TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

MIN QALB 🥰 PAGE 24-25

 2, 11:30 AM] Zafafa: *_MQ 24_*




Tafiya sukeyi ahankali cikin motarsa Babu me Magana sai sanyin AC da qamshin turarensa daya Gama Kama motar dama can yake ratsata Yana Bata wani sabon yanayi cikin zuciyarta Wanda yasata fadawa tunani.,


Tuqinsa yakeyi cikin nutsuwa shima Yana jiyo siririn sahirtaccen qamshin jkinta na Shiga hancinsa ahankali Wanda kusan shima yasashi Shiga tunanin banbanta yanayin qamshinta Dana zarah.,

Istigfari yayi saurin Yi cikin ransa Yana Dan tsuke fuska tareda 'dan qarawa motar gudu.


Ganin sun kamo hanyar blue fox yasata saurin kallonsa murmushi na sauka Kan fuskarta tace"


Rabin ran Anty Dan Allah muje blue fox akwai abinci me kyau da dadi acan.......


Wani irin kallo ya juyo ya aika Mata Jin sunan data kirasa dashi Wanda yasashi qurawa cikin Idanuwanta Ido Yana son sake tabbatarda Abinda takirasa dashi  _Rabin ran anty_  yanda tafada sunan batareda kulawar komaiba yasashi yimata wannan kallon itama Jin idanuwansa akanta yasata kasa juyowa ta qurawa waje Ido Yana damqe hannunwanta dake rawa zuciyarta na harbawa.


Jin shiru yasata Dan dagowa tareda juyowa ahankali ta kallesa hankalinsa na Kan hanya saita qurawa fuskarsa da fararen hannuwansa dake tuqin motar cikin nutsuwa da qwarewa,

Kan fuskarsa ta tsayarda kallonta tana yaba kyawu da tsarin fuskarda ubangiji yayi Masa me daukeda da tarin kwarjini da Kamala,

Dogon hancinsa ta kalla zuwa manyan idanuwansa batasan lokacinda ta lumshe ido ba hawaye na gangarowa daga cikinsu batareda ta gogesuba cikin ranta tace"


Meyasa zuciyata ta zabi wahalar da rayuwata data Dr ta hanyar son Dan uwa mafi soyuwa agaresa?

Dukkanin kyawu da Abinda MD yakedashi Dr khalil dinta nadasu harma yafi MD din kyawawan halaye masu sanyaya Rai hasalima kusan kamanninsu daya sbd duk mahaifinsu Modibbo suka dauko har Khalil dinta ma yagi MD din hasken fata saidai MD ya nuna Masa gogewa da hutu irin na Boko da yawan qasashe suka hudasa sai kalar fatar mahaifiyarsa daya dauko me sheqi.


A harabar blue fox din yayi parking tareda Dan juyowa ya kalli gefenta tayi saurin share hawayenta tana bude motar ta fito tana washe baki cikin tsananin farin ciki ta juyo daidai ya zagayo tace"


Yau duk abindake restaurant dinnan saina cire kwadayinsa na tsawon aikin danayi anan din.


Bai kalletaba yayi gaba ta biyosa tana sake bayyanar da murnarta ta zuwa gurin.


VIP direct suka nufa inda tuni aka hau sintirin attending dinsu ga mamakinta kusan Rabin ma'aikatan gurin an sauyasu Nan ta bada odar abinci kusan kala hudu da tarkacen su fruit salad harda ice cream da furar blue fox din me shegiyar Madara da Laban yoghurts.


Table dinsu kusan kasa daukan abubuwan yayi sai kawai yayi odar  noodles with veggies salad da power drink yafara ci cikin nutsuwa Yana kallonta tana cin abincin cikin tsananin Jin Dadi Dan harwani lumshe ido takeyi tana cika bakinta da Naman kazar chicken rings dataji carrot da spices.


Yana kallo ta Gama yagalgala kazar ta janye gefe ta jawo shawarma tafara ci itama ta ajiye ta janyo soyayyan dankalin dayaji egg source 

Furarta ta janyo ta kurba ta lumshe ido tana cewa''


Wayyo Dadi" kafin ta aje tacigaba da cin noodles Kuma.


Jingina yayi da Bayan kujera Yana zuba Mata iduwansa masu karya kuzarinta tareda dukkanin nutsuwarsa Yana kallonta kamar ya baby a gabansa.


