TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Babu so page 51

    *_❤‍🔥BABU SO....!!❤‍🔥_*

                 _(Miya kawo kishi?)_




              *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*


https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718



*_51_*




.........Kwance ta kai tana faman tuttura lips gaba, a zuciyarya kam babu abinda take sai masifa, sai dai babu damar yi a fili. Tashi tai zaune zaram kamar wadda aka tsikara tana kallonsa, ganin ya koma ya zauna gaban laptop ɗinsa.

     “Yaya MM?”.

Shiru ya mata yaƙi ya amsawa, amma tsabar bazata iya haƙuri ba saita cigaba da maganarta kamar sharetan da yay bai zafeta ba.

           “Amma dai can ɗakin zaka koma ka kwana kamar ranar idan ka kammala aikin ko?”.

      Banza yay mata nanma, takaicinta ya bayyana har tana jin tuƙuƙimsa a maƙoshi, harara ta dallama bayansa, cikin jin zafi ta fara ɗaukar pillows ɗin gadon ɗaya bayan ɗaya ta jera a tsakkiyar gadon tun daga farko har ƙarshe tana muy-muy da baki alamar magana take. Ƙarshen gadon ta koma da salon kwanciyar kai da ƙafa ta kwanta badan zuciyarta ta bata nutsuwar haƙurin sake kwanciya ɗaki ɗaya, gado ɗaya da shi ba. Dan tayi alƙawarin kafin cikar wata ukunnan bazata taɓa bari ya samu nasara a kanta ba.

    Duk abinda take yana jin motse-motsenta sai dai bai juyi ba, aikinsa kawai yake badan yana fahimtar wasu abubuwan ba. Bayan shuɗewar kusan mintuna arba'in da biyar yaji shiru ta daina sukur-sukur da motse-motsen da takeyi, kaɗan ya juyo ya kalleta, a can ƙarshen gado take ƙudindine da bargo ta juya masa baya. Ya maida kallonsa akan pillows ɗin data jera, kansa ya girgiza kaɗan wani ɗan guntun murmushi na suɓuce masa. Hankalimsa ya maida ga aikinsa, wanda ya sake jansa kusan awa guda, ganin two ta kusa ya ga hamma yanata jerawa ya sashi tattara komai ya ajiye. Alwala yayo, ya shimfiɗa abin salla, sallar nafila ya gabatar raka'a biyu, yay addu'oi dan barci sai faman rinjayar idonsa yakeyi. Bai cire shingen datai musu ba yay kwanciyarsa bayan yayi addu'oi. Babu jimawa barci yay awan gaba da shi shima.

     Duk da ta rigashi kwanciya shine ya rigata farkawa, ya yunƙura da ƙyar ya tashi bayan karanta addu'ar barci, shanyayyun idanunsa da har yanzu barci ke cike a cikinsu ya zuba mata ta ɗan hasken lamp dake a ɗakin kaɗai. Yanzu kam ta juyo fuskarta, sai dai tana a inda take kwance tun jiya. Sai da yayo alwala sannan ya tasheta, a ranta ALLAH-ALLAH take ya fice ta sama ƙofarta key, sai da yaga ta shiga toilet sannan ya fice zuwa sashen Fadwa itama ya tashesu. Koda ta fito kai tsaye ƙofar ta nufa, amma wayam babu keys ɗin alamar ya zare. Ta dallama ƙofar harara da murguɗa baki.

       Sai da gari ya ɗanyi sha ya shigo, har sannan tana zaune tana azkar. Batare da ta yarda ta kallesa ba tace masa ina kwana. A taƙaice ya amsa yana kaiwa kwance dan barci ne fal idanunsa. Jin ya fara sauke numfashi ta ɗan juya ta kallesa, ya juya mata baya, amma ta fahimci barci ne ya ɗauke sa. Itama dai ƙarasa azkar ɗin tai ta koma ta kwanta tunda ba wani aikine da ita ba.....


       ★★★★


  Tsabar yanda ta kwana da abubuwa masu yawan gaske a ranta tana idar da salla sashen Gwaggo ta nufa. Burinta kafin su Daddy daga massallaci su shigo ta shige, dan ita yanzu ko ɗakinsa bata zuwa, shi kuma yaƙi ce mata komai akan hakan. Gwaggo na zaune tana lazimi Mommy ta shigo, kallonta kawai take baki a sage, sai dai kuma batai mamaki ba musamman akan sanin halin rashin haƙuri irin nata. Mommy ta gaisheta kamar yanda ta saba, damuwa ƙarara akan fuskarta.

