TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Saran boye page 26

 πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»

TEAM----ZAFAFA BIYARπŸ”₯😘πŸ₯°πŸ˜


ALLAH ka gafartama iyayenmuπŸ˜­πŸ™πŸ».


*_LITTAFIN nan na kuΙ—i ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haΖ™ura domin ALLAH karki karanta_*.



No. 26


..............Cike da jin haushin Yoohan Nu'aymah ta fito daga sashen hajjo. Hakan yayi dai-dai da shikuma Yoohan Ι—in zai koma dan ya kammala wayar.

         Karo sukayi, goshin Nu'aymah ya bugu da sarΖ™ar Cross Ι—insa. Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja kaΙ—an yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Nu'aymah bata taka Ι—an step Ι—in Ζ™ofar falon hajjon dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata faΙ—i.

           Yoohan ya tabbatar idan ya barta ta faΙ—i zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faΙ—o jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a Ζ™irjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yay azamar Ι—ora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe ruf.

         Cikin tashin hankali Nu'aymah ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma yaΖ™i sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faΙ—uwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu, cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta faΙ—in ma yaga Ζ™arshen rashin kunya.

          Duk da tsawan da yay mata bata nutsuba, sai ma cigaba dayin mutsu-mutsunta nason Ζ™wacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu, dan a rayuwarta da hankalin kanta kuma hakan bai taΙ“a faruwa da itaba. Ko hannu bata yarda samarin gidansu wani ya riΖ™e mata balle akai ga runguma irin haka. Sai gata yau kwance a Ζ™irjin Ζ™aton kahiri, da ko yayunta basu taΙ“a aikata haka a gareta ba. gashi ya rufe mata baki babu damar magana. Kuma Ζ™arfi ba Ι—aya ba.........

       Jin ya manneta da bango sai tashin hankalinta ya Ζ™aru, dan ta zata wani abun kuma zai aikata mata, ta kasa nutsuwa ta fahimci taimakonta yayi. hannayenta duka biyu ta saka tare da dukan Ζ™arfinta tana Ζ™oΖ™arin ture masa hannunsa daya rufe mata baki da shi. Ko gezau baiyiba, saima wani shegen kallo da yake binta da shi tamkar ya manta a inda suke, ga fuskarsa a matuΖ™ar Ι—aure balle kai tunanin da biyu yay hakan, sai dai shima zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri.

      “Ouch!!” ya faΙ—a da sauri yana janye hannunsa da ya toshe mata baki da shi, dan kuwa daddagewa tayi ta gasa masa cizo a tafin hannun. Yaja da baya yana yarfe hannun nasa da faΙ—in, “Are you mad?!”.

       Nu'aymah da har yanzu jikinta bai bar rawa ba ta galla masa harara tana share hawayenta. “Eh banda shi. ALLAH ya isana kuma, wlhy ka sake gigin taΙ“ani saina fasa maka kai, danni ba Ζ΄ar iska baceba!”.

      “Silly girl! Waye Ι—an iskan?” ya faΙ—a da turanci kamar yanda ta faΙ—a itama yana galla mata harara tare da cafkota, iya Ζ™arfinsa ya fisgota tayo baya ta sake faΙ—awa jikinsa. Mannata jikin bangon ya sakeyi, ya toshe mata baki da Ι—ayan hannunsa. kafin ya Ι—ago Ι—ayan hannun ya kalli inda ta cije sa, yamutse fuska yay ganin yanda shatin haΖ™oranta suka fito masa, ba wajen data ciza Ι—in kawaiba, tafin hannun gaba Ι—aya yayi jaa abinka da ba'asan wahala ba...

       Nu'aymah ta rikice iyakar rikicewa yanzun kam, dan ta yarda a ranta da gaske Yoohan son cutar da ita yake. Ƙilama abinda ya kawosa gidan kenan. Sake kaima Ι—ayan hannun cizo tayi. Yayi saurin janyewa ya maye gurbin hannun nasa da bakinsa. Shi kansa baisan yaya akai hakan ta faru ba, ya tsinci kansa ne kawai da haΙ—e bakin nasa da nata ya shiga kissing Ι—inta.

