TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

MIN QALB PAGE 5-6

 09033181070[3/8, 1:22 PM] Zafafa: *_MIN QALB 5_*

_Mamuhgee_



##Zafafa biyar#pay@ 09033181070 or 09032345899 


Usi ne yafara ankarewa dashi yaga yanda qarara idanuwansa da fuskarsa suka nuna tsananin qyama da takaicin Abinda idanuwansa suka gane Masa Nan ya fahimci cewar yarigada ya ganta yayi saurin dauke idanuwansa dga kallonsa yayi sbd tsananin kwarjini da cika masa ido da  yayi yai saurin yin qasa da murya Yana cewa'"


Amah kiyi saurin barin Nan kokuma ki maida kudin.


Batareda ta fahimci Abinda yafadaba ta kallesa tana cewa'' oya yi sauri mutafi nagama ramawa kura aniyarta  anan,

Insfector Garba Kuma zaizo yasameni a gida nasani acan zan fanshe wannan tozarcin dayamin agaban baqonsu da ko kallo bai isheniba bare na tsaya harsu gama kulasaba kafin su dawo kanmu.


Gaba tayi tana zuge zip din Jakarta data saka kudin usi na biyeda ita Yana satar waiwayen baqon dake bayansu fuskarsa a hade ko inda suke bai kallaba ua nufi motarsa Yana duba agogonsa dake nuna Masa lokacin ganawarsa da mahaifinsu yayi gashi shi mutum ne dayake aiki da lokaci komai lokacinsa yake ware Masa sbd tsari dayayiwa rayuwarsa.


Amah ko takan babbar motarsa batabi ba sbd gama quluwa datayi da Abinda Garba yayi Mata.


Usman kuwa suna fitowa tafiya kadan sukayi yaja ya tsaya jikin wata bishiya Yana sauke ajiyar zuciya ya zauna Yana jingina kansa jikin icen ya sake sauke numfashi ya kalleta yana sakin 'yar dariya kamar Babu rauni da tsamin duka a jikinsa yace"


Amah kina ganin akwai ranarda zamuyi rayuwa kamar sauran mutane masu daraja???


murmushi itama ta saki tana kallonsa cikin kulawa da rashin nuna damuwa kafin ta bude Jakarta ta shafo kudin dake ciki tana kallonsu tace"


Bama buqatar wani rayuwa ko gatan daya wuce muyi rayuwarmu ayanda take,

Karka saka wani Rai a wani rayuwan bayan kasan mu din asalin 'yayan bola ne,

Bamuda wani rayuwa bayan Wanda muke ciki a yanxu.


dariya Usi yayi hadi da miqewa tsaye yafara tafiya yana Dan dingyashi saboda raunin da akai masa a kafa sosai yake masa zugi

 cikin sake quluwa Amah tabi shi da idanuwa tana tunano irin kalar rashin arzikinda zatayiwa Garba.

 

Tafiya sukeyi suna firarsu cikin nishadi sbd su Sam Babu Abinda suke ajiyewa arai ya damesu.



Suna shiga gidan da Aunty Salamatu suka fara cin karo aikuwa ta soma sakin numfarfashin masifa dan Sam bata manta dibar albarkan da Aman tayi Mata ba kafin fitarta,


 Amah na ganin hakan ta fuske ko kallonta batayi ba ma tai wucewarta zuwa dakinsu jakarta ta ajiye hadi da cire karamin hijab dinta ta fito ta nufi qofar dakinsu kawu ta tararda 

 Usi zaune tare da Kawu wanda ke tambayar Usin" wane shegen kurtun Dan sandan ne yayi maka wannan ta'asar???

 

Qwafa yayi Yana taba qafarsa dake Masa zogi yace"


Ai kawu idona idon Sargent salisu saina saka anyi Masa zanen yarbawa har a goshi da qeya,


Shikuma insfector Garba duk Yakuma zuwa gidan Nan gurin amah saina Masa askin kwalba.


