TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Makauniyar soyayyah page 17_18

 *STORY & WRITTEN*


  *BY*


*MARYAM AHMAD PAKI*





*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*🤝🏽




*Ina mika gaisuwa ta ga*

*Miss Marriam novels group*


*Maejeeddarh Othman* (Home of Hausa novels group)


*Ummi*(Kainuwa Writers fans)


*Mhiz Tawerh* (nima ina yin ki sosai)


*Fannata ta Annabi* (zinder)


*Hussaina Paki*(‘yar garin mu)


*Da sauran wanda ban samu damar anbata ba sabida yawan Ku*


*Na gode da son da kuke ma novel d’in nan*🤝🏽


*Allah ina rok’on ka 🙏🏽🙏🏽🙏🏽 kabar mu da masoyan mu a du inda suke*, *ka nisanta mu da masu mana hassada da bak’in ciki da k’iyayya*




*Wannan karan ban samu wanda suka ba da amsar question of the day na tambayar da nayi na cewa* 

*ya sunan bishiyar dake cikin aljanna*?

*Amsar ita ce* *Jannatul kuldi*


*Ina jin dad’in yadda kuke gwada hazak’ar ku*.


*Allah ka k’ara mana ilimi mai amfani*.





*Tunatarwa*


Hak’uri ya kasu kasha uku 🤟🏼


* Hak’uri gurin yi ma Allah biyayya 


 * Hak’uri saboda kiyaye dokokin Allah da sa'ba mishi


* Hak’uri gurin jarrabawa


Dukkan hak’uri yana tare da nasara, ya Allah ka bamu ikon hak’uri.






17&18


Ko da muka je gidan yaya Aminu, hira muka zauna muka yi da Anty jiddah kasancewar ta ita ma ‘yar hirar gashi tana da jan mutane kamar ba dangin mijin ta ba.


Muna cikin hira da ita ne take ce mana "ina ko Faruk, kwana biyu bai lek’o mu ba, bari in munyi waya dashi zan ce mai kar ya bari azumi yazo bai yi aure ba, in ba haka ba, zamu ba dashi sadaka"


Dariya muka yi gaba d’aya kana Anisa tace "ya koma Abuja, yana can yana fama da fad’an shi"


Ni ce na k’ar’bi zancen da cewa "ai da su Momi za su taimaka su mishi aure saboda ina jin har da rashin auren ne yake sa shi wannan fad’an da yake yi, amma kuma ina tausayawa matar da za ta auri yaya Faruk saboda ba k’aramin hak’uri za ta yi da fad’an shi da miskilancin  sa ba"


Murmushi Anty Jiddah tayi kana tace "ni da zai bi shawarata da na za’bar mai kalar type d’in shi saboda ita yarinyar za ta iya dashi"


Zaro ido nayi ina cewa "pls Anty kar ki fara, ki tausayawa ‘yar mutane, ki jik’anta in ba so kike ki sa yarinya ya aure ta, ta fara k’ashin wuya a rasa dalili ba alhalin yaya Faruk ne yake gasa mata gyad’a a hannu"


Anisa ce ta kar’bi zancen da cewa "Anti in dai zai ji shawarar taki, pls ki masa magana saboda yayi auren nan nima in samu sakewa a gida saboda komai a takure nake yi kamar a gidan yari" ta k’arashe zancen kamar za ta yi kuka.


Dariya muka fara yi saboda yadda take maganar, abin har ran ta haka yake.


Haka muka ci gaba da hirar mu kamar wasu k’awaye.


Sai da muka ci abinci sannan muka yi sallar la’asar, ba yadda ba tayi ba akan mu jira yaya Aminu ya dawo ya kaimu amma muka k’i, saboda in har muka jira shi ba lallai ya kaimu gidan k’awar mu ba amma yanzu tun da driver muke, ba mu da wata matsala.


Sallama muka yi mata kana muka nufi gidan Aisha k'awar mu.


Tun da muka je gidan muka dasa hira irin ta k’awaye, muna cikin hirar ne nake sanar dasu yanda muka yi da yaya Faruk ran da zai koma Abuja.


Dariya suka yi gaba d’aya, ganin dariyar tasu kamar da manufa suke yasa na d’aure fuska kamar ba dani ake hirar ba.

Anisa ce ta k’ara kallo na ta fashe da dariya tana cewa "wato Sister a yanzu na samo satar amsa a dramar da kuka yi da yaya Faruk da kuma dalilin da yasa ya hana mu chat da kuma takura mana da yake yi"


Kamar ya? Na tambaye ta.

 

Wani kallo ta min tana k’unshe dariyar da take bakin ta saboda yadda ta ga na d’aure fuska.


Fatima! Zargi na ya fara hararo min cewa yaya Faruk son ki yake yi! Anisa ta fad’a.


Dam! na ji k’irji na ya buga saboda yadda maganar ta zo min a bazata.


Dariyar rainin hankali nayi sannan na k’ara d’aure fuska.