       Yanda take kuka da turesa da yakushinsa ne ya sashi janyewa daga gareta da sauri. Duk da halin daya ganta na Ζ™ololuwar shiga ruΙ—ani da tashin hankali hakan bai hanashi kallonta ba, tare da zazzaro mata manyan idanunsa da suka sauya kala zuwa ja.

      Harga ALLAH Nu'aymah ta tsorata yau kam, dan ta tabbatar tunda har ya iya mata wannan abun a cikin gidansu to lallai zai mata duk abinda yazo masa rai. Tunda tasan su basu Ι—auki keta mutuncin mace a komai ba. Amma tsabar Ζ™arfin hali irin na mutuniyar taku ana sakar mata baki sai ko ta murguΙ—a masa bakin da sake zuba masa harara. iya Ζ™arfinta ta turashi dan har yanzun yana manne da ita ne a bangon, amma ko gezau baiyiba balle tasa ran samun hanyar kuΙ“uta. Waige-waige take gudun kar wani ya fito ya gansu a haka, tana kuma hawaye, cike da tsiwa cikin harshen turancin data san yafi fahimta sosai tace,

        *_“Dama ku babu abinda kuka iya sai son taΙ“a mata da Ι“ata musu rayuwa, ALLAH ya isana Ι—an iska kawai. shiyyasa wanda baya salla an haramta ma sa jin daΙ—in duniya. Sannan zai gamu da wahalhalu a wurare guda huΙ—u: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin Ζ™abari da ranar hisabi. A duniya ana Ι—ebe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a Ζ™yamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da wulaΖ™anci da yunwa da Ζ™ishirwa. A cikin kabari ALLAH zai Ζ™untata ma sa, a hura ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kumurci a tsakanin fatar jikinsa da namansa. A ranar hisabi za a baΖ™anta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla-dalla, sannan a haΙ—a shi da zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Lallai, sallah ita ce ginshiΖ™in addini. Idan kaΖ™i gaskiya zaka faΙ—a Ι“ata. Idan ba ka ji nasiha ba, zaka yi da-na-sani. Wanda baiji bari ba ya ji hoho!......”_*

     Ta Ζ™are maganar da sake turashi da Ζ™arfi. Yanzun kam da kansa ma ya matsa ya bata hanya, da gudu tabar wajen kuwa tana kukanta har yanzun.

         Cike da takaicin kansa ya rumtse idanusa da Ζ™arfi, tare da Ι—ora hannunsa a goshi yana murzawa da abaton “Oh lord!, mina aikata?!”.


★★★★


         A wani Ι—an lungun sashensu Nu'aymah ta maΖ™ale tana sauke tagwayen shashshekar kuka, har zuwa yanzu jikinta baibar rawa ba, sai faman waige-waige take tamjar ance mata Yoohan Ι—in biyota yayi.

       Ta Ζ™anΖ™ame jikinta lokacin da abinda ya farun ya sake dawo mata a rai, yanda gashin jikinta ke wani mimmiΖ™ewa zai tabbatar maka da tsigar jikinta tashi takeyi.

     Da sauri ta saka hannu tana share hawayenta saboda jin tahowar mutum. ‘Na shiga uku ya biyo ni’ ta faΙ—a a fili zuciyarta na wani irin zallo tamkar zata faso Ζ™irjinta ta fito........

       “Nu'aymah lafiya na ganki anan? Mi kikeyi ne haka?”. 

      Duk da ganin Aunty Kubrah ce ba Yoohan Ι—inba hakan bai hana Nu'aymah sake rikicewa ba, ta shiga inda-inda jikinta na tsuma. “A..Aunty babu ko.. Komai”.

       Kubrah data kafeta da ido taΙ—an murmusa, sai kuma ta juya bayanta tana faΙ—in, “Ki kwantar da hankalinki ai ba biyoki yayi ba, na tabbatar kuma babu wanda ya ganku a gidan nan”.

