TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

DABI'AR ZUCIYA ❤ page: 47 - 48

 47

D/Z


A gaba ta zauna kamar yadda tsarinsa yake,suna shiga motar jauhar na kiransa a waya,saiya hada wayar da speaker din motar yana amsa wayar.


Duk yadda taso dauke hankalinta daga hirar tasu hakan ya gagareta,saita samu kanta da bibiyar duk wata hira da jauhar din ke masa,shi kuma yana qoqarin amsata,wanda kana jin yadda yake amsawar dauriya kawai yakeyi da qoqarin tursasawa kansa,don hirarma batayi tsaho ba yace mata


"Am on my way to office,i will call you when I'm back" 


"Ok honey,byeeee" ta fada da wani baby voice da take amfani dashi wajen ganin taja hankalinsa.


Shuru ne yaci gaba da wanzuwa,wanda mintunan da suka qara basu wuce biyar ba ya tsaida motar bakin makaranta,ta dauki jakarta ta fita tana cewa


"Na gode" ta maida murfin ta rufe bayan tabar masa sauran qamshin turaren data durfafa a yanzu.


Yana motsa motar zuwa gaba yana hangen sanda ta shige makarantar ta madubi,saiya dauke idonsa ya maida hankalinsa sosai ga tuqinsa,yana qoqarin daga wayar amiru data shigo.


Shaida masa yayi yana nan dawowa da yammacin yau,amma zai dan zauna gidan hajiya qaraman kafin ya qaraso nan gida,yaji dadin dawowar tasa wannan karon da wuri,sabida amirun shi daya ne amini ga samir,wanda yake iya tattauna matsala ko damuwarsa dashi,hakanan yakan samu courage na aiki a duk sanda amirun ke cikin kamfani,saidai dole wani lokaci akan rashi a kusa,sabida shike kula da dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya barmusu shida 'yan uwansa mata biyu dake aure a wata qasar.


Yau din tana aiki tana duba novel din,don da qagu taga qarshensa,sosai labarin yake dibanta gami da tafiya da ita,batasan sam haka soyayya take ba sai yanzu,batasan haka rayuwar auren masoya take ba sai data karanta littafin,saita tsinci kanta tana hasaso kanta da gina rayuwar soyayya irin ta cikin littafin,amma kuma dawa?,a yiwa kanta tambayar data katse dukka zaran tunaninta.



Idan ta dauko soyayyar da tayi a qauye sai taga ashe badan badamarsu kawai sukeyi,basusan meye ma ainihin soyayyar ba,kawai wani abu suke mai kama da wasan kwaikwayo.


Zamantakewar aure a karkararsu kuwa dama ta jima da sanin cewa ana yinta ne illegally ,abubuwan dake faruwa kwata kwata basuyi kama da zaman aure ba.


Ita kadai a kitchen tana aikin abinci tana sakin murmushi a duk sanda ta tuna da labaran novel din,sun sanyata nishadi ba kadan ba,abinda kuma ya jawo mata delay kenan,tayi nawar gama girkin da takeyi,har akayi kiran sallar magariba.


Ajjiyewa tayi taje tayi sallar sannan ta dawo tana duba abinda ya rage din,a hankali tanayi tana duba sabon novel din data karbo din.


Bakwai na dare motar tayi parking a parking lot na gidan,zaratan samarin guda biyu suka fito daga cikin motar,fuskokinsu wasai,suna taba hira har suka qaraso qawataccen parlour din hajja.


Tana daga zaune taji sallamarsu,murmushi ya wadata a fuskarta,farincki ya cika zuciyarta,ta bisu da kallo tana musu fatan dacewa da samun mataye na gari,a yanzu babban burinta shine taga dukkaninsu sunyi aure,sabida tsakanin ita da yayan nata yara maza biyune rak dasu,sai mata,ita uku shi biyu,tana fatan wadan nan da Allah ya basu yaci gaba da albarkacesu,su kuma tara musu zuri'a me dumbin yawa.


Waje suka samu suka zauna cikin nuna mata kulawa,amiru ya zamo ya gaidata yana mata sannu da jiki,yayin da samir shima ke sake mata sannu kamar ba daxu yabar gidan ba.


Hira suka fara tabawa kadan kadan,wadda ta shafu tafiyar tasa,da kuma abubuwan da suka faru bayan bashi nan.