Cikin takaici kawu yace"


Shi garban me kama da an sulala naman Kai shine yasa aka maka wannan dukan? Kokuwa shi Sargent salisu din dayafi kama da danyar alala yayi gaban kansa yayima wannan dukan kamar wanda yayi kisa¿


Maman basiru dake kusa dasu tana aikin wanke rishonta ta tabe baki tana cewa'"


To meya raba dambe da fada¿


Tsuke fuska kawu yayi Yana kallon iyami dake fitowa daki daukeda robar garin tuwo dazata gyara yace"


Iyami kinajin matar nan nafadamin mgn bazakiyi Mata dukanda mijinta ba mijintaba ko yayanta bazasu ganetaba,

Waini iyami kodai auren dole ne mukayi?da kike wulaqantani ne kokuwa talauci haukane?


Dariya usi yasaki Yana cewa'"


Wlh kawu talauci haukane tunda gashinan duk bamuda hankali....


Butarda dake gefenda ya dauka a hasale 

Usin na ganin hakan ya tashi da sauri 

Kawun ya jefasa Masa Bata tsaya koina ba butar sai kan galan din kalanxir din maman basiru Wanda zata zubawa rishon take ya kwanta tana tsiyayewa dama kawun can yayi niyar jefawar ya tsuke fuska yahau masifar usi ya rainasa.


Usu kuwa dariya yake Yana kallon maman basiru dake kallon kalanxir dinta cikin tuquqin zuciya Tama rasa Abinda zata ce musamman ganin fuskar kawun tasan yanxu tana mgn zai Kira mijinta yace suje police ayi musu iyaka Dan aikinsa kenan cewa aje police ayi Masa iyaka da mutum.


Allah ya isana tace cikin ranta tana cewa bakinta yaja Mata saka baki cikin maganar Wanda Basu barin kowa da Allah.


Amah dake kawowa ta kalli maman basiru da idanuwanta sukai rau kamar ta saki ihu sbd takaici ta saki dariya tana cewa'


Iyami wlh karki Bari usi ya rainaki kaman yanda ya Rena kawu.


Kallon Usin iyami tayi tace'"

Kaje ka kimtsa idan kungama Abinda kukeyi kaida kawun,

Wlh usman ka daina biyewa wata fitinar.....


Iyami ki fito fili kice ni basai kin tsaya layi ba.


Nidai yanxu bance kaiba..


Iyami Anya kinason shiga aljanna kuwa?


Amah na ganin haka tasan fadan zasu Fara tayi saurin fiddo da kudin Jakarta take kalmar dake bakin kawu ta katse Yana qoqarin hadata.


Iyami ma aje robar hannunta tayi tana matsowa

Kawu ya bita da harara da qananun idanuwansa masu kama Dana 'yan Korea yace"


Ke amatu maida kudin Nan jaka sai anjima zansan me zaayi dasu tashi tafi daki dasu ki aje.


Kawu albashina ne na karba gurin aiki da niyar belin usi saigashi Basu karba ba sbd rawar jikin sunga wani baqonsu.


Nasani ai dama kedai tashi dasu daga Nan kafin wani ya wafce su.


Fizge jakar iyami tayi tareda cire kudin tana cewa'"


Wlh Babu dakinda zata kaisu Dan nasan ba albashinta bane,

Amatu kifadamin gskia inda Kika samo kudin Nan??


Kallon kawu tayi daya qura Mata ido Yana jiran jin Abinda zata fada saidai yanda tayi da fuska yasa ya fahimci inda kudin suka fito ya gyara zama tareda murzawa idonsa toka ya matse fuska yace"


Iyami so nawa nake fada Miki kidainawa yarinyar Nan haka?

Addua akeyi Allah ya shiryamanasu yabasu abinyi,

Kinga banason kina irin haka saiki tozarta gaban maqiya ga gida cikeda da maqiya komai muke ciki kunnuwan munafukai akanmu.


Kallon takaici tamasa tareda tura kudin cikin zaninta tana cewa'"


Allah yasa kugane yakuma shiryaku ku duka.


Ganin maman junior shugaban munafukan gidan ta shigo yasa ya hadiye maganar dayayi niyyar yi tareda cewa amatu "jeki.


