TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 14

 *_Mamuhgee14_*

saurin sauke Kai tayi tana qoqarin komawa fuska a daure yace"


Ke zo nan.


Muguwar faduwa gabanta yayi ta 'dan dago takallesa taga fuskarnan a tamke ba Wasa ya juya ya nufi dakinsa.


Hijabinta ta jawo tasaka jikinta na sanyi ga tsoro da fargaba fal cikin ranta

Ta juya ta kalli gefen da iya talatu ke zaune taga ko dagowa ta kalleta taqiyi ta wuce tabi bayansa qafafunta na 'dan daukar rawa sbd fargaba da tsoro gashi baba baya nan Dan kullum cikin Mata kashedin zuwa dakin zakin yake ko kebewa dashi.


Saidata wuce iya talatu ta dago tabi bayanta da kallo Dan tana kalle dasu tayi kamar batasan meke faruwa ba,


Dire robar hannunta tayi da Dan qarfi tana cewa"


Allah ma yasa yayi Mata ciki ko zamu samu masifarsa ta rage idan yaga Yana Shirin zama uba,idan Kuma rabon wahala ne ke jiranmu kamar yanda dattiya yafada Allah ya nesanta dashi Amma wlh masifa wlh Nima ta isheni duk wani tattalin arzikina kullum a karyewa yake sbd masifar Zaki da badan Allah yayini da farin jinin sana'ar samuba da tuni na kakkarye Babu sauran jarin da kuma tuni nabi bayan dattiya a yawon ta zubar dinsa.


Ita wlh ma ringa cusa masa Nadiya zata riqa Yi daga yau tunda dama ance duk iskancin mutum idan yayi aure Yana raguwa idan Kuma aka haifar masama dainawa yakeyi 

Sudai sunason Zaki ya daina ta'addanci ko zasu samu su shaqi iskan duniya hankali kwance duk da wani lokacin baqaramin dadi takejiba idan tafita duk anguwar dataje indai akwai yayan banza saisun taso sun gaidata ana cewa gwaggon sarki Zaki ce Saidai Kuma wlh tanason itada 'yan dabbobinta su sakata su Wala a gidan duk da dai tasan ba inda zasu a gidan zasu tare Amma dai zai daina Basu gwale gwale komadai yayane.



Nadiya kuwa tana isa baqin qofar dakin dake soron gidan ta tsaya tsoronta na qaruwa takasa shiga sai fargabar kar babanta yazo yaganta anan din takeyi gashi ana hango ta waje tunda soro ne,


Kamar daga sama dattiya dake zaune taredasu mal idi dasu mal zailani a bakin masallaci yaga kamar idanuwansa na hango masa hijabi hijabi a soron gidan ya hadiye wani yawu qut da qarfi tareda miqewa Yana gyara zaman hularsa dake kife a kansa kamar ya zura kwano sbd batada wata karyewa ko Dan wani qarfin starch da hula kedashi.


Hankalinsa na soron gidansa yace"


Ina zuwa Bari na dubo wani Abu cikin gidan yanxu....


Ko gama Kai qarshen zancen baiyiba ya wuce Yana Dan sauri Dan kuwa idan har Nadiya ce zata shiga dakin Zaki dantaga bayanan dukan tashi Kisha gishiri zai Mata Dan wlh bazai yarda ya qare a 'yayan troway ba,

Ruqayya ta Haifa masa acema yanxu yarsa ta Haifa masa.


Aikuwa itace'"yafada Yana qaro sauri zai shigo tun daga wajen yake cewa"


Ke Nadiya karki Bari na iso na sameki gurin nan wlh dukan akuya zanmiki idan nasameki agurin wuce ciki maza maza.....


A tsorace ta juyo jin maganar babanta jikinta yasake daukar rawa ta juya da sauri zatayi cikin gida taji anriqe hannunta da wani irin hannu dayasa dukkanin jikinta zazzabi ya sauka Dan kuwa take rawar jikinta ta qaru.


Idanuwa cikeda hawaye ta juyo sukai ido biyu da Zaki daya riqeda hannunta jikinsa ba riga dagashi sai wani sabon three quarter Mai zanen sojoji ajikinsa daga gani baigama shiryawa.


Hawayen idonta ne Suka tsinke suna gangarowa sbd babanta.


Dattiya nashigowa soron afusace zaiyi mgn Zaki ya fizgota cikin dakin dama labulen dakin koyaushe a sake yake.


Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci dattiya baisan lokacinda ya banke labulen dakin ba zai shiga a masife.