Karo na kusan hudu wayar samir tayi tsuwwa yasa hannu yayi rejecting kamar yadda yakeyi tun dazu,hajiya qarama ta dubeshi


"Ka daga mana ba kiranka akeyi ba?" Saiya jinjina kai


"Barsu hajiya,idan na gama komai zan kira" maganar amiru ta katse zancan


"Nifa tunda na shigo nakejin qamshin girki hajiya,kuma anmin fuska,a amatsayina na baqo yaci ace an tarbeni da wani kyakkyawan girki nan" kallonsa tayi ta tabe baki


"Idan abun bai maka dadi ba kayi zuciya ka kawomin mata qarshen watan nan,ni dama na gaji da ganinku wallahi a gabana,shi wannan kamae bashi da idanu saida aka zaba masa mata,wadda har yanzu nikam ban gama yarda da ingancinta ba,kai kuma har yanzu shuru,to gwanda gwanda shi da kai ma" gyara zamansa yayi sosai yana duban hajiyan


"Wato hajiya kada ki damu,tana qarasa NYSC zan gabatar miki da ita in sha Allah" baki ta sake tabewa


"Zuwa yaushe kenan?"


"Nan da wasu 'yan watanni ne,tana dawowa" kai ta dauke haushi yana cikata,badon sanin halin yaran zamani ba,da tuni kowanne ta zaba masa mata sun aurar dashi an huta,to amma ita kanta tana adawa da auren dole


"Data gama abincin da tuni ta kawo,amma yanzu ma nasan tana dab da gamawa" ta amsa musu,sai samir ya miqe,don da gasken shikam yunwa yakeji,wunin yau banda baqin coffee babu abinda ke cikinsa,sai cake guda biyu


"Bari na samo wani abun"


"Yauwa mutumina,ka hado dani please" hara rarsa yayi


"Idan ka matsu kaje ka dauka da kanka,yaron gidanka ne ni?" Dariya ya saki


"Ban isa ba,ataimaka min" bai sake ce masa komai ba ya wuce cikin kitchen din.


Bai lura da ita ba sai daya isa cikin kitchen din daga bakin qofa,saiya dakata a hankali da tafiyar da yakeyi din,tana tsaye riqe da littafin tana karantawa,fuskarta na fitar da wani murmushi dake nuna nishadin da zuciyarta ke ciki.


Sanye take da daya daga cikin kayan da jawahir ta bata,high tummy skert me wata belt a jikinsa me fadi wadda gabanta ke dauke da tambarin kamfanin DG daya bayyana asirin shafaffen cikinta,daga baya kuma mazaunai da qugunta da suka fara bajewa suka bayyana,sai long sleeves t.shirt turtle neck wadda ta dace da kalar peach din skert din me adon green,dan kwalin kanta shima peach ne me santsi sosai,wanda ya hadu da santsin gashinta ya hana dankwalin zama yadda ya kamata,hakan yasa ya zame daga kanta ba tare data sani ba.


Fuskarta yabi da kallo,fatarta data koma chocolate colour ta haska sosai cikin peach color kayan data sanya,daga gaban goshinta gashin kanta ya kwanta sosai ya sauka zuwa kafadunta.


Wani motsi yaji zuciyarsa nayi,yabita da kallo sanda ta furta


"Yes,anzo wajen" qasa qasa bada wani qarfi ba,saboda laushi da zaqin murya da Allah ya bata daya dade da sani tun a qauyen dinya,saita kife littafin,ta tafi ta juya miyarta ta kuma dan dana.


Fararen idanunta da suka qara girma da gaske ta dinga rarrabawa bayan ta gama dandanar miyar taji da sauran tsami,saita ajjiye ludayin,ta matsa gaba kadan gaban wata locker ta jikin bango dake sama,inda hajiya ta nuna mata nan suke ajjiye kanwa koda akwai buqatar amfani da ita,tasa hannunta ta bude locker tana fatan Allah yasa tsahonta yakai,saboda ta kere mata sosai.



Hannunta ta sanya ta laluba sosai,saidai bataju komai ba,saboda gwangwanayen sun shige can ciki,don haka ta duba hagu da damanta ko akwai abinda zata taka takai saidai babu,abinda yasa ta fara yin dage kenan tana tana ta zura hannu amma a banza.


Murmushi ya qwace masa saboda yadda yaga tana yin dagen,gami da tsalle duka,ya sauke hannayensa daya rungume a qirji,ya fara takawa a hankali zuwa inda take tsayen.


Ko kusa ko alama bataji wani alama na shigowa mutum ba ko qarasowarsa inda take,sabida socks ne kawai a qafarsa,sai dumin tsaiwar mutum da kuma jinginarsa data ji a bayanta,kamar anyi huggin nata ta baya kenan,saidai babu hannunsa guda daya daya tabata illa ya miqa hannunsa cikin locker yana qoqarin dauko mata abinda ta kasa daukowar.


Da fari ta tsorata,harma ta juyo da sauri,bugun zuciyarta na sake qaruwa gabanta na faduwa,saidai suna hada idanu sai komai kwance mata,tsoron yayi nasa waje,sai kunya nauyi da gudun zuciyarta wadda taci gaba da harbawa cikin qirjinta da sauri da sauri.