Saida tayiwa komai ci rabi aje rabi kafin ta qoshi ta dauki ice cream dinta ta bude ta diba tana hadiye yawun matsuwa taji sanyinsa ya sauka a bakinta taji anrike ice cream din

Da sauri ta dago idanuwansu suka shiga cikin na juna ahankali ya girgiza Mata cikin qaramin sauti yace"


This is not good for your health......


Kasa motsi tayi ta harya zare ice cream din daga hannunta ya ajiye idanuwansu na cikin na juna Saida waiter din dake tsaye yayi gyaran murya da qarfi Yana sake miqawa MD din bill dinsu.


Fuskewa yayi Yana Dan tamke fuskarsa ya juyo ya Ciro ATM card dinsa ya miqawa waiter din batareda ya karba bill dinba.


Bayan andawo Masa da atm din anyi clearing bill dinsu suka fito suka Shiga mota sukabar gurin.


A mota shiru tayi tana sauraron karatun Qur'an din dayasa a motar Yana fita ahankali saitaji tana sake samun nutsuwa da yanayin da suke ciki na kasancewa da juna ahaka.


Koda suka dawo zabeera har bacci yafara daukarta cikin motar shiyasa da yayi parking sai bai tayarda itaba hakama bai kashe motarba sbd AC ya zauna ya fiddo wayarsa Yana duba saqon dayaji shigowarsa sunacin abinci.


Ahankali ta bude idanuwanta dake cikeda bacci ta zuba akansa tana lumshe ido ahankali ta furta"


Tabbas Ina cikin tsananin son MAHMOUD ZABEERA Kuma so me qarfi Wanda nakejin kamar ruhina zai rabu da gangar jikina idan nayi nesa dashi,

Lumshe ido takuma Yi tareda budesu akansa cikin sauti me taushi dazai iya jinta tace"


Nagode.


A natse ya juyo ya kalleta da nasa idanuwan dasuka nuna sunfara Jin bacci taji zuciyarta na qara narkewa da sonshi tayi saurin dawowa hayyacinta tareda tashi zaune tabude motar da sauri ta fice hartana hadawa da Dan gudu tayi ciki.


Kai tsaye bedroom dinta ta nufa ta fada Kan gadon tana sakin hawayen dataketa riqewa tace"


Amatu kidawo hankalinki Mana,

Kidawo Amatunki da kowa yasani,

Amatun Dr khalil matar Dr khalil, 

Babu kowa a zuciyarki sai Dr khalil sbd shine Wanda zuciya da ruhinki keson aure.


Ta jima ahaka kafin ta miqe tafada toilet ta wanko fuskarta tayi fitsari tazo ta kwanta tareda lullubewa tana qudurtawa ranta gobe zata amayarwa Salman abindake zuciyarta kafin ta rufe zuciyar gaba daya ta mallakawa Dr khalil dinta Wanda idan har tana Raye Inshallah batada miji sai Dr khalil.


Washe gari tunda wuri ta tashi yau da kanta ita tafara Kiran Dr 

Meeting zasu shiga Amma ganin kiranta Saida ya tsaya ya dauka yaji lafiyarta kafin yace idan yafito zaikirata.


Wankanta tayi ta shirya cikin riga da skirt na atampa kalar blue tayi Mata kyau sosai ta yafo gyalen akanta sbd Bata dauro dankwalin kayanba.


Palo ta fito ta nufi kicin da kanta yau ta dafawa kanta indomie da dafaffen kwai guda biyu sai custard data hado Wanda yaji uwar Madara takoma dakinta acan tayi breakfast dinta tana gamawa ta fitoda kayan ta maida kicin Takoma daki ta sake kwantawa tana tunanin Dr da irin dibbin soyayya da qaunar daya Bata,

Ya juyawa iyayensa baya akanta alokacinda aka koresa ya amince zaibar komai da komai ciki hadda iyayensa da 'yan uwansa da rayuwar daya taso ciki duk sbd ita

To menene Dan itama ta danne zuciyarta ta tauyeta daga Abinda takeso ta bashi koba komai Al'amarin da zuciyarta ta dauko me girma ne sbd mijin anty zarah ta haramtawa kantashi Koda sonsa zai kasheta har abada su biyun Nan anty zarah da Dr bazata taba barin susan halinda zuciyarta ta Shiga akan mutuminda sukafi qauna da komai arayuwarsu.....


Kiran Salman ne yashigo wayarta cikin nutsuwa ta daga tana qoqarin kawar da damuwarta tace"


Likitan qashi na duk Nigeria""ta qarasa tana Yar dariya.


