TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Sanyi da zafi page 22

 💫 SANYI DA ZAFI 💫

✍🏻M SHAKUR


EPISODE 2️⃣2️⃣


Dasauri ta tashi tafice alwala tayo tashigo agurguje tasa hijabi ta tada salla tana sallamewa daganan kan daduman ta hango kafan Mama yanda suka kumbura suntum dawani irin sauri ta taso tazo wajen tace “innalillahi” dan yatsa tasa ya nitse akafan yanda jikin Rashida yahau rawa saida ta tsorata tace “Ma…..m” tama kasa magana tsabagen yanda zuciyanta ke bugawa saikuma ta juya a haukace zata fita daga dakin hijabin dake jikinta Mama takama hakan yasa da sauri tajuyo saikuma ta duka, ahankali Mama da bakinta baya motsi sosai tace “kaini nai fitsari nai alwala nai salla” gyadamata kai Rashida tayi da sauri tace “to Mama” tawuce tafita takai ruwa bayinsu sannan tadawo daukan Mama tayi ta dagata Mama ta tashi kafan natama nitsewa yake dasauri Rashida ta zaunar da ita tace “Mama  tsaya nakawo po kiyi fitsarin adaki namiki alwala” ta zaunar da ita tacire hijabin ta ijiye tafice taje chan hanyan bayi ta dauko po ta wanke tadawo dakin da taimakonta Mama tayi tai tsarki tadauko tafito tadawo ta goge wajen tass sannan tamata alwala ta daura ta kan dadduma dantai salla hannunta Mama takama tamata murmushi tace “relax babu abinda zai sameni daga hannunki inajin yanda zuciyanki ke bugawa” kallonta Rashida tayi idanunta sun cika da hawaye baki tabude zatai magana saita kasa tafashe da kuka tace “Mama wlh ina sonki Mama, Mama kene rayuwana gabaki daya Mama kiyakuri kiji sauki I know damuwana yasa BP ki yatashi bare naje nakira Musa yaron Baba Liman ya kaimu asibiti, Mama kiyafemin wlh wlh wlh bazan kara saki magana ba, Mama kina cewa nabari nabari kinji Mama wlh na rantse da Allah” dayan hannunta Mama takai saman fuskanta ta goge hawayen dasuka zubo ahankali Mama tace “come” matso da fuskanta tayi kiss Mama tamata a goshi muryanta chan kasa tace “I love you Rashida remember this always konai fushi dake bahar zuciyata bane kinji, stop crying I will be fine muje asibitin jeki kira Musa” tai maganan tana kara goge mata fuskan tass tashi Rashida tayi tadauki hijabinta tafice daga gidan, gidan Baba Liman tawuce a kofar gidama taganshi ganinta yasa kafin tamayi magana yace “lafiya?” Ahankali tace “Musa nazo kira yakaimu asibiti jikin Mama yatashi” ahankali Baba Liman yace “Subhanallahi Allah yabata lpy jeki kimtsa zan biyoshi muzo” juyawa tayi takoma gidan Mama nakan dadduma kallonta tayi da kafafun dasuke amike kaman kara kumbura suke every minute, wata yar jakarsu ta dauka ta shiga debama Mama su t-shirt da zani she’s a student doctor she know case din Mama is not something daza’a sallamesu gobe, tadau zanin gado wankakke da hijabi itama tasa yan kayanta dan daga wajen zata dinga zuwa department dinsu ta kwaso duka kudin dasuke dashi tashiga kirgawa gashi sun kashe kudi akasuwa ranan salla, Mama sai kallonta take yanda jikinta ke rawa kaman tamata kuka tadai daure bataso ma tanuna mata kalan azaban datakeji saisa take daurewa sunayen Allah akwai take kira abakinta, 85k sukedashi tadauki wayanta tanada about 51k a account, jakan makarantan da da komi keciki tagoya ta gungura jakan takawo tsakar gida daidai lokacin an buga gate dasauri ta gungura box din waje su kasa a keke ahankali tace “Musa zoka tayani mu dauketa bazata iya tafiya ba” daga