Sosai idanunsa suka mata wani irin tasiri,kamar yadda yaji dumin jikinta da tudun bayanta a lokaci guda suna wani ratsashi tare da saukar da wani yanayi a jikinsa,kusan lokaci daya suka sauke idanuwansu,ita ya sauk su qasa tana kallon tiles din kitchen din,shi kuma ya mayar cikin locker din ya fara sauke mata gwangwanayen ciki da daya da daya,kamar wanda cutar kasala ta kama,lokaci guda qamshin man datayi oiling kanta dashi ya cakuda da turaren jikinta yana shige masa hanci.


Sai daya sauke mata dukka gwangwanayen sannan yaja baya a hankali yana jingina bayansa da kantar kitchen din


"Zabi saina mayar,ko kuma nabar miki su duka?" Ba zata iya amsawa ba saboda yadda jikinta ke dan rawa rawa,ita kadai tasan feeling din daya haifarwa jikinta,irin abinda bata taba jin ya motsa cikin jikinta ba.


Da idanunsa ya kafeta sanda take budawa tana duba wanne ne kanwa ke a ciki,yabi hannayenta da kallo wanda ada basu da wani kaurin kirki,amma a yanzu sun ciko sosai,idanunsa suka sauka kan wani abun hannu guda uku dake daure a tsintsiyar hannunta,na dutsune irin dutsen shirin nan shigen na fulani,saidai wadan nan wasu irin masu garai garai da sheqi ne,butter colour ne masu dan girma circle shape.


Rubutune a dutsen tsakiya daya kaso hangowa,ya zuba idanu sosai amma bai gane me aka rubuta ba,har zuwa sanda tace


"Na gama" da siririyar muryarta,ya qarasa a hankali,saiya kama tsintsiyar hannunta,wanda hakan ya sanyata daga idanu ta dubeshi da sauri,sai taga dutsen yake kallo wanda aka rubuta i'm in love da qananun baqaqen rubutu.



Dazu dazu ta siya abun hannun a makaranta,an jima ana saidashi,duk da yadda kuma 'yan ajinsu keta siya bata taba marmarin siya ba,saboda akwai mai sunan samari a jiki da yawa,kowa yana siyan me sunan saurayinsa ne,sai dazu da aka kawo wadan nam design din sukayi mata saita dauka.


Yana gama karantawa ya dago suka hada idanu,tayi saurin dauke idonta tana jin bugun zuciyarta na sake ninkuwa fiye da da,wani irin maganadisu idanunsa ke dashi,ta dade da ganin haka,tun ranar daya tsaidata zai shigar da haladu wajenta,abinda ya janyo a sannan ta kasa maida masa maganganun da tayi niyya kenan.


Ya lura wanu nauyinsa da kuma kawaici take masa,sai yaqi sakin hannun nata,yaci gaba da kallon abun hannun,a hankali ya sakar mata hannun sannan ya fara diban containers din yana maidawa,hakan ya bata damar yin gaba da sauri ta jiqa kanwar,ta matsa gaban tukunyar ta bude ta zuba,ta juya miyar ta tattabatar komai yayi,saita kasa juyowa sanoda tana da tabbacin yana cikin kitchen din,baisan shi mugun nauyinsa takeji bane?,tanason ta qarasa aikinta ne tabar kitchen din,amma wanzuwarsa a nan ya hanata ci gaba da yin komai.


Littafinta na saman freezer din da zai dauki abu,bai kula ba ya bude sai littafin ya fado qasa,ya sunkuya a hankali ya dagashi,zai gyara mata alamar data saka na shaidar inda ta tsaya,saiya buda shafin,idanunsa ya sauka a inda ta saka alamar.


Layi hudu ne,amma suna dauke da wasu zafafan kalaman soyayya,da alama sun jima suna dakon soyayyar junansu,sai ranar jarumin ciki yake bayyanawa jarumar soyayar da yake mata.


Alamarta ya maida mata,ya rufe littafin ya dora mata a gefanta,sannan ya bude freezer din ya dauko fresh milk da basuyi sanyi sosai ba,yana da buqatar daukan cups,saidai kuma tana tsaye a wajen,hakan ya sakashi takawa,ya sake tsaiwa dab da bayanta,dyk da kusancun baikai na daxun ba amma saida numfashinta ya dauke na wucin gadi.


Dai dai sanda ya miqa hannu ta gefan wuyanta zai dauka cup din ya jefa mata tambayar data sanyata diriricewa


"Waya koya miki karanta litattafan soyayya?,bakisan koya maka soyayya suke ba?,ko kin shirya yinta a yanzun?" Kalmomin daya gaya mata kenan da suka shige deep inside her da wani irin sound me nauyin amo.


Tambayar tayi mata tsauri da yawa,hakanan batasan kalar amsar da zata bashi ba,saita zabi yin shuru


"Yaka dade ne,am starving fa,fuska kawai nayi" suka tsinci murya amiru tsakiyar kitchen din,abinda yasa samir ya janye baya a hankali hannayensa dauke da kofunan,ya dubi amiru wanda idanunsa suka hango masa kaltum dake tsaye bakin tukunya,taqi kuma juyowa


"Gasunan acici,ka fado waje babu sallama"


"Don zan shigo kitchen sai nayi sallama?,wanne sabon salo ne kuma hakan?" Ya amsa masa tana matsawa gaba tare da gocewa gefen saraki daya tsaya a gabansa ya kare masa abinda yakeson ganin


"Ashe mana,dole mu zauna da yunwa ashe jawahir ke girki" ya fada da salon tsokana irin wadda sukewa juna lokaci zuwa lokaci shi da jawahir din.


Dole ta juyo saboda batason yacu gaba da dauka jawahir din ce


"Ina yini" ta fada tana sake takurewa waje daya,tare da Allah wadan rashin fitowa da mayafinta da batayi ba


"Oh, sorry.......ashe ba ita bace,kamar kaltum ko?" Ya fada yana nunata da yatsa,saita daga kanta kawai


"Ma sha Allah,lafiya lau" ya amsa yana juyawa,saiya hangi samir tuni yayi gaba yama kusa ficewa daga kitchen din,don haka ya juya yabi bayansa,bakinsa fal da maganganu.



Tunda ya fito samir din ya karanci maganganu ne fal bakin amirun,don haka yaqi bashi damar cewa komai ma,ya maida hankalinsa ga hajiya qarama dake masa bayanin tanason suje azare qarshen watan nan,fada take musu sosai shi da amiru


"Dukkanku zuba muku idanu ai nayi,naji wanda zai fara maganar zuwa a cikinku amma ba'a samu ba,wasa wasa so kuke gaba daya a watsar da zuwa azare,bayan kunfi kowa sannin ammi tana da rai,kai koda bata da rai hakan bame yuwuwa bane,to ku shiga taitayinku da kyau na gaya muku,tunda shi yayan yana kallonku ya qyaleku,saboda haka ku shirya.....bikin salis za'ayi da farida,kuma dukkaninsu 'yan uwanku ne auren zumunci ne,saboda haka zuwa ya kamaku,kowanne ya kammala uzurinsa kafin sannan,ashirin da biyar ga wata nakeso mu wuce dukka harda su jawahir da najwa,uwarsu kuma idan taga zataje taje,wannan ba matsalata bace" can qasan rashi samir ke sakin murmushi yana kurbar fresh milk dinsa,har kwanan gobe dai hajiya qarama ba zata sauya ba,bai taba ganin wani abu data riqa ta kuma qi jininsa irin mummy jidda ba,taqi gaya masa dalili,kuma shima ya kasa ganowa,abu daya ya fahimta,tanayin komai ne akansa da mahaifiyarsa,mahaifiyar data gudu ta barshi,ta zabi ta shiga duniya ta barshi.


Jin zuciyarsa ta fara quntata da wannan tunanin yasa ya janyowa hajiyan wata hirar,tunani ne dake sanyashi yanzu yanzu ya burkice,shi yasa ba kasafai yake barin kansa yinsa ba.


Babu jimawa kaltum ta fito ya shirya komai,saidai wannan karon gaba daya jikinta lullube yake da wani cotton mayafi mai kyau baqi,ta gama shirya komai ta matso wajen hajiya qarama tana rusunawa


"Hajiya an gama" addu'a tayi mata sosai cikin kulawa da yabawa,har zuwa sanda kaltum din ta wuce daki bakin hajiya qarama baiyi shuru ba yaba mata take,mutum ce ita da bata raina ko manta alkhairi komai qanqantarsa


"Saraki.....wannan yarinyar....wankan engine akayi mata ne?,kasan rabona da ganinta kwana uku bayan zuwanta garin nan?"


"Wa ya sani ne?" Ya bashi amsa yana miqewa zuwa dining inda hajiya qarama ke kiran suzo ga abincin suci


"Anya kuwa kana kallonta da kyau samir?,kaga yadda ta canza? black skin din nan ta koma wani beautiful chocolate color?,ba sirantaka,komai nata moderate,baka gani ba wai?"


"Ban sani ba!,ba aikina bane wannan observation din, shut up your mouth kaci abinci malam" ya fada masa yana tsareshi da ido


Kai ya dauke ya fara zuba abincin,saidai bai iya yin shurun ba


"Saifa na fada malam,anya ba akwai abinda ka gano ba a sannan kayimin wuff ka amsha aurenta ba?" Haushi ya cika samir,ya rasa me zaiwa amiru ya huce,dama tun asali ya sanshi,mutum ne da yasa ainihin diri da halittar mace,aka haka yake da zabe zabe da ruwan idanu,a nan halinsu ya saba,kuma akan wannan suke fada,saiya dauka wani qaton saving spoon ya jefi amirun dashi,Allah yasa ua goce,don ba shakka daya sameshi saiyaji babu dadi


Kallonsu hajiya qarama data qaraso wajen kawai tayi ta tabe baki


"Har yau ku bakusan kun girma ba kenan" zuwanta ya yanke maganar,saidai duk sanda suka hada idanu da amiru saiya karanci maganar bata isheshi ba kenan.