Tana juyowa Ido biyu tayi da maman Junior wacce da alama daga kasuwa take ko dan jakar dake jikinta da uban mayafin data yafo daya gama miqewa da zufa ta dauke Kai ta wuce tana tsokanar junior dake gefen maman daukeda leda dayake yaron mutumintane suna dasawa sosai 

Ko kallon maman taqiyi sbd ganin irin kallon masifar datake binta dashi tareda harara.




***

Bakin Babban gate din ZABEERA motarsa ta tsaya batareda yayi horn masu gadin suka bude Masa da sauri tsananin girmansa dasuke gani fiyeda kowa a gidan idan aka cire iyayen familyn.


Da kansa ya tuqo motar sbd yabar malam take gida da yaronsa suyi sorting matsalar data kaisa hannun 'yansanda harya kwana station.


Sake kallon agogonsa yayi bayan ya kashe motar kafin yafito a nitse ya rufe motar ya nufi doguwar hanyar dazata sadashi da sashen Modibbo wato mahaifinsu.


Tafiyar mintuna hudu ce takaisa shashen Yana tura babbar qofar palon ummi na fitowa babbar 'yar gaban goshinta nuratu na gefenta kowannensu fuskarsa Babu alamar farin ciki Wanda daga gani ummin ce ke cikin baqin cikin nuratu ke tayata damuwa.


Dattijuwace saidai hutu da tsananin jin Dadi da ilimi tareda gayu yasa shekarun nata sun dai 6oye sbd jikinta dayakeda kyau sosai.


Kallon daya zakayi Mata kasan itace matar gaban goshin me mallakar gidan sbd tsananin Isa da ikon datake nunawa.


Cak ta tsaya bayan ganinsa zuciyarta na qara tafasa da takaici saidai tayi controlling fitowar fushin nata ta kallesa da fararen idanuwanta 


Batareda ya kalli fuskartaba Yana kallon qofa cikin nutsuwar muryarsa data sanya nuratu Dan matsawa gefe tana kama kanta sbd tsananin kwarjininsa yace"


Umme barka da yamma,

Kina lafiya??


Kamalalliyar fuskarsa dake daukeda wani sirrin kyau ta kalla tana danne bacon ranta tace"


KHALIL baya daukan maganata ka fahimtar dashi inason yayi aurene sbd lafiyarsa sbd mganarka kawai zai saurara sbd Kaine ubansa.


Tana fadar hakan ta wuce Bata tsaya jiran Abinda zaice ba sbd tasan ba maganar zaiyiba ko zasu shekara ahaka tasan dai yaji Kuma ya fahimta.


Wannan shine daya daga cikin Abinda ta tsana gamedashi shine tsabar miskilancinsa datake kallo amatsayin ji da Kai ganin yafi dukkanin 'yayan ZABEERA zama successful business tycoon Wanda yake muamala da manyan gwamnati da sarakuna.



Kai tsaye yashiga cikin palon na Modibbo bakinsa na fitarda sallamarda modibbon ne kawai yaji ya amsa sbd sanin yanda mgn ke fitowa abakin 'dan nasa.


Gaban Modibbo din ya zauna tareda dagowa cikin girmamawa yace"


Barka da yamma modibbo,

Ka yini lfy?


Alhmdlh MAHMOUD

Ya iyalin naka??


Alhmdlh"kawai yace tareda kallon 'dan uwansa dake gefensa zaune ya sakar Masa wani qayataccen murmushi Wanda duniya dashi kadaine zakaji yayi doguwar magana ta fira a kaf family haryayimasa murmushi Wanda ko mahaifinsu iyakacinsa dasu bin umarni da biyayya Amma Khalil ne kadai Wanda ke ganin sakewar Mahmud din ciki kuwa harda matarsa wadda iyakacinsa da ita zaman biyayyar aure da bin umarni tareda mutunta juna.


Cikin murmushi Khalil ya kallesa Yana cewa'"


Allah ya taimaki ZABEERA na hudu.


Batareda ya kallesa ba ya murmusa har fararen haqoransa suka bayyana sbd wannan wata zolayace da Khalil din yake Masa tun suna Yara sbd ya tsokanesa musamman yanxu dayasan karban wata sarauta shine Abu na qarshe dazaiyi arayuwarsa sbd ya tsaneta indai akansa ce.


Gyaran murya Modibbo yayi tareda kallonsu suka nutsu tareda maida hankalinsu akansa yasake gyara murya cikin bada umarni da hukuntarwa yace"


Mahmud safiyar yau ZABEERA ya aiko da saqon a sanar dakai waadin mallakar kujerarka ta ZABEERA na hudu Dana bayarda sunanka yacika

Zaka shirya komawa masarauta tareda iyalinka.


A matsayin mummanan sako ya dauki zancen sbd zuciyarsa da Bata karbi abinba ko da a mafarki saidai Kuma Sam fuskarsa Bata nuna alamar gamsuwa ki rashinta Khalil kawai ne zai qarar da cewa wannan ba Abu bane me yiyuwa a rayuwar md zabeera din.


Cikin girmamawa yace"


Modibbo idan naje Naga ZABEERA akan wannan alamarin Ina fatan bazan 6ata maka ba???


Kallonsa Modibbo yayi na tsawon sakanni kafin yace"


Idan har kana tunanin sanarda mahaifina ne cewa baka karba saqonsa ba tabbas zaka Sa6a ne.


Cikin sake nuna biyayyarsa yace"


Inshallah ba hakan bane.


Karka damu zakaje Amma sai ranar tafiyarka gaba daya.


Shiru yayi na Dan lokaci kafin ya miqe tareda cewa'"


A yini lfy Modibbo.


Ficewa yayi Khalil na biye dashi suna fitowa ganin yanayinsa yasa Khalil barinsa yaje yasamu nutsuwa tukuna duk da Babu Abinda ya nuna na damuwa ataredashi.


Motarsa yaja ya qarasa sashen dayake can kusan qarshen babban gidan Wanda yake nasa yanayin parking yafito yashige.


ZARAH dake zaune palon tareda me aikinta ta dago Kai tana ganinsa ta ajiye wuqar datake yanka gwaiba da ita ta miqe tareda qarasowa gabansa tana Masa sannu da zuwa cikin nutsuwa daidai shigewarsa hanyar dazata sadashi da zuwa sama inda dakinda yake ya amsa Mata da madaidaicin sauti sbd Bata iya wulaqanta ta sbd darajar sure dakuma biyayyarta tareda darajar Modibbo daya aura Masa ita.


Ganin yanda ta taso din Dan kulawa yasa yadan tsaya tareda kallonta cikin Ido sosai Yana qoqarin Bata mahimmanci yace"


Ina buqatan light abinci Mara nauyi.


Murmushin qara ganin girmansa tasaki sbd yanda akoyaushe yake mutunta zamanta matarsa har kaqoranta suka bayyana ta matsosa sosai tareda kama hannun damansa ahankali ta riqe cikin nata ta dago ta kalli fuskarsa da ya juyo ya kalleta tace'"


Thank you MD ZABEERA.


Kallonta yayi yace"


Ina jira""ya haye saman tana binsa da kallon kauna fuskarta cikeda murmushi kafin tajuya ta nufi hanyar kicin tana cewa'"


Hafsat zo ki niqamun kayan Miya a blender.




**

Umme tunda Takoma palonta ta zauna tana sauke numfashi tanason saukar da zuciyarta ga wannan al'amarinda yake faruwa da ita ako yaushe.,

'yayanta kusan sune koma baya a cikin familyn ZABEERA,

Dukkanin 'yayan Modibbo matane su goma sha shida Khalil da Mahmud ne kawai maza Kuma sune dukkanin wani burin Modibbo ya Dora akansu sai gashi ita nata 'dan shine wani iri Sam ko kyashin 'dan uwansa bayayi duk da Shima Barr ne babba me zaman kansa Kuma yanada nasa arzikin daya Tara bana mahaifinsu ba Amma Sam bai kamo MAHMOUD ba Wanda duniya shi kowa yafi sani a familyn ZABEERA yanzu.


Burinta idan har MAHMOUD yafi Khalil ta wani bangaren to shi zai karbi zabeera na hudu ta yanda zai take MAHMOUD din ta fagen suna,arziki,mulki,dakuma martaba a idanun mutane saigashi Rana tsaka su Modibbo da zabeera sun zaba MAHMOUD Wanda Sam bazata yardaba.