Musa har Baba Liman biyota sukai ciki, Baba yakalli Mama da idanunta ke a kulle sabida tsananin ciwo yace “sannu da jikin Maman Rashida sannu” gyadamai kai tayi batare data bude idanubta ba, Baba Liman yace “kawomin ruwa Rashida namata addu’a” dan yana ganin Mama yasan ita kadai tasan metakeji, kawomai ruwa tayi da sauri karba yayi yayi addu’o’i ciki yabata yace “bata tasha ki shafa mata sauran akafa” karba tayi cike da tsantsan so tace “Mama sha Baba Liman yamiki addu’a” ahankali Mama tabude idanunta dasukai jazur tadaurasu kan Rashida tadan bude bakinta kadan samata ruwan Rashida tayi tasha kadan sannan ta tsiyaya a hannunta ta shafa mata a kafafun sannan ta ijiye a gefe tace “Musa zoka tayani” zuwa yayi atare suka daga Mama tsaye sannan suka dauketa chak suka fita da ita a keke suka sata dawowa ciki tayi tadan gyara ko’ina agurguje sannan tadauko key tafito ta kulle gidan da kofansu tazo tashiga keke tazauna Musa yatada keken Baba Liman yace “duk yanda ake ciki kinkirani, Allah baki lpy Maman Rashida” Ameen Rashida ta amsa Musa yaja keken itakuma tashiga kiran HOD nata wacce suke kira da Mrs Bugaje wacce take Doctor Mama, kusan a kira nabiyu ta daga sabida girkin salla yau yawon salla, tana dagawa tace “Rashida how are you sorry ina kitchen ne I missed call naki is everything fine”? Ahankali tace “Ma jikin Mama ne kafafunta sun kumbura sosai she’s in pain muna hanyan tafiya hospital” Dasauri Dr Bugaje tace “take her to A & E, she must be treated as emergency, bari I will call Dr Usama yau ina off but I will come once na gama girki for my family, don’t worry okay Maman ki will be fine” gyadamata kai Rashida tayi tana sharce hawayen dakeson zubomata daga idanu sannan ta katse wayan, suna kaiwa asibiti A & E tawuce ba’asa sun jira anything ba sabida Rashida is a Dr aka sa Mama agado akai ciki da ita Dr Usaman yazo Rashida takasa komi, all ciwon Mama tadamata da hankali yake but hakanan she’s getting a special vibe daga wannan kaman zaifi kowannne worst duba da kafafunta tana tsaye inda yagama dubata, sannan yajuyo yakalli Rashida Dr Usama yazo yace “follow me” binshi tayi ahankali har zuwa office nashi saikuma yajuyo ya kalleta dan murmushi kadan yamata cikeda hikima na manya yace “calm down Dr Rashida sit” tana tsaye tace “tell me meke damun Mamana Dr” Dr Bugaje warned him about telling her anything yabari saitazo hakan yasa yace “is just blood pressure ta yatashi” tana kallon kwayan idanunshi tace “tell me I can handle anything I know People living with HIV (PLHIV) dakuma HBP (High blood pressure) Hypertension sunada significantly high risk of cardiovascular events abubuwan daya danganci matsalan ciwon zuciya da mutuwa, which is thought to be due to a complex interplay of various factors including immune dysfunction, endothelial dysfunction, and inflammatory changes, nasan Mama na is at risk of coming down da stroke, heart attack, heart failure, kumburin jijiyoyin daukan jini na jikinta, taushewan vessels dake daukan jini daga zuciya zuwa jiki, kidney issues, high cholesterol, dakuma matsalolin iya numfashi” hijabinta takama tadaura daura kan fuskanta tana matse idanunta sosai dakeson suyi kuka tace “just tell me wanne daga ciki ke damun Mamana?” Wlh ayanda yaga Rashida shi kanshi saiyaji bazai iya gayamata ba gwara Mrs Bugaje tazo tagaya