        “Wai Nafisa kuwa anya hankalinki na jikinki? Wace irin rayuwace wannan duk kin firgita kanki akan abinda bai taka kara ya karya ba. Da alama yau ko barcin kirki ma bakiyi ba ko?”.

    “Humm Gwaggo ina naga ta barci nikam, kema kin san babu wani barci dazan iya a wannan halin. Ki duba fa kiga Shareff ya ɗauke ƙafa gaba ɗaya a gidan nan tamkar ya manta dani a raye, ko'a waya baya kirana tumma yanzu kenan za'a rabani da yarona. Maheer ma yaƙi zuwa duk da shi nasa bai cika damuna ba nasan fushin banza da wofi ya sakama ransa bayan ni gata naima rayuwarsa. Gwaggo taya zanyi barci a wannan yanayin to? Na kasa gane kan Shareff sam. Son yarinyar nan yake da yake gudun haɗuwarmu ko yaya ne?”.

        Ƴar dariya Gwaggo tai. “Banda abin Nafisa halin namiji kuma kika manta! Shi yanzu Mustapha a wannan gaɓar bake kaɗai ba kowama zai iya rasa gane kansa ai.....”

    “Gwaggo to saboda mi? Ni wlhy kaina duk ya kulle”.

       “Uhhm haka dai, tunda kin ruɗa kanki ba dole kanki ya kulle ba. Kina tunanin duk ƙin da yakema yarinyar zai kawo ido ya saka mata ne a gidansa”.

    Kaɗan ya rage Mommy ta haɗiye harshenta. Cikin in ina da shiga ruɗani take magana. “Gwaggo wai kina nufin ya kwanta da yarinyar nan?”.

          “Har kuwa ki ganta da ciki nan da watanni kaɗan”.

“Aiki dana tsine masa”.

    “Ki tsine masa! Kinga Usman da Ai'sha sunci riba a kammu kenan. Ki kiyayi harshenki da ambaton tsinuwa ya ƴaƴanki saboda kawai ranki ya ɓaci. Ki koyi nutsuwa a duk lokacin da kikaci karo da abinda bai miki ba. Nafisa idan kikai sakaci k da kanki zaki tabbatar da nasarar maƙiyanki akan ƴaƴanki. Yanzu dakin kwantar da hankalinki tun bayan da akai rikicin farko akan auren nan da yanzu mun kai ga mafita. Mustapha da kike gani hatsabibin yaro ne mai shegen zurfin cikin tsiya da wayo. Gaggawa a al'amarinsa ba shi bane mafita, kuma tsananinki ba shi bane zaisa muci nasarar rabashi da yarinyar cikin sauƙi, musamman da matarsa dama ta kasance shashasha, dan nikam sai yanzu nake dana sanin yin wannan haɗin nasu”.

       Da mamaki Mommy tace, “Wani abun ya faru ne Gwaggo?”.

    “Nafisa ai shiyyasa nace ke ɗin ruɗaɗɗiyar mutum ce, yo banda haka halin Fadwa har wani ɓoyayye ne da zaki kasa ganewa. Duk wani baƙin halin Halima shine tare da ƴarta, kodan shi Mustaphan bamai yawan magana bane da kullum zai zauna faɗa miki matsalarta shiyyasa kike kasa fahimtar halinta?”

           “Gwaggo bawai ban fahimci wasu abubuwa bane, dan ni kaina yawan kirana da takeyi kullum tana kawomin ƙararsa ya mata kaza ya mata kaza yana cimun rai, sannan Aysha ta faɗa min ko abinci sai ta gadama takeyi a gidan sai dai mai-aiki, Shareff da ko'a gidan nan baicin abincin masu aiki”.

      “Humm zatayi abinda yafi haka ni na sani. Amma karki damu zamu fara gyara mata zama. Yanzu abinda nake so da ke ki sassautama zuciyarki komai, ki nunama su Muhammadu komai ya wuce kin ajiye makamanki, shima ɗin Mustapha ki kirashi a waya ya sameki ki nuna masa komai ya wuce. Mu kuma daga nan zamu fara namu yaƙin, badai wata uku shi Ibrahim ya bata ba, to duk yanda zamuyi sai munyi nanda wata ukun tabar gidan, babban fata na dai ace bai taɓata ba. Kai koda ya taɓatan ma ba komai”.