Shima 'yar dariyar yayi Yana gyara zama cikin motarsa yace"


Zakije mukai usi airport kokuwa na tafiyata?


Wuntsilowa tayi bakin gado tana janyo dankwalinta da gyalenta ta fito tana cewa''


Ai karma kamin haka idan ban takasa a matsayin 'yar uwarsa da bamu taba rabuwaba arayuwa sai yanzu to zan takasa amatsayin matar Dr khalil tunda bayanan Dan shine yafi kowa cancantar ganin wucewar usi Dan shine yakawo wannan murmushin akan fuskarsu na samun cikar buri su samu ilimi kamar sauran 'yaya.



Ganinta kawai yayi tana bude gaban motar ta shigo ta zauna tana kashe wayar tace"


Muje ko¿


Dariya tabasa ya girgiza Kai Yana cewa' 


Amatun likita bokan turai.


Kallonsa tayi tana cewa'' 


Nidai muje tun kafin na huce da zafi zafina nafito Dan yiwa USI huduba.


Jan motar yayi suka fice suna Dan taba fira ahankali har suka Isa gida inda su kadai ake jira suzo dauki usin.,

Tunda tashigo gidan idanuwanta suka sauka Kan 'yan gidan kaf a tsaye cirko cirko tsakar gidan kowanne fuskarsa cikeda yanayin damuwar rabuwa da USI din ta juya ta kalli kawu dake zaune radionsa a kunne Amma yanayin fuskarsa yasa taji idanuwanta suna qoqarin cikowa da hawaye tana kallon iyami sai kawai ta qaraso da sauri Yana sake hawayenta ganin yanda Usin yake tsaye riqeda hannun iyami Yana Bata qwarin gwiwa.


Usman din ta kalla tana share hawayenta tasaki murmushi Dan cirewa kowa damuwa takai Masa duka a baya tana cewa"


Ki yanda kasa kowa cikin damuwar tafiyarka bayan duk hutawa zamuyi da rashin Jin ka musamman maman junior da anty salamatu ko???""tafada tana kallon maman junior da anty salamatun dake qarasowa da jakarsa data fito Masa da ita.


Murmushi maman junior tayi tana cewa''


Usi Allah yabaka sa'a kamaida hankali kayi karatu ko zaka tallafa Mana wata Rana idan lokacin cin amfanin karatun yazo sbd Kaine kasan wahala da gwagwarmayar rayuwa damukeyi anan gwamnati batamasan da ire irenmuba.


Maman junior kada ki damu daya bayan daya dukkaninmu sai usi yakaimu Hajj da umrah da albarkar wannan karatun dazaije Amma idan kuka tsaya Kuna Masa wannan fuskar ta marayu ta Yaya zaije da gwarin gwiwarsa ai kawai ki Masa tashin hankali da hayaniyar da kuka Saba shizaisa yaje Yana tuno kowa ayanda halayyarsa take....


Dariya dukkaninsu suka dauka Nan aka hau hayaniya ana Masa Allah ya kiyayaye shima sai hakan yasashi Jin Dadi ya saki fuska Yana amsa musu kowa ana Masa alqawarin Abinda za'ayi Masa idan akai kudi.


Kawu da iyami dasu akeje har airport inda suka taru su duka da hayaniyarsu suka cikawa Salman motar da hayaniya sai suke qara burgesa musamman Amatun dake qoqarin Hana kowa shiga damuwar tafiyar Usin bayan ita Yana iya hango tsananin damuwa da fargabar rabuwa da Usin a idanuwanta tana daurewa ne kawai.


Suna Isa ko zama basuyiba aka Kira jirginsu Salman ya kallesa Yana basa sauran dukkanin bayanan da Dr yace yayi Masa tareda basa takardun komai Dana atm card na account din da aka bude Masa tareda wadataccin kudi aciki ya miqa Masa tareda Dan rungumesa Yana cewa''


Zaka ringa ganina akai akai inshallah har sai kagama sanin komai da komai just take care brother,

Kuma Ina fatar zaka saka mijin 'yar uwarka alfahari dakai wata Rana.


Kallonsa yayi ya kalla Amatu Yana qirqiro murmushin qwarin gwiwa yace"


Inshallah Dr khalil saiyayi murmushi ga wannan aikin alkhairin nasa.


Gyada Masa Kai tayi tana qoqarin maida hawayen dake subuce Mata 

Suka rungume suna tana sakin hawayenta gaba daya suna zubowa ba tsayawa.

Cikin kunnenta yace"


Amatu Ina Miki fatar samun Abinda kikeso arayuwa Wanda zaisaki farin ciki,

Inaso Kuma kimin alqawarin Babu wani Abu dazai sauya matsayin Dr acikin rayuwarki kimin alqawarin da ke da kanki zaki kirani Dan sanar Dani aurenki da Dr Khalil idan lokacin yayi.


Rintse ido tayi hawayenta na sake gudu ta janye jikinta tana kallon qasa tace"


Usi zuciyata takamu da son wani Wanda ba Dr khalil ba so me girma Amma wlh shima son Dr khalil bai sauyaba a zuciya da rayuwata,

Ba laifina bane sbd bansan yaushe hakan yafaru ba,

Bansan ta Yaya zan kankare wannan son daga zuciyata ba Amma nasan ta yanda zan dannesa dannewar da har abada bazai tasoba bare wani yasan dashi zanbarshi cikin Raina har mutuwata,

Jan kuka tayi ahankali tana cigaba da cewa''


Usman ayau ni Amatu nayi maka alqawarin bazan taba auren kowaba sai Dr khalil,

Nayi alqawarin Dr bazai taba fuskantar sauyawa daga gareniba sbd shi kadai na zaba amatsayin mijina Inshallah...."wani siririn kuka taqarasa maganar dashi zuciyarta na wani irin nauyi.


Baiyi mgn ba ya juya gurinsu kawu yayi musu bankwana ya wuce Yana danne zuciyarsa dake Jin tsananin damuwa da tsoron Abinda Amatu ta fada,

Shin yayi Mata adalci satayin alqawarin auren Dr Bayan tafada Masa akwai Wanda zuciyarta ke tsananin so???


Baya tunanin baimata adalciba sbd a nasa gani da sanin Babu Wanda zata aura ya sota ya qaunaceta yabata farin ciki da kulawa fiyeda Dr khalil zabeera Dan haka koma waye zuciyarta keso farin cikinta da kulawar dazata samu daga Dr yafi matasu ahankali zata manta sonta zuciyarta ta koya son KHALIL din.



Ahanyarsu ta komawa Babu me mgn acikinsu kowa yayi shiru Yana tunani kamar basune suketa hayaniya ba a hanyar zuwa.


Su kawu tunanin rahuwarsu dasu Usin sukeyi sbd dukansu basa gabansu yanzu sai sukejin kamar rabuwa sukayi dasu gaba daya musamman iyami datakejinsu kamar itace ta haifesu gashi yanxu ta tashi Babu ko daya a gabanta.


Shikuma Dr Salman yasan irin ciwo da radadin datake ciki na zabar danne sonta tabi Abinda rayuwarta da 'yan uwanta keso.


Ajiye su kawu sukayi suka nufi gida har lokacin Babu me Magana acikinsu Saida yayi parking qofar part dinsu anty zarah sai ga MD ZABEERA yafito Yana amsa waya fuskarsa sai sheqin kwarjini takeyi ya nufi motarsa ya bude ya shige drivernsa na ciki yaja sukabar gurin idanuwanta na binsa da kallo har motar ta bace Salman na lure da ita ya saki numfashi ahankali yace"


Duk zabin dazakiyi Amatu kisani ni Salman zabeera Ina bayanki dari bisa dari saidai bazanso ki zabi Abinda zai kawo damuwa da qunci cikin rayuwarkiba,

Soyayyar MD ZABEERA Babu Abinda zata baki sai damuwa sbd bazai baki soyayya da kulawar da kike nemaba infact baimasan kinayi ba Koda yasani Babu so agabansa sbd keda idonki Kinga hakurinda matarsa keyi akansa Wanda mu bazamu iya ganinki kina irin wannan rayuwarba so please AMATULLAH for our sake kadaki saka kanki cikin quncin dazaki sakamu muma.


Share hawayenta tayi tasaki murmushi me ciwo tace"


Dr Salman zabeera daga yanxu anan munrufe maganar MD ZABEERA sbd soyayyarsa ba Abu bane Dani Amatu zansamu,

Soyayyarsa wani bangarene me girma a zuciyata da bazan iya cirewa ba saidai Kuma illace ga mutane da dama Dan haka na zabi azabtuwa da ita ni kadai acikin Raina bazan Bari ta azabtarda masoyanaba dan haka daga yanxu Babu mgnar MD ZABEERA da AMATULLAH,

Zuwa yanzu nasan kagama sanin Abinda yake faruwa kasan banida aure da Dr Khalil dan haka idan har ka daukeni kamar Yar uwa wadda kake tsananin qauna to ka nesantani duk Abinda zai cigaba da zurafaf soyayyar MD ZABEERA ka tayani nitsawa da kutsawa cikin son KHALIL ZABEERA sbd na riga na yanke shi na zabarwa kaina.



Kallonta ya tsaya Yi zaiyi Magana tayi saurin girgiza Masa Kai tana share fuskarta da tissue din motar tana murmushi tace"


Zancen ya wuce Kuma ai"" dan sake batarda zancen ta Dora da fadin" 

ni yanzuma so nakeyi kafara koyamin wannan turancin naka na turawa idan Dr yadawo so nakeyi nabasa mamaki.


Dariya yayi Yana jinjinawa gwarin gwiwarta na kawo dariya Kan fuskarta da boye abindake zuciyarta Wanda hakan na daya daga cikin Abinda yake burgesa gameda ita.


Fitowa sukayi suna fira sama sama suna dariya kamar Babu Abinda yafaru.


Anty zarah na ganinsu ta daga wayar hannunta tana cewa''


Cikinku fa daya zankira sbd Ina ganin bangantaba nasan Kaine kawai zaka fita da ita.


Ko zama beyiba suka gaisa da anty zarah din ya juya ya fice sbd mum dinsa daketa qwalo Masa Kira.




Fes ta sakewarta Takoma Amatun ta me rayuwarta cikin Raha da Jin Dadi,

Duk wani Abu ko inda tasan zata hadu da MD ZABEERA ta tosheta gaba daya data fahimci lokacin dawowarsa yayi take komawa daki takira Dr ko USI ko Salman suyita firarsu cikin nishadi.


Kulawa kuwa da qaunar da anty zarah take Mata sai ninkuwa sukeyi sbd yanzu kwata kwata ta daina cire cikon datakeyi sbd umarnin Dr khalil ne Dan shima yanzu so yakeyi daya dawo Susan dubarar Yi maganar cikin Nan yaqare su fuskanci reality itakuma anty zarah data qwallafawa cikin Rai har MD ZABEERA yiwa zancen takeyi idan tasamu fuska sai hakan yafara basa tunanin Dole daman Suma wata ran suyi sha'awar samun 'da ko 'ya.



Sannu ahankali sabo da shaquwarta da Dr Salman yayi qarfi Dan shima saitakejinsa kamar usi da baya kusa duk wani gurbi na 'dan uwa me kulawa ya cike matashi Dan dukkanin shawararta da sirrinta dashi takeyi ta yanda shima baya boye Mata komai sai suka zama tamkar wasu best friends kokuma Yan uwan dasukafi kusanci da kowa.


A bangare daya Kuma yanzu su umme sun Dakota gaba itada Haj maryam sbd ganin dukkanin yayansu sun qare da rawar qafa agunta sai suka sanyota gaba ba itaba ba anty zarah ba tun abin baya damunsu harya Fara damunsu zancen yajewa ummah mahaifiyar anty zarah tazo tayi musu mgn sai abin yazama fitina akayi tashin hankali tun abin na dagasu sai yayi tsanani akai kusan qaramin yaqi a familyn Wanda yasa akayi taro na musamman Amma duk da haka sai abin yaqara jawowa Amatu baqin jini sbd ganin kamar itace takawo fitina cikin familyn ZABEERA sai aka Fara camfata ga nuratu data sanyota gaba sosai tafara bincike a kanta sbd gano haqiqanin gaskia Dan bazata taba Bari Dr khalil ya auri wata banzar karuwa ba yabarta.



Zuwa yanzu satin Dr khalil uku cikin na hudu da tafiya suna saka ran dawowarsa gobe shiyasa take cikin farin cikin data kwana biyu batayiba sbd tashin hankali sbd wannan fitinar da akayi yasa Andi saka doka me tsanani akanta akan kullum taje ta gaida uwar mijinta Wanda duk taje da bacin Rai take dawowa.