Kamar daga sama taji daga bayanta ance"


Aisha wannan karon damar kice ta qarshe kisa Khalil yayi aure ko su Modibbo zasu sauya shawara su zabesa sbd shi wancan miskilin baya buqatar kujerar zabeera,

Duk wani suna ko arziki ko girmanda ake buqata ya samu abinsa da kansa amatsayinsa na Architecture MD ZABEERA so yanzu zabi ya rage naki na kisan yanda zakiyi.


MD bayada uwa a duniya bayada dangin uwa a duniya to kina tunanin idan yazamo zabeera na hudu waye zai nuna Miki iyakarki idanba zainab uwar matarsa ba wadda ko kadan kinsan Bata qaunarki.


Rintse ido ummen tayi tana jinjina 'dacin da zuciyarta keyi da zafi tace'"


Babu Abinda yakai ciwon hassada zafi a zuciya wlh Maryam,

Tun kafin MAHMOUD yazo duniya bandamu da uwarsa ba harta haifesa ga bar duniya bantaba kulawa dashiba duk da tsananin biyayyar dayakemin Amma tunda yafara zama wani abu a rayuwa Abu yazo ya dameni wannan masifa dame tayi Kama wlh zuciyata takasa samun nutsuwa shawon shekarun cigabansa

Amma wannan karon zanyi Abinda bantaba yiba.


Dawowa gabanta haj Maryam tayi tareda zama kusada kejerar dake kallonta tace'"


Me kenan???


Miqewa tayi tsaye tana takawa ahankali tace'"


A duniya Babu Abinda Modibbo da zabeera suka tsana irin cin Amana da zubarda mutunci,

Zansa su tsanesa tsana mafi Muni wadda zatasa sunansa yafita daga cikin zabeera bama zabeera kawaiba duk duniya ma saisunji yafita ransu sundaina ganin mutuncinsa.


Murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana cewa'"


Wane laifi?

Wane cin Amana Kuma???


Laifin ciki

Da laifin zubarda mutunci ta hanyar aikata 6anna.


Wani murmushin haj Maryam tasaki tana cewa'"


To waye yayiwa cikin ni ki fahimtar Dani yanda zangane.


Baiyiwa kowa cikiba Amma kudi zasusa ace yayi cikin.



Aisha kina tunanin akwai Wanda kudi zasusa tace MD yamata ciki karki manta MD mutuminda kowa ke mutuntawane wannan maganar bamai karbuwa bace mu canza shawara.


Maryam kudi duk inda kike tunanin su sun wuce Nan,

Akwai mutane birjik a duniyar Nan dazasuyi aikin komai sbd kudi musamman kudi irin wainda zan zubar akan wannan aikin.

##Mamuh##

#ZAFAFABIYAR##

[3/10, 9:05 PM] Zafafa: *_MIN QALB 6_*


Wani 'dan murmushin mamaki haj Maryam tasaki tana miqewa tsaye bayan ta ajiye qaramin pillow din kujera data dauka ta Dora a cinyarta bayan zamanta,ta tsaya gaban umme din ta kelleta tanason Bata qarfin gwiwa da Abinda take Shirin yi tace'


Aisha Idan har wannan mafitar kike tunani zata bullar damu ga Abinda mukeso to haqiqa Ina taredake ako wane mataki dazamubi Wanda zai kaimu ga nasa,

Saidai Abu daya anan shine abin dubawar,shi Mahmud din tayaya zai zauna yana kallo ya karbi wannan false accusations din Wanda zaiyi tarnishing image dinsa a idon duniya.


Kallon haj Maryam umme tayi tareda sakin murmushin farko a ranar ta yau tace'"


Mune zamuji Masa ciwo Kuma mune zamu zuba Masa gishiri a ciwon Kuma mune zamu hanasa sosawa,

Abinda kenan wato shine Kinga Maryam narigada nasan weakness din MAHMOUD wato duk duniya rauninsa biyu ne wato mahaifinsa da Khalil,


As long as Modibbo zai zuciya akan wannan alamarin to tabbas MAHMOUD yagama yawo sbd duk wani cigabansa rushewa zaiyi.