     “Gara dai karya taɓatan Gwaggo, danni bana fatan haɗa kowace sabga da Usman balle shegiyar matarsa”.

    Ƴar dariya kawai Gwaggo tayi da faɗin, “To ALLAH yasa haka. Yanzu dai inaga kima Sakina magana yau taje mana gidan taga yaya zaman nasu yake”. 

      “Wannan shawaran yayi gwaggo, bara na sanar mata yanzun nan kuwa”.

     Daga haka suka cigaba da tattaunawa kuma har gari yay haske sannan Mommy ta koma sashenta zuciyarta na ɗan sassauta nauyin da tai kwana biyu. Masu aikinta ta bama umarnin haɗa abincin Daddy. Duk da sun ɗanji mamaki babu wanda yace komai tunda ba huruminsu bane, itako ta shige domin shiryawa tunda dama girkin tane.....


        ★★


    Kusan ƙarfe takwas ta farka. Ganin har yanzu shi barcinsa yake hankali kwance sai ta koma ɗayan ɗakin tai wanka ta shirya a can. Ganin har lokacin baida alamar tashi saita nufi falo ta gyara duk da ba wani datti bane ba. Yunwa takeji matuƙa, dan haka ta haɗa tea ta dawo falon tai zaman sha tana buga game a waya. Koda ta kammala a falon ta cigaba da zama tana game ɗin har kusan ƙarfe tara. 

     “Wai mutumin nan bazai tashi bane? Koya manta yau monday akwai office?”.

   Ta faɗa tana kallon agogon dake falon, miƙewa tai kanta tsaye ta nufi bedroom ɗin. Mamaki ya ƙara kamata ganin har yanzu dai a kwance yake, (Lallai babu lafiya) ta ayyana a ranta tana ƙarasawa gaban gadon, dan ita dai a sanin datai masa na rashin wasa da aiki inda ƙalau yake babu yanda za'ai yakai yanzun yana barci. Fuskarsa ta ɗan tsurama ido dan kwance yake a rigingine. Lumshe idanu tai da sake buɗewa a kansa, ita shaida ce Shareff ƙyaƙyƙyawa ne, ƙyawu irin na masu kwarjini da cikar haiba bawai na fitar hankali ba. ALLAH ya bashi dukkan kamala ta cikakken mutum tamkar wani babba. Baida yawan hayaniya, sannan bai da yawan fara'a. Mutane da yawa kance mata yanada sauƙin kai da daɗin zama, sai dai ita har yanzu bata ganinsu tattare da shi, dan zata iya bugar ƙirji tace babu wadda yatsana a rayuwarsa ƙila sama da ita, ta rasa minene laifinta a gareshi. Ta taɓe baki da juya idonta, a fili ta furta “Yo karya soni ɗin nima ai ba son sa nake ba humhh”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki ta juya zata bar wajen a bazata taji an riƙota. A firgice ta juyo dan ta tsorata, sosai idanunta suka firfito waje dan batai zato ko tsammanin shi ɗin bane tunda taga barci yake. Idanunsa ya ɗan rufe ya sake buɗewa a kanta tare da fisgota ta faɗo kansa.....

      “Wayyo Yaya zaka karyani ne?”.

Komai baice mata ba, sai dai kafeta da idanunsa dake a yanayin wanda ya tashi barci. Ƙoƙarin son zame jikinta take a nasa amma ya hana hakan ta hanyar ɗora hanunsa a bayanta ya tallafeta da ƙyar a saman jikinsa, fuskarta dake a gab da tashi ta kautar gefe saboda yanda yake kallonta tsigar jikinta har tashi take. Ɗayan hanunsa yasa ya maido fuskar tata a saitin tasa har yana jin saukar numfashinta. 

       “Kina yin miye tsaye a kaina?”.

   Idanunta ta waro sosai, sai kuma ta tura baki da ƙara ƙoƙarin janye fuskarta dan bazata iya jurar kallonsa ba. “Ni to mizanyi? Kawai nazo tadaka ne dan naga lokacin office yana wucewa”.

      Agogon dake ɗakin ya ɗan kalla tare da maido idanunsa a kanta lokaci guda. “Dama ango na zuwa office ne?”.

    Sosai ta yatsine fuska tamkar wadda aka faɗama wani mugun abu. sai kuma ta taɓe baki da sake yunƙurin barin jikin nasa........✍




Post a Comment

0 Comments