Har suka gama cin abincin suka gama hirarsu bata sake fitowa ba,daga qarshe dai yadda amiru yaso kwana gidan bai yiwu ba,saboda daddy daya kira yanason ganinsu,dole tare suka tafi.






48

D/Z



Kwanakin da suka biyo baya ta maida hankalinta ne sosai ga jarrabawar da take gabanta,cikin ikon Allah kuma sai ta dinga zuwa mata da sauqi sosai kamar yadda jawahir ta gaya mata,sai abun yayi mata dadi qwarai a ranta.


Tafiya azare ta kama,kuma dukka kowa yayi amannar zuwa,har mummy da hajiya qarama bata damu da taje ko kar taje ba,sai gashi kamar ma tafi kowa damuwa da tafiyar,tun kafin ta isa garin kuma ta aika da tata gudummawar mai tsokar gaske ga bangaren gidansu amarya data ango,kamar dai yadda ta saba hidima kan jiki kan qarfi duk sanda wani sha'ani ya tashi daga dangin professor.


A satin da za'a tafi a zaren professor ya tako gidan da kansa wajen hajiya qarama,da alama kuma zuwan yana da alaqa da maganar auren samir da kuma bikin azaren.


Kaltum kusan itake kula da duk wani baqo da hajiya qaraman zatayi,tunda taji tace yaya rashid zaizo kaltum tayi abinci da abun sha na musamman saboda professor din,hatta hajiya qaraman bata sani ba,sai da yazo sannan taga kaltum din nata shirya masa kalolin abinci


"Kina wajen hajiya kenan?" Professor ya fada bayan ya gama amsa kasuwar kaltum dake duqe,hajiya ce ta karbi xancan ma tun kafin kaltum din tace komai


"Wallahi yaya,nace ina kuka samo haziqar yarinya haka,bason jiki ba ganda babu qyuya,na dade banji mutumin da naji dadin xama dashi ba kamar yarinyar nan" kada kai professor yayi,shi kansa yana yaba yadda yarinyar ke hidima da kowa cikin,duk da ba zama yake sosai ba amma yana lura da hakan,karon farko da zuciyarsa tayi sanyi da wuri kan wani abu da samir yayi gaban kansa ya aiwatar dashi ba tare da yarjewarsa ba


"Ki koma daki ki huta hakanan kinji,kya samu damar duba karatunki,zasu qarasa aikin"cewar hajiya qarama,tunda daya daga cikin masu aikinta ta dawo,dayar kuma ta kawo wadda zata riqe mata aikin kafin ta dawo. Kai ta gyada tana shigewa ciki.


Hira sukayi sosa irin ta zumunci ita da dan uwan nata,wanda dama duk sanda irin hakan ta faru yakan jima a gidanta,akwai shaquwa da qauna sosai tsakaninsa da hajiya qamar,daga qarshe ta fadi abinda take ganin ya kamata ya bayar kan hidimar bikin,ta kuma shaida masa ranar da ita zata tafi


"Ke kuma sai yaushe zaki tura taki gudunmawar hajjaju,naga jidda wannan karon ta rigaki bayarwa" ya fada yana saka hannunsa a aljihun babbar rigarsa yana ciro kudi.


Baki ta tabe tana duban wani barin


"Dama haka takeso ace,tayi qoqari,amma ni bana abu don a fada ko kuma saboda gasa,Allah sarki raihana.......har batason ace tayi wani aikin alkhairi,takan ce tayine saboda Allah,kuma shi take bida ya mata sakayya"


Wani kallo ya yiwa hajiya qaraman,tayi zaton abunda ya saba shi zaiyi a yanzun ma,saidai ga sabanin tunaninta sai taga ya dauke kai ba tare da yace komai ba,yaci gaba da irga kudaden daya debo din.


Miqewa yayi yana ajjiye mata kudin


"Wannan ki riqe a hannunki,nasun kuma zan saka a tura musu su cire ta banki" baki ta sake tabewa


"An gode,Allah ya qara arziqi ya rabaka da sharrin maqiya da munafukai" ya saba da jin wannan addu'ar daga bakinta,itama kuma tasan cewa an kawo qarshen hirar shi yasa daya miqe ma yana mata sallama ma bata damu ba.


Da kaltum hajiya qarama taso tafiya azaren,saidai kuma abun yazo da akasi,don randa xasu tafin ita da yaranta guda uku da jikokinta shida ranar kaltum din tana da sauran jarabawa guda uku,hakan yasa dole hajiyan ta barta suka wuce ita da yaran,da kuma jawahir banda najwa da ita tace sai ana ya jibi daurin aure zata je,ba zata iya zuwa azare ayi sati ba tana da schedules da yawa.


