TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 19

 _*Mamuhgee 19*_

Jin nishinta da motsin data daina yasashi daukar wayarsa ya kunna fitila ya haskata,


A miqe take jikinta gabaki daya ya saki ta daina motsi sai bakinta dake budewa alamar tanason Jan numfashi Amma takasa.


Aje wayar yayi lokaci guda ya isa gurinta tareda cirota da sauri ya Dora kan katifa Yana Kiran sunanta tareda 'dan jijjiga fuskarta Yana kallonta cikin tashin hankali Saidai Yana qoqarin dannewa.


Sakewa jikinta yaqarasayi numfashinta ya tsaya cak.


Wannan karon da qarfi ya girgizata Amma Sam tariga ta some batasan yanayiba.


Bai tsaya komaiba ya dauketa tareda wayarsa da key din mota da atm ya fito Yana kallon fuskarta yanaji kamar zuciyarsa zata buga.


Qafa yasa yayi kyauren fita gida shuri 'daya take qofar tabude ya fice baiko tsaya nemansu nanuba ya nufi motarsu dake pake gurin masallaci ya bude da hannu daya yasakata.


Yana qoqarin shigane Nanu yafito riqeda fitila da wata sharbebiyar Adda tana kyalli cikin duhun sbd motsinda yajiyo.


Ganin mutum na qoqarin shiga motarsu yasa ya Dalla fitila ga mamakinsa yaga Zaki da sauri ta qaraso Yana cewa"


Sarki matsala ce????


Batareda ya kallesaba yafara qoqarin shiga motar 

Nanu yayi saurin cewa"


Sarki kawo naja kamar zaifi saika kulada ita a bayan.


Miqa masa key yayi sbd bayason doguwar hayaniyarda zata tayarda mutane suka bar gurin suna Hawa titi Nanu yabata wata irin wuta na mugun gudu.


Dattiya dayaji anyiwa qofar gidan mugun bugu cikin bacci yayi mugun zabura tareda lalubar fitilarsa Yana qoqarin kunnawa Amma taqi kunnuwa.


Ahankali ya miqe tsaye tareda nufar qofa Yana tafiya ahankali.


Bude qofar dakin yayi yafito yanabin bango atake qirjinsa yayi mugun bugawa lokacinda ya hango qofar gidan a wangale

Wani mugun zufane ya karyo masa yadawo daki da sauri qafafuwansa na mugun rawa yasawa qofar dakin sakata yafara lalubar inda talatu take.


Da Dan qarfi ya buga qafarta ta zabura tana cewa"


Wayyo Allah innalillahi.


Wani sabon zufane ya gangaro masa ya bude baki qasa qasa yace"


Talatu yau ranar rabuwarmu tazo wlh barayine Suka shigo Kuma tunda kikaji tsit wlh sungama kashesu Zaki Ni wlh bantara komaiba ahaka nazo duniya ahaka zankoma yau mutuwar wulaqanci zamuyi Dan wlh kashemu zasuyi tunda bamuda abun Basu....


Yana kaiwa nan sai kawai muryarsa ta fara rawar kuka yanason dannewa.


Iya talatu kuwa kuka take sosai harda shesheka tana tuna irin rayuwarda sukayi a baya tanajin tausayin zasu mutu yau wace irin rayuwa zasu tarar.


Har akayi Kiran asuba suna zaune suna jiran tsammani zuwa lokacin tuni idanuwan iya talatu sukayi luhu luhu sbd kuka dattiya ma yayi sharben hawaye harya gaji.


Saidaya tabbatarda anfito masallaci har gari yafara Dan washewa kafin ya bude daki ya leqo Yana qwalawa zainab Kira.


Cikin maganin bacci ta fito tana amsawa.


Yana ganin haka saiya qarasa fitowa Yana goge zufa ya daure fuska yace"


Waike Sam bakya tashi sallah kan lokaci ko??kullum Saidai baccin lalaci maza wuce kije kiyi sallah kafin na fasa bakinki a gurin.


Wucewa tayi tana murza ido tana Dan tura baki.