Blue fox sukaje akayo musu gyaran Kai da qafafu akaiwa Amatun Jan lalle a hannuwa 

Basu bar gurinba sai yamma sosai sukayo gida Salman ne ma ya daukosu suna yin parking motar MD ZABEERA nayin parking akusa dasu ita tafara juyowa daidai shima ya juyo idanuwansa suka sarqe cikin na juna

##mamuh#






ZAFAFA BIYAR👇👇👇


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


SARAN BOYE

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

[4/5, 4:22 PM] Zafafa: _*MQ 25*_



Saurin dauke idanuwanta tayi tana juyar da kanta zuwa wani gefen tana cigaba da dariyarta ta firar dasukeyi da Salman Wanda shima ya lura da yanayinda Amatun tashiga sai ya basar kamar yanda itama ta basar suka fito suna cigaba da zancensu.


Gurin MD din ya nufa ya bude Masa mota ya fito Yana gaidashi tareda fada Masa saqon Dr khalil daya basa sbd yakasa samun wayoyin MD din duka.


Itadai gaba tayi tashigewarta ko Palo Bata tsayaba sbd sanin ciki sukayo

Anty zarah ce ta tsaya tai Masa sannu da zuwa ganin Salman yasata itama wucewa sbd yanda ya amsa kamar bazai amsa ba karya kwafsa Mata gaban Salman din itama bedroom dinta ta wuce Kai tsaye sbd dukkaninsu suna buqatar wankene kawai Dan ko yunwa basa ji Dan Babu kalar cimar dasuke buqata wadda Salman be siya musu ba Wanda kusan hakan yasa tafarajin qaiqayin ciwon Abinda rayuwarta take ciki na rashin kulawa daga kowa musamman mijinta Wanda shine yakamata ace ya jiyar da ita dadi da nushadin rayuwa amma Bata samu hakan daga kowa ba sai yanzu sanadin Wanda batamasan meye ake Kira gata da arziki ba a rayuwa gashi ta sanadinta suna nishadantuwa da rayuwarsu da Basu San komaiba sai bin umarni da oda.



Wanka tayo ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya dogon hijab tayi sallah tana idarwa taje ta dauko yoghurts a fridge ta zuba cikin cup ta qara Masa madarar gari sosai ta juya sosai tadawo daki tana Sha tana daukarwa Dr khalil hotunan lallenta tana tura Masa saigashi yakira.


Daukar wayar tayi tana murmushi qasa qasa tace"


Kai Dr baka shanye rada ba.


Wani siririn numfashi ya sauke Wanda yasata aje spoon din hannunta cikin kulawa tace"


Yadai???

Lafiya najika kamar kana bacci?


Murmushi me sauti yasako Mata Yana gyara kwanciyarsa da lullubinsa yace"


Lafiya kalau kawai sanyin garin Nan ne yafara tabani tun satin daya gabata garin qasar ta daina shafamin lafiya Amma ai alhmdlh tunda gobe zamu dawo.


Ajiyar zuciya ta sauke tana cigaba da Shan yoghurts din tace"


To Meyesa zaka zauna harka Dade haka a inda baya shafa maka lfy???

Gwara da gobe zaka dawo da yau saina daga maka hankali kabaro.


Murmushin qarfin hali yayi Yana cewa''


Gobe idan nadawo me Kika ajemin?


Wani juyi tayi tareda kifewa kan carpet tace"


Saika dawo zaka gani.


Fira sukeyi ahankali sbd yanayin yanda yakejin jikin nasa sbd sanyi ya shigesa sosai Wanda yafara yiwa lafiyarsa barazana Dan yanaji ciwonsa yafara tashi ahankali.




****Miqewa Nuratu zabeera tayi daga zaunen datake a cikin restaurant din blue fox tana juya envelope din data karba tana sakin wani irin qyayataccen murmushi tace"


Manager kayimin Abinda zai juya rayuwata nasamu Abinda nakeso kaima kasamu wadda kakeso,

Wannan taimakon naka yabani farin cikin danayi shekaru bansamu ba sbd Dr khalil zabeera shine farin cikina,burina dakuma zuciyata...


Kallonta yayi tareda miqewa tsaye yace"


Ina fatar zan mallaki Amatu kamar yanda kikaimin alqawari??


Karka damu idan ka iya takunka zakayi amfani da damarka ka sameta daga lokacinda aka watsota daga rayuwar farin cikina da zabeera ma gabaki daya.


Barin gurin tayi tana sake riqe envelope din farin cikinta na qaruwa ta nufi motarta tashiga ta rufe..