Jin cewa samir bazai samu tafiya ba sai ana ya gobe daurin aure tace ta zauna nan gidanta tunda masu aikinta suna nan,ya taho mata da kaltum din itama taga jama'a.


Hakan ya yiwa kaltum din,saidai jawahir bataso hakan ba


"Don Allah idan kin gama exams kafin ranar ki gayamin,Allah zan yankar miki ticket da kudina ki taho bauchi a ranar" murmushi kawai tayi mata,itakam banda ma hajiya nason taje da babu abinda zata,zatafi farinciki ace qauyen dinya akace taje,taje ta gano ummanta,don a yanzu bata da burin daya wuce haka.


Su amiru kuwa washegarin randa su hajiya suka tafi shima yabi bayansu,saboda akwai abota sosai tsakaninsa da angon fiye da samir,don yafi samir ma zuwa azare,hakan yasa professor ya sakashi ya tattaro ya dawo gidan hajiyan,saboda yace kada a bar mata gidan babu wani babba namiji sai masu aiki,dama kuma yana da niyyar hakan,saboda gyara daya bayar ayima sassansa,har mummy na tsokanarsa gyaran me?,shi daya kusa tafiya yabar gidan gaba daya?.



Ko daya kaltum batasan yana gidan ba,don ba shigowa ciki yake ba,iyakarsa sassan da suke zama yawancin lokuta shi da amiru idan suna gidan,hakanan da safe yake ficewa sai dare yake shigowa bayan ya gama sabgoginsa.



Yau tunda ta tashi takejin mararta babu dadi sosai,duk kuwa da cewa tun sanda ta gama shanye magungunanta dama takejin wani iri a mararta,amma na yau yafi na kullum,a haka ta samu ta rarrafa taje makaranta ta dawo,sai tayi lamo tun la'asar a bargo tana karatun novel tare da daukan darusa masu yawa,saboda jarrabawa biyu suka rage musu,kuma dukkansu masu sauqi ne,bata da wata matsala ko fargaba akansu,hankalinta kuma na rabuwa kashi biyu,saboda yadda mararta ke sake daurewa.


Bata tashi ba saida akayi sallar magariba,tayi alwala tayi salla,ta zauna saman abun salla kamar yadda ta saba kullum tsakanin magariba da ishaa,saboda lokacine na amsa addu'a,lazumi take a lokacin,idan ta gama kuma ta duqufa da addu'o'i kan ingantar rayuwarta data iyayenta.


Bata tashi ba saida tayi sallar isha'i,daga nan tayi bandaki tayi wanka da brush,kamar yadda yanzu ta sabarwa kanta ya zame mata jiki,ta tsane jikinta tayi oiling gashinta ta hadeshi waje guda tayi masa tufka daya sannan ta dauki wasu riga da wando milk colour masu taushi da kauri da hajiya qarama ra bata su,cikin wasu ragowar tsarabarta zuwanta saudiyya da professor ya kaita shekara biyu baya ranar ta dauko jakar ta gansu a ciki.


Tsaiwa tayi tana kallon kanta yadda kayan suka karbeta,ita kanta a yanzu takan jima tana kallon kanta yadda ta sauya lokaci daya,tasan mutane da yawa idan akace musu wanna kattumen da suka sani ce saisun qaryata kafin su yarda ita dince,abu daya ne yake daqila mata farincikinta,idan ta tuna ummanta da kuma habi,ko a wanne hali suke ciki?,ko habi ta haife abinda yake cikinta?,ko ummanta ta warke?,uwa uba kuma idan ta tuna ko zata karade duniya ba zataga dan uwa rabin jiki bilalunta ba,ita dashi sai a lahira,sai taji hawaye sun sauko mata,dukkan wata walwala tata da jin dadinta sun kau.



Yau a sanyaye ta koma ta zauna,ta jima a haka tana nazari,kafin ta sanya hannu ta shafi mararta dake sake qulle mata,wunin yau bataci wani abun azo a gani ba,abincinta na rana dana dare tasan duk suna kitchen din a ajjiye,kuma ko yanzu bata jin cin komai,bata da matsalar dafa ko cin abinda takeso,kamar yadda kowanne cikin masu aikin gidan hajiyan batayi masa shamaki da cin abinda ranshi keso ba ta hanyar data dace,babu almubazzaranci babu barna ko ha'inci,tana da kyauta da kyautatawa dukkan wanda ya zauna tare da ita,itakam.kaltum ba zata iya lissafa adadin kyautatawar hajiyan gareta ba,ko diyar data haifa a cikinta iyakar abinda zatayi mata kenan.


Komawa tayi ta sake kwanciya tana jawo littafin tana cije labba,wala'alla ko zuwa anjima zata iya jin yunwa ta tashi ta nemi abincin.


