TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 12

#MAMUH*_BURI DAYA Yana cikin Zafafa2020 na siyarwane  ba free ba idan baki biyaba ki nemi wainnan numbers din kibiya ki karanta cikin amincin allah._*


07067124863

08030811300



*_Mamuhgee12_*

Kasa shiga motar yayi hakama yakasa juyowa

Zuciyarsa nason qin gasgata abinda kunnuwansa Suka jiyo masa musamman yanda numfashi ke sauri gurin fita.


Dukkanin yaransa kuwa wuta Suka dauke Basu nuna farin cikinsuba daya wanxu cikin zukatansu sbd jimami da radadi dasuke ciki na Rashin dayan jigonsu JJ.


Ahankali ya juyo bayan ya rintse idanuwansa ya bude atake Suka qara kadawa Suka rikide.


Kallon kawun yayi daketa miqawa mutane hannu Yana yaqen dole Dan kuwa shima ayau din zuciyarsa dif take da damuwar wannan aure Saidai baida yanda zaiyi Dan kuwa wani bangaren auren Zaki ga nadiyarsa shine mafita Dan kuwa idan tana matsayin matarsa Babu shegen da zaiyi Gigi ko gangancin ko yiwa inda take mugun kallo,

Saidai ta bangaren rayuwar aure yasan Zaki bazai taba kulada Nadia ba musamman ganin yanda yafi hukuntata akan kowa.


Hada ido sukayi sukayiwa juna kallon cikin ido kowanne zuciyarsa cikeda damuwa da tsananin bacin Rai Saidai hakanan ya juya yafada mota sukabar gurin Dan zuwa dauko gawar JJ azo ayi Mata sallah.


Suna barin gurin aka fara watsewa sbd wasu da dama basusan da rasuwar JJ ba.


Acikin gida kuwa lokacinda dahiru yashigo bayan daurin aure shine yafara shigowa ya nufi dakin iya talatu dake 'dan cikeda mutane anata hayaniyar biki ya miqa Mata goro da dabinon daurin auren yana cewa"


Ga goron nan ki ajiye har baban yashigo andaura aure da yardar Allah Saidai abin mamakin baba baya qarewa mu munxo da sanin Bello ne mijin saigashi mukaji baba agurin yacewa liman da Zaki za'a daura auren.


Saurin kamo goron daya kusa zubewa iya talatu tayi tana kallon dahiru tace"


Zaki fa kace????


Eh, Allah yabasu haquri da juna shine fatar kawai tunda andaura.


Numfashi iya talatu tasaki tana sake zare 'yan fici ficin idanuwanta cikeda mamakin dattiya da Rashin sanin abin fada kawai tace"


To Allah ya sanyaya zuciyar Zaki mudai da wannan danyen hukuncin na babanku.


Kallon zainab dake tsaye gefenta tana waya da wasu qawayenta datakewa kwatancen gidan tace"


Auren nan kinji da Zaki aka daura.


Wani zaro ido tayi cikeda mamaki da son qin gasgata zancen tace"


Yaya Zaki yanxu shine mijin Nadiya????


Kwarai kuwa cewar dattiya daya shigo gidan.


Aikuwa nan aka dauki guda ana Allah ya sanya albarka.


Zainab kuwa daki tayi da sauri Dan fesawa Nadiya zancen.


Qare Mata kallo tayi daga bakin qofar tana kwatanta irin dacewarda zasuyi da ace zasuyi zaman aure kamar na kowane maaurata Saidai tasan Yaya Zaki Kam ko kallo Nadia bazata ishesaba duk da wasu lokutan tanayi musu kallon masoya duk da irin tazarar halaye da banbanci dake bayyane a tsakaninsu.


Qarasowa tayi cikin dakin ta zauna kan katifar dake dakin tareda aje wayarta tana daukar Hoda tafara shafawa fuskarta da Bata rabo da kwalliya koyaushe hankali kwance race"


Andaura aure dai yau kukan auren Bello yaqare Saidai na Yaya Zaki....


'dago jajayen idanuwanta tayi takalli zainab din ahankali batareda hawayen cikin idonta sun gangaroba sbd kokawar da zuciyarta keyi gurin auna zancen kafin ta yarda dashi a zuciyarta.


Aje hodar zainab tayi tareda kallonta tace"


Baki yarda bane ko me?kike min kallon qurulla...


Sallamar dattiya tasasu kallon qofar dakin atare,

Zainab ta miqe tareda daukar wayarta da gyalenta ta fice Dan tarbo baqinta.


Cikin sanyin jiki data fara ganin mahaifin nata dashi akaro na farko rayuwarta taga yashigo ya tsaya akanta zuciyarsa ba wani dadi yakalleta tayi qasa da Kai hawayenta na sake saukowa sbd yanayinsa kawai ya tabbatar matada zancen da zainab tafada gskia ne da Yaya Zaki aka daura Mata aure.


Cikin sanyin murya yafara cewa"


Nadiya Allah yayi yau nasauke nauyinki dayake kaina amatsayin mahaifinki Dan kuwa na 'daura Miki aure ayau din da Zaki Wanda shi na zabar Miki amatsayina na mahaifinki Dan haka Babu wani Jan dogon bayani Saidai Ina Miki adduar Allah yasa hakan shine alkhairin rayuwarki duk da nasan Babu abinda Zaki tsinta acikin auren zakin.


Qaramin kuka Mai ban tausayi ta fashe dashi Babu sauti Yana ji yajuya ya fice Yana jin wani qululun baqin ciki da takaicin zakin.


Sosai tayi kuka Wanda sai yanxu take jin gwarama auren bellon tunda shi Yana sonta yanxu wannan auren wace irin rayuwa baban ke tunanin zatayi da mutuminda ko kallon inda take bayayi da daraja bare ma matsayin Mata.


Cikin yan biki kuwa Babu Wanda ya damu da wannan juyi da akayi hidimarsu sukeyi hankali kwance saidaima rasuwar JJ ce dake 'dan rage musu armashin abun duk da dai shiru har yamma tasomayi su zakin Basu dawo da gawar JJ dinba bare ayi jana'iza.


Har guraren magriba Babu labarin dawowarsu bare ayi jana'iza tuni aka gama yinin bikin aka watse ba maganar Kai amarya tunda gida daya suke ataqaice ma Babu gurin kaita.


Ahaka gida ya watse aka barsu sukadai yan gidan Dan ko dangin mahaifiyarta da maraicen Suka tattara Suka tafiyarsu ko Dan ganin angon nata ba irin Wanda zasu tsaya suyiwa nasihar riqe 'yar marainiyar 'yarsu bane Dan kuwa su kansu ranar dasuka fara zuwa sukaga bataliyar makamai da yaransa a qofar gidan a tsorace sukeda gidan har Suka tashi tafiya musamman yanxu dasukaji shugaban bataliyar shine mijin yarsu.




***

Lokacinda Suka koma asibiti Sun Jima suna neman likitanda case din yake hannunsa gashi yashiga theater Dole Suka jira yafito sbd asibitin ta dikko Dilla ce dokace ba'a bayarda gawa sai likitan daya karbeka yazo yasaka hannu kunsaka sai abaku gawar.


Sai kusan yamma Dr jimoh yafito zuwa lokacin ran Zaki yafara baci Amma sbd yanason mutunta gawar JJ bazaiso yin kowane irin Abu na ta'addanci ba akan gawarsa sai angama komai akwai Wainda zaiyi settling scores dasu.


Atare Suka nufi dakinda gawar take bayan ansaka hannu da komi.


Tura qofar dakin sukayi Dr jimoh yayi saurin qarasowa ciki Yana kallon gadon ganin baiga gawar ba.


Kallon nurses dinda ke bayansa yayi suma Suka kallesa da tsoro da mamaki...


Wani irin kallo zaki yayiwa likitan Yana jiran qarin bayanin inda gawar JJ take Dan zuwa lokacin yagama zuciya zai iya tada asibitin kowama ya mutu ahuta.


