TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 1-2 page 1-4

 _Page 0 1_



*Ga masu buƙatar na tallah ta masu hajar su zasu na biya ₦2000 . Idan a status kacal za'a yi Miki advert ɗin zaki biya ₦1000 only ...Sai ku tuntuɓi wannan number nawa 08081202932... Please wacce tasan zata karata Wannan labarin ta karanta shi yanzu tun daga page 1 bana so sai nayi nisa ki biyo ni akan na baki from the beginning ba zan iya ba gaskiya, ayi mun uzuri hidimomin nada yawa🤦🏻‍♀️...Sannan Ayi Haƙuri da posting din zaku ga ba tsawo babu yawan read more .*


8:30pm.

A hankali take shiga layin tana kallon Ɗiyar nata lokaci bayan lokaci ,wacce tayi laƙwaam a hannu mahaifiyar nata . Ƙare ma matan kallo nayi tare da yarinyar wacce ba zata Wuce shekara ɗaya ba a duniya .  Malam mai Adaidaita maza yi gaba wurin Wancen Gidan mai Dakali zaka Sauke ni . Cikin Ɗan ɗaga murya mai Adaidaitan yayi magana duba ga yanda ake tsala Ruwan Sama ,dole sai ya ɗaga murya na bayan sa zai jiyo sa Saboda Ƙaran Saukar Ruwan saman . Ina kenan Hajiya..? Da hannu tayi masa Alama yayin da cikin sauri ya ƙarika bakin ƙofar Gidan yana faɗin " Hajiya mun iso . Sauke Gajeruwan numfashi tayi tana saukowa daga napep din cikin sauri tare da kudundune yarinyar nata da Mayafin ta . Kaɗan jira Ni mintuna biyu zaka koma dani filin Saukar jirgi na nan aviation. Kamin me keken ya bata amsa tayi saurin shigewa cikin Zauren Wannan Gida saboda Ruwan da ake yi . 


Tun daga zauren Gidan take jiyo hayaniyar matan Gidan , tamkar ba ruwa ake yi sama ƙasa ba . Girgiza Kai tayi tana kallon Amrah yarinyar da bata san komai ba a rayuwar ta , a hankali ta furta " Allah ka gani ga Amrah nan ba barma A hannun ka da kulawar ka , Allah ka kare mun Amrah daga cikin sharrin mutanen Gidan nan . Rintse ido tayi tana tuno da Sasa sasa na wannan Gidan ,don gidan yawa ne yawan su kuma ya haura mutum saba'in yara da manyan su . Rungume Yarinyar tayi idanun ta na Saukar da Hawaye masu zafi da raɗaɗi , ina Son ki Amrah amma dole ce tasa zan barki,nan shine Miki dahir dole tasa zan kawo ga dangin ki , Ni mai sauƙi ce Nasan ko mun daɗewa zaki nemi ne domin kuwa ke Yar halak ce duk dan Halak baya mantawa da Uwar da ta haife shi . Motsawa tayi da Ƙarfi tana ɗaga ƙafarta tare da shiga Gidan kai tsaye bakin ta Ɗauke da Sallama..." Assalamu alaikum . Tayi maganan tana kutsa kanta zuwa Farfajiyar tsakar Gidan.  Mata ne ta gani sunfi Ashirin a cikin ruwa wannan tana sukola wannan tana Aikin shiga madafi ( Kitchen) inda ko rufi babu sai uban hayaƙin itace dake fita kaman An ƙona taya . Kowa Aikin gaban sa yake a ruwa sam basu damu da lafiyar su ba kona yaran su  da suke ta aikin taya su aikin gidan . 


Hasko fitila Larai tayi tana furta " Innalillahi wa'inna ilaihir kasa ƙarikewa tayi saboda gulma dake cin ta a rai ,cike da Ɗaga Murya ta ke fadin " Hafsatu kece.? .Jummai ne dake kitchen tayi Saurin fitowa tana faɗin Wacce Hafsatun ke kuma da Wane haka.? . Wata kuwa Hafsatu kika sani bayan Dakta Hafsa dai da kika sani . Sakin fitila Jummai tayi a ƙasa tana kama Ƙwankwaso tare da cewa " Au kin dawo kenan.? Kin karasa inda zaki kai Yar zinan taki shine kike kokarin maƙala mawa mamacin da ya mutu shekaru Bakwai da rasuwar shi sai a yanzu zaki kawo yarinya yar shekara daya kice wai cikin Auwalu ne ? Kai Hafsatu kiji tsoron Allah dakta Hafsa ki tuna ALLAH fa Ɗaya ne . Kayya Jummai Ai da kin barta munji ta bakin ta , da kuma mene tazo yau .? Wancen karon dai munji tace ta Haihu yanzu kuma fa mene ya faru.?  Baba Zuwai tayi maganan wacce take fitowa daga Ɗakin ta duka kuma sunyi zaman kishi da Hafsatu . 


Ƙwallah ne ya gangaro fuskar dakta Hafsa a hankali ta furta " ba sai na maimaita maku matsalar da aka samu ba domin na faɗa muku tun fari ,amma Amrah Wallahi Bata da Uban da ya wuce Auwal Ɓaidu . Laha'ila ......!!! Muryar mata da yawa na tsakar Gidan suka hada baki suna fadin " Ɓaidu kika ce bayan Sunan mijin naki mai rasuwa har sunan uban da ya haife shi kika faɗi? . Jummai ne ta kalli Baba Zuwai tana cewa " A'a Illar Auren bariki kenan ai . A bariki ya Auro ta ,yo duk mijin da ya Auri mace yar Lagos ai dama sharri da bariki a jinin su take . To ki tattara ki fita kamin mu hadu muyi Miki shegen duka . Allah sai mun sauya kamannin ki wanda ke kanki ba zaki gane kan ki ba . Zuwai tayi maganan cike da zafin kishi yayin da Jummai ta kalli Hafsatu tana cewa " Kece dai Yar bariki amma mijin mu ALLAH yajiƙan sa da Rahma mutumin kirki ne soja adali ,kisisinan ku ta yan duniya kikayi kika shigo kika Aure sa . A yanzu ya mutu Baki da Gado mai Gwaɓi shine kika yi cikin shege tsawon shekaru biyar sai yanzu kice wai kina da cikin shi kwanciya cikin yayi sai yanzu ya fito duniya. Dalla tattara ki bar mana cikin gida kamin ..... Ya isa Jummai . Hafsatu tayi maganan tana tsiyayar da Hawaye . Ruwa na dukan tsakiyar kan ta . Fiddo da Amra tayi wacce ta rufe a Mayafin ta ,kana tace " Ga Amrah Nan ne Gidan su ,ba da ita nazo cikin gidan nan ba ,anan na same ta . Don haka itama yar Gida ce . Na kawo ta Wurin ku saboda bata da Wasu bayan ku . Ku riƙe Amrah koma duk Abin da zakuyi mata Ni dai na sauke nauyin da ya rataya mun ,na dawo da ita dangin mahaifin ta . 


