa tayi qasa da kanta kafin yaqarasa sauke takaicinsu baba akanta.


Dakinsa yashiga daidai shigowar zainab da hijabin data aro gurin anty samira amaryar baba idi sbd sanin Yaya Zaki nanan tunda taga bataliyarsa a qofar gidan.


Tashi baba idin yayi Yana sake daure fuska Yana Harare Harare ya fice Yana cewa"


Allah dai baya bacci tunda gumi akace dai mutum ya hada gurin neman halas Kuma mun hada Amma gashinan.


Kawu Dattiya najinsa yaqiyin magana sbd kar ajisu Dan shidai yagaji da wannan masifar daga yanxu zai ringa iya yinsa gurin raba hanyarsa da Zaki Dan yagama sani yanxu Kam tsaf Zaki zai iya ganin bayansa,

Shi wlh dama yasani yabari neyo ya auri ruqayya dabataje ta samo musu wannan iftila'in ba Dan kuwa gwara ta'addancin neyo so ba adadi akan na Zaki tunda gashinan sbd harta haihu ta rasu Bata daina qaunar neyoba tunda Zaki ma aliyu haidar neyo tasaka masa gashinan sunan neyon yabisa.


Tashi Nadiya tayi sum sum ta dauki bokiti ta Debi ruwa da tsintsiya ta nufi bayi tafara wankewa sanin duk yafita yashawo Rana idan yadawo Yana wanka.


Tana gama wankewa tafito kenan shikuma zai shiga baisan da itaba 

Itama batasan dashiba sukai karo tayi saurin yin baya zata fadi

Da hanu daya yariqo hannunta a tsorace ta dago Saidai takasa kallon fuskarsa kafin tasake dagowa ya jehota waje tareda rufo bayin.


Dattiya da tun dazu ya miqe zuciyarsa na tsalle ganin Zaki zai shiga bayi 'yarsa na ciki Yana ganin anjehota waje yasake ajiyar zuciya sbd Rashin madafa sai kawai yahau Nadia da fadan Rashin dalili,


A zuciyarsa kuwa sauqi yakeji da duk iskancin Zaki baya ko kallon mata bare nemansu da lalata sbd 'yar Nadiarsa yake gudun a lalata tunda ita zainab uwarta ta daure mata gindi tana yawonta bai saniba ko tagama lalacewar,


Ita kuwa Nadia ko maqure masa ita akayi za'ayi lalata da ita batada muryar idon neman ceto,


Kai shidaima gwara yayi mata aure ya huta ta huta itama Dan haka zai bama 'dan gidan mal zailani dayake sana'ar gyaran su fanka dama tunda yace Yana sonta.


NADIA kyakkyawar black beauty ce Saidai ba baqa bace sosai Sam batada wani jiki sosai hakama tsawonta daidai misali Saidai kusan dukkaninta daka ganta kasan mahaifiyarta ta 'dauko Saidai 'dan duhun fatar na mahaifintane ta dauko.


Sanyin haline da ita shiyasa ayukanta Suka zama suma a sanyaye takeyinsu.


Juyi tayi kan shimfidarta tareda bude ido ahankali sbd kamar jin alamar wani acikin dakin....


Faduwa gabanta yayi da qarfi sbd tunanin hakan datayi gashi tsakiyar dare ne komai Bata gani sbd duhu gashi ita ko fitila batada.


Miqewa tayi zaune tafara laleben kofin silver datake kwana dashi kullum sbd amfani dashi dan irin haka.


Tana cikin lalaben taji ta lalabo qafar mutum wata muguwar zabura tayi jikinta na tsananin rawa tayi bayi tanason ihu takasa sai hawaye tafara qoqarin tashi zata gudu taji kowanene ya damqota tareda matseta a bango Yana dariya qasa qasa.


Rawa jikinta keyi sosai tana qoqarin kwace kanta hawaye tuni Suka fara jiqa rigarta musamman ma wani irin tsamin giya dake tashi ajikinsa.



 

Post a Comment

0 Comments