Jawota cikin jikinsa Zaki yayi Wanda yasa kusan numfashinsu daukewa atare musamman sbd Babu riga ajikinsa gashi itama hijab din ta robace duk ta kwanta jikinta.


Kasa dagowa tayi sai qoqarin zamewa datakeyi jikinta na rawar tsoron abinda ke faruwa.


Shikuwa Zaki ko ajikinsa ya matseta cikin jikinsa tareda kallon dattiya dayayi mutuwar tsaye cikin Izza yabude baki yace"


Wlh taku 'daya idan ka qaro cikin dakin nan saina Mata abinda bakaso ayau din nan...


Wani irin zafi zuciyar dattiya taqara dauka cikin tsananin baqin ciki da fushi yace"


Naji to saketa tayi cikin gida.


Bai saketaba ya juya da ita jikinsa har bakin katifarsa ya saketa fuskar nan tamke ko kallonta bayayi yace"


Ke kwanta anan.


Juyowa yayi Yana fuskantar dattiya da idanuwansa sukai kamar ruwa sun ciko aciki ya nuna masa qofa da ido Yana Kai hannu kan zib din wandonsa kamar zai cire.....


Da sauri dattiya yafito dakin yayo cikin gida ko gani sosai bayayi yana kaiwa kusada talatu ya zube yayi zaman Yan bori tareda dafe Kai ransa na suya yace"


Wannan wace irin masiface ruqayya tasani aciki ta barni????


Uban waye baban Zaki Dan kuwa tabbas daga tsotson marasa kunya da mutunci yafito,


Wane kalar balaine nake ciki agabana wannan Dan yawon ta zubar din ke tabamin 'ya haryana cewa zaiyi....

sai yakasa fada ya juya zancen cikin fargabar abinda ke can Yana faruwa a dakin zakin yanxu,


Jiyake kamar yaje ya siyo maganin suma yasawa Zaki yayi suman wata biyu bai tashiba.


Itadai iya ko kallonsa batayiba taci gaba da aikinta tana cewa"


Allah yabamu jikoki masu qashin arziki da tagomashinsa tunda dai gashinan 'yayanmu Babu maishi saimu roqa daga jikoki.


Wani mugun kallon takaicinta yasako Mata tareda miqewa a fusace yayi ball da bokitin sauran tsiminta yawuce Yana zuba sabon masifa da kowa agidan.


Shimfida tabarma yayi a qofar dakin zainab ya zauna Yana mita Babu inda zashi saiyaga fitowar Nadiya Dan kuwa yau saiya karyata a gidan nan.



Bai juyoba ya dauki rigarsa Mara hannu Mai hula yasaka tareda ficewa bataredama ya nuna tunawa da ita a dakinba,


Ahankali tasamu kuzarin sauke wani wahalallen numfashi bayan fitarsa,


Zamewa tayi qasa ta zauna tareda qanqame jikinta dake rawa har lokacin,

Tsananin kunyar babanta takeji kamar zata kasheta

Batasan ta Yayama zata iya kallonsaba yanxu.


Tunowa tayi da Yaya zakin saitaji kunyarta da tashin hankalinta ya ninku hartana sakin wani irin kukan Rashin sanin abinyi.


Shikuwa Yana fitowa sanin tana ciki yabada umarnin kar Wanda ya shiga dakinsa duk da damacan idan bashine ya aikesu basa shiga dakinsa.


Zama yayi cikinsu Suka hau ayyukansu harsaida alee dikko ya biyo ya daukesa tareda securities dinsa Suka fita shima yaransa Suka Mara musu baya cikin tasu motar.


Har aka fara Kiran magriba Bata fitoba nan hankalin dattiya yasake tashi Dan bai lurada fitar Zaki ba duk tunaninsa suna ciki.


Zuwa lokacin dukkanin jikinsa yagama yin sanyi Dan har wani mutuwa jikinsa yayi Dan kuwa yasan yanzu komai dayake gudu yariga yafaru Saidai Nadiya tayiwa kanta Dan batasan gatan dayake son mataba ta Shirin rabata da wannan auren qaddara dayakeyi.


Miqewa yayi daqyar jiki amace ya dauki buta ya nufi bayi Dan gabatarda alwalar magriba da aka gama Kira.


Yana fitowa bayi itama tana shigowa tsakar gidan a rarrabe da bango kanta a qasa takasa dagowa takalli ko dayansu sai hawaye dake gangaro Mata.