        Wani muguwar faΙ—uwa gaban Nu'aymah ya sakeyi daboda jin furicin Aunty Kubrah. Cikin rawar harshe Nu'aymah tace, “Aunty Kubrah wlhy ni.......”

       “Kinga kwantar da hankalinki Nu'aymah babu maiji, indai nice ko Hajarah baza taji wannan zancenba balle wani a gidan nan. Amma inason ki faΙ—amin gaskiya, yaushe kuka fara wannan abun ke da shi?”.

       “Innalillahi! Aunty wlhy bamu taΙ“a yiba, yau ma na rantse shin......”

       “Kinga ya isa. Share waΙ—an nan hawayen idan baso kike ki tonama kanki asiri ba da kanki”.

       Nu'aymah duk ta sake rikicewa, tama rasa fahimtar inda maganganun Aunty Kubrah suka dosa saboda tashin hankali. Duk da ta share hawayen sun gaza tsayawa. Hannunta Kubrah ta kama har lokacin fuskarta da murmushin da Nu'aymah ta gaza fahimtar na minene. “Kinga muje sashenmu, idan ba hakaba Umm sai ta fahimci abinda ya faru, ko kinfi buΖ™atar hakan?”.

     Da sauri Nu'aymah ta shiga girgiza mata kai, “A'a wlhy Aunty, banason Umm ta sani dan zata kasheni, dan ALLAH karki faΙ—a mata, wlhy kuskurene ba kuma laifina bane ba, na rantse da ALLAH Aunty ban taΙ“a yiba, ko hannuna Namiji bai taΙ“a riΖ™ewa ba”. Ta Ζ™are maganar da rushewa da wani irin kuka maiban tausayi.

     Komai Kubrah bata sake cewaba ta kama hannun Nu'aymah suka nufi sashensu. Ta Ζ™ofar baya tabi da ita, dan Ζ™annen Addah su Aunty Basira suna falo zaune dasu Addah suna hira. Batare data bari sun gansu ba ta shige da Nu'aymah bedroom Ι—insu. Zaunar da ita tayi sannan itama ta zauna a kusa da ita. Har lokacin kuma Nu'aymah kuka takeyi, zuciyarta na Ζ™arajin tsanar Yoohan matuΖ™a........

         “Ko shine Ameer Ι—in Saurayinki?”. 

     Da sauri Nu'aymah ta Ι—ago tana kallon Kubrah, sai kuma ta shiga girgiza mata kai, “Aunty dan ALLAH ki yarda dani, wlhy Ameer ba saurayina bane. Wannan kuma bama musulmi bane ba, baΖ™one yau na fara ganinsa”.

        HaΙ—e fusaka Kubrah tayi tamau tana kallon Nu'aymah Ι—in. “Karkimin Ζ™arya Nu'aymah, inba hakaba wlhy na fasa rufa miki asirin, a yau da daddare zan sanarma Hajjo da Baba malam da Umm komai. Ki faΙ—amin tun yaushe kuke tare? Sau nawa kuma yay amfani da ke?”.

       Duk sai Nu'aymah ta sake daburcewa, dan tama rasa wace amsa zata bama Aunty Kubrah, gaba Ι—aya ta kasa fahimtar manufar Kubrah.......

     Kamar Kubrah tasan tunanun da Nu'aymahn keyi, sai ta sassauta fuskarta tana gyara zama. Ta Ι—an rage kaushin muryarta kuma ta koma magana cikin lallashi. “Nu'aymah kinsan dai yaya nake a gareki, duk abinda zan iya gani gasu Hajarah raina ya Ι“aci idan nagani daga gareki dolene naji zafi, Ι—iyar Ζ΄ar uwar mahaifiyata ce kuma ke, dan kuwa Umm tamkar Ζ΄ar uwar Adda take, tamafi min wasu Ζ΄an uwan Addan. Yanzu Nu'aymah da wani ya ganki a gidannan Ζ™aton banza yana lalubeki mikike tunanin zai faru?, idan ma iskancin zakiyi ai gara kuyisa can a waje wani bai gankiba ko, amma a cikin gidanku? Babban gida mai daraja irin wannan? Wane kallo kikeson aima iyayenki maza damu kanmu Nu'aymah?”.