Shima a dubarance yayi alwalar dan karta gane shima baiyiba yakoma daki ya tayarda sallah iya talatu ma said lokacin ta fito tayi alwala Takoma yin sallah.



Suna isa asibiti a gaggauce aka karbeta sbd yanda jikinta yayi sanyi sosai kamar zata sandare Dan tuni ta miqe kamar bazata iya lanqwasuwaba.


Likitocin dake on call (NIGHT DUTY) suna ganinta Suka gano abinda ke damunta Dan kuwa data Jima ahaka to shikenan za'a iya rasabata dankuwa zata iya mutuwa abinda yaji likitocin na fada kenan kafin ace yafito.



Zama yayi kan waiting kujerar dake bakin gurin tareda Dan rintse idanuwansa ya fitarda numfashi Mai qarshi idanuwansa na kadawa zuwa ja sbd bacin Rai da tension.


Nanu dayaga yanayinsha Saida yasha jinin jikinsa Yana zazzare ido a qofar Yana fatar kar abinda yasamu nadiyar sbd sarkinsu.

 

Saida gari yayi haske sosai har lokaci yaja guraren qarfe takwas wata nurse tafito tazo gaban zakin tace"


Bismillah Dr na son ganinka.


Miqewa yayi yashiga cikin dakin 

Yana shiga saidayaji wani irin zafi ya daki fuskarsa sbd dakin ya dauki dumi sosai anrufe windows ansaki labulayensu sun kunna na'urar dumama daki sunkai kusan qarshe Wanda hakan yasa jikin nadiyar yafara sakewa daga sandarewar dayayi sbd sanyi daya shiga qashinta sosai.


Kallon Dr dake rubutu a file dinda aka bude Mata yayi batareda ya kalli inda take kwance ba Yana sauraran bayanin dazai masa.


Saida Dr yagama rubutu kafin ya miqawa nurse file din yace"


I've written all the drugs + the injection dazaki Mata immediately after her plasiadmin so just write and give him duka abinda zaisiyo.


 juyowo yayi ya fuskanci zakin tareda Dan juyawa ya kalli nadiyan cikin yanayi na damuwar halinda nadiyar ke ciki Dr din yace"


Maganar gskia yarinyarnan wahalace da sanyi suke neman yimata illa sbd sanyi yashiga jikinta sosai harya kama qashin gefe gefen cikinta wanda Kuma tarinsa ke yagar maqoshinta Wanda yake tashe.,


Saikuma qashin bayanta dake neman 'dan lanqwasawa sbd aikin wahala.,


Ataqaice da gskia tana cikin tsananin hali na cutar sanyi dakeson kamata gabaki dayanta,


Sannan bakwa ganin yanda aiki da ruwan zanyi duk ya yayyanke Mata qafafuwa Amma Sam bakuyi tunanin zuwa asibiti da wuriba shiyasa wasu qwayoyin cutar sukaita shigarta ta nan.


To yanxu dai gashinan munyi duk abinda yakamata muyi Dan ceto rayuwarta Kuma alhmdllh gatanan she's stable now Amma zamu riqeta tsawon kwana biyu harsaita qara zama stable nurse zata baka takardar abinda za'a siya, Allah ya sauwaqe.


Rabasa yayi zai wuce cikin shaqewar murya zakin yace"


Shi toshewar moqoshin akwai mafitarsa????


Tsayawa Dr din yayi tareda juyowa yace"


Eh kala kala ne akwai Mai warkewa akwai Wanda baya warkewa nata yanxu bamusan wane iri bane tukuna sai munyi Mata hotuna da awo zamu iya ganewa.


Gyara tsayuwa zakin yayi suna fuskantar juna da Dr yace"


Yaushe yakamata afara wainnan.???


Duk lokacinda ka shirya zamu komai Saidai Banda yanxu saita warke ko zamu fara Mata na wannan fannin so inaga mu Bari zuwa kamar qarshen watan nan Dan zuwa lokacin duka drugs dinta tagama shansu.


Ok thanks""zakin yafada Wanda yasa Dr sake kallonsa sbd izzarsa da cika idonsa ga tsare gida dayayi yasa Bai masa masifa sosaiba akan halinda nadiyar ke ciki Dan ta basa tausayi matuqa yarinyar dama shi mutum ne Mai matuqar tausayi.