Da sauri talatu ta ajiye aikin daurin datakeyi tana yiwa nadiyar kallon tsaf kamar yanda dattiya yayi Mata kafin ya dauke Kai cikin ransa Yana tsinewa Lagos ma gabaki dayanta da Wainda ke ciki tunda acan uban Zaki yake,

Shi kenan Zaki yakaisa ya barosa.


Iya kuwa wata irin guda ta rangada tareda miqewa da sauri ta nufi nadiyar zata kamota tayo ciki da ita dattiya ya fizgo nadiyar cikin baqin ciki ya turata yace"


Ni mahaifinki naki dokar Rashin zuwa dakin wannan dangin Lagos din kika take maganata kika tafi sbd kin rainani Ni ban isaba ko???

To tunda haka kika zaba wlh kingama zama cikin gidannan ki koma can gurinsa na barmasa tunda ya koya Miki kalar rashin kunyarsa da Rashin mutuncinsa....


Saurin zubewa tayi qasa tana kuka tana girgiza Kai da qarfi.


Wani wawan Marin takaicinta ya sakar Mata yanajin radadin abin aransa Dan kuwa baiso rayuwarta ta wagarce a hakaba yaso taje gidan aurenta tayi rayuwar aure kamar kowa Amma wannan rayuwar da Zaki Babu wani rayuwar aure aciki tunda anan suke zaune agabansu za'a riqa Haifa musu jikoki Sam bai hango ta yanda zasuyi rayuwar aure anan ba.


Wannan abin ke cimasa Rai shiyasa yayita gudun faruwar hakan sbd za'ayita nunasa ana cewa acikin gidansa ake cikin jikokinsa aciki ake haihuwarsu aciki suke girma,ba wannan rayuwar yaso Mata...


Janta yayi da qarfi ransa na qara quna ya jehota soron gidan da qarfi daidai shigowarsa shikuma ba zato ta fado kirjinsa.


Kuka takeyi sosai sbd tsoron ganin fushin baban dabata taba ganiba tayi saurin barin jikinsa tareda durqushewa gefe tana kuka sosai.


Cikin bacin rai kawun ya kallesa ganin yanda yake qoqarin shigewa dakinsa ko kulasu yaqiyi kamar baiga meke faruwaba yace"


Ka Gama daure dauren fuskarka da izzarka ta banxa Wanda Babu ta inda ka gaji sarauta anan Saidai can a qasar dangin oduduwa

Wlh bazan zama wulaqantaccen mutumba dazai taraku agida ku ringa zubamin Rashin kunya ba.,


Gatanan dagayau tadawo dakinka gwara nasan ta tare zaman aure takeyi da in ajeta Ina zagayen banxa Kuna nuna Rashin kunyarku gwara ku qaratacan Kuma wlh kace bazata zauna a dakinkaba to ku tattara kubarmin gidana kuje can kusan nayi.....


Fara neman daburcewa yakeyi sbd fararen idanuwan da zakin ya kafesa dasu,


Fara rawar murya yayi ga fargaba ga bacin Rai yace"


Eh kadaiji abinda nafada bazaku maidani dattiyan banxaba.


Wani malalacin murmushi Zaki yayi tareda Dan kallon gefen nadiyar cikin ko in kula yace"


Ke tashi ki shiga ciki.


Kasa tashi tayi sai kukanta dake qaruwa.


Cikin tsawa yace"


Zan karya Miki qafa fa.


Miqewa tayi da sauri ta nufi cikin gidan dattiya ya daka Mata tsawa yace"


Wuce dakinsa ai daga yau kin tare zaman aure zakiyi tunda kin nuna kinshirya.


Kallonsa takeyi tana tsananta hawaye ta juyo ta nufi dakin zakin ta rakube bakin qofa.


Dogon tsaki yaja tareda nufar qofa Yana cewa"


Wlh andai cuceni Ni dattiya.


Shikuwa shiru yayi agurin tareda rintse idanu ya bude ya juya ya watsar Mata wani mugun kallo Yana cewa"


Zaki min shiru agurin kosaina karya wuyanki agurin.


Tsit tayi tareda qarasa shigewa bayan qofar.


Fasa shiga yayi ya fice shima Dan sallah.


Yana ficewa tayo cikin gidan Dan yin alwala itama tana share hawayenta dasukaqi tsayawa tana kallon iya talatu dataki saka baki a alamarin.

#mamuh*_BURI DAYA na kudine idan baka biyaba ka nemi wannan numbers din ka biya ka karanta cikin aminci_*




Post a Comment

0 Comments