Zare coat din saman kayansa Dr jimoh yayi Yana taba gadon murya na rawa yace"


Nurse Ahmad go and call all the nurses on duty and Dr ib Idris now.


Jiki na Bari kuwa yafice ko gani dukkaninsu basayi sosai sbd carriers dinsu ce zatayi rawa tunda maganar Rashin ganin gawa akeyi anan.


Cikin qanqanin lokaci hankalin asibitin yatashi sbd dai duk iya bincikensu anyi gawar JJ dai ta Bata Saidai abinda yafi daure musu Kai da mamaki duk security sun tabbatarda Babu gawar da'aka fita da ita Saidai Idan gawar na cikin asibitin a boye kokuwa sai kuwa idan gawar ce tafita da kanta.


Wannan zancen shiya qara hasalta zuciyar Zaki atake yaransa Suka tsare dukkanin qofofin asibitin Babu shiga Babu fita 

Nan hankula Suka tashi Dan kuwa Dole hukuma tashigo ciki sbd ganin irin illar da za'ayiwa Wainda basujiba Basu ganiba. 


Alee dikko dake zaune cikin lafiyayyen palonsa riqeda tumbler yanashan Champaign hannunsa riqeda wayarsa da AM DILLA wato dansa yakirasa yafada masa halinda ake ciki gashi zancen na neman shiga hannun media Wanda zai iya lalata sunan asibiti bama ita kadaiba zai iya taba asibitocinsa da kamfunan maganinsa Wanda bazai iya daukar hakanba Dole something has to be done.


Zeel dilla dake shigowa palon tareda am cikin wata irin Isa da iko tareda wani irin mulki ta qaraso kujerar gefensa ta zauna cikin kwanciyar hankali tadauki remote tana cewa"


Karka Bata ranka tun yanxu sbd ainihin tension din nazuwa matuqar baka kawarda Zaki a duniyarba gabaki daya.


Miqewa yayi tareda zuba hannayensa a aljihu ransa na qara baci sbd da ace wani ne yau yayi wannan abin ko haka baza'a kawoba baibi gawar dayake nemanba,

Amma Zaki na neman caza masa Kai Wanda yake kawarda hakan Dan kawai Yana buqatar zakin Saidai wannan karon Dole zai dauki mataki duk da Yana tunanin abinda zai faru ranarda Zaki zai gano abinda yake Shirin masa

Amma Dole za'ayi hakan Dan kuwa Babu wata Rai dabaya iya kawarwa akan dukiyarsa daya Tara da abubuwa da yawa matuqar yanada damar iyawa.


Juyowa yayi yakalli am dake faman amsa waya Yana bawa security orders na duk yanda za'ayi ayi kar abari media su fitarda abin nan.


Sake kallon am din yayi Kai tsaye yace"


Kaje asibitin da kanka asan yanda za'ayi ayi a nunawa Zaki cewar JJ bai mutuba ya gudu ne......


Cikin wani irin yanayi zeel ta kallesa tana cewa"


Wat???

Kana tunanin Zaki daqiqi ne kamar qaton danka dake gabanka...


Hade fuska am yayi tareda juyowa zai katseta ta 'daga masa hannu tana cigaba da cewa"


Kana tareda shine Amma kamar idanuwanka sunkasa ganin meyene a a tattaredashi,

Wannan zancen idan ma kayisa kana bude qofofin yaqine dashi Dan kuwa kafi kowa sanin waye JJ agurin Zaki.


Cikin fushi da bacin Rai ya katseta da cewa,


Stop giving me lectures akan yaronda na haifa nesa.,idan kinada wani option akan hakan ne just tell us and stop wasting my time bayan kinsan the power of media.


Miqewa tayi tana kallon cikin idonsa tace"


JJ na hannuna Kuma Yana cikin asibitin and he's alive bai mutuba...


Cikeda baqin ciki dayafi mamakinsa yawa yake kallonta duk da yasan wani lokacin zeel tamafisa sanin hanyoyin Rashin Imani Saidai bayason abinda zai taba sunansa koyayane sbd shine kadai yasan irin abubuwan dayayi kafin yayi sunan.



 

Post a Comment

0 Comments