          “Dan ALLAH kiyi haΖ™uri Aunty Kubrah, wlhy bazan sakeba wannan ma Ζ™addara ce da kuma kuskure”.

      “ALLAH yasa hakane to”. Kubrah ta faΙ—a tana wani Ι—auke fuska da Ζ™yaΙ“e baki.

             Nu'aymah na kuka tace, “Wlhy da gaske nake Aunty. Dan ALLAH ki yarda dani”.

         “Nu'aymah idan ban yarda da ke ba minene amfanin musawar to?, tunda idan kunbar gabanmu ALLAH kaΙ—ai yasan mi kuke aikatawa, masu iya magana fa kance rana dubu ta barawo, Ι—aya tak ta mai kaya. Yau Ι—inma ai bakiyi tunanin zan ganku ba”.

          Ƙasa Nu'aymah ta zube tana kuka tamkar ranta zai fita, ‘Ita mizata faΙ—ama Aunty Kubrah ta fahimceta ne wai? Wane rantsuwa zatai mata danta yarda ba da yardarta kafirin nan ya aikata hakanba a gareta?’.

       Sai da taci kuka sosai, Kubrah na zaune na kallonta kafin ta Ι—agota ta rungumeta, “Kukan ya isa haka, aina yarda ba laifinki bane. Na miki hakane kawai dan kisan baki dai-dai ba”.

         “Na gode da kika fahimceni Aunty, kuma namiki alΖ™awarin hakan bazata sake faruwa ba insha ALLAHU”.

     ΖŠagota Kubrah tayi ta share mata hawayen tana murmushi, “Shikenan naji, kuma na miki alΖ™awarin babu maijin zancen nan a gidan nan kinji, kije bayi ki wanke fuskarki kizo ki sake shafa hoda dan karma wani ya zargi wani abun kuma kinji ko. Ki kuma saki jikinki inba hakaba Umm zata gane, kuma kinsan halinta. Zatabi duk hanyar data dace dan tasan gaskiyar abinda ya sakaki kukan”.

           “Insha ALLAHU bazan bari ta gane ba Aunty, bara ma na wanke”. Ta Ζ™are maganar tana miΖ™ewa da sauri ta nufi bayin su dake cikin Ι—akin. Tana wanke fuska tana kallon bakinta a mirror. Wasu hawayen sai sake Ζ™oΖ™arin zubowa suke tana dannesu da Ζ™yar. A fili tace, ‘Na tsaneka mugu Ι—an iska mai suffar samudawa, bazan taΙ“a yafe makaba wlhy”. Ta Ζ™are maganar da fashewa da kuka.

     Taja kusan mintuna biyu tana kukan kafin ta wanke fuskar ta fito. Fitowar tata tayi dai-dai da shigowar Hajarah da wayar Kubrah a hannu. Da mamaki Hajarah take kallon Nu'aymahn, dan ita dai bataga shigowarta sashen ba.

       “Nu'aymah yaushe kika shigo ne? Gashi kamar kinyi kuka?”. Da sauri Nu'aymah ta girgiza mata kai, sai kuma ta kalli Inda tabar Aunty Kubrah dan tana zaune a wajen, tana jinsu kuma amma ko kallonsu taΖ™i tayi balle ta nuna alamar tasan mi sukeyi ma. “Babu komai Aunty Hajarah, kaina ne kawai ke Ι—an ciwo”.

      Ƙarasawa inda Nu'aymahn take Hajarahn tayi, ta Ι—ago fuskarta cike da nazari........

       “Wai miye hakane? Tace miki babu komai kanta ke mata ciwo miye na damunta ne kuma?”.

       Baya Hajarahn taja kanta a Ζ™asa tace, “Kiyi haΖ™uri Aunty Kubrah, ga wayarki dama Alhaji ne ya kiraki”. Ta matsa inda take cike da girmamawa ta bata wayar.

      Tana amsa ta nuna mata Ζ™ofa da ido. Da sauri kuwa Hajarahn ta fice. 