Qofarda Dr yarufo bayan fitarsa ya dade Yana kallo kafin ya juyo ahankali ya kurawa gadon datake kwance ido.


Yaune Rana ta farko a rayuwarsa daya yake Mata kallon tsaf tun daga kanta har qafafunta.


Kwance take miqe andaura Mata ruwa sai qafafuwanta da aka dannade gurin yatsin qafarta da bandages,


Doguwar rigar data Saba bacci da itace ta kode ta wande sbd wanki da tsufa.,


Fuskarta fayau Babu komai sai uwar rama da duhun datayi sai kanta dake kwance sbd zainab data saka Mata relaxer Dan Dole sbd bikin Yaya dahiru Saidai tun ranarda akayi Mata taba sake warware shiba tasake gyarawa Dan tanada cika da tsawon gashi ba laifi.


Sarqewa numfashinsa yafarayi ya dauke ido daga kanta yanajin wani irin zafi da tiririn zuciya na cinsa Dan da akwai inda zai sauke abinda yakeji na zafi a ransa da sunga balai da masifarsa Basu taba jiba.


Dama nurse ta bar masa takarda tun suna mgn da Dr tafice.


Daukar takardar yayi ya fito fuskarnan yau tafi tako yaushe Rashin annuri 

Nanu yataso da sauri Yana masa maganar jikin nadiyar.


Takardar ya miqa masa tareda ATM dinsa kawai ya juya ya koma batareda yace komaiba.


Da sauri Nanu ya juya ya nufi pharmacy yafarajin kudin tukuna kafin yaje yaciro Dan akwaima atm jikin pharmacy na asibitin.


Zama yayi kan kujerar dakin dake nesa da gado ya Dora qafa daya Kam daya tareda rintse idanuwansa dasukai ja ya juya maganar Dr a zuciyarsa gameda maqoshinta na Rashin mgnarta.


Har lokacin sallar azahar suna asibiti sai bayan dasukayi sallah yadawo gida yashiga dakinsa ya zauna tareda dafe Kai Yana furzarda numfashi Jin kansa Kai zai buga sbd tunani da ciwo.



Cikin gidan kuwa da hankalinsu yatashi Rashin ganin Nadiya da zakin gakuma anyita dubowa basanan sai hankalinsu yatashi musamman da dattiya ya rafka mugun tagumi yace"


Dama nasan barayin jiya da dare bazasu shigo su tafi lami ba

Shikenan sun daukemin 'yaya wlh kashesu zasuyi..

Take idanuwansa Suka cicciko.


Zainab madai tayi kuka har idanuwanta sun kumbura hakama iya talatu sbd duk da halayensu suke a wani irin barkace suna so da qaunar junansu zuri'ar ta dattiya.


Take zance ya bazu sai zuwa jajentawa akeyi.


Ana haka zakin yadawo bayan qarfe biyu harda rabi.


Nan dattiya ya taso haryana neman faduwa ya nufi dakin zakin Saidai a yanayinsa yagansa saiyaji duk baiji dadiba Rashin ganin Nadiya atareda Zaki saiyaji qafafunsa na neman gazawa murya na 'dan sanyi yace"


Ina 'yata???

Ina kabaromin ita????


Baison hayaniya shiyasa Kai tsaye batareda ya dagoba yace"


Tana asibiti batada lafiya.


Wata ajiyar zuciya dattiyan ya sake sbd sai lokacin yaji hankalinsa ya kwanta ya juya cikin gida ya sanarwa iya talatu kafin ya azalzali zainab data shirya suje asibitin ta zauna da nadiyar.


Bai tsaya sauraren tension dinda kawun zai iya qara masaba yace Nanu yakaisu asibitin yadawowarsa.


Aikuwa Yana kaisu yadawo,

Koda sukaje ta har lokacin Bata farfadoba sbd kosu kansu likitoci basaso ta farka yanxu sai bayan 24hrs jikinta yagama samun isashen hutu da dumamawar dasukeson yasamu.




Post a Comment

0 Comments