TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

SAKAYYAH page 72

 *_Last Page_*


Uncle Naseer kuwa, daga ƙugunsa zuwa ƙafafunsa ya ƙone ƙurmus kana bai mutuba yayin da fuskarsa yayi baƙiƙƙirin yanayin halittar fuskarsa ta sauya tamkar an babbaka kare. Mamansa, Babansa kuwa atake rai yayi halinsa Uncle Naseer kuwa cikin ƴan kawo agajine suka daukesa suka kaisa asibitin cikin.

 Taraba.

Daga ƙarshe dai dole Lamiɗo aka kira Lamiɗo kam lokacin da akace Uncle Naseer yayi hatsari sosai yayi mamaki kasancewar baisan zuwansa garin ba kana yayi mamaki da akace iyayensa sun mutu...

    Lokacin da Lamiɗo ya isa asibitin ya samu ina baki ɗaya Uncle Naseer babu abinda yake Banda jujjuya kai cikin tsananin azaba da Kiɗima sosai Lamiɗo ya tsorata da ganin yanda halittarsa ta sauya baki ɗaya jikinsa yayi sanyi ya sake jin tsoron Allah da kuma tsoron saɓawa Ubangiji.


Uncle Naseer kuwa Cikin matsanancin kuka da radaɗin azabar daya game jikinsa ya kalli Lamiɗo kana ya riƙe hannunsa tare da cewa.

“Na ƙulla sharri na kulla rashin imani na ƙulla shirka da riya da yawa gashi Allah ya kamani lokacin da banyi zato ba lokacin da nake tsaka da shirya makirci na zama abin tausayi kuma abin ƙonawa cikin wanan azabebuyar wuta”.

Kai Lamiɗo ke girgiza wa cikin tsananin tausayi da son kwantar mishi da hankali Amman ina.

Cikin ihu da kururuwa Uncle Naseer ya cigaba da cewa.

“Gashi tun daga nan duniya Allah ya fara ƙonani da wuta ina ga naje lahira nayi tsafi na sadaukar da mutane da yawa nasha jini”.

Kai Lamiɗo ya girgiza cikin sanyi da mamaki yace.

“Babu amfanin wannan maganar Naseer kawai ka tuba zuwa ga Allah kayi ta Istigfari”.

Cikin kururuwa da azaba Naseer ya girgiza kai tare da faɗin.

“Bazam iya ba bana jin zan iya tuba Ni mushrikine na haɗa Allah da wani saboda duniya wayyo nashiga uku na lalace kaicona wayyo Ni wayyo kaina”.

Kallonsa Lamiɗo yayi cikin mamaki yace.

“Baka iya tuba kuma toh kana so ka mutu da zunubi ne?”.

Kai kawai Uncle Naseer ke girgizawa ya gaza buɗe bakinsa ya nemi gafarar Ubangiji alamar Allah ya hana shi samun rahamar sa haka sai ya cigaba da surutai yana kururuwa tare da faɗe-faɗe da kuma abinda yake aikatawa cikin azaba da zugin da jikinsa ke masa yace.

“Ni nake zama Maciji na tsotsa jinin Amina naso in kashe ta Allah bai ƙaddara ba kwananta yana gaba ita. Asirinta ya ruhu naso in cutar da ita Allah bai nufa ba amma laifin Mahaifiyarta su suka nuna kwaɗayin kuɗinsu ga yanda rayuwa ta zamo mini”.

Ya ƙare maganar cikin tsananin kururuwa da firgita yayin da yake fisge-fusge yana zabura kana idanunsa suka zazzago cikin ihun azaba yace.

“Ka gani ko zan mutu kuma in na mutu cikin wuta zan shiga kaga wutar da ake nuna min kalletafa sai ci take tamkar ba abinda zai kashenta”.

Cikin rashin sanin madafa da tarin tsoron Allah Lamiɗo yace.

“Naseer ka daina kururuwa ka tsaya kayi salati da istigfari”.

Yana cigaba da ihu tare da firgita yace.

“Inyi salati kana ganin wutar da ake nuna min cikin wutar nan wai za'a jefani? Kuma kace inyi shiru”.

Haka dai ya ci gaba da tona wa kansa asiri ɗa'a fade-faɗe abubuwan d yake ganin, yinin wannan ranan ya mutu aka tattarasu dasu da iyayensa aka binnesa...


