TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Gimbiya Hakima page 17-18

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»

         *GIMBIYA HAKIMA* 

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»




 *🌎MANAZARTA* 

 *WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–Š️


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»``` 

________________________________




  _STORY AND WRITING_ _BY_ 


    _Jameelah jameey πŸ–‹_ 


    *(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*  


   





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*



 _Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._ 


 ```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR 

BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




17&18





Yau karfe biyu Gimbiya Hakima take da lectures sai da su Lantana suka ji kamar su fasa ihu... 




"Lantana baki da hankali?  Wai dan Allah har sai yaushe zakiyi hankali?ke duk yanda aka nuna maki baki gane sai kace mai kwakwalwar kifi.. 




"Allah ya huci zuciyarki, wallahi akasi ne aka samu.. 



"Akasi! Akasi kikace Lantana, to yau zan nuna maki ni Hakima ban yarda da wannan kalma mai suna akashi ba.. 



"Allah ya taimakeki, Ina neman sausauci, insha Allah banzan sa..... Tas!! Kake ji Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana nuna ta da yatsa sannan ta fara cewa, "ke wata kallar kidahuma ce? Inba kina kidahuma ba daga goge riga saboda sakarci irin naki kinbi ki toya, ni dallah can tashi kibani waje tsohuwar banza... 



"Godiya nike Allah yaja da tsawanci kwana uwar marayu, nan Inna Lantana taja yan kafafunta ta tafi, tana hawaye saboda tunda take da Gimbiya Hakima bata taba yi mata wani abu da taji haushi kalar wanna, dan ko ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha Mari a wajen Gimbiya Hakima Amman yau taji haushin abun sosai.. 




"Azima, "Naam Allah ya taimakeki, "tashi ki sake goge man takalmin nan, dan nasan wacer mahaukaciyar hauka kawai tayi man.. 




"Angama ranki yadad'e, nan Azima ta sake goge ma Gimbiya Hakima takalmi, duk ba abunda takalmin yayi, Amman haka ta sake goge mata shi.. 




Gimbiya Hakima ba ta tashi tafiya makaranta ba sai karfe daya dai-dai gashi tana da dan nisa tsaka ninta da makaranta gashi lecture din karfe biyu gareta.. 



"Bala kayi sauri bansan na makara, "angama Gimbiya, haka Gimbiya haka ta kama azalzalar Bala yayi sauri, haka suka samu suka isa, karfe biyu saura suka yi parking a bakin depertiment dinsu.. 





Sauri sauri Gimbiya Hakima take saboda hango Yarima Hakim da tayi yana tafiya cikin natsuwa yana shirin shiga lecture.. 




Duk tasan yana ganinta hakan bai yana Gimbiya Hakima sauri ba, ita acewarta sauri take, Amman Yarima Hakim gani yake kamar bata san taka kasa, dan danan ranshi ya baci sosai Amman zai barta ta shiga dan shi kad'a yasan abunda zaiyi mata.. 



Gimbiya Hakima na shiga taje wajen Maryam ta zauna, gaisawa kawai suka yi Yarima Hakim ya shigo.. 




Kowa ya natsu ya maida hankalinshi waje Hakim, dan suna jin dadin koyawarshi, dan prof Hakim ba daga baya ba wajen iya lesson, dan haka shiyasa kowa ya kama kanshi ya naba'a dan ya samu abunda ya samu.. 




Baki daya hankalin Gimbiya Hakima yana kan lesson din da Hakim yake dan harga Allah taji dadin koyawarshi dan ba karamin ganewa take ba.. 




"Hey stand up yayi pointing din Gimbiya Hakima, Amman sai tayi kamar ba da ita yake ba, dan ta lura malamin nan yana da san raini ita kuma ba daukar raini zata yi ba... 




"Ke! Ke wata kallar kidahuma ce? KO baki jin turanci? Babanki yayi asarar kudin registration, dallah can stand up idiot nonsense stupid girl.. 




Haka Gimbiya Hakima ta mike ji take kamar ta tsiga kasa ta nitse dan kunya, dan ba karamin kunya taji ba ta yanda taga kowa a ajin ita yake kallo kamar wanda tati sata... 




Sai da Hakim yayi kusan minti ashirin sanan yayi time din Hakima... 



Duk tayi laushi ta gaji, Amman ta daure dan bata san yan ajin suga gazawarta.. 



Questions masu wahala Hakim ya fara jefo ma Gimbiya Hakima, Amman ga mamakinshi yaga tana bashi amsa, sai kawai yayi mata wani question nan ta kasa bashi nan yace mata... 



 "Get out of my class, nan Hakima ta tashi ta wuce tazo dai dai fita Hakim yace meet me in my office, classrest ka anshin man matrix number dinta ka kawo man office dina. 



"Ok sir, class captain yace, sannan ya cigaba da yi masu lecture, bayan ya gama ya Kama gabanshi.. 



Ita ko Gimbiya Hakima direct gida ta wuce ranta bace.. 



"Allah ya taimakeki, Allah yasa lafiya dan ban saba ganin uwargijiyata cikin s

Wannan yana yin ba? 




"Azima so nike na san waye shi, waye ubanshi a cikin Nigeria, da har zai ci man mutunci a cikin mutane Azima? 




"Tabbas ya tabka babban kuskure, dan bai san dawa yake magana ba shiyasa da baiyi maki abunda ya san ranki zai baci ba ranki ya dade.... 




"Kyale shi Azima, yanda yasa na zubda hawaye ta dalilin shi, shima sai na sashi zubda hawaye da idonshi, sai ya san ni GIMBIYA HAKIMA duk wanda yaci tuwo dani miya ya sha... 




Haka dai su Lantana suka Kama fadanci sannan suka samu Gimbiya Hakima ta sauko daga dokin fushi, sannan suma hankalinshu ya kwanta haka har tayi bacci.. 



_________________________________




Hakim bayan ya koma gida wanka yayi yasa kayan shan iska ya tafi bayan gida domin shakatawa.. 



"Fulani,wai kinji abunda naji su Gimbiya Kilishi suna cewa, wai ko da bala'i sai sun kashe yaya Hakim... 




"Laaa nima Maryama wallahi nima naje rannan suna maganar suna maganar randa na tafi shan iska ni daya banda ke Sadiya, har Mino tace man wancen satin har magani Lanto ta kawo asa mashi abinci, wai yana ci zai mutu, ke wani abunma bai faduwa makircin da asirin da suke yi ma yaya... 




"Kunga duk kuyi man shuru da wannan surutun naku na banza, koma maiye mufi karfinsu da Ayar Allah dan haka ku cigaba da neman tsarin Allah ba na mutun ba.. 




"To shikenan Fulani Allah ya tsaremu, "Amin Maryama.. 




"Dan Allah Kilishi dubarshi sai kace wani sarki, wannan idan aka bashi sarki shida uwarshi banzaye zasu maidamu cikin gidan nan, tun yanzun yana wannan mulkin Ina ga ya zama sarkin.. 




"Kyaleshi Gimbiya lokaci kawai nike jira, wallahi indan har lokaci yayi Hakim jama'ar zaria baki daya mantawa zasuyi da anyi wani mutun Hakim, duk san da suke yi mashi ko, ke harta wanann munafukan yan biyun kannan nashi sai na shafe da babun su, balle uwar tasu... 





"To wai yaushe wannan lokacin zaiyi Kilishi? 



"Nan ba da dadewa ba, kedai kisa ido kiyi kallo, "shikenan Kilishi.. 




Nan suka gama meeting dinsu na kullun, sannan suka tafi.. 




Sudai su Gimbiya Kilishi basu da magana sai ta HakimπŸ’πŸ»‍♀️, laile ko suna da aiki wanann shi ake kira aikin burus inji tusaπŸ™…πŸ»‍♀️.. 




Sai da suka gama sannan suka tashi.. 



________________________



"Allah yaja da ran uwar marayu ga abinci nan yana jiranki... 



Kallon Bilkisu kawai tayi, sai ta shiga toilet ta zubo ruwa a roba ta kawo mata ta wanke hannunta.. 



Hakan na nufin yau bata san zuw parlour yin dinner dan haka shiyasa ta wanke hannunta, bayan ta gama wanke hannu, suka hada kayan suka kawo mata.. 




Ana cikin zuba mata ta Azima taji tace, "tsaya! Azima waya ce ku dafa man kus-kus? 



"Allah ya ja da ra'n Gimbiya Hakima ai ba kus-kus kawai muka dafa maki ba, harda macaroni, sannan kuma ga coffee nan duk munyi maki.. 




"Uhmmm! 



Nan Azima ta zuba ma Gimbiya Hakima macaroni, nan suka zauna suna bata labari taci har ta gama ci, sanan suka kwashe kayan suka je suka wanke, sannan suka dawo Lantana da Bilkisu suna tausa, ita kuma Azima tana karanta mata novel har tayi bacci sannan suka wuce suma suka kwanta.. 



 

Post a Comment

0 Comments