To wani hanzari ba gudu ba ta Ina zamu Fara wannan Shirin?

Ma'ana ta Ina zamu Fara neman me wannan aikin? musamman fa Kinga aikine me tsananin hadari sbd 6atawa mutum kamar MAHMOUD suna a duniyarnan babban risk ne ataqaice ma kamar mutuwace kake kirawa rayuwarka sbd kamar yanda yake dinnan a natse zuciyarsa a bushe take,

Duk Wanda zaiyi Mana wannan aikin dole Muna buqatar Wanda zuciyarsa tagama mutuwa akan kudi.


Karuwa,,,,,,


Mene??? umme tafada da 'dan sauri tana kallon haj Maryam din sbd qyamar ma sunanda tafada.


Yes karuwa nace sbd karuwace kawai zata iyayin komai akan kudi,

Ita kadaice zata iya wasa da mutuwa akan kudin sbd sunanta matacciya daga lokacinda wannan alamarin ya lalace.


Dafe goshi umme tayi tana cewa'"


Maryam daina fadar sunan karuwa acikin zabeera sbd fadar sunanta kawai babban laifine a cikin ahalin Nan,

Kawo karuwa acikin zabeera shine laifi mafi Muni dazamuyi Wanda yafi Abinda muke Shirin aikatawa.


Aisha Idan har zamu iya qetare duk wata iyaka mu aikata irin wannan abin to inaga kawo karuwa ba komai bane,

Wannan zancen ma bai kamataba munayinsa acikin zabeera ki shirya gobe muje gyaran qafa zamu tattauna acan kafin Nan kin yanke shawara.


Ficewa tayi tana ayyanawa aranta dole Khalil yazama zabeera na hudu sbd 'yarta nuratu da ita su samu kyakkyawar gaba me kyau.


Umme kuwa kasa zama tayi palon ta wuce dakinta tana dafe kanta dake sarawa sbd damuwar data sawa kanta ga mafita na neman gagararta

Duk abinta bazata iya kawo karuwa ba a zabeera sbd sanin tsananin alada da Matsin dokoki irin nasu Wanda sune asalin zabeera da Abinda yasa suka fita dabam acikin mutane,


Familyn ZABEERA family ne dasukeda wani irin tsatsauran raayi da dokoki Wanda suka zame musu tamkar addini,

Basa auren bare,basa zama da bare,basa barin 'yayansu Mata suyi karatun jamiaa a qasar Nigeria saidai qasashen qetare na laraba sbd karsu barsu anan kowa yagama sanin 'yayansu wainda suke tamkar suna musu kulle ne sbd ko muamala basa barin yayansu suyi da mutane sosai,


Asalinsu Hausa Fulani ne saidai yanayinsu yasa ake musu kallon Fulani sbd yawancinsu farare ne masu 'yar doguwar fuska kalar Fulani,

Sarauta tasa dokokinsu da tsaurin raayinsu yin yawa saidai Kuma babban Abinda yasa suke buka mulki da iko shine Babu wani Dan ahalin daya taba karya doka ko qetareta,

Suna tsananin tsoro da bin umarnin manyansu musamman ZABEERA na daya acikin 'dakinsu asalin dahir zabeeran farko MUHAMMAD USMAN ZABEERA wanda suke Kira da ANDI,

Andi shine mahaifinsu Modibbo mahaifinsu MAHMOUD Wanda yake amatsayin zabeera na biyu Wanda yayi shekaru akai kafin yayi murabus ya sauka yabaro asalin zabeera dake cikin babban birninsu ya barwa qaninsa mulkin Wanda shine amatsayin zabeera na yanxu Kuma shine zabeera na uku Wanda ayanzu ne zaayi na hudu.


Andi shine shugaba mafi tsanani da duk zabeera ake tsoro ake Kuma gudun bacin ransa dagashi dai Modibbo daya kusan zartashi fiyeda komaima na tsananin zafi da dokoki,


Babu wani abu magi qyama agurinsu irin cin Amana da Abinda zai taba martabar ahalin,

Duk babban attajiri tareda manyan Yan siyasa abokanan hurdar familyn ZABEERA ne shiyasa ake matuqar giramamasu da mutuntasu,


Kaf familyn Babu wani sakewa atsakanin iyaye da 'yaya sai bin doka da oda sbd Sam basa Wasa ko sakewa 'yayansu shiyasa 'yayansu ke tsananin shakkar manyansu Dan kaf familyn Babu wani 'da dazaice yataba ganin dariyar manyansu iyaye maza saidai iyayensu Mata,


Modibbo keda Mata uku kowacce tanada Yara hudu Mata Banda mahaifiyar MAHMOUD wadda keda shi shikadai ta Haifa ta rasu tun yanada shekaru bakwai a duniya sai umme datake da Khalil bayan 'yaya Mata hudu,


Umme itace tafi kowacce mace zuba iko da Isa agurin Modibbo sbd zamanta uwargida itace Kuma uwar manyan 'yayansa da duk sunyi aure kusanma wasunsu sunkusa aurarwa Suma.


Umme Bata qaunar 'dan daba nataba saidai Kuma bazata iya cutatar dashiba 'yayanta su kadaine 'yayanta bayansu ba ruwanta da 'dan kowa Koda kuwa zataga masifa ta tunkarosa ne,


MAHMOUD shikadaine yataso a cikin iyalan Modibbo baida mahaifiya,

Yataso ne acikin wani irin kadaici ya rayu acikin kadaicin,

Tun Yana yaro baida Wanda yataba janza ajiki harya girma,

Shi kadai yake komai nasa na rayuwarsa iyakacinsa da mahaifinsa gaisuwa da bin umarnin baitaba jansa ya tambayesa Yaya rayuwarsa take tafiyaba tunda mahaifiyarsa ta rasu bama shi kadaiba kaf duniya baida Wanda yataba jansa ajiki yaji ya yake ba,

Baida kowa aganinsa,

Baitaba shiga cikin 'yan uwansa ba sbd basayi dashi,

Shi kadai yake kwana,

Shi kadai take tashi,

Ahaka yayi rayuwa ahaka harya girma,

Da kansa ya koyi faduwa da yanda zai tashi kansa,

Da kansa yasan yayiwa kansa fada ya tsaya ya nemi ilimi dan yin rayuwa dashi,

KHALIL shikadaine 'dan uwansa dayake dashi Wanda yake tsananin qaunarsa duk da yanda umme ke hanasa muamala dashi saidai Sam qaunarsa Khalil ke Masa Babu Mai iya kwabarsa akan shifa alamuransa,


Khalil na tsananin kaunarsa fiyeda wainda suke daki 'daya Wanda kowa yasan da hakan shiyasa tare sukai karatunsu tun primary har secondary saidai kasancewar Khalil din ba lafiyayye bane asthmatic ne Kuma irin chronic din Nan shiyasa daga secondary suka rabe MAHMOUD Modibbo ya turasa Sudan karatu shikuma umme taqi yarda yaje koina.


A Sudan yaqara samun cikakkiyar rayuwar kadaici Wanda ta hade da rayuwar kadaicin daya baro sai hakan yazame Masa wata sababbiyar dabia wadda yazama rayuwarsa,


Baya fira sbd baida abokan fira,

Yayi gwagwarmayar karatun degree a Sudan na tsawon shekaru shikadai batareda yazo gida ba kokuma wani daga gidan yazo gurinsa,

Babu wani Wanda yataba kiransa yajisa tsawon shekarun bayan khalil sai Modibbo Wanda shine yake kiransa badai shi yakirasaba,


Baitaba damuwa da kadaicin rayuwarsaba da baida kowa sbd ahaka yataso

Hakan shiya kashe duk wani walwala ko muamalarsa da mutane sai kadaici yafi Masa Dadi da nutsuwa fiyeda komai,

Bayasan hayaniya ko shiga jamaa sosai sbd yafi samun nutsuwa a inda kadaici yake.,

Ahaka rayuwarsa ta nitsa inda yasamu nasarori bayan cikakkiyar gwagwarmayar rayuwa dayayi a cikin neman ilimi me zurfi,

Gwagwarmayarsa tazo da nasarori da dama wanda yasa yayi fice cikin manyan mutane da qusoshin qasa,

Zamtowarsa wani qusan Shima sai sunansa yaqarawa zabeera family suna da martaba sosai,

Ya mallaki abubuwan arziki da dama wanda kaf zabeera yanzu Babu abokin karawarsa idan ba Modibbo ko Andi ba wainda sukafi kowa dukiya,

Nasararsa tasa yanzu kusan kowa dangi binsa yakeyi saidai kasancewar bai Saba da a jasa ajikiba yasa baya sakewa da kowa ataqaicema baya iya rayuwa cikin mutane yafison zamansa a Sudan inda acan nasarorinsa suka Fara acan yafi samun nutsuwa idan ya kadaice abinsa

Yana daukar lokaci baidawoba Dan yanafin shekara wani lokacin kafin yazo Wanda duk zuwansa sbd Khalil ne kawai yake zuwa sai Modibbo Wanda yake matuqar giramamawa fiyeda komai arayuwarsa,

Ta bangaren 'yan uwansa kuwa sosai yake sake musu kudi duk da Babu wani sabo ko sakewa a tsakani Amma yakan Basu duk wani abu musamman umme dayake ganin qimarta sbd Khalil batareda yaduba yanda yataso ba sbd idan yace yaduba yanda yataso to zaitsani kowa arayuwarsa.


Ganin kamar MAHMOUD din yayi musu nisa sosai Wanda yanzu suke alfahari dashi amatsayin Dan zabeera sbd mutunci da girma tareda qimarda yake sake kawowa zuriar sai suka yanke shawarar nemar Masa auren 'yar qanin Modibbon Wanda yake kan kujerar zabeera ayanxu ZARAH,


Zarah ta auri MD ZABEERA cikeda alfahari da auren sbd samun miji yanxu kamarsa dibbin nasara ce arayuwa,

Tana tsananin qaunarsa saidai sanin yafi karfinta yasa ko a mafarki Bata tunanin aurensa saigashi Allah yayi shidin mijintane Wanda taqara haukacewa a tsananin qaunarsa,


Baya musu arayuwarsa sbd baisaba doguwar mgn ba ko ta fannin business dinsa ko deals dinsa Abune nayi ko bari bayasan dogon Bata lokaci shiyasa baibi wani dogon sawa Kai ciwon kaiba ya amince musamman da akayi saa zarah mace ce me tsananin nutsuwa da hkr ga biyayya da fahimtar Abu Sam Bata cusa kanta gurinsa tunda akayi auren

Rayuwa suke ta mutunta juna da kiyaye gudun shiga haqqi.,


Shi mutum ne marason damuwa da hayaniyar mutane akusa dashi shiyasa idan har yananan ko volume din tv bata sawa sosai sbd karta damesa,


Bata taba yin wani abu Dan damuwarsa ko sakasa ciwon Kai ba shiyasa yake respecting nutsuwarta musamman dayake dama baya shaawar mace arayuwarsa saidai sbd girman Modibbo da Andi dakuma qimarta yasa yake qoqarin bawa auren nasa haqqin.



***

Yau amatu Bata fita aikiba Saida tagama hutawarta a gida kafin tayi Shirin aikin ta fito tareda usi Dan dama kullum tare suke zuwa aikin


Suna Isa tun a harabar gurin suka fahimci da masu kudi a gurin saidai rashin saar dasukayi gefen VIP saloon dinsu sukaga motocin Wanda sunsan Babu rabonsu yau acikin aljihun masu wainnan motacin masu kama da tarwadar ruwa sbd sheqi.


Direct gefen restaurant suka nufa usi na cewa"


Juyawa zanyi amah zanje gurin insfector Garba naji uban me zaimin dayake nema na tun Daren jiya.


Tana shigewa tace' idanma ni yakeson katayasa lallashi kafada Masa duk yabari nayi Ido biyu dashi Aina sace Masa shegen cikinsa me kama da tayar motar Mai.


Juyawa yayi Yana cewa' nizan Fara nuna Masa kalar rashin mutuncina kawuma nacan Yana jiran ganinsa.

#mamuh#

______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.


        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta vWhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.


______________________




#MIN QALB❤️

Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

Post a Comment

0 Comments