mata, dan murmushi yace “I actually called you nagaya miki yanayinki din nan zai saka Maman ki cikin tashin hankali, calm down Mrs Bugaje is coming wuce kitafi” wani irin kallo tama Dr saikuma ta tashi tawuce takoma A&E din tazauna kan kujeran dake gaban gadanso takalli Mama da idanunta ke kulle sai bakinta daketa motsi na la’ilaha illallah tanashan azaba takai hannunta takama tarike gam, kawai she’s just looking at Mamanta feeling pains she wish itane akan gadon kwance ta dauke ciwon instead of Mamanta, tana zaune awajen wayan jakanta yashiga kara na Mama cirowa tayi taga Liman dauka tayi takai kunne yace “Yaya jikin nata me akace Rashida?” Ahankali tace “Dr Bugaje nake jira tazo gatanan a hanya” anatse yace “kome ake ciki ki kirani Allah bata lpy” ahankali tace “Ameen ta katse wayan” ta ijiye.


Around 12 Mrs Bugaje tashigo office nata tafara zuwa ta ijiye bag nata da komi ta sanya lab coat tafito Babban mace ce dazata kai 50yrs haka office na Dr Usama taje tadan jima kafin sutaho ward din tare Rashida na zaune rikeda hannun Mama taji muryan Mrs Bugaje cikeda wasa irin na professional Doctors din nan tace “Mama yaya mukayi ni da ke?


Wat was our agreement? Dasauri Rashida ta juyo ta kalleta, handglove tashiga sawa tana murmushi tana kallon Mama kaman irin nothing serious din nan sannan tataho gaban gadon tace “open your eyes for me Mama kar Rashida tafashemin da kuka anan dukta damu” ahankali Mama tashiga bude idanunta da kyar tabude kadan sunyi jazur takalli Rashida dake tsaye gefen Mrs Bugaje tai zuru zuru bakaramin dadin hakan Mrs Bugaje tajiba tace “good job Mama, tell me meke damunki? Meya tadamiki da hankali haka dahar kika bata agreement namu na bazaki dinga tunani be?” Mrs Bugaje tai maganan tana duba kafafun Mama tana dubawa kumhurin yanzu ya wuce guiwowinta ma, cikin wani irin murya da baya fita Mama tace “Jummai, Jummai zata halakamin rayuwan yarinyana, Jummai nason halakamin yarinya” dasauri Rashida tai wajen takama hannunta da sauri tace “Mama dama abinda kiketa tunani kenan babu wacce zata iyamin komi I can defend myself kinji kidena tunanin” girgizakai Mama tayi hankalinta nawani irin tashi takalli Dr tace “Mrs Bugaje hide…….hide my daughter…..banson ta cutarmini da yarinya, nasan Jummai nasan bazata  kyaleta ba, Jummai Jummai, yarinyana, Rashi……Rashi….Rash….” Kawai sai Mama tafara yunkurowa tana wani irin nishi kaman zata mutu numfashi kaman yana gagaranta ma, Mrs Bugaje tai maza takama kafadarta tana maidata gado tace “Mama calm down calm down Mama I will hide Rashida babu abinda za’a ma yarinyarki” inaaa kaman ma Mama batasan inda kanta yakeba wani irin gasping breath Mama keyi dayasa Rashida kawai tadaura hannunwanta kan baki tana wani irin kuka tana kallon Mama dataga Mrs Bugaje da Dr Usama are trying to save at all cost Mama tasha ciwo but not irin wannan bata tabajinta this scared arayuwanta ba Mama is her biggest strength for the first time arayuwanta taji karfinta jarumtarta ma gaxawa she don’t even know ina kanta yake tadaiji an jijigata ance “Rashida!” Firgigit tadawo daidai Mrs Bugaje ne tace “come with me” dasauri takalli Mama dataga an sama oxygen a hanci wasu ma’aikata na gungurata zuwa wani wajen dabama tasani ba har office na Mrs Bugaje taje zaunar da ita Mrs Bugaje tayi akan kujera itama tazauna ganin