A cikin wannan kwanakin kuwa Baffa Jimeta yace Hajja Nana ta tattara kayanta su koma Yola ya gaji da zamanta a Jauro Yaya haka ya ɗaukota ta dawo Adamawa da zama ba don ta soba, Amman bini-bini zatace ya kawota haka kuwa dole yake kawotan tai kwanaki azo a ɗauleta tana komawa bazata rufa wataba zatace a Kaita.


Amina kuwa Alhamdulillah rayuwa ta cigaba da tafiya mata cikin kwanciyar hankali tana ta Istigfari tana zaune Lafiya da Mahaifin Samira wanda har ta samu ciki.

Wata rana ta fito daga gidan Samira kasancewar basu da nisa tayi mata rakiya kasancewar aminaine har zuwa yanzu suna Aminanta kansu.


Suna fitowa suka ga wani mahaukaci yara na binsa suna ta ihu yana cewa.

“Nine dai Boka Kar'uzu na aikata shirka na ɓatar da mutane na shuka zunubai da yawa Ni nariƙa yiwa mutane Sihiri!”.

Cikin tsananin mamaki da rawan jiki Samira ta kalli Amina tare da cewa.

“Amina wanna Boka Kar'uzu ne fa”.

Da sauri Amina ta dafe ƙirjinta tace.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wallahi Samira shine rayuwa ba tabbas duk wanda ya saki Allah ya kama waninsa ya shiga uku”.

Cikin sanyi Samira tace.

“Wallahi kuwa Allah ya yafe mana Ubangiji yajiƙanmu ya gafarta mana zunubanmu”.

Cikin kaɗuwa da rauni Amina tace.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”.

 Boka Kar'uzu kuwa cikin ihu irin na ƙazamai lalatattun mahaukata da ƙarshen su ya munana ya cigaba da ihu yana faɗe-faɗe yaje zai tsalle ke kwalta wata ƙatuwar Mota ta buge kansa atake yayi daga-daga akan kwaltan mai motar kuwa ko tsayawa baiyi ba ya gudu.

Irin ƴan iskan samarin nan ne suka sa Shebir suka kwashe Jejjegen naman gawarsa suka tura aƙaton kwalbet da ruwa ke gudu ruwa yaja gawarsa ya wuce ya kai sa cikin Fadamar Gembila kifaye suka samu abinci.


Haka dai Rayuwa ta cigaba gaba da tafiya mai aikata Alkhairi ya fuskanci Alkhairi mai aikata sharri ya fuskanci sharrinsa ra'anul aiyn...


Morocco rayuwa ta cigaba da tafiya cikin daɗi da kwanciyar hankali Keyah yayi kuɓul-kuɓul dashi ya shiga wata na takwas har ya fara tsayuwa Moddibo ne zaune a tsakiyar falon Didi yayin da Keyah ke rarrafe cikin Murmushi Moddibo yace.

“Iyeeee Toyi manga toy-toy Toyi manga toy-toy manga”.

Yana ɗan tafa hannunsa Keyah kuwa ƙoƙarin miƙewa yake yana ƙyalƙyala dariya.

Didi dake gefe tayi Murmushi tare da cewa.

“Ohhh zai fa haukataku in baku nutsu ba fa”.

Dariya Moddibo yayi kana yace.

“Didi kin gani dai ya fara tsayuwa ko”.

Kallon Keyah dake tsaye ya dafe jikin kujera tayi tare da faɗin.

“Toh Barka tunda ya fara tsayiwa yayi kyau anyi Sa'a Barka”.

Matar Ibraahim dake gefen Didi tayi Murmushi tare da cewa.

“Wallahi kuwa Didi kallifa ya tsaya fa”.

Sai kuma ta juya ta kalli Khausar tace.

“Ba ina faɗa Miki ba shekaran jiya ya riƙe kujera ya tsaya ba. cewa kin dai ji baki yardaba tunda ba ki gani ba Lalla Khausar”.

Murmushi Khausar tayi tare da cewa.

“Ato yanzu kam na gani da idona Oum Keyah”.

Cikin sauri Matar Ibraahim ta rungume Keyah tare da faɗin.

“Allah ya raya mana kai da Imani Keyah”.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

Miƙewa tayi ta ɗauki Keyah tana masa wasa ta nufi Side ɗin sa.

Khausar kuwa Ahankali ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace.

“Yah Mu'allim na kwana biyu banji labarin Asma'u ba tun ranan sunan Addah Asiya fa bamu sake haɗuwa ba”.

