TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Buri Daya page 16

 *_Mamuhgee16_*

Maganar yaji kamar tafara isarsa ya datse Kiran tareda sakin qaramin tsaki Yana jefa wayar kan katifarsa sbd jin yafarajin haushin komaima Dan sai yanzu ne ransa ke baci da alamarin danshi bai zata kawun da gaske yakeba ya dauka duk cikin borinsa ne dayakeyi idan yatashi abinsa yanzu Banda raini uban me wannan yarinyar zatayi a dakinsa Banda ganin makwancinsa mitssss.


Gaban wardrobe ya nufa ya tsaya tareda zare shirt din jikinsa take qaqqarfan surarsa qirjinsa ya bayyana wasu irin damtsen hannuwansa dake murde Suka kayar Mata da gaba tasake cusa kanta cikin qafarta tana sakeyi kamar tayi bacci.


Jin bai tareda gajiya ko kadan yasa baiyi tunanin wankaba sbd dare yayi Dan kuwa tunda yafita suna wata ma'aikatar kudi tareda dikko wadda yabude a boye ana buga masa kudin bugi na billions of naira.


Acan suke duk yinin ranar sbd ma 'aikatar can take cikin daji Kuma dama duk sukaje yaransane ke zagaye dajin da mugayen makamai suna gadi harsai sun fito shiyasa dikko ke qara jin Zaki Dan kuwa tsaronda Zaki da yaransa ke basa ko hukuma dayake sakarwa manyan daloli basa basa wannan tsaron gashi Sam basa tsoro duk wani Abu dazai Sha gabansu fitt suke Gama masa aiki.


Kai tsaye katifa ya nufa yahau ya kwanta tareda rufe jikinsa da bargo ya lumshe fararen idanuwansa ahankali Yana sauke numfashi.


Jin shiru bayan Yan mintuna saita dago kanta ahankali ta juyo ta kallesa taga yayi bacci batasan lokacinda ta lumshe manyan idanuwanta ba tareda sakin ajiyar zuciya sbd tsoronta daya 'dan rage.


Zamewa tayi tayi kwanciyarta a qasan tareda sake Jan hijabin jikinta ta rufe qafafunta sbd 'dan sanyi da akeyi.


Ahankali tayi baccinta bayan tayi addua saidai kusan baccin nata rabi da Rabi ne saiyi takeyi tana zabura sbd tsananin tsoro data sawa kanta na kartayi bacci sosai tayi wani laifin Bata saniba.


Asubar farko ya farka kamar ko yaushe ya tashi zaune kan katifa tsawon mintuna yagama jinsa yayi daidai kafin ya zuro qafafunsa zai tashi yaji ya taka mutum.


Cikin wani irin fitinannen tsoro da firgita ta zabura jin mutum ya takata cikin bacci 

Shima cikeda mamaki ya lalaubo wuqa qarqashin pillonsa yakai hannu inda yaji mutum din zai damqo koma waye cikin Rashin sa'a ita Kuma ta zaburo kenan hannunsa ya sauka kan qirjinta gashi Bata kwana Sam da breezier.


Wani irin shock sukaji lokaci daya tayi baya da qarfi cikin tsananin firgici tana neman hanyar guduwa jikin na wani irin mugun rawa sbd tsananin firgicewar datayi Sam kamar kb ne takejin yadawo ta manta a inda take.


Jin tana neman qofa cikin duhu a firgice zata fita yasa yayi saurin fizgota ta dawo jikinsa Dan shima farko Sam ya manta da akwai wata a dakin ya dauka wanine yashigo masa.


Sosai jikinta ke rawa tana fixge fixge tana bude baki yagane ta fice hayyacinta sbd tsananin tsoro da firgita Wanda yawanci indai antaba attempting rape naka to kana iya shiga irin wannan firgicin wasu lokutan,


Riqota yayi da kyau tareda girgizata Amma Sam ta fita hayyacinta da qarfi yasake jijjiga tareda kiran sunanta akaro na farko rayuwarsa tun girmansa sai kawai gani yayi ta sulale ajikinsa some.


What?yafada cikin 'dan takaici da bacin Rai Yana qaramin tsoki kafin yasake jijjigata yaga ta sake sakemasa ajiki.


Saida yakuma sakin qaramin tsaki kafin ya dauketa gaba 'dayanta ya kwantar a katifar kafin ya lalubi wayarsa ya kunnu fitila ya haskata.


Gabaki daya rigarta a cinyoyinta take shi hijab dinta kuwa gurin furgicinta ya cire,


Dauke Kai yayi tareda sake sakin siririn tsakin takaicin wannan kayan takaicin da aka kawo masa.


Juyawarsa yayi ya fice Dan zuwa alawalar zuwa sallar asuba daza'a tayar lokacin.


Cikin gidan yashiga ya dauki buta yacika da ruwa ya nufi bayi.


Yana fitowa aka dallesa da fitila Mai shegen haske.


Kallon daya kawun daya kasa bacci yayi masa ya dauke Kai ganin Babu riga ajikinsa sai kawai yaji kamar yaje masallaci ya zauna yayita rusa kuka ana ja masa ayoyin alqur'ani kozaiji sanyin abinda yakeji aransa.


Shikuwa ko kallon inda kawun yake baiyiba yayi alwalarsa ya wuce Dan yasan Sarai ubanda kawun yafito tsinta da asubar farin sbd ko sallar asuba kawun bai cika fitawoba Amma yanzu saboda tsabar yayi abin yasha masa Kai shine yafito ga dukkanin alama ko bacci baisamu yiba aikuwa wlh inda hakane daga yanzu yaringa sashi fitowar asuba Dole Dan kuwa baisake fitowa da riga da asuba saiya saka masa 'dan qaramin hawan jini.


Dakin yashigo ya saka doguwar jallabiya fara qal ta Sallah ya fice zuwa masallaci batareda yakalli ko gefen katifarba.


A masallaci tunda dattiya yashigo yake hararar gefenda zakin yake Yana babbata Rai har aka fito.


Koda yafito masallaci Saida ya tsaya qoafar gida ya kwankwasa qaton shagonda yaransa ke cike taf suna bacci yace su tashi suyi sallah.


Yana shiga dakin tana bude idanuwanta ahankali.


Kallo daya tayi masa ta tuno abinda yafaru ta miqe da sauri tareda kallon jikinta taga batada hijab gashi yariga yashigo dakin sai kawai tayi qasa da Kai tafara tsiyayo hawaye.


Wata irin tsawa ya daka Mata cikin Isa yace"


Zaki tashi kiyi sallah ne ko saina karya wuyanki a gurin.


Da sauri ta zabura ya sauko katifar jikinta na mugun rawa kanta a qasa  ko hijab Bata tsaya daukaba ta fito alwala gashi lokacin gari yayi haske sosai.


Da babanta tafara cin karo a tsakar gidan ya kasa ya tsare a qofar dakinsa yayi shimfida duk sanyin safiyar bayaji sai radio daya kunna yakai murya qololuwa duk ya Hana mutan gidan bacci da labaran bbc Wanda shima ko zaa kashesa a gurin baisan me suke fadaba and signal din Babu kyau duk hayaniyar zizar radio ne.


Kallo daya yamata yayi saurin dauke Kai Yana qarawa radionsa murya kansa a sama alamar duk ubanda ya tabosa alokacin masifarsa zai sauke masa.


Sum sum ta qaraso ta dauki buta ta Debi ruwa ta shige bayi ko kallon baban takasayi sbd tsoro da kunya.


Tun acikin bayin tayo alwalarta shiyasa ko data fito butar kawai ta aje ta wuce yabi bayanta da muguwar harara.


Da sallama muryarta na rawa ta shiga dakin 

Amatuqar gigice tayi saurin sauke idonta akansa jikinta da zuciyarta na sake daukar rawa har qafafunta Saida Suka fara hardewa ganin dukkanin qaqqarfan jikinsa a bayyane.


Push-up yakeyi na motsa jikin safe daya Saba safiyar kowace Rana

Dagashi sai three quarter na wandon Adidas 

Bayansa dake fari sol sai kyallin 'yan qananun zufa yakeyi.


Rakubewa gefe tayi tana matse jikinta harta qarasa gurinda hijabinta yake ta dauka tasaka ta sake matsawa gefe ta tayarda sallah.


Harta gama sallar bai gamaba saima wasu qarafuna masu nauyi dataga ya dauko Yana dagawa a hannunsa.


Miqewa tayi a hankali ta nufi qofa zata fita kamar daga sama taji muryarsa yace"


Idan kika bude qofar dakin nan saina karya wainnan shegun qafafun naki.


Cak ta tsaya tsoronta na qaruwa ta dawo batareda ta dago ta kalli inda yakeba Takoma inda ta kwanta jiya ta zauna tareda kwantarda kanta kan gwiwoyinta gabanta na tsananta faduwa.



Duk wani motsa jikinsa Saida ya gama zuwa lokacin ya hada zufa sosai sai kawai ya dauki towel da brush ya fito.


Kai tsaye cikin gidan yashiga har lokacin Dattiya na zaune sai iya data fito tana Shanya garinta dabai Gama bushewaba jiya.


Wani mugun kallo dattiya yabi jikin zakin dake tsiyayar zufa ga farar fatarsa ta asalin Igbo sai daukar ido takeyi musamman shi zakin da Sam baisan wahalaba.


Ji yayi kamar idonsa zai kawo ruwan baqin ciki saikuma ya dake Yana tsuke fuska aransa Yana cewa"


Wlh wannan basamuden kashemin yarinya zaiyi da sunan aure tunda ba wani qwari daukar lalurarsa tayiba Amma Koma meyene laifin idi ne dabai basa shawarar qin hada wannan aure ba.


Kashe radionsa yayi ya miqe ya fice a fusace


Ko gaisuwarda zakin yamasa ta can qasan maqoshi bai amsaba.


Ruwan brush ya Diba yafito qofar gida inda masarautarsa ke cike da yaransa sunata faman gyara makamansu.


Nan yazo ya zauna nanu ya qaraso Yana gaishesa sbd yanxu shine mafi kusansa.


Sama sama yake 'dan fira da yaransa sbd har cikin ransa yakeson dukkanin yaransa dasuke qarqashin sa suma shiyasa suke matuqar qaunarsa da kiyaye masa Dan duk cikinsu Babu Wanda ba 'dan gani kashenin zakin ba.


Ita kuwa daga zaune tasake bingirewa da wani sabon baccin safenda rabonta dashi harta manta batamasan ya dadin baccin safen yakeba tunda batayi.


Tana bacci yashigo haryayo wanka yazo ya shirya ya fita.


Cikin bacci taji ana buga qofar dakin ta bude ido ahankali ta tashi zaune da sauri taji ansake buga qofar ta miqe tareda gyara hijabinta ta nufi qofar ta bude.


Nanu tagani tsaye tayi saurin sauke Kai cikeda tsananin kunya.


Cikin sakewar fuska da girmamawa yace"


Gashi akace akawo Miki.


Hannunta na rawa ta miqa ta karba har lokacin takasa dagowa.


Juyawa yayi ya fice itakuma takoma ciki ta aje ledar ta dauki brush tayi cikin gida neman Maclean wurin zainab.


Rana ta fito sosai shiyasa kodatashiga da zainab da iya duk suna tsakar gidan zainab na waya iya kuwa tanata ayukan sana'arta tana hadawa da mitar Rashin fitowar nadiyar ta tayata ayyuka.


Aje waya zainab tayi da sauri tayo gurin nadiyar sukai cikin daki tana tsokanarta akaro na farko saita samu kanta dayin murmushi Wanda yasa zainab sakin ihu da qarfi tana tsalle.


Abin saiya sake saka Nadiya murmushi ta qarasa da sauri ta dibi Maclean din ta fito zainab din na sake biyota.


Brush tayi tana gamawa taxo gurin iya talatu tai Mata alamar gaisuwa 


Iya talatu ta bita da ido ganin sai sunkuyar dakai takeyi itama sai abin yabata dariya tace"


Nadiya karma ki kuskura kice wannan soke soken kan zakimin na kunya acikin gidan nan jeki ki karya kixo ga ayyuka nan sunyi yawa.


Tareda zainab Suka koma dakin ta ajiye brush dinta kafin ta juyo zainab ta bude ledarda Nanu yakawo tana zuba wani ihun jin dadi tana cewa"


Wayyo wlh har yunwata ta qaru

Yaya zakine ya siyomiki wannan dadin da safiyar fari.


Take away ne guda biyu 

Na chips da kwai sai na source din hanta dataji cabbage.

#MAMUH*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*




Post a Comment

0 Comments