yanda take kuma saita kara tashi tabude fridge na office din taciro cold water tamika mata tace “sha” ahankali Rashida tabude tadan kurbi kadan daidai lokacin Dr Usama na shigowa dawasu papers kusan guda 5, Mrs Bugaje ta karba tace “thank you Dr” gyadamata kai yayi yace “bari nakoma” yajuya yafice papers din Mrs Bugaje tasaka glass tana dubawa kusan 20min sannan ta ijiye tareda sauke glasses din takalli Rashida daketa kallonta she doesn’t even know what this small girl will do, ahankali tace “Rashida tun kina 100 level nasan how strong you are, bantaba ganin strong resilient student arayuwana like you ba wacce at a very young age shoulder responsibilities Mamanta da school da komi na rayuwansu, I supported you all through pull some strings na tabbatar kina gamawa da clinic dinki by 1PM wanda ba’a taba dagama student kafa haka ba, but I made it happen sabida I see you I see rayuwan dakikeyi a daughter like you deserve standing ovation, dan haka banson ki karaya this time fight this also kaman yanda you fought komi na baya kuka cigaba da rayuwa kinji Rashida” gyadamata kai Rashida tayi tana kallonta tana rike duka abubuwan datakeji azuciyanta, Dr Bugaje tace “BP Mama yakai level din da ko makiyina bazanmai fatan yakaiba, legs nata are starting to have stroke sabida blood vassel nata na zuwa wato Artherties nata are blocked jini baya fita da kyau, now dole mu mata procedure call……” ahankali Rashida tace “arherectomy!” Ijiyan zuciya Mrs Bugaje tasauke tace “yes, minimal invasive procedure ne dazamuyi dan muyi flushing buildup din daya cika vessel din sabida jini yasamu yawuce wajen freely, that is one” tadan sauke ijiyan zuciya tadauki paper gabanta tamika mata tace “ga result na express ECG da Dr Usama yasa aka mata can you read ECG da kyau?” Gyadamata kai Rashida tayi da sauri takarba tana karanta rhythm din, cikin wata kalan sassanyar murya Mrs Bugaje tace “I think zuciyan Mamanki is failing!” Wannan karan ijiye paper Rashida tayi agabanta tadaura hannunta saman idanunta ta matse hawaye still yana diddiga from side, wlh kawai dan ita Dr ne but she wants to cry for the girl, ahankali tace “matsalan HIV is yanacin kwayoyin garkuwan jiki, dazaran cuta tashigeka HIV yana cinye wayan nan garkuwan na jikinka da naturally suke fighting cuta kowace iri, it’s a long shot but banso kiyi loosing hope we can still save your Mom” har lokacin Rashida batasaki idanunta ba hancinta kawai yake motsi tip na hancin yayi jazur wani tsinkakkiyar majina na lekowa daga hancin, ahankali Mrs Bugaje tace “Rashida” dago kanta tayi tana sakin idanunta cikin muryanta dahar yakoma kaman na me mura tace “naam” wani paper again Mrs Bugaje tabata tace “idan kinaso muyi treatment nata ayi procedure sannan ai connecting Mama da machine dazai taimaki heart dinta dake failing sannan ayi tackling BP da stroke din, to this is just a rough estimate na kudin dakike bugata rough estimate dan zaifi haka anything heart magungunan shi da treatment nashi is expensive, plus oxygen da yanzu muka sata akai dazai dinga tayata breathing you need about 2.5M!” Kallon list din take kawai, ta ina zata sami kalan kudin nan? Wani aiki zatayi tasami kudin nan just today sabida afarama Mama treatment sai alokacin kawai taji kuka yazomata kawai tafashe da kuka da karfin gaske tawani zube kasa daga jikin