Kan uba ..! Waye zaki kawo mawa Yar Zina ya riƙe.? Jummai tayi maganan tana kama ƙugu kamin Baba Zuwai tace " To da yake akwai ƙannin Auwalu da yayyi ku matan su ai sai ku amsa tun da za'a nuna mana boko dole a rufe mana ido ga gaskiya mun san shi . Mata ne sunfi talatin suka taru duka matan gidan ne wasu jin Hayaniya yasa su fitowa .jin maganan da Jummai tayi yasa su duka hada baki suna cewa " Wane.??? Taɓ ai ko babu mazaunin yar zina a ɗaku nan mu . Baba Zuwai ce ta kalli Hafsa wanda gudun Hawayen idanun ta ke ƙaruwa.  To kin dai ji ,don Allah ki dauki yar ki ki fita da ita kar ku bata mana suna ,ace gidan Kanol Auwal Ɓaidu har da yar zina .Kinga kin cuce mu mijin mu baiyi yawon duniya ba ki rufa mana Asiri . 


Kallon Amrah tayi tana Fiddo da ita tare da Aje ta a ƙasa Ruwa sama ruwa ƙasa . Wani irin tsala ihu yarinyar ta fara Wacce ko tsayuwa ba tayi sai rarrafe . Ga Amrah nan duk yanda kuka yi da ita mai kyau ne , Ko ku riƙe ta tamkar Ƴa ko kuma ku Ɗauke ta ƳAR TSAKAR GIDA,duka wannan zaɓin naku ne . Nayi gaba kuma ba zan Waiwayi Amrah ba har girman ta . Tana gama Faɗin haka ta juya tana ficewa daga cikin gidan . Yayin da su Baba Zuwai ke fadin kai da Allah kowa ta tafi Ɗakin ta mu shige , da kanta idan ta leko taga yar ta a Tsakar gidan zata ɗauke ta ,waye zai riƙe ƴar Zina.? . A'a wane kuwa . Matan suka mara mata baya suna shigewa dakunan su har da masu rufo kofa wasu na sakin Labulayen su . Wani irin ihu Yarinyar Jaririyar da Bata wuce Shekara daya ba take yi a tsakar gidan tana rarrafawa tare da bulayi a tsakar Gidan , ruwa na dukan ta haka take yanka ihu tana ware² ko zata ga Mahaifiyar nata amma kuma bata ganta ba ......!

*Ga masu buƙatar na tallah ta masu hajar su zasu na biya ₦2000 . Idan a status kacal za'a yi Miki advert ɗin zaki biya ₦1000 only ...Sai ku tuntuɓi wannan number nawa 08081202932... Please wacce tasan zata karata Wannan labarin ta karanta shi yanzu tun daga page 1 bana so sai nayi nisa ki biyo ni akan na baki from the beginning ba zan iya ba gaskiya, ayi mun uzuri hidimomin nada yawa🤦🏻‍♀️...Sannan Ayi Haƙuri da posting din zaku ga ba tsawo babu yawan read more .*


**

Ihu yarinyar take tsalawa a yayin da Ruwa sama Ruwa ƙasa ake yin shi yana kuma zuba a kan ta . Data rarrafa ta nufi can Wani wuri sai taga babu hanyar ɓillewa ,don wasu da yawa a cikin gidan Rufe Ɗakunan su suka yi ,wasu kuma Labulayen su suka Sauke . Yarinya ƙarama yar shakera Ɗaya sam bata san komai a rayuwa ba ,a yau ne ta fara karo da Menene ake kira da Jarrabar Rayuwa . A yau ne tafa ganin kan tana bulayi a tsakar gida babu mai ɗaukar ta bare kuma Rarrashi . Tsawa aka yi mai ƙarfi Wanda yasa Amrah ƙanƙame jikin ta na Firgici da tsoro tana Ɗauke wuta . Wanda a daidai can Ɗakunan gidan Yara kamanta yan shakara Daya Wasu na hannun iyayen su Wasu kuma na jikin iyayen su sun Rungume .  Assalamu alaikum gafara dai mutanen Gida , Baba Adamu yayi maganan yana hasko fitilar Sa zuwa tsakar Gidan wanda ya kasance Yayan mahaifin Amrah ne . Wato kanol Auwalu Ɓaidu . Kan sa rufe da buhu wanda yayi matara akan sa kaman lema . Cikin Sauri yake shirin nufar sasan sa inda matan sa da yaran sa suke . Hasken fitilan sa ne yasa Amrah gigif tana jan dogon ajiyar zuciya tare da ƙara saka kuka mai karfi irin na urincewan nan . 


Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ...Baba Adamu ya furta yana faɗin Yar Waye wannan a tsakar gida ? , wannan wani sakarci ne yar Waye haka a tsakar gida .? Yayi maganan cikin daga murya yanda zasu iya Juyo shi , cikin Sauri ya nufi inda Amrah ke Zaune yana Kai hannu tare da Ɗaukar ta . Habi...! Habi...!! Ya hau kirar sunan Habi don a tunanin sa Yarinyar data Haifa ne kwanan nan . Don basa gane yaran gidan saboda yawan su . A ragen lissafi idan ka lissafa yara da manya na cikin gidan ya'yan su sun kai hamsin in ma basu wuce ba . Jiyo Muryar Baba Adamu yasa kowa Saurin fitowa daga Dakunan su ,don sun san bala'i irin nashi . Kallon su yayi yana haske su da fitilu tare da kallon yarinyar dake karkarwa na sanyi , wanda a dai dai wannan lokacin Ruwan ya fara Ɗaukewa sai dai Walƙiya da Tsawa . Yarinyar Wacece wannan? Wani irin rashin kula ne ya same ku ace ana ruwa ku bar yarinya a tsakar gida tana ihu ita ɗaya ?. 


Baba Zuwai ce ita yar na isa ta kalli Baba Adamu tana cewa " Ai Malam daka Sauke yarinyar nan ƙasa don ba yar sunna nace Fache Yar Zina.! . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Ƴar Zina kuma Zuwaira.? Yayi maganan yana kallon Kyaƙyƙyawar fuskar Amrah Wanda yayi kama dana Fulanin zuryan . Eh mana Malam , Yarinyar da Hafsatu ta haifa ce nan ta kawota yanzu bata ta daɗe da fita ba , Wai a cewan ta yar marigayi ne kanol wanda mutuwan sa shekaru fa bakwai kenan .? Lumshe ido Baba Adamu yayi yana Girgiza kai kana yace " Yanzu jinin Auwalu ce kuka bari a Tsakar gida ruwa na dukan kan ta sama da ƙasa . Yarinya ƙarama Wacce ko tsayuwa bata yi bare tafiya ?. Saboda zafin kishin ku na banza da Wofi . Sakin baki matan Gidan suka yi suna kallon Baba Adamu wanda yake surfa faɗa inda yake shiga ba nan yake fita ba . Larai ce ta kalli Shi tana cewa " Malam ka natsu don Allah kasa hankalin ka ma'aunin ka a mizani . Shekaru fa Bakwai da mutuwar Auwalu mijin mu sai yanzu a kawo yarinya yar shekara Ɗaya ace wai Yar sace .? Ko don Hafsatu bata da da a cikin gidan nan take bakin ciki da gadon yaran mu .? . Kayya Haba Larai Haba wai yanzu da gaske kike wannan maganan, To Auwalu ba shekaran sa bakwai bane bashi a gida shekarun sa 9 ne. Sannan kuma da kuke tacewa Auwalu ya mutu ? A ina kuka Gawan sa , kawai kuce Auwalu ya ɓata kuma har yau ba'a gansa ba . Ina Addu'ar Allah ya bayyana Auwalu a duk inda yake Domin shine kadai Zai raba Wannan Gardaman . 


Jummai ce ta kalli Baba Adamu tana faɗin " Ikon Allah sai kallo , Malam yanzu fa kace Shekarun sa 9 da ɓata , kar ka manta daga tura su yaƙi irin nasu na Soja shine fa har yau babu shi babu labarin sa . Kar ka mata Su majojin ne suka sanar mana Auwalu ya mutu ba'a ga Gawan sa ba . Yo tayaya wannan yarinya zata zama Yar sa ,itafa shekaranta ɗaya ne a duniya ,shi kuma shekarun sa 9 da barin duniyar baki daya . Humm Numfasawa Baba Zuwai tayi tana katse Jummai tare da cewa " Malam Wallahi duk Abin da Hafsatu zata ce sharrin sune na yan boko yan bariki .ta ganmu talakawa Zata zo ta cuce mu ,shine take fadin Wai cikin kwantawa yayi sai a yanzu da ya tashi shine ta haifo Wannan yarinyar wa take Amrah ce ko waye oho yar zinan ta dai ." Kayya...! Kar na ƙara jin wannan kalmar daga bakin ko wannen ku , Amrah ya ce a cikin gidan nan . Kuma jinin mu jinin Auwalu .  Itama zata Zauna tare da Yan Uwan ta da dangin ta . Zuwa safe zanyi magana da Mazajen naku duka .kowa ta wuce ta bani Wuri .


Sumi² kowa tayi Ɗakin ta duk da da magana a bakin ko waccen su Amma kuma babu daman Amayarwa . Ɗaga Asabarin Ɗakin sa yayi yana shiga bakin sa ɗauke da Sallama wanda bai jira Amsawar Matar nasa ba yake fadin " Lanti Maza Ɗauko bargo a rufe Amratu,yanzu dama kina cikin gidan duk Abin dake Faruwa kina ji a daki.? . Muskutawa Lanti tayi ba tare da ta basa Amsa ba ta nufi uwar Daƙin ta tana fiddo da bargo tare da miƙa masa don ko hannu bata kai ba bare ta amsa Amratu dake rawar Sanyi da cira . Amsan Bargon yayi yana saurin rufe Yarinyar tare da Kallon Lanti wacce ta motsa bakin ta tana cewa " Ina ji , kasan komai na cikin gidan nan bana shiga saboda banda mutumci ba zan ɗauki cin kashin ko wacce mata ba . Don haka yau yarinyar nan zata kwana a dakin nan ba zan hana ba ,amma gobe sai dai ta kwana a dakin matan Uban ta gasu nan har biyu.  Tana gama Fadin Haƙa ta juya tana kokarin shigewa daga ciki ne sai Baba Adamu cike da dan sarewa yace " Lanti wannan itama tamkar Yar ki ce bayan nan ita marainiya ce gaba da baya babu uwa babu uba . Mune kaɗai gatan ta a yanzu . Eh kayi Gaskiya malam Amma kar ka manta mu kan mu yayan mu sunyi yara rai takwas ne a dakin nan  ,kaga su can ne zasu riƙe ta , Ni dai abincin da zan Bata har girman ta ba zan hana ba. Amma bayan nan babu Abin da zan yi a kan Wannan yarinya . 

Humm Shikenan Lanti Maza Daura Ruwan Ɗumi kiyi mata Wanka zuwa safe Za'a yi magana sosai . 

