TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 46

 EPISODE 46

Bacci yadade bai mata dadi kaman na jiyaba ahankali tabude idanunta ta kalli saman dakin dudda wuta akashe tana iya ganin komi shiru tayi shikenan Mama tarasu? ljiyan zuciya tasauke mai huci ta tashi zaune ahankali tadaura hannunta kan kumatu she can't even explain yanda takeji in words idan ta tuna da Mama tarasu all this while she has not been praying for Maman ta kuka kawai take tashi tayi ahankali gabaki dayan jikinta smells like Riyad kaman har yanzu tana jikinshi gently ta tashi tawuce bayi ta shiga maida kofan tayi tarufe saikuma ta tsugunna zuciyanta namata ciwo Mutuwan Mamanta is hurting her is even killing her slowly takasa yarda Mama tarasu shikenan bazata kara ganin Mama har abada ba? Taya zata cigaba da rayuwa batare data kara ganin Mamanta ba brush tadauka tasa toothpaste tahau wanke bakin tafashe da kuka sosai taba brush tana kuka mutuwan Mama is just too much for her to handle da kyar tagama tayi abinda zatayi tayo alwala tafito hijabin dake kan dadduman ta dauka tasaka tai sallan asuba Qur'ani daya gani a drawer ta mike hannu tadauka tana kallo rabon datai karatun Al Qur'ani harta manta kullum saidai taita jin waka batada yawan bautan Allah wani zubin harda how busy her life is da ayyuka da sauransu but that is not an excuse maybe sabida ma hakane yasa Allah ya karbi ran Mama she promised dagayau saita karanta Al Qur'ani everyday of her life.Bayan hannu tasa ta goge hawayen sannan tabude Khafi tafara karantawa Ya ilahi! Ashe muryanta dakeda dadin waka was trash tana rera kirala kaman balarabiya and yawanoi kuka take tana karatun Ammi tadade tsaye jikin kofan tana juyota she's happy yanda ta mike dakanta yau hartai salla tana karatu May Allah comfort her and ease her pain Ammi tafadi sannan tawuce tasauka kasa.

Wuraren 8 ya shirya yasauko kasa hannu yasa yadanna wani boturi cikin sec wani bafade yashigo falon yawani zube gaban Riyad din dake zaune yadaura kafa daya kan daya yace "na gaida Sarkina Mai darajoji daban daban, kwana lafiya Sarki na...." "Sarkin Gida!" Riyad yakirashi kai tsaye hakan yasa yatashi yana zaune akasa agabanshi yace "Allah taimaki me Martaba" agogo Riyad yadauka yashiga daurawa a writs nashi yana kallon wayanshi dake vibrating akan kujera Mom ne ke kiranshi yace "bayan nahau kujeran mulki akwai abubuwa da dama dana nuna banaso" da sauri Sarkin Gida yace "kwarai! Irinsu shiryaka, masu aiki awajenka, Mai soro, shamaka baya muna maka tattaki duk inda zaka da

sauransu"

anatse Riyad yace "yanzu duk inaso kufara yi, ka

shiryamin fadawa wayanda ka aminta dasu" dasauri Sarkin gida yace "angama ranka shi dade" he wants to punish Haleema hakan yasa ayangance yace "Sarkin Gida" dasauri yace "ubangidana Babana Sarkina kuma gani nan me kake bukata?" Karasa saka agogon shi yayi tasss sannan yadago yakalleshi yace "ka dakatar da duka bayin dake aiki a bangaren Sarauniya Haleema na kwana bakwai cikinsu harda jakadiyanta, sannan a tsare bangaren nata ban yarda kowa yakai mata ziyara ba ko ita tafita ba saida babban dalili wanda sai an sanar dani" dasauri Sarkin Gida yace

"angama ranka shi dade" da hannu yamai alamu yatafi sannan yadaura kafa daya kan daya still yana kallon call din

Mom bai dagaba he's just feeling lack of attachment towards her after abinda tamai jiya, yana zaaune awajen har lokacin zuwa fada wasu fadawa guda biyu suka shigo aka shiryashi tsaf sai walkiya yake yafito aka maramai baya zuwa fada bayan yama Haleema sako tamai breakfast.

"Mom menamai haka zaimin wannan hukuncin? Ba'a taba yin matan sarki da sarki ya hukuntata hakaba sai akaina kaman ina gidan yari kuma wai ya aiko nahadamai breakfast yagama da fada zaizo yaci taya zan fara aikin banda wacce zata taimakamin" ran Mom yariga yagama baci da kyar tai controlling temper nata tace "kije kimai abinda zaki iyayi, na ganshi zan mai magana za'a dawo miki da ma'aikatan ki" Mom ta katse wayan ta ta tashi kitchen tashiga saita tsaya tana kallon kitchen din bawai bata iya girki bane but she just realized cewa tadade tanacin banxa she can count how many times tama mijinta girki bama tacika yi ba, kotayi ma itada yan aikinta ne, ganin yanda zata fara aikin yanzu take kaman wani uwan tashin hankali ruwan shayi tasa a wuta saitai frying egg tasa a kula da bread tai arranging a dinning around 11 taji adawa na sanarda ya iso bude kofan flat nata yayi yashigo dasauri ta tashi daga jikin kujera tana kallonshi yayi wani irin mahaukacin kyau ahankali tace "ina kwana" batare daya kalleta ba yace "kalau" zama yayi akan kujeran falon yace "kawomin abincin nan" danjim tayi gabanta na faduwa kada yace bazaici ba tawuce dinning flask na shayi tafara daukowa ta ijiye kan table takoma tadauko tray na cup da bread da spoon sai honey ta ijiye sannan takoma ta dauko wani kula mai kyau takawo ta ijiye gabansa still kallonsa take, yadan jima yana amsa wayan dayake sannan ya katse yakalli komi na gabanshi kafin yasa hannu yabude kulan yaga egg datamai frying sai yaji abu ya tsayamai awuya Haleema knows the way he eats atleast tana gani adakin Mom.

Dan lumshe idanu kadan Riyad yayi kafin yabudesu yadaura akanta ganin yanda idanunshi sukai ja batasan sanda ahankali tace "Baby ni kadaine fa kasa an sallami ma'aikata na, this is the only abinda na iya maka fixing quick" ahankali yatashi dan komawa baya tayi ganin yanda yayi kaman zaki baice mata komiba yabude kofa yafita dag dakin tadan harari kofan tace "what is bad about this continental breakfast please? Da kanason abinci dayawa da baka sallami yan aiki na ba, akanme ina matar sarki zan dinga wahala ina shiga kitchen? Antaba hakane?.

Har bangaren Ammi fadawa suka biyoshi ciki ya shiga

Ammi bata falo dinning yawce one thing about gidan Ammi is there's always food anytime kaje gidan zama yayi a dinning yasa masa da pepper soup da shayi ya jera a tray dake wajen, kallo sama yayi ganin bai hango Ammi ba yasa yatashi manyan kayan jikinshi yacire na ciki ya ijiye awajen yabar jumper dake jiki na soft milk yard yawuce sama ahankali hannu yasa yabude kofan dakin, zaune yaganta ita kadai tana sanye da wani A-shape gown na atampa sabo kal dasafen nan Ammi takawo mata sababbin atampopi 10 set taga ledan an rubuta SapphirebyAishaSambo, gold atampa ne yamata kyau yabi jikinta tass dan size din Meenat Ammi ta bada, kawai burst dinne sukaso su mata kadan dan tafi Meena boobs but still kayan sun shigeta and she looks so beautiful aciki, kanta ba dankwali tadalyi parking gashinta kawai tana zaune ita kadai tana kallon window dakin da Ammi tabude mata sabida haske ya shigo dakin looking super lonely.

Kamshin turarenshi kadai taji yasa tajuyo da kanta tazubamai idanunta dahar yau suke a kumbure lumshe idanu kadan tayi tabudesu still kallonshi take kaman yau tafara ganishi maida kofan yayi yarufe yashigo cikin dakin har zuwa wajen datake tray abincin ya ijiye sannan yajuyo da kanshi ya kalleta hakanan kawai taji gabanta yafadi motsi lips dinta sukayi murya chan kasa tace "ina kwana" dan tsayawa yayi yana kallon kwayan idanunta da sauri ta sauke idanun nata kasa, saukan hannunshi taji kan wuyanta da saida kirjinta yabuga dasauri takalleshi hada ido sukayi still kallonta yake batare daya cire hannun nashi daga wuyanta ba ahankali yace "have you eaten"? Gyadamai kai tayi ashagwabe da shima saida heart dinshi yabuga yadaure murya chan kasa yace "me kikaci"? Wani iri hannunshi yakesa takeji ajikinta amman da kyar tace "tea" ganin yanda takeyi yasa yadauke hannun daga wuyanta waist dinta yakai hannun yakama tareda dagota tashi daya yakawota dab da jikinshi kaman zai hada fuskansu numfashi tafara da sauri da sauri dake sauka a fuskanshi tana kallonshi kaman yanda yake kallonta tamai bala'in kyau ya tsare lips nata da idanu yana tuna how they felt ranan a mouth nashi kafin ya janye idanunshi da kyar daga lips din ya daura kan idanunta murya chan kasa yace "I want to feed you banson gardama okay" gyadamai kai tayi da sauri gently yasaketa ya zaunar da ita gefenshi yasa spoon ya yanki sinasir din yasa miya yakai bakinta batai musu ba tabude baki tana kallonshi murmushi yamata yasa mata abincin abaki tafara taunawa ahankali tana kallon yanda yake murmushi dimples dinshi ke motsi yana smiling he's so handsome kaman mace wih, gutsura shima yayi yakai bakinshi yaci sannan yasake kaiwa bakinta tabude ahankali ta amsa shima yakai yaci karan shattering glasses sukaji dayasa afirgice Rashida tarikemai riga da sauri daidai nan yaji muryan Mom tace "fitomin da d'ana ko badake nake magana ba kika maidani mahaukaciya Riyad! Alkyabban waye anan?" Lumshe idanu Riyad yayi yabude ahankali yakalli Rashida data rikeshi tana kalion kofan dakin itama murmushi yamata yakama hannunshi daga jikin rigan yace "cigaba da cin abinci ina zuwa! Don't come out kinji" gyadamai kai tayi gently yatashi yana gyara riganshi yawuce kofa Rashida tabishi da kallo gabanta na faduwa dum dum dum sosai kaman wani abu zai faru da ita cus haka tadingaji ranan da Mama tarasu. 




Post a Comment

0 Comments