Cike da kulawa Moddibo ya gyara zamansa yace.

“Toh badamuwa in Sha Allahu da daddare zamu je”.


Bayan Khausar sun idar da sallar Isha'i suka tafi gidan Asma'u afalon suka same su zaune Dr Jameel na zaune ƙasa Asma'u na saman kujera kallon Khausar Dr Jameel yayi tare da cewa.

“Yawwa gwara ma da kika zo”.

Cikin kula Khausar tace.

“Toh meke faruwa?”.

Ta ƙare maganar tana miƙawa Asma'u Keyah data miƙo hannu”.

Karbansa Asma'u tayi cikin sanyi murya take masa wasa tare da cewa.

“Keyah ɗan Albarka”.

Wangale baki yayi yana ƙyalƙyala mata dariya ƙyal-ƙyal-ƙyal rungumesa tayi tare da sumbatar sa kana tace.

“Allah ya maka albarka”.

Khausar na Murmushin yanda Asma'u ke nunawa Keyah soyayya tace.

“Ameen!”.

Moddibo kuwa ido ya ɗan zubawa Asma'u dan ya lura kamar fuskantar na ɗan kumbere kaɗan more especially eyes ɗinta. 

Ajiyar zuciya Dr Jameel ya sauƙe kana yace.

“Ki ganta nan wai ita tana ga bata da rabon haihuwa tunda duk gwaje-gwajen da za'a yi anyi lafiyanta ƙalau nima lafiyata lau, amma gashi har yanzu bata da ciki shine take ta kuka b'na faɗa mata lokacine, ta kwantar da hankalinta”.

Cikin sanyi tayi Murmushi hawaye na zuba a idanunta tace.

“Ka gani fa Addah Asiya ta haihu Dija ma ta haihu amma Ni har yanzu ko ɓatan wata ban taɓa yiba ina so in haifawa Keyah Mata”.

Murmushi Khausar tayi tare da faɗin.

“Ai zaki haifa masa lokacine fa Asma'u yaushe ma akayi Auren badan haihuwar wuri da ake yiba”.

Lumshe Idanunta hawaye suka zubo kana ta taune lips ɗin ta na kasa tare da faɗin.

“Hmmm Khausar yanzu fa kusan shekara biyu muke nema tunda mun cika shekara ɗaya da wasu watanni da yin Aure har na biyu muke nema”.

Araunane taci gaba da cewa.

“Khausar am har yanzu fa ban haihu ba ko ɓatan wata ban taɓa yiba kuma duk gwaje-gwajen da za'a yi anyi ance lafiyata lau shima Dr bashi da matalan komai”.

Gyaran murya Moddibo yayi kana yace.

“Kiyi haƙuri Asma'u lokacine idan ban manta ba Ummi ta faɗa mana sai da tayi shekara bakwai ana takwas ta samu cikin J ɗina.

Tace mana a randa ta cika Shekara tara ta haifi Jameel dan haka kema ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu Babu abinda zai faru sai alkhairi kinji ko My dear”.

Ya ƙare maganar cikin kulawa a matsayinsa na babban yayanta.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Toh shikenan Yah Moddibo yana iya amma dai ku sani a addu'a Allah ya kawo min masu albarka ”.

“In sha Allahu zakmu yita Miki addu'a ”.

Sai kuma ta juya jin Khausar na cewa.

“Kima kwantar da hankalinki daga Yaye in kawo Miki Keyah shikenan zan bar miki ɗanki”.

Murmushi tayi tare da kallon Moddibo tace.

“Allah dagaske Yah Moddibo zaku bani?”.

Zamansa ya gyara tare da cewa.

“Toh me aciki Asma'u ɗana ai ɗan kine, kuma ɗan Khausar ɗan kine”.

Cikin jin daɗi tace.

“Toh Allah ya raya mana shi da Imani ”.

Atare suka amsa da Ameen ya hayyu ya ƙayyum.

Haka dai ranan sukai ta hiransu suna bata ƙarfin guiwa sai karfe 12 suka tafi.


   Bayan wata biyar Khausar ta yaye Keyah kana ta kaiwa Asma'u kamar yanda ta mata alƙwari satinsa uku agidan Asma'u ya saba da yaye ya daina tambayar Nono.

Inda ya zamana mafi akasarin zamansa a tsakanin su koda Moddibo ya matsa aje a ɗauko sa Khausar zata danne sa akan abarwa Asma'u.

Bayan Yaye Keyah da wata Uku Allah ya sake baiwa Khausar wani cikin.

Bayan shekara watannin tara da kwana tara ta haifan ɗa namiji aka sa masa sunan Abualeey Youseef ana kiransa da Ayman haka ranan sunansa aka ta biki da hidindimu bayan ta haihu da wata biyu matar Ibraahim ma ta haihu hakama Dija da Asiya da Matar Yah Abba duk sun haihuwa, Ameena ma ta haifi ƴan twagaye duka maza, Samira Sani ma ta haifi yarta mace Masha Allah itama Khausar ta kuma haihuwa Uwar ƴaƴa maza.


Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya akwana a tashi asarar mai rai.


Keyah yana da shekara takwas Ayman nada shekara shida sun girma sunyi kyau gwanin ban sha'awa sunyi kuɓul-kuɓul dasu zuwa lokacin ƴaƴan ta maza Uku Keyah, Ayman, Haiydar mai shekara huɗu daga nan bata sake haihuwa ba sai yanzu da take rainon ciki na huɗu wanda yama ɗan girma.


Ahankali Khausar dake zaune a babban Falonsu na ƙasa ta ɗan ɗago kanta ganin yaran na sauƙowa daga matakalan Benin Keyah na gaba Ayman na biye dashi Jikinsu sanye da wani Gezner Fari ƙall ƙafafunsu sanye da half covel golden color na maza mai masifar kyau yayin da kansu ke dauke da hula Zhanna bukar blue mai ratsin fari daya dace da kayan jikinsu sosai sukayi nasifar kyau tamkar ka sace su ka gudu.

Anutse Moddibo da shigowar sa kenan daga Fada ya durƙusa tare da buɗe musu hannayensa alamar suzu ya rungumesu.

Da gudu yaran suka rungumesa.

Sai kuma suka maida kallonsu kan Ibraahim kana suka haɗa baki wajen cewa.

“Uncle Ibraahim mun gama”.

Ibraahim dake riƙe da ƴa mace Kyakkyawa mai suna Mifra wacce bisa alamu ƴar sace da sauri Ayman yace.

“Mifra Oyoyo zo?”

Da sauri tazo ya rungumeta sai kuma suka kalli Moddibo dake cewa.

“Ina zakuje?”.

Keyah na Murmushin yace.

“Zamu tafi gidan Ummina”

Kasancewar da Ummi suke kiran Asma'u.

Yana murmushi yace.

“Toh ku gaida Ummin ku” ya ida mgnar yana kamo hannun Haiydar dake ƙoƙarin kwanciya a jikin Khausar yace.

“Tashi kuje kaima”.

Cikin lingwaɓar da kai yace to kama ya miƙe. 

Kai suka gyaɗa kana suka fice tare da nufar gidan Asma'u.


Suna shiga gidan suka sameta kwance a falo ta lulluɓe jikinta da bargo tana rawan sanyi cikin sauri da kulawa Keyah ya ɗaura hannunsa kan Fuskarta tare da cewa.

“Ummina meke damunki?”.

Cikin alamun zazzaɓi da rawan jiki tace.

“Zazzaɓi nake ji Keyah”.

Da damuwa atare dashi yace.

“Uncle ya sani?”.

Kai ta girgiza tare da cewa.

“Bai sani ba ɗazun ne ya fara min”

Cikin sauri ya juya gudu kna yace.

“Bari naje na faɗawa Uncle Ibraahim yazo ya ɗauke ki mu tafi asibiti”.

Ya ƙare maganar yana fita dai-dai lokacin kuma Ibraahim ke reverse ɗin motar yana shirin fita cikin ɗan ɗaga murya yace.

“Uncle Ibraahim ka tsaya”.

Ahankali Ibrahim ya tsaya cikin damuwa Keyah yace.

“Ummina bata da lafiya Uncle Ibraahim ka Kaita asibiti”.

Kai ya gyada tare da cewa.

“Toh”.

Kana ya yayi Parking tare da zaro wayarsa ya kira Dr Jameel ya sanarmasa.

Shi kuwa Keyan da gudu ya koma cikin gidan hannunta ya kamo tare da cewa.

“Ummi tashi mu tafi asibiti”.

Ahankali ta gyada kai tare da miƙewa ta gyara mayafinta.

Kama ta tasasu a gaba duka fita.

 Tun suna mota ta kira Dr Jameel ta faɗa masa gasu ahanya Ibraahim ya kawo mata yara yanzu zai kawota asibitin nan yake cemata ai Ibraahim ɗin ya gaya mishi.


Suna isa asibitin Dr Jameel da kansa ya karɓeta kana yayi mata duk gwaje-gwajen daya kamata nan yaga ashe tana da ciki har na tsawon uku batare da sun sani ba cike da farin ciki ya ɗagata sama ya riƙa juyata kafin ya sauƙeta cikin matsanancin farin ciki yace.

“Sweetheart albishir”.

Tana ɗan lumshe Idanunta tace.

“Goro”.

Wani kallo ya mata still fuskarsa ɗauke da Murmushi yace.

“Wani kalla”.

Ɗan ware idanunta tayi da kuma yanda zazzaɓin ya fara sauƙa tace.

“Fari ƙall”.

Sake rungumeta yayi kana yace.

“Ciki ne fa dake Sweetheart?”.

Cikin mamaki da wani irin farin ciki data kasa tantance yanayin da take ciki tace.

“Ciki?da gaske?”.

Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

“Wallahi da gaske Sweetheart kina ɗauke da cikina ajikin cikin da muke muradi da mararin samu”.

Ahankali tace.

 “Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un?wata nawa?”.

Cikin farin cikin daya kasa ɓoyuwa asaman fuskarsa yace.

“Har wata uku fa”.

Da wani irin sauri ta ɗauki waya ta kira Ummi Ummi na ɗagawa tace.

“Ummi Ummi ina da ciki har na wata uku”

Cike da matsanancin farin ciki da jin daɗi Ummi tace.

”Alhamdulillah³ nayi farin ciki Ubangiji Allah ya raba lafiya kice na kusa zuwa”.

Murmushi Asma'u tayi kana tace.

“Yawwa Ummi dama kin daɗe baki zoba tun sunan Ayman baki sake zuwa ba dan haka kima fara shiri kin kusa zuwa”.

Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.

“Toh Allah yakai mu da lokacin rai da lafiya”.

Ameen ta amsa tare da katse kiran ta kira Khausar ta sanar mata murnan da Khausar tayi ba a cewa komai.


Ummi na gama waya da Asma'u ta kalli Bashir da Haiydar dake zaune gabanta wanda zuwa yanzu sun zama manyan Samari sun mallaki hankalin kansu.

Wanda tuni an gama maganar Auren Raudat da Bashir.

Haiydar kuma ya auri ƴar Aunty Ruƙayya.

 sosai sukayi farin ciki jin Asma'u nada ciki kana atake awajen suka kirata suka tayata murna...


Zuwa yanzu kuwa Khausar ta haife cikinta, an samu ɗiya mace, ansa mata sunan Didi suna kiranta Eeman


  Bayan watanni Allah ya sauƙi Asma'u lafiya ta samu ƴa mace wacce taci sunan mahaifiyar Dr Jameel A'isha suna kiranta Ishmah.

Anyi suna lafiya an gama Alhamdulillah Ummi da Mommy sunzo wajen suna.


          *BAYAN SHEKARU ASHIRIN*

Alhamdulillah ƴaƴan su sun girma sun mallaki hankalin kansu an haɗa Auren Keyah da Ishmah ƴar Asma'u.

Sai Ayman da Mifra ƴar Ibraahim.

 Alhamdulillah Raudat ma ta haifi ƴaƴanta mata biyu duk sun girma Hakeem ɗan Lalla Hafsat ya Auri Fatma ƴar Dija Haiydar kuma ya Auri Ruƙayya yarinyar Rahama.


Alhamdulillah rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar yanda ake buƙata.

Bayan anyi biki an watse.

Ahankali Khausar ta shirya cikin shiga ta alfarma sai baza ƙamshi take sanye take cikin wasu tausasan rigar bacci masu masifar kyau da santsi idan ka ganta zaka yi zaton yau akayi Aurenta duk da cewa sun Aurar da ƴaƴan su amma tana da kyakkyawan jiki wanda Babu wanda zai ce ita ta haifi wannan yaran ga autarma Eeman an zama manyan ƴan mata wacce ba abinda ya bari na mahaifiyarta har rawan kan.


Anutse ta tura ƙofan bedroom ɗin ta ta shiga idanunta suka sauƙa akan Moddibo daya sake zama magidanci baza kayi zaton ya wuce 45years ba saboda kyawun jikinsa nutsuwa, jin daɗi kwanciyar hankali sun sake wanzuwa acikin rayuwarsu yana ganinta ya buɗe mata hannunsa anutse ta ƙara sa tsakiyan tare da faɗawa jikinsa ya mata wani Amintaccen runguma ahankali yake cusa yatsun ƙafansa aƙasan nata ganin haka yasa ta ɗaura ƙafafunta asaman rumfar ƙafansa anutse ya riƙa tafiya da ita har yaje bakin kofa yana isa ya rufe ƙofar saurin kallonsa tayi tare da cewa.

“Yah Mu'allim ya zaka rufe ƙofa”.

Goshinsu ya haɗe waje ɗaya still ƙafafunta na kan nasa yace.

“Um Minha Vidaa (My life) rufe wa zamuyi saboda kada _Aysha Aliyu Garkuwa_ ta shigo ta samu abin rubutawa Fan's ɗinta”...


    Acan gidan Dr Jameel kuwa Asma'u ce zaune tare da ƴaƴanta wa'anda ta haifa bayan ta haifi Ishmah ƴaƴa maza guda biyu wanda ɗaya an yiwa Moddibo ta kwara suna kiransa da Moddibo sai takwaran Abban Jameel suna kiransa da Abba ahankali tace.

“Yah Moddibo”.

Anutse ya kalleta cike da girmamawa yace.

“Na'am Ummina”.

Tana gyara zamanta tace.

“Yaushe zakaje Nigeria ne?”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Ummi kwanan nan dai nake son zuwa amma nafi son mu tafi da Abba idan ya gama exams ɗinsa”.

Kai ta gyaɗa tare da faɗin.

“Toh ba matsala nima dama nayi kewar Ummina idan yaso zamu tafi tare”.

Dr Jameel dake gefe yai mata wani kallo mai cike da so kauna yace.

“Nima ɗin dani za'a je saboda nayi kewar Abbana da Ummina”.

Hira suka cigaba dayi mai cike da farin ciki da ƙaunar junansu...

 Acan bangaren Ibraahim rayuwa tayi musu daɗi da matarsa.


Haka bangaren Asiya ma Alhamdulillah rayuwa na tafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali ɗan ta ya Auri ƴar Amina da suka haifa da tsohonta...

Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya hankali ya kwanta ya kowanne ɓangaren...



_TAMAT BIHAMDULILLAHI..._ Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Na godewa Allah daya bamu aron rai da lfy da lokaci da dama ya nuna mana forkon littafin nan lfy tare da aramana daman ganin ƙarshensa lfy dani daku masu karatu. Toh Alhamdulillah. Yah Allah mun gode maka, muna kuma neman yafiyarka da gafararka da rahamar ka, Yah Allah ka yafe min kurakuran dake cikin wannan littafin ka shafe zunubaina kayi min gafara da rahama da jinƙai dani da masu karatu. Abinda mai dai-dai Ya Allah ka haɗamu a kan ladan, ya Allah ka nuna mana forkon wanda zan fara lfy da ƙarshensa duk lfy, ya hayyu ya ƙayyum kasa al'ummar Annabi su amfana da alkhairan dake cikin littatafai na ka tsaresu da sharrin dake ciki.

*Yafiya! Yafiya!! Yafiya!!!*

*Ina mai neman yafiyarku makarantan littatafai na, mace ko namiji babba ko yaro wacce muka taɓa mgn da ita da wacce bamu taɓa mgn da ita, na kusa dani dana nesa. Wala Allah akwai abinda nai Miki ko nai maka ko cikin rashin sani ko ajizanci ko kuma yanayin gajiyawa da raunin ɗan adam ki kuma yanayin ɗan fusatan lissafi ko gaza danne fushi, Ka! Ku! Ki! Haƙuri ku yafe min, kuyi min azurun na fama da yawan jama'a, ni na yafewa duk wacce taimin abu cikin rashin sani, Amman wlh ban yafewa masu fitarmin littafina su tura a wasu groups ɗin ba domin misali ka bawa ɗan uwanka mutum ɗaya biyu wannan da banner da turawa a groups mutum dari ko sari biyu ko uku ku dari hudu ai wannan kai kankama kasan me sunanka madadin samun wani suyi Murmushin group a kuma kwashi zunubi*

Post a Comment

0 Comments