**

Da misalin ƙarfe 9:01am na Safe ne duka mata da mazan Gidan aka taru a babban Zauren gidan don dama haka suke yi idan zasu yi magana mai muhimmaci , an turza an raya Kowa yace ba zai Amshi Amrah ba ,sai da Baba Adamu ya bude ma Baba Zuwai Wuta ne akan dole Amrah a dakin ta zata zauna ,idan kuma taki sai dai ta fito daga Dakin ta bar shi ,don dakin na Mahaifin Amrah ne da Sauran yayyun ta . Jin haka yasa Don dole Baba Zuwai Amincewa ba don taso ba. Sai ma cewa tayi a ga filin tsakar Ɗakin can taje ta zauna . Haka dai a karkare babu mutum daya mai goyon bayan zaman Amrah a cikin gidan sai Baba Adamu wanda ya dauki nauyin cin ta da shan ta ,amma rayuwar ta a dakin matar mahaifin ta zata yi shi wato Baba Zuwai .  A safiyar Ranan Koko Lanti ta dama tana zuba ma Amratu nata tare da kaiwa Dakin Baba zuwai don a bata . Amma  haka yarinyar nan tayi ta bulayi har rana babu wanda bata Abinci ,gashi a yanzu bata kukan sam ,alamu ya nuna yarinyar akwai Haƙuri duk da idanun ta kaɗai zaka kalla ka tabbatar da tana jin yunwa matuƙa . Amma Babu imani Baba Zuwai ko kallon Amrah bata yi . Sai dai yarinyar ta zauna ita kaɗai idan ta gaji kunsan Yaro baya zama wuri Ɗaya sai ta rarrafo ta fito tsakar Gidan . A haka har karfe Biyu na Rana . A wannan lokacin manyan idanun yarinyar duk sunyo waje hasken nan nata kaman tsada har ya fara duhuwa na wahala . 

*Ga masu buƙatar na tallah ta masu hajar su zasu na biya ₦2000 . Idan a status kacal za'a yi Miki advert ɗin zaki biya ₦1000 only ...Sai ku tuntuɓi wannan number nawa  08081202932. 😹Ina ganin comment din ku nakan yi dariya some times,wasu lokutan kuma sai naji zuciya ta takaraya😢 duba ga rayuwar Amrah And Hafsat's pain...Wata ma fa cewa tayi wai laifin na Hafsa ne and After all this ta kuma dawo tace ita mahaifiyar Tace ....So proud of you my Guyz much love.*

**

*Aƙwai maganin infection na gida kasadan wanda zaki sha na tsawon kwana ki bakwai ,fatattan duk Wani Sanyi da abun da ya shafe shi yake yi ...fara shin mu akwai na 5k zuwa 7k  Bama sai da na kasa da hakan ,domun kuwa Maganin mu mai inganci ne . Ga masu buƙata zasu iya tuntuɓan wannan number 08081202932/09061466409*


Rarrafawa Amrah tayi tana shiga cikin Taɓalɓalin Gidan gaba Ɗaya kamin yarinya ya sauya . Zulai ce da take Wanke wanke ta kalli Amrah tana hararan ta tare da cewa " Wallahi yarinyar nan tazo inda nake sai na Wanke fuskar ta da Mari . Shegiya ƴar Zina Kawai guba . Tana maganan tare da Wanke wata ƙatuwar Tukunya na Umman ta Wacce take sana'ar dafa Awara ta sayar da yamma . Cike da Yarinta da Rashin Sani ,kun san yaro idan yaga Ruwa Amrah ta rarrafa da Gwiwowin tare da hannayen ta tana nufar inda Zulai ke Wanke -wanken . Kama Bokitin tayi tana Miƙewa tsaye tare da kai hannun ta tana tsunduma Yan yatsunta cikin Ruwan . Kan uba nan ..! Zulai tayi maganan tana Ɗagowa tare da kallon Amrah Wacce suna Haɗa Ido ta washe mata baki Hakoran ta yan guda biyu na bayyana tare da Wangale mata baki tana Dariya . Ɗaga Hannu Zulai tayi tana Wanke fuskar ƙaramar yarinyar Amrah da Mari wanda Sai da yannan Numfashin ta ya kusa Ɗaukewa tana jan iska tare da Yanka ihu mai ƙarfi . Dan uban ki gobe idan ina Wanke-wanke ji taho inda nake , kin gama yawo cikin tabalbali zaki zo ki ɓata mun Ruwa da kwanoni Uwar ki nace bar Wurin nan .! Zulai tayi maganan cikin Tsawa wanda yasa Amrah Urin cewa tana Cigaba da yanka ihu sosai . Baba Zuwai dake Ɗaki ne take cewa " Ƙara ma yar iska Wacce aka haifo ta a kwararo aka zo a liƙa ma Mahaifin ku da ya dade a ƙasa mamaci haba wannan duniya ina zaki je damu ne.? 


Ikilima ce wacce shigowan ta yayi dai dai da duk Abin dake faruwa , Domin kuwa jiya ta dawo daga makarantar kwana da take yi sun sami Hutu , duk halin da ake ciki ta sani a wannan gidan ,yanzu ma daga Gidan kawarta take ,ta kai mata ziyara , itama Ikilima Yar kanol Auwalu Ɓaidu ce Mahaifiyar ta a gidan itace Baba Zuwai . Ganin yanda kowa ya cigaba da Aikin sa babu wanda ya kalli Amrah dake ihu haka babu Wanda yace ma Zulai Dan me ta duke Amrah yasa Ikilima cikin Sauri har da dan gudu a kuma zafafe ta nufi inda Zulai ke Wanke-wanken. Zulai wannan Wani irin zalunci ne ?, Mene Amrah tayi Miki yarinya ƙarama Wacce bata san komai ba zaki daga Hannu ki kama marin fuskar ta . ? . Kallon Ikilima Zulai tayi tana murguɗa mata baki tare da mata kallon Sama da Ƙasa tana cewa " Ashe Bata san komai ba ,to na Mare ta ,nan gaba ta kara zuwa inda nake Abun da yafi Mari ma Zan mata . Kan Uba..! Zulai Mari kika ce zaki mata Wannan Jaririyar zaki mara.? Kamin Zulai tayi Wani magana ne Ikilima ta Ɗaga Hannu tana Sauke mata Wasu irin lafiyayyun Mari Tassss Tassss har sau biyu . Don Allah kar ki fasa , tun da baki da imani muguwa Azzaluma kawai . 


Hayaniyar su ce ta balle nan kika ga yara da iyayen su sun taso sun fi talatin ,babu mai ba Ikilima Gaskiya sai dai bakin ta da Kwace ta ,don ita akwai iya sababi tasan ya ake tijara bata da hakuri ko kadan ,sai dai akwai ta da tausayi . Cike da jin takaicin ta Baba Zuwai tace " Shegiya yar banza akan Yar zina ce zaki kama Dukan jinin ki ?. Gaskiya baki da Ɗabi'a Ikilima  . Mama Ko me zaku ce sai dai kuce , ba zan bari ina gani a zalunci karamar yarinya ba , Idan Zulai jina ce itama Amrah jina ce , Baba ne ya haife ta . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una tabbas akwai Hauka a kwakwalwar ki Ikilima . Cewan Zulai tana Kallon Ikilima ido cikin ido . Murmushi Ikilima tayi na tijara kana tace " ba zaki fahimci akwai Hauka a kaina ba Wallahi sai ranan da kika yi kuskuren kara taɓa Amrah ,mugaye Azzalumai . 


Fito Sarari ki zage mu , yar na isa..! Jummai tayi maganan tana kallon Ikilima , Wanda baba Zuwai ta amshe tana cewa " To ai Shikenan ku barta , Ikilima daga yau ki zama uwan ta uban ta don Allah kinji, idan zaki koma makarantar kwanan ki tafi da ita tun da jinin ki ce . Daukar Amrah Ikilima tayi tana Wuce su ba tare da ta kuma tanka masu ba. Ɗakin baba Zuwai ta nufa da ita tana shiga ne tayi ido biyu Da fida na tara cike da koko . Kallon Amrah tayi Wanda a yanzu tayi shiru tayi lakwam a hannun ta . Amrah Zaki sha koko ko na saya Miki Awara .? Tayi maganan tana kallon agogon dakin da ke nuna mata karfe biyu da rabi na Rana . Da ido Amrah tabi ta don bata magana ba ta iya ba sam . Durkusawa tayi tana ɗaukar Kokon tare da zama gyefen tabarman ɗakin tana fara ba Amrah kokon wanda cikin sauri yarinyar ke masa shan Ruwa saboda Yunwa . Sai da ta kusa shanye babban fidan sannan ta dakata tana kwantawa a jikin Ikilima , Ƙwallah ne ya ciko idanun Ikilima tana kallon Amrah tare da tuno da mahaifin su . Muskutawa tayi don debo ruwa ta bata ko zata sha ,amma nan taga yarinya ta bungure Alamun barci ya dauke ta . Wannan yasa Ikilima samun zani tana Goya ta a gadon bayan ta . 


Caɓe Baki baba Zuwai tayi wacce take shigowa kamin tace " Don Allah Ikilima dauke ta ki tafi Dakin kwanan ki ku tafi can , wallahi kuma indai kin zabi haka ne a cikin gidan nan to zaki wahala . Juyawa Ikilima tayi a hankali tana faɗin " Mama Wannan Fa Marainiya ce duk gidan babu Maraya kaman ta , Baba ya rasu .....ke da Allah yi mun shiru, Ahir din ki.! Daina alakanta mun miji da yar zina , fita kar raina ya ɓaci . ? Humm Numfasawa Ikilima tayi tana ficewa da Amrah. 


A wannan Rana Amrah kukan rashin uwa kadan tayi Ikilima itace sayan mata Wara itace biscuit komai da yaro ke bukata kaman ta take bata , haka wuraren La'asar ta fita da ita tare da shuga gidan kawanta anan makotan su . Bata dawo Gida ba sai bayan Magriba don ko da aka kawo mata Tuwon dare ,cewa tayi ta koshi don taci a gidan Kawanta Hajara . Don acan ta cika cikin ta dana Amrah . Ganin Ana juya da Tuwon ne tace ke kawo mun nan da safe Maci da Amrah . Amsan Tuwon tayi tana Rufewa gyefe tare da dawowa kan Katifan ta tana rungume Amrah wacce tayi nisa a barcin ta. To yanzu Idan na koma makaranta wa zai kula da Amrah , ina jin tausayin yarinyar nan ,don kuwa Su Matan Gidan basa da imani ka kadan . Haska fuskar Amrah tayi da fitilan Nokia din ta kamin tace " Tabbas akwai Wani abu a ƙasa ,amma Amrah ba da kowa tayi kama ba Fache Baban mu , manyan idanun ta yanayin shatin Giranta duk wanda yasan Baba ya kuma ga Amrah yasan jinin sa ce...! Dole zan Haƙura da makaranta ko na shekara daya ne Don na bata kula ta kara Wayau daga bisani sai na tafi . 


A haka yau da gobe babu lokaci na tafiya kullum babu dadi Rayuwar Amrah a cikin gidan . Gaba daya Ikilima ta kashe karatun ta na tsawon shekaru biyu , baba Adamu shine cin Amra da shan ta ..kulawan ta kuwa Ikilima ce . A haka har Amrah ta kai shekaru uku a cikin gidan . A wannan lokacin ne Ikilima ta koma makaranta , don duk wani maraici Amrah ta gama sanin shi . Yarinya ce hakurarriya bata da magana sam . Abun dake bata Ran Ikilima shine rashin zuwan Amrah Makaranta tayi magana har ta gaji . A haka Amrah takai shekaru Bakwai babu Makarantar boko sai na Allo da take zuwa . A dai dai Wannan lokacin Wahalar duniya a cikin gidan Amrah keyi ,itace tallahn Gyaɗa da Safe zuwa karfe biyu da La'asar ta tafi Tallahn Awara . Sam bata hutawa haka Abinci sai ta kwana bata ci ba . 


Amratu Amratu...! 