Bayan ta zauna cikin motar kallon envelope din tayi tana cewa"


AMATULLAH K SALEH wannan shine asalinki tun kina Yar bolarki har zuwa yanzu,

 rayuwar alfaharinki tazo qarshe,

Kinyi kutse a tsakanin masoyanda ba'a iya rabawa sbd son danakewa khalil hankalinkima bazai daukaba bare ki iya rabamu,

Kina alfahari da kanki dakuma gatan da Kika samu daga Khalil, Modibbo da Andi ma gaba daya

Zan ruguza rayuwarki gabaki daya sai nasaka kowa ya tsaneki fiyeda yanda tunaninki zai dauka,

Ki shirya komawa rayuwar sata da dauke dauken da Kika fito bayan kinyi shari'a da familyn ZABEERA na Bata sunan da kikaso yimusu.


Cikin handbag dinta ta sakashi ta ajiye jekar gefenta tareda tayarda motar tabar gurin cikin mugun speed Dan amatse take data Isa zabeera sbd so takeyi kafin Dr khalil zabeera ya iso an dade da korar Amatun daga rayuwarsu,


Agogon motar ta kalla taga qarfe biyar ta yamma takusa gashi guraren yamma jirginsu Khalil ake sakaran zai sauka,gudu taqarawa motarta tana kallon titi.





***Cikin riga da skirt na lace maroon tayi adonta tareda daura dankwalin lace din ta sanya Yan kunne marasa tsawo sosai kalli agogo tana zama bakin gado da wayarta a hannu tana daukar hoto tace"


Kowane lokaci yanzu Salman yace Dr zasu iya saukowa Meyesa yau nakejin wani iri cikin raina kamar inajin kunyarsa ne kokuwa wani abin daban.


Shiru tayi gabanta na 'dan faduwa taji duk batajin sukuni ta miqe tana ajiye wayarta gefen gadon ta miqe tareda fitowa zuwa Palo gurin anty zarah ko zata debe Mata yanayin da fira.



Tana fitowa anty zarah na fitowa daga nata bedroom din sanye da doguwar Turkish abaya red itama tayi kyau sosai sai qamshi takeyi kamar Amatun sai abin yabasu Daria kusan atare suka saki dariyar Zarah na cewa''



Wannan da kishiyoyi muke bansan wa mijin zai Fara kalla ba sbd kalar duk jajaye ne Kuma kalar ja idan ba mantawa nayiba tana cikin kalar da MD ke tsananin so sbd ance kalar kayan mahaifiyarsa kenan kafin ta rasu sbd sarautar da mahaifinta yataba Yi.


Kallonta Amatu tayi tanayin shiru cikin tunanin kalamanta aranta tace"


Anty zarah Allah yasa kada 'yan Amin na kusa su karba Miki zancenki sbd ita Magana ana fadarta ne da fatar 'yan Amin su amsa shiyasa ake cewa kafada alkhairi ko Kayi shiru.


Wucewa gaba anty zarah din tayi Amatu naci gaba da binta da kallo zuciyarta na sake shiga fargaba saita kuma komawa daki zata zauna kenan saiga Kiran wayar Salman da sauri ta dauka Dan dama shi zata Kira ya debe Mata kewar tunaninta..


Salman ka......


Muryan Dr khalil taji yace"


AMATULLAH.


Wani irin sanyi da farin ciki taji ya kwaranya cikin ranta batasan lokacinda tasaki wani irin qaya taccen murmushi ba tana furta" Alhamdulillah ya Allah.


Har cikin ransa yaji dadin hakan ya kashe wayar tareda miqawa Salman batareda yace komaiba suka kamo hanyar gida.



Koda suka iso gida a gurin ummensa ya sauka Dan itama a matse take da ganin Dan nata musamman sbd kwanakin wata sabuwar qauna da kewar danta ke kamata shiyasa itama a matse take da taga abinta Nan aka hau hidimarsa kayan abinci da snacks kala kala anyi Masa taredasu fruits dasu fura duk dai wasu kayan marmarin kewar gida anyi Masa Nan yaci abinci tareda ita da Haj maryam da salman da Nuratu wadda koda ta iso gida kusan ataredasu Khalil din ta shigo Dan motarsu na gaba kafin Tata 

Ganinsa yasa takasa riqe farin cikinta da zumudinta tama manta da Abinda tadawo dashi Nan ta zauna cikinsu anacin abincin tana faman kula da duk motsinsa da Abinda yake so iyayensu kuwa sai washe baki sukeyi sbd dama shine burinsu hada Khalil din da Nuratu.


Bai bar gurin umme ba sai magriba ya wuce gurin Modibbo acan sukai sallah taredashi da salman da MD ma Wanda ya shigo ana magribar.