Yau da wuri ya dawo,don a nan unguwar ma yayi sallar magariba kana ya shigo gida bayan yadan tsaya wajen masu gadi sun dan taba hirar da bata fi minti biyar ba,duj da cewa ba jimawa yake wajensu ba,amma hakan yana musu mugun dadi,ta yadda baya qyamatarsu,ko kuma nuna banbamci ko fifikon dake tsakaninsu.


Yana fidda kayan jikinsa yana kiran wayar jawahir,yana sone yaji ina yarinyar take,saboda akwai siyayyar da yakeson mata,ya dade yana son mata wasu 'yan siye siye,saboda ko babu komai tunda har agiyarsa ta hau kanta to dukka sharuddan kulawa yahau kansa a musulunce,to amma baisani ba ko tare suka tafi dasu jawahir din,don baisan taqamaimen ranar da xasu gama jarrabawar ba.


Bugu biyu jawahir din ta daga,da qorafi ta fara kamar kullum


"Yaya,ban tabajin azare ba dadi ba irin wannan karon,don Allah yaya kaida kaltum ko taho sooner" murmushin daya qawata fuskarshi ya qara mata kyau ya saki sanda yake zare tie din wuyansa


"Mr qorafi,babu gaisuwa,babu jin ya nake sai qorafi"


"Am sorry yaya"saita fara gaidashi ya amsa mata,yana tambayarta azaren tana bashi amsa,tare da bashi labarin yadda aketa tsara bikin,saboda an dade ba'ayi biki ba a familyn sai yanzu,sannan kuma ma auren zumunci ne tsakanin angon da amaryar.


Yana da jumurin sarare,abinda yasa alaqarsu da jawahir keda tsaho da kuma nisa,yasan cewa tana da sauqin kai kamar yadda take da surutu,amma banda daddynsu duk cikin gidan babu mai iya bata attention dinsa yadda takeso,shi yasa yake jumurin biye mata.


A handsfree ya saka wayar,har ya gama shanye yoghurt din daya tsiyayo,zuwa sannan ya soma cire socks dinsa saboda wanka da yakeson yi,ya gama jin cewa kaltum din na cikin gidan,saboda haka yayiwa jawahir bayanin zai shiga wanka,ya katse wayar,ya dauki qaramin towel ya shige bathroom din.


A hankali ta ajjiye littafin hannun nata,ta miqe ta zauna sosai kafin ta janyo dankwalinta me santsi ta daura akanta.


Tunani tayi ta fara samun ruwan dumi sosai tasha ko ruwan lipton ko xata samu sauqin cramping din da mararta keyi,don taga walida qawarta idan tana ciwon mara shi take sha,kuma cikin ikon Allah tana samun relief.


Kitchen ta isa kai tsaye,ta samu daya daga cikin masu aikin ta kammala komai,tana daukar cooler din tata abincin,wanda indai ta dauki cooler din ta shiga dakinta kuma saida safe,saboda tana da saurin bacci ne.


Dukkansu tsakanin kaltum dasu girmamawa ce ga junansu,da dan murmushin qarfin hali kaltum tace


"Har kwanciya baba?" Dariya ta danyi


"Tome zan zauna yi,gida babu kowa hajiyarmu bata nan,ai saida safe kawai kaltume....am.....amma ga abincinki nan tun na rana fa banga kinci ba" fuska tadan motsa kadan


"Yau banajin dadin jikina ne baba shi yasa" cikin fuskar alhini tace


"Ashsha....Allah ya sawwaqe,to ko za'a sanya hasanu(yaron gidan) ya yiwa yallabai samir magana ko dan qaramin dakin shan magani kije?" Kai ta kada tana mamakin dama yana gidan,rabonta da ganinsa tun ranar nan,ranar data tsaye mata a rai,take kuma yawan tuna abubuwan da suka faru a ranar


"Ruwan dumi xansha yanzu,ina kuma saka ran zanji dadin jikina"


"To....to Allah ya qara afuwa" da haka sukayi sallama,baba ta fice da flask din abincinta.


Tana tsaye ruwan ya tafasa,ta dauko cup ta juye ta dawo falo.



Tana daga tsaye take surbarsa saboda tana ganin kamar zaifi tsarga mata,tana gab da shanyewa taji motsi kamar an buda qofar falon,saita waiwaya a hankali tana dan jin tsoro ya kamata,duk da tasan cewa gidan cike yake da tsaro,babu wani abu da zai gifto su har nan.



A hankali yake takowa cikin parlour din,idanuwansa zube kam wayar hannunsa da yake amsa kiran dake shigowa,wanda handsfree ya sanya mata.


Yayi wani sassanyan kyau cikin wasu yellow din Kaya da sukayi matuqar fitar da sigar kyans da kwarjininsa.


Idanu suka hada shida ita,nauyin daya zuba ciki nata idanun ta hanyar nutsa nashi idanun cikin nata ya sanya ta janye kallonta,yayin da shi kuma yaci gaba da kallon nata yana ci gaba da amsa wayar.


Kamar kowane lokaci da zai dora idonsa akanta,zuciyarsa ta soma masa lissafe lissafe a kanta,baisan yana mata kallon from head to toe ba sam,koda wani ya fada zai iya qaryatawa,maganar amiru ta soma dawo mishi akan canzawarta,tabbas hakane,shima ya gani,ya hango abubuwa masu tarin yawa,kayan jikinta sunyi matuqar amsarta da haskata,baisan yaushe chocolate colour skin ta fara masa kyau a idanuwansa ba,murya can qasa yace


"Bye" yana katse wayar tare da sokata a aljihunsa,har yanzun kaltum dake tsaye yake kallo,wanda taci gaba da tsaiwar ne saboda a ganinta sam bai kyautu ta ganshi ba ta kuma wuce,duk da yadda takejinta a takure saboda kayan jikinta,wanda suka bayyana albarkatun qirjinta qwarai,don ta dauka daya daga cikin brasier din da jawahir ta sako mata cikin kayan.


"Ina yini" ta fada da zazzaqar muryarta ba tare data juyo ba,sautin ya tafi a hankali cikin kunnensa,yadan rage girman idanuwansa kadan


"Kina lafiya?"


"Alhamdulillah" ta amsa shi still ba tare data juyo ba,hakan ya bashi mamaki,tsaiwar me take ta bashi baya haka?,idanunsa saman hips dinta na wasu sakanni,saiya dauke kai,yana sake matsawa zuwa inda take tsayen,yana jin a ransa kamar akwai wani abu da take boyewa batason ya gani ne.


Koda ya qarasa din sai da yayi dana sanin zuwan,tsigar jikinsa ne ta dinga zubawa,ya dauke idanunsa ta hanyar daukan remote yana lalubar tashar da akace masa yau zasu sanya wasan polo live daga Amsterdam lokaci daya kuma yana bata umarnin


"Ki dauko hijabinki kizo muje" babu musu a tsakaninsu,ko wanne ciwo takeji a jikinta ba zata iya masa jayayya ba,don haka ta ajjiye cup din hannun nata da sauri ta juya ta nufi daki,duk da haka sai daya dan bita da kallo kafin ya sake janye idanun nasa yana sakin ajiyar zuciya.


Bata jima ba ta fito ta hijabin sallarta har qasa,ta sameshi ya bawa tv attention,da alamu yana jin dadin kallon,saita saci kallon tvn don ganin me yake kallo haka,a iya dan zamanta dasu ta karanci yana son doki da wasan dokin ma gaba daya,duk da haka haka ya ajjiye remote din ya miqe ta bishi a baya.


Kamar kowanne lokaci shuru ne ya musu rakiya har zuwa makeken kantin zamani,wanda yake maqare da dukka nau'in kayan amfani.


Yadda suke haba haba dashi ya tabbatar mata ba qaramin customer bane,kuma ba qaramin jin dadin zuwansa suke ba da alama,kujera ya samu nan ya zauna,yace ta shiga ta zabi dukkan abinda taga tana so,sai tayi saroro,saboda sam bata taba zuwa ita daya ba,yawanci da jawahir suke zuwa,daga bisani ta fara takawa a hankali a tana duddubawa har tayi nesa da wajen da yake zaunen.


Tayi nisa sosai cikin babban kantin amma haka taketa shawagi,ta kasa zaben wani abun azo a gani,saboda kome tayi niyyar dauka sai tayi tunanin me tsada ne,ta qyale kada taje a lafta masa kudi,saboda nan din ta fuskanci komai nasu kudi ne tsububu a cikinsa.


"Hey baby" taji an fada daga bayanta,saita waiwaya da hanzari,suka hada idanu dashi yana jifanta da murmushi,matashin saurayine wanda a qiyasce bazai wuce shekara ashirin da biyar ba,sanye da qananun kaya,hannunsa riqe da wayarsa,yana da kyau dai dai misali,hakanan kana kallonsa kasan dan gayu ne


"Bari na tayaki zaben,na fuskanci tun dazu kike yawo kin kasa daukan komai" kafin tace wani abu ya karbi dan kwandon hannunta,ya fara duba kayan mata na amfani yana jefawa a kwandon,yana kuma dan janta da hira ta yadda zata saki jikinta dashi.


Sannu a hankali ya fara cika kwandon da kayyakin amfanin mata,saita ci gaba da binsa a baya,duk da cewa amsar kowacce tambaya tasa daga eh sai a'ah.


Su n kusa qarshen layin da suke ciki,kamar ance ta daga idanu ta hangi samir a tsaye daga qarshen line din kayan turaruka,dukka hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya kum tsaya qyam ya raba qafafunsa kamar wani soja,babu digon annuri a saman fuskar tasa,sai idanuwa daya kafesu dashi ita da saurayin........

Post a Comment

0 Comments