Muryar Baba Adamu ya katse Amrah dake Wanke-wanken kwanukan Gidan nan baki daya , rayuka sun fi tamanin . Na'am Baba ." Tayi maganan cike da Sanyayyar Muryar ta na yara.  Murmushi Baba Adamu yayi yana Fiddo da takarda yana cewa " Amratu na kin ga wannan Admission ne na Makarantar masu kudin can Sun dauki nauyin karatun marayu 10 a wannan shekaran sunan ki ya fito Amratu, zaki fara daga Aji biyu zuwa har aji shida .duka a kyauta . Yayyyyy....! Baba Ina so Baba nimm....Don Allah rufe mun baki ,wani makaranta za'a saki ? ,Tallahn gyaɗan Safen Wa zai mun .? Baba Zuwai tayi maganan tana fiddo da idanun ta na masifa waje . Jummai ne tace " Ni kuma Tallahn Waran La'asar din fa.? . 


Shiru Amrah tayi yayin da Baba Adamu yace " Amrah a gobe zata fara zuwa makaranta kunga ledar nan uniform din ta ne ciki da komai da komai aka bata su hukumar makarantar . Tallahn safe ku nemi mai yi maku Tallahn rana idan ta dawo tayi . Jeki tafi ki Cigaba da aikin ki . Summ² Amrah ta wuce tana dukufa tare da Cigaba da Wanke-wanken . Da ido suka bi Baba Adamu har ya shige sasan shi . Tabdijam yanzu makarantar ya'yan masu kudi zai kaita ,mu namu yaran suna na gomnati?? . Larai tayi maganan yayin da Zuwai tace " Humm Fifiko ke abun bari ta fara zuwa zan ci uban ta ne , karatun wallahi ba zata yi ba . Yanda ta shiga Batasan komai ba haka zata fito Batasan komai ba. Shewa Jummai tasa ka da sauran mutanen tsakar gidan suna fadin " Dakyau Baba Zuwai .! 

**

Safiyar litini Amrah murna take yi sosai sam ta manta da ɓacin ran cikin gidan . Sanye take cikin uniform rigar fari da Sanyi akai . Skirt ne iya gwiwa sai takalmin makarantar babu arzikin Safa bare jakan makaranta , Don Littafai biyu baba Adamu ya saya mata wanda ta zuba su a leda . Hijabin makarantar iya Kafaɗa ne wasu ma basa saka Hijabin sai hula musamman su yara . Saurin fita daga Taskar Gidan tayi don gudun Tsiya da zata sha . A wajen Gidan can nesa ta tsaya tana Jirar fitowar Baba Adamu .  A hankali  take bin titin layin nasu da kallo tare da kallon ƙaton gidan dake gaban ta , benen saman gidan take kallo , dai dai ana buɗe Gate ɗin gidan.  


Laa kayan mu iri ɗaya ...! Tayi maganan a zuciyar ta tare da bin Dan Saurayin da ya fito daga Gidan sanye cikin uniform irin nata Amma shi da dogon Hannu ne alamu SS yake . Kallon Driver n shi yayi yana cewa " No yau a keke zan tafi ,ba sai kazo dauka na ba . Sabon keken shi ya hau tare da gyara School bag din shi yana fara Driving ɗin keken wanda daga ji kasan bana kasar nan bane .  Ta gaban Amrah yazo yana kokarin wuce ta idanun Nurain ya Sauka akan Ta . Tun daga saman ta har ƙasa ya kare mata kallo idanun sa na dira akan jakar ledar Hannun ta . Nan take ya hau kyakyata dariya har yana sakin kan keken yana kecewa da Wani irin Dariya . Hi student...! Which school are you going now.?  . Tsayawa Amrah tayi tana kallon sa sam ta rasa inda ya nufa , don bata ji mai yake cewa ba . Tsayawa yayi yana ɗan yin jimmm tare da kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta dai dai tana dago da Lulun idanun ta wanda suka ciko da ƙwallah fuskar ta a dan shagwaɓe alamu tana gab da fashewa da kuka ne . Wow fine girl . Are you in primary section? . Amratu... Amratu...! Muryar Baba Adamu ya katse su inda tayi Saurin juyawa tana kokarin nufa inda Baba Adamu yake .  Kallon bayan ta Nurain yayi yana bin uniform din ta da ko guga babu ta fito kaman wata bujiya yana ƙara saka dariya tare da Wuce ta . 


Bayan ta karisa inda Baba Adamu yake ne ta kalle shi tana cewa " Baba wannan Shima kayan Makarantar mu iri ɗaya. murmushi baba yayi yana cewa" Eh ai shi anan yake , kin ga gidan mahaifin shi can ,su ya'yan masu kudi ne , Duk girman Gidan nan shi kadai ne a ciki iyayen sa suna Kasar Waje , acan suke rayuwa ,yanda naji wai shi yaron ne ke son yin karatu a nan kasar . Hummmm Kama hannun Baba Adamu tayi cike da Yarinta tace " Baba ya kalle ni yana mun Dariya Kuma yana wani magana banji komai da yace ba . Kallon ta Baba yayi yana cewa " Amratu kenan , Amratu baiwar Allah ...! Hau mu tafi ka kiyi latti .  Ɗago ta yayi yana daurata a gaban tsohuwar keken sa yana gungurawa tare da bin gyefen hanya don kaita makarantar............

*Ga masu buƙatar na tallah ta masu hajar su zasu na biya ₦2000 . Idan a status kacal za'a yi Miki advert ɗin zaki biya ₦1000 only ...Sai ku tuntuɓi wannan number nawa  08081202932.*


Gidan Ɓaidu Ya hargitse tun bayan Tafiyar Baba Adamu don kai Amrah makaranta ,Inda baba Zuwai ke shiga ba nan take fita ba . Masifa kaman zasu raba Gidan wuri biyu . Nufar Ɗakin Lanti Jummai tayi tana budo labulen ta tare da cewa " Mu dai kam yau Lanti ki fito kiyi mana bayani,kodai Mahaifiyar yarinyar nan tana ba mijin ki Wani abun ne wanda mu bamu Sani ba . Zumbur Lanti tayi tana Miƙewa daga kishingiden da take a tabarman tsakar Dakin nata . Cikin Sauri ta fito tana nufo Farfajiyar tsakar gidan tana bin matan Gidan da kallo ,kana daga Bisani tace " A'a wallahi Ahir A cire sunan mijina akan komai naku , duk tsiyan da zaku yi ku tsaya a iya kan Amrah amma rainin naku kar ya tsallako kan Adamu . Baba Zuwai ne tana cilli da hannun ta na Jaraba gata ƙatuwa amma sam bata jin nauyin jikin ta don kiban ta ya zama na cuta . Nonuwan ta kaɗai aka barka dasu kaya zasu zama maka babba . Domin kuwa ko wani Guda Ɗaya yayi kai da jikin jariri ,Amma haka take surfa masifa tana cewa " Ai bamu muka saka Adamu ba , shi ya saka kan sa. Ya za'a yi ya dauki yarinya ya kaita makaranta kai tsada duk fadin Kaduna babu makaranta mai tsadan shi wai a raina mana hankali ace kyauta ne aka dauki nauyin ta . Koda ba muyi boko ba ,ai muna da ilimin sanin Rayuwa.  Kallon Su Lanti tayi tana Cewa" Lallai kun dade da manta Wacece Lanti , akan mijina zan iya yin komai Wallahi kun Sanni farin sani . Tabbas kun manta irin faɗa na ,don Ni bana cacan baki sai dai cika Aiki , a nawa tunanin a yanzu an girma ne shiyasa nayi Watsi da komai , ashe har yanzu da sauran Haukan Ƙuruciya akawunan mu duka . Bara ina zuwa ....! Tayi maganan tare da juyawa tana nufan Madafin su ( Kitchen) . Ganin haka yasa Jummai kallon Baba Zuwai da Sauran matan Gidan kamin Zuwai tace " Wai mene take shirin yi ne .? . 


Cike da sassataccen Gwuwa Jummai tace baya ne zata dawo gaba ai . Motsin fitowan Lanti suka ji daga Madafi nan take Kowa ya kalli inda take tahowa hannun ta dauke da Guggun ice irin manyan iccen nan na jego yana ci da Wuta ,don alamu daga Murhu ta fito dashi , nufo su take kaman Boss wanda tabbas sun san a da baya haka suke faɗan su acikin gidan ,wannan ta dauko taɓarya wannan bakin Wuta wannan bokitin ƙarfe . Wani irin zurawa da Gudu Zuwai tayi nonon ta na dukan ɗaya tana shigewa cikin Ɗaki tare da rufo ƙofa . Haka suma suka Gudu suna yin ɗakunan su babu Wanda ya tsaya . Ku ƙananan yan matsiyata ne ,da kun sani ku tsaya Ni ban iya cacan baki ba ayi aiki a zahiri ne da jiki shine za'a sani .


**

A makarantar Hi Academy an gama tantace Amrah an kuma miƙata zuwa ga Malaman Ajin su Wato Aunty Jamaima wata inyamura nan igbo ce . Nufar Primary 2 tayi da Amrah tana shiga Class tana faɗin " Good morning Class.! Good morning Aunty.." Ɗaliban suka haɗa baki Wurin Gaishe da Aunty Jamima. Kallon Inda Amrah take tayi tana faɗin " Ga sabuwar Zuwa sunan ta Amrah Adaam Ɓaidu . Wow nice name.... your Welcome classmate ( Muna maki Barka da zuwa ) . Sam Amrah bata ji mai suke cewa ba , sai dai bin su da kallo da take yi , Anty Jamima ce tayi mata Wuri A second seat don kowani dalibi seat din shi ,shi kadai ne da wurin aje jaka da Lunching Box . Sabon Rayuwa take ganin kan ta a ciki ,a haka take kallon kowa na Ajin da Ɗaliban ke ta mata Murmushi irin na baƙuntan nan .  Tun da Aunty Jamima ta fara masu karatun har ta gama Amrah bata san inda ta dosa ba , a haka ta fita wani malamin ya shigo shima yayi nasa . Third period na fita aka tashi break nan take Yaran Ajin suka nufo wurin zaman Amrah kowa na gabatar mata da kan shi da turanci ,ta ɗan fahimta abun da suke nufi Amma kuma ita dai Ba turancin nan take ji ba , hasali wannan shine karon ta na farko da ta fara shigowa Aji da makarantar baki ɗaya indai aka cire Allo . 


Nurain Whare are we Going now.?  . ( Ina zamuje yanzu Nurain). Nurain ne ya kalli Abokanan nasa yana Murmushin nan nasa don shi mutum ne mai fara'a sosai ga surutu . Please come and Excout me to Primary Section , Akwai wata sabuwar Ɗaliba da nake son Ganin ta before a koma break . Kallon sa David yayi yana cewa " New comer .? Kasan tane ? . A'a ban san ta ba , kawai dai a hanya na ganta ɗazu , komai nata Dariya yake bani , oya common guyz . Sanin Halin sa da in yace Abu dole a bi masa yasa su bin bayan su suna nufan Primary Section, tun daga Primary 5 suka fara shiga , suna shiga duka daliban suke tashi su Gaishe su suna fadin " Good morning seniors....Bai tsaya basu Amsa musamman idan yaga bai ga Wacce yazo nema ba sai ya fita ya faɗa wani Ajin . Nufa Primary 2 suka yi inda a bakin Windown Ajin ya tsaya yana Hango inda Ɗaliban Suka Rufe Amrah tsayawa Su David suka yi suna kallon yanda kowa ke gabatar ma Amrah da sunan sa tare da Son zama Abokin ta . Amma bata ce masu komai. I think she don't know how to speak in English . David yayi maganan yana kallon Nurain Wanda idanun sa ke acan Seat din da Amrah take . Eh Nima tunanin da nake yi kenan .  Ihun Wata yarinya suka ji tana daka nawa Ɗaliban Tsawa tare da cewa " Ibeg You Are disturbing her (Kuna damun ta ) . i think this girl doesn't know how to speak in English so please just leave her alone . Kallon Marian suka yi wacce ta kasance Yoruba amma Musulma ce . Tsoron Marian ake ji a Class din don bata da kirki ga tsiya ,hakan yasa kowa kama bakin shi . Excuse me pls , ku bani Wuri .  Tayi maganan tana zama a saman desk din da Amrah take . Cikin Harshen Hausa tace " Aunty Jamima tace mana sunan ki Amrah Adaam Ɓaidu Right.? So can we be friends, zakiyi ƙawa Dani ?.  Kallon ta Amrah tayi tana watsa mata manyan idanun ta kamin ta gyaɗa mata kai alamun eh . No that's not good, Nima magana Zaki mun kaman yanda nayi Miki Amrah ,kin yarda muyi Ƙawance tare ?. Cikin Zazzaƙar Muryar ta mai cike da sanyi na haƙuri tace " Eh na Amince . Murmushi Marian tayi tana Kama Hannun Amrah tare da Ɗagawa sama tana ɗaga murya tare da cewa " yanzu yan Aji dani da Amrah Mun zama Ƙawaye.  Chioma ce cike da jin Haushi tace " And SO What.? Se mene kuma , mun ji to . Tayi maganan cike da Tsiwa tana barin Ajin . Taɓe baki Marian tayi tana kallon Amrah tana cewa " Shekaruna 8 kefa?. Ni kuma Shekaruna 7. Murmushi Marian tayi tana kallon Gyefen littafin Amrah tare da duba rubutun nata Wanda ko sunan ta bata saka a littafin ba . Ɗan jimmm tayi kamin tace " baki taɓa shuga Makaranta bane .? Gyaɗa mata kai Amrah tayi ,wanda kamin Marian tayi magana Nana ta katse su tana cewa " But you are not suppose to be in primary 2 , kamata yayi akai ki primary 1 ai. It is your business.? Gulma da saka ido to Ɗauke ta ki kaita Primary 1 din idan akan ki take . Marian tayi maganan tana dalla ma Nana harara . Karan kada kararrawa ne yasa Amrah Juyawa tana kallon inda daliban ke shigowa da gudu ajin idanun ta ne ya sauka akan Window inda Nurain yake da Abokanan sa ,suma idanun su na akan ta . Murmushi yayi mata a zuciyar shi yana cewa " Ohh Duk maganan ma dana yi mata ɗazu bata jini Bama Ashe .? . Juyawa sukayi ba tare da yace mata komai ba suna koma Section din su . 


2:30pm . (Closing hour).

Ana tashi Amrah ta fito ga yunwa dake cin ta ,don ko karyawa ba tayi ba , har jiri take gani , gashi tasan idan ta koma gidan ba Abinci za'a bata ba sai Tallah da zata Dauka na Awara .  A farfajiyar makarantar daga masu shiga school Bus sai masu shiga moton gidan su wasu kuma manya irin yan SS suna tafiya a keken su . Hanyar ƙasa ta kama tana fara tafiya tare da kallon titi nan biyu ko wanne na wucewar manyan Abin hawa ne . Hi Amrah...!!! 


Jin Muryar shi tayi Wanda cikin sauri ta juyo tana kallon Nurain a keken sa dake bayan ta yana murmushi. A daidaita zaki Hau ne na taran Miki .? Kallon sa tayi tana Girgiza kai alamun a'a . Ɗan kallon ta yayi yana ƙare mata kallo kamin yace " Ke scholarship ne aka dauke ki anan .? Eh . But me yasa bakya magana.? Kurr tayi masa da ido cike da Yarinta idanun ta na kawo ruwa tace " Idan ina magana Baba Zuwai duka na take yi... Shiiiii Don't cry please kar kiyi kuka , Ni ki rinƙa mun magana saboda baki ga nima ina Miki magana ba ?. Eh kana mun . Yauwa yanzu zo tanan na goya ki a keke na mu tafi..... Cike da Yarinta ta Wangale masa baki gyefe da gyefen Kuncin ta yana loɓa .  Common Amrah yi sauri rana bai damunki.? Sam bata basa Amsa ba ta nufi inda Nurain yake da hannun sa ya Ɗagota yana Ɗaurata a gaban keken nasa yana fara tafiya da ita tare da bin Wani hanya wanda bata san wacce hanya bane don sun sauka a titi . Murmushi yayi yana kallon ta tare da cewa " Kinga tanan yafi sauƙin kaiwa Gida nan da nan zamu je gida. Da gaske ..? . Eh mana .!  Ruwa ruwa zai sauko Kayi Gudu . Amrah tayi maganan tana kallon sama don a watan August ake nan da nan ruwa ya sauko ,don a wannan lokacin yayyafi aka fara .  Dariya Nurain Yayi yana dakatawa da tuka keken yana cewa" Tsoron Ruwan kike ji.? Gyaɗa masa kai tayi tana cuno dan mitsulun bakin ta gaba na yarinta tana cewa " Idan ruwa ya duke Ni to da kayan zan kwana Baba Zuwai ba zata bari na cire ba a jiki na zai bushe ,Ni kuma ina jin Sanyi sosai . Wacece Baba Zuwai.? . Wangale masa baki tayi tana faɗin " Mama nace . Ɗan jim Nurain yayi kamin ya kafe ta da ido a zuciyar shi yana ayyana anya Mahaifiyar tace kuwa .? May be bata san Maman ta bane ko ta rasu . Ruwa ne da iska ya sauko a lokaci daya . Ihu Amrah ta fara sa masa tana faɗin " Shikenan da tsumammun kaya zan kwana , kuka take yi sosai wanda Ganin haka yasa Nurain saurin nufa Wani rumfan mai tsire ,don mutumin da Yamma yake fara fitowa . Amma kamin su kai tuni ruwan ya gama sauka a jikin su sun tsime sosai....... Ganin yanda take Kukan yasa shi ɗan murmushi cire da son kwantar mata da hankali yace " I'm sorry Amrah , Amrah kin ma san sunana kuwa.? . Goge Hawayen fuskar ta tayi tana cewa " A'a . Fuskar ta ya ɗan Tallabo yana cewa sunana Nurain... Kasa Furta sunan tayi da kyar ta ce" Nurry.................



Post a Comment

0 Comments