     Kubrah ta maida dubanta ga Nu'aymah dake a tsaye har yanzu. “K kuma ki bada himmar tonama kanki asiri kinji ko, ki wuce ki shafa hodan, idan kuma sokike wani ya sake shigowa to”.

        Gaban Mirror Nu'aymah ta Ζ™arasa. Ta shafa mai da hoda harda kwalli, duk da dai hakan fuskar dai babu walwala.

     Amma sai Kubrah batace mata komaiba suka fito falo inda su Hajarah ke hira tare. Zama tayi kamar yanda Addah dake kallonta ta Umarceta. Su Aunty Basira nata tsokanarta da faΙ—in ina tsarabarsu ne?.

       Tun tana noΖ™ewa dai harta Ι—an ringa amsasu, amma ta gaza sakin jikinta yanda ya kamata sosai. Duk motsinta Hajarah da Addah na lura da shi, sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu. 

      


___________________________

    

          A Ι“angaren Yoohan kuwa duk yanda su Hajjo sukaso ya zauna jiran dawowar baba malam ya gaza hakan. Yace musu zai dawo da safe yanzu yanada wani uziri.

      Badan hajjo taso ba ta barshi. har Ζ™ofar gida su Yah Ahmad sukai masu rakiyya shi da Manager. Inda su Solomon ke jiransa a mota. Kasancewar basu iske baba malam ba yasa bai shiga dasu cikiba. Yace su jirashi a waje. Dan da Ζ™yarma Su Ahmad suka lallaΙ“ashi ya shiga cikin gidan. Da farko ya ce zai koma tunda baba malam ya fita. Dan dama yaso yin surprise Ι—insa ne shiyyasa bai sanar masa shigowarsa kanon ba ma.

         Har drivern sa ya tada mota ya tsaidashi. KuΙ—i ya ciro a cikin jakarsa rafa guda na Ι—ari biyar sabbi Ζ™al ya miΖ™ama malam Ζ™arami yana faΙ—in, “Please a bama yarinyar nan barka da salla. Na manta ban bata ba”.

       Malam Ζ™arami da ya fahimci Nu'aymah yake nufi sai yay murmushi. bai musa ba ya amsa yay masa godiya, dan suma daya basu sukaΖ™i amsa a ciki Ι“ata rai yayi, wai basu Ι—aukesa Ι—an uwansu ba. Hakanne ya sakasu amsa tunda yace barka da salla ce.

         Duk abinda ke faruwa Solomon na saurarensu. Dama cike yake da haushin sake zuwa wannan gidan. Ya kuma Ι—auki alwashin suna komawa wannan karon sai ya sanarma madam Chioma. Dan tsaf ya fahimci waΙ—an nan mutanen zasu iya jan hankalin Ogan nasu tsaf, musamman yanda suke masa hidima kamar wani sarki. Yanzu haka a gabansa aka saka babbar leda a booth wai kayan barka da salla ne aka bama Yoohan Ι—in a cikin gida. Ya cije bakinsa yana satar kallon Yoohan daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu kamar mai barci ta mirror.

    

      Babu abinda kema Yoohan kai kawo a zuciya da ruhi sai kalaman Nu'aymah. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da ac dake aiki a motar bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi ba. Mafarkin da yayi shekaran jiya da baba malam ya kuma sake maimaita shi yau da safe ya shiga tariyowa shima.        

       ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo mafarkin nasa da yayi a karo na biyu kenan,

        *Ya kanga kansa a mafarkin a gaban wani kogo Ζ™aton gaske, cikinsa akwai wani irin wuta dake ci mai ban tsoro, dan duk iya hasashensa ya kasa kamanta Ζ™arfin wutar da zafinta a zahiri. Aduk lokacin da yake a gaban wannan kogon dake zuwa masa a mafarki, ya kan tsinci kansa cikin matsanancin mawuyacin hali da ruΙ—u, sai dai kuma abin mamaki sai ya ga baba malam acan gefensa cikin shiga ta kamala, a wasu irin korayen ciyayi masu bada ni'imtaccen yanayi yana masa murmushi da miΖ™a masa littafin nan na musulmai (Al-Qur'ani), yakan ringa ce masa_______* 

        *_“Yoohan wannan shine zancen ALLAH, littafi dake Ζ™unshe da kowane irin sirri, littafin da aka aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) da shi. kanada sauran daman riΖ™o dashi domin ka samu tsira daga wannan narkon azabar dake gabanka. Kazo gareni, zan nuna maka hanyar sanin UBANGIJINA kamar yanda ya aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) a garemu ya nuna mana muma, ya kuma koyar damu. Ni Sooraj bin Hashim, na rantse maka da ALLAH, babu wani addini na gaskiya sai musulinci, babu wata hanya Ζ™yaΖ™yΖ™yawa sai ta bin UBANGIJI, babu wani abin taΖ™ama da riΖ™o sai MANZON ALLAH. Inhar kabi ALLAH, kai koyi da koyarwar MANZON ALLAH, ka riΖ™e gaskiya da amana, ka tsare gangar jikinka daga saΙ“ama ALLAH, ka nema dukiyarka ta hanyar halak, kaji tsoron zalintar mutane, ka kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ALLAH bazai jarabceka da shiga wannan taskar azabar dake a gabanka ba. Domin UBANGIJI ya tanadi gidaje guda biyu, WUTA DA ALJANNAH, ya kumayi alΖ™awarin cikasu da mutane. Dan haka Yayha kazo gareni, kazo ka karΙ“i kalmar LA'ILAHA ILLAH, MUHAMMADURRASULULLAH (S.A.W)._*

          A wancan ranar da yay wannan mafarki ya wayi garine a yanayin sanyin jiki, da tunane tunane kala-kala. Ya kuma yini zuciyarsa na rinjayarsa da amsa wannan kira. Sai dai daya tuna wani gagarumin al'amari sai yay azamar Ζ™waΙ“ar kansa harma da alΖ™awarin nisanta kansa da su baba malam Ι—in. Dan yau Ι—in nanma da Ζ™yar manager ya lallaΙ“a shi sukazo nan Ι—in. duk da kuwa yana a cikin kanon yau kwanansa biyu kenan ma.


       Kafin su Ζ™arasa hotel Ι—in daya sauka sosai ya tsinta kansa cikin ruΙ—anin kalaman Nu'aymah da mafarkinsa. Sai Ι—unbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai taΙ“a yarda da shi ba. Ya Ι—an ciza leΙ“ensa na Ζ™asa da Ζ™arfin tsiya, Ζ™irjinsa na sake masa zafi.

     Motocin na tsayawa baiko jira an buΙ—e masa ba ya buΙ—e da kansa ya fice. Daga Solomon har sauran guards Ι—insa tsaye kawai sukai suna kallonsa cike da mamaki da tsoron yanayin nasa. Da sauri Solomon yabi bayansa shima dan yasan ba lafiya ba dai. Gashi key Ι—in Ι—akin Yoohan Ι—in yanama a hannunsa ne.

     ΖŠan gudun da yayine ya sakashi cimmasa. Dan haka suka Ζ™arasa Ζ™ofar Ι—akin tare. Solomon ya buΙ—e masa tare da matsawa ya bashi hanya dan ya shiga. 

        Batare da yace masa komaiba ya shige, shi ma Solomon Ι—in sai ya bisa yana faΙ—in, “Sir lafiya kuwa?”.

        Cak Yoohan ya tsaya da ga yunΖ™urin shiga Bedroom Ι—in da ya keyi, batare da ya juyoba ya Ι—agama Solomon Ι—in hannu da masa alamar ya barsa.

      Da baya-baya Solomon ya rinΖ™a tafiya harya fice da ga Ι—akin, yaja masa Ζ™ofar a hankali gabansa na faΙ—uwa da yanayin ogan nasu.............✍


πŸ€”πŸ€”πŸšΆπŸ»Tofa, Dr Yoohan yaya dai?🚢🏻




Post a Comment

0 Comments