Bayan sungama sallah anan suka zauna tareda Modibbo Yana tambayar MD Amatu sbd duk yau da jiya Bata Zo ta gaidashiba kamar yanda ta Saba shiru MD din yayi Yana Dan sauke Kai yace"


Inshallah duk suna lfy sbd Nima na kwana biyu bana zama gobe ma insha Allah Nima zanyi tafiya zuwa Germany.


Allah ya taimaka ya tsare yabada sa'a Kuma.


Amin dukkaninsu sukace suna qoqarin miqewa cikin sautinsa me saka nutsuwa yace"


Khalilu matarka Ina saka ran a lissafi saura wata uku haihuwarta ko???


Tsit sukayi dukkaninsu su ukun 

Take zufa tafara Dan tsatsafowa Khalil din MD kuwa fararen idanuwansa ya zuba Masa Yana jiran jin amsar da Khalil din zai bada sbd shidai wadda ake maganar cikin akanta tana zaune gidansa Amma baitaba ganin ciki a jikinta ba gashi ana maganar saura wata uku haihuwa.


Dan gyara murya Khalil yayi cikin girmamawa yace''


Inshallah haka ake saka Rai saidai cikin yazo da tangarda ne sbd rashin girmansa ya bayyana cikin baida lfy inasaka ran ma gobe zanje da ita asibiti musake dubawa.



Cikin watanni da dama baa fada baida lfy ba sai yanxu?


Sarqewa Dr khalil din yayi Yana Dan gyara murya yace"


Ayi mini afuwa Modibbo nayi kuskuren rashin sanarwar.


Shikenan ba damuwa kuje Allah ya Bata lfy.


Amin"Khalil din yace suka miqe suka fito tare suna tafiya zuwa hanyar sashensu dayake direction guda.


Tafiya sukeyi su biyu Banda salman daya wuce ya nufi motarsa yafita zabeera ahankali kowannensu shiru Babu me mgn dama sun Saba haka suke koyaushe idan suna tare saisun jima shiru kafin su Fara mgn Wanda MD ne me wannan halayyar shikuma Dr khalil Yana girmama kowane irin Hali da MD ya zabawa kansa da rayuwarsa.


Tsayawa yayi ahankali batareda ya juyo ya kalli khalil dinba yace"


Bansan wane mataki ka dauki wannan alamarin ba Amma ya kamata kasan kana saka kanka cikin hadari along with her.. 'dan shiru yayi kafin ya juyo ya kalli khalil din cikin wani irin yanayi yace"


Atleast kayi tunanin Hali da Abinda zata fuskanta kafin kasata a irin wannan tight spot din sbd yanxu ku duka Kuna situation dinda only God can help so kafin komai ya fita hannunka kasan Abinda kakeyi ka dawo daidai,the truth doesn't cost anything but a lie could cost you everything.


Kallonsa Khalil yayi tareda sauke ajiyar zuciya cikin damuwa yace"


Bansaniba ko kasan Abinda nake qoqarin boyewa Amma bazaka iya fahimtar dalilina nayin hakan ba sbd komai yazone alokacinda banyi tsammaninsaba Babu mafita bayan wadda na dauka a wancan lokacin da yanzu ma..


Denying the truth doesn't change the fact cewa ka dauki hanya Mara bullewa,

Ka zauna kayi tunani zaka samu wata mafitar wannan batayi ba.


Yana Gama fadar haka ya wuce gaba batareda ya juyoba yayi hanyar sashensa.


Shiru Dr khalil zabeera yayi yana tunanin maganganun MAHMOUD din wainda suka sakashi zurfin tunanin sbd tabbas qaryarsu takusa qarewa wadda idan bai nemo mfitaba asiri ya tonu to daga Ummensa har Amatu dashima suna cikin matsalarne,

Babban burinsa daya dawo dashi shine maganar auren Amatun tukuna sbd duk wasu kayayakin aure na akwati ya siyosu yazo dasu saitin akwatinsa cif ya hado kayan aurensa Wanda ko gidan bai kawosu ba daga airport gidansu kawu suka Fara ajiyesu kafin su qaraso gida.



Ajiyar zuciya ya sauke kafin shima yabi Bayan MD din zuwa ganin Amatu da tun Yana gurin umme take kiransa yaqi dauka sbd kada farin cikin ummen ya gushe.

##Mamuh#



Kuyi hkr kuyi manage da wannan 

Post a Comment

0 Comments