 

"Anisa Kenan! ke a ganin ki mun dace da yaya Faruk? let me tell you something, na san yaya Faruk na da duk wani qualities da mace take buk’ata a gurin namiji, but to me, ba na daga cikin su saboda ke shaida ce na yadda tamu ba ta zo d’aya dashi ba, kuma ana yin aure ne idan jinin ku had’u da mutum ko ra’ayin ku amma ni duk a ciki, ba bu ko d’aya, So plss kar k’i k’ara bi na da irin wannan bak’ar fatan though shi yaya Faruk d’in ma bai ce yana so na ba kuma a yanayin girman kan shi, nasan bazai kula ni ba saboda har yau kallon yarinya yake min" 


Yanayin fuskar Anisa ce ta canza zuwa ‘bacin rai saboda maganar da na fad’a akan yaya Faruk bai mata dad'i ba kuma in da kara ai bai ci in fad’a mi shi haka ba don haka tace "Fatima ya kamata in zaki fad’i Magana ki tauna, kuma in da ka’ra bai kamata ki fad’i wannan maganar a gaba na ba saboda kar ki manta yaya na ne kuma zan ji zafin duk wanda ya zage shi a gaba na kuma duk wannan abun shi yaya Faruk bai sani ba, ni ce na ce ina zargin haka"


Jiki na ne yayi sanyi saboda ban zata maganar za ta ‘bata mata rai ba don haka nace "Sorry Sister, ban san maganar zata miki zafi ba, but am sorry to say, ba na iya ‘boye abin da ke cikin raina ne"


Duk wannan conversation d’in da muke yi, Aisha ba ta sa mana baki ba sai yanzu ne ta k’ar’bi zancen da cewa


 "Sisters ku bar wannan chapter d’in is not useful tun da shi yaya Faruk d’in bai fito ya fad’a ba, so plss dukkan ku kuyi hak’uri"


Dariya muka yi gaba d’ayan mu amma a raina na k’udurta k’ara nisanta duk wani alak’a da za ta had’a ni da yaya Faruk, duk da a yanzu ma ba abin da ke had’a ni dashi sai takurawa da fad’a.


Haka muka ci gaba da hirar mu kana muka canza akalar hirar tamu zuwa ga yadda jarabawar mu ta Waec da Neco take ta matso wa.


Misalin biyar da rabi muka mik’e dan tafiya gida saboda Dadi na hanyar shi ta koma wa gida.


Rako mu Aisha tayi har inda Driver d’in mu yake, sai da taga fitar mu daga gidan su sannan ta daina d’aga mana hannu.


Ko da muka isa gida, toilet na fad’a na watsa ruwa saboda yadda ba na shiri da zafi yayin da Anisa ta fad’a gado tana lumshe ido

San da na fito daga wankan, samun ta nayi tayi nisa a bacci.

Duka na kai mata a jikinta ina hararar ta, a firgice ta mik’e tana murza idanu alamar magagin bacci.

"Ke wai wace irin lazy ce, daga d’an fitar nan da muka yi shine kika wani baje kina bacci a zafin nan, kin wani saki baki sai kace wanda muka tafi a k’afa" nace da ita.


Amsa min tayi da cewa "in ban yi bacci ba me zan yi, kina ganin tun d’azun muka fita, ai dole ka gaji"


Simple English wears na sa, na juya ina kallon ta nace "yi ta barci ni kinga ma na bar maki d’akin" na fad’a ina fita daga d’akin.


Ko da na fito parlour ba kowa, zama nayi a d’aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake k’awata parloun.

Wani film naga ana haskawa a tashar Mbc Bollywood mai suna *Ramaiya vastavaiya*

Hankali na ne ya tafi kan film d’in saboda ina son indian film especially love film din su.


Yanda jarumin film d’in RIYA ya baro garin su ya tawo garin buduwarshi SONA duk da ba wani kud’i gare su ba, hasali ma ba a cikin gari suke zaune ba, ya taso a cikin daula, amma hakan bai dame shi ba illa ma hak’uri da ya dinga ba yayan Sona d’in akan ya barshi ya zauna tare dasu. 

Sharad’in da yayan Sons d'in ya gindaya ma jarumin ne ya ban mamaki,

Saboda yayan yace zai ware mai fegi d’aya na gona ya nome hatsi kuma zai dinga wanke shanu amma duk ya yarda.


Hmmm lallai na yarda india sun iya wahala akan so in ba haka ba yaushe zan yarda da wannan sharad’in.


Sai naji jarumin ya burge ni saboda ina so in ga masoya nason junan su tsakani da Allah.


Anisa ce tazo ta zauna kusa dani tana cewa "Fatimah! d’an ban labarin film d’in tun da ba a fara da ni ba’

Yamutsa fuska nayi ina cewa "pls Anisa don’t interrupt me, naga ke baki san yadda nake ji da lovers bane shi yasa zaki ce in baki labari alhalin ba gama film d’in nan aka yi ba".


Ta’be baki tayi tana cewa "ke idan kina kallo sai ki maida film kamar gaske, wai da kike zancen lover’s kina soyayya ne da zaki san mahimmancin so? Anisa ta tambaye ni.

Hararar ta nayi kana nace "in ma ina soyayyar ai kin fi kowa sani"

Murmushi Anisa tayi kana ta ce "irin kune Fatimah in kuna so baku iya son abu kad’an ba"

"Kan ki ake ji" na ba ta amsa a tak’aice.


Ba wanda ya sake Magana a tsakanin mu, muka maida hankalin mu kan allon talabijin d’in muka ci gaba da kallo.

Sai da film d’in ya k’are kana na juyo na kalli Anisa na ce "Sister dan Allah soyayyar Riya da Sona bai burge ki ba"

Kallon mamaki take min sannan tace "sun burge ni, sai aka yi yaya? Ta k’arashe zancen cikin zolaya.


Tsadadden murmushi kawai nayi ba tare da nace mata komai ba.

Haka muka ci gaba da hirar film d’in, kiran sallar magrib ne yasa muka mik’e muka nufi d’aki don ba da farali.

[3/23, 13:02] Maryam Ahmad: *MAKAUNIYAR SOYAYYA*💝💖💞




Post a Comment

0 Comments