kujera ta dunkule paper a hannunta tana kuka sosai tashi Mrs Bugaje tayi ta zagayo ta duka ahankali agabanta idanunta sunyi jaaa tadafata tace “I know bakida this kind of money bakida hanyan samunsu Rashida it’s okay ya isa kukan we will not let Mama die” wani irin kallon Mrs Bugaje take tana kuka, Mrs Bugaje tace “Rashida I’m a family woman kwanan nan nama yarana dake UK registration na school wlh banda kudi but I will give you 200k sauran kudin kuma akwai this student loan da student ke iya applying idan kafara internship duk albashinka za’a dinga karba as payment for the loan, but matsalan shine CMD kadai ke signing and approving but baya gari dole mujira yadawo which bamuda lokacin the next option is student doctors and other people’s help seek for donation for Maman ki yawanci an sanki ansan situation na Mamanki they will help you hopefully zamu iya tashi da something, in the meantime kudin nan dazan baki dayan chanjin dake hannunki jeki sayi necessary magani dasu drip da ake bukata sabida afara ma Mama treatment kinji and pay for oxygen also dan na this hour kawai zasu bata idan baku biyaba bazasu bata again ba, Stop crying, remember na gayamiki you have to be strong ke kadai Mamanki keda shi, kene kadai zaki iya kula da ita, stand up dagata Mrs Bugaje tayi tace “Allah baya hada bawa da abinda yafi karfinshi kinji” gyadamata kai Rashida tayi takama hijabinta ta goge fuskanta tass, jakanta Mrs Bugaje tadauka ta bude taciro bandır na 100k guda biyu wanda sabida ita ta taho dashi tabata tasan basu dashi cus tun awaya Dr Usama yagaya mata komi tace “take” tsayawa tayi tana kallon kudin Allahu Akbar tunda tafara girma tafara aiki bata taba accepting wani kudi daza’a bata sabida Mama ba saidai Mama ta amsa yau gashi ita ake bama kudin taimako zata karba hannunta tamika dahar rawa suke ta amsa tama kasa godiya sabida shock Mrs Bugaje ta dauki precribtion sheet dawasu papers tabata tace “jeki sayo magungunan sannan kibiya kudin ECG da aka mata ki kowamin a ICU” gyadama Mrs Bugaje kai tayi tafito tafiya kawai take taje ta bibbiya kudin ECG tasayo magunguna dasu drip tabiya kudin oxygen na kwana uku dan per hour ake biya shi, da kudin da Mrs bugaje taba tada kudin account dinta da na hannunta duka sun kare sai naira dari biyar daya rage mata this is duka kudinta gaba da baya, dawowa tayi ta tsaya gaban ICU mrs bugaje tafito ta amsa tace “now go round ask for help from this Doctors kinji” gyadamata kai tayi tajuya batamasan taya zata faraba stufent Dr dinsu duk sunje hutun salla public holiday wayanta ta dauka tasami waje ta zauna tai shiru yau ne rana na farko datai realizing good human relation ma wani abu ne arayuwa mu’amala me kyau yanada ranan sa, duk yanda kakaiga you don’t need anybody las las you still need everybody saidai in Allah bai jarabceka dawani abu ba, yanzu kotai magana a group ma yan class dinsu zasu taimaketa? Yawanci tayi fada dasu, yawanci bata kulasu kosun kulata, daurewa tayi tashiga typing komi na neman taimako Mamanta na critical condition tana neman 2.5M ta tura group din da acct details nata bini bini tana duba info kusun gani taga duk sun gani Layla ma fitowa tayi tafara hira a group din babu ko Allah sawake few friends nata suka shigo suka biyemata suna hira suna turo emojis na dariya.




Post a Comment

0 Comments