TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 3 page 11-14

Cike da tsantsan ɓacin rai Aslaam ke Sauraren Maganan Mom Wanda yafi komai ɓata masa rai . Wannan wai shi wani irin dan rainin hankali ne ? Nurayn me ya ɗauki mutane ne Mom? , Me sunan Abun da yayi mana gadaran arziki da tsananin tijara , me yake taƙama dashi kuɗi.? Ko kuwa giyar hauka ne ?. Muryar Mommy ne ya katse sa tana furta Nurayn idanun sa fa a makance yake , Soyayyar Amrah...“ Mom ya katse ta cike da ƙunar rai kana yace “ Na lura ke supporting din sa kike yi , sam baki ga abin da yayi ba , Ka ja Yarinya ka tafi da ita , Tsawon kwana ki sannan wai kuma ka dawo kana hulɗar Rayuwar ka , mu bamu san inda ya kaita ba , yana ikirari matar sa ce , Wai wannan wani irin mutum ne ?. Yau zan same shi wallahi duk inda Amrah take sai ya faɗa mana ya kuma dawo da ita shi ya haife ta ne .? . Kallon sa Mom Aslaaamm tayi kana ta ɗan Girgiza masa kai alamun a'a , don ta lura Aaslaam zuciyar sa shima a sama yake . 


Hannun ta takai tana dafa shi kana tace " Aslaam ka natsu ka kwantar da hankalin ka , Nurayn yana zafin son Amrah har abada ba zai taba cutar da ita ba . 


Cutar wa momy na Nawa? Mutumin da ya kama budurwar sa yayi mata dukan Mutuwa har kike tunanin ba zai iya cutar da matar sa ba . 


“ Da banbanci tsakanin Budurwar tasa Naana da kuma matar sa Amrah wacce yake so  da bata kulawa tun tana ƙaramar yarinya , a nawa tunanin ko mene Nurayn zai yi yana da dalilinsa sa . Ohk Mom na fahimce ki yanzu . Nurayn dai yayi dai dai kenan.? . Wai a Nigeria babu ƙungiyar kare hakkin dan Adam ne😹 naga a Turai ma akwai animal compassion. Dabbobi ma ana kare masu hakƙin su bare Ɗan Adam . Don haka Nurayn hukuma ce zata hukunta shi . Ohhhh ALLAH...! Momy tayi Maganan tana hade hannayen ta na ta ga ta kan ta . Kallon Nurayn tayi tana cewa " Yanzu fa Nurayn matsayin dan uwan ka yake , siriki kuma a gare ka . Ko ba komai yana Auren Ƙanwar kace.  Komai zaka yi ka duba ba yanzu ba gaba an zama one family . 


Ashe ma Auren nasa ya maidu? , cewan Nurayn yana kallon Gyefen sa tare da kai hannun sa yana shafa suman kan sa tare da furzar da Huci . Kallon Mommy yayi kaman zai mata magana sai kuma kawai ya juya yana fadin " Babu buƙata . 


Bin bayan sa Mommy tayi da kallo , tana Girgiza kai don ta fahimci damuwar Aslaam rashin sanin halin da Amrah ke ciki,don ya tsorata da lamarin Nurayn tun daga yanda yaji labarin yayi ma Naana wacce har yanzu iyayen ta ana kai ruwa rana . 


**

Kallon Nurayn Zaid yayi suna tsaye a compound din gidan Mom Sa'adah , wanda Tsawon kwanaki bai taho gidan ba sai a yau , sanadiyyar Aminin nasa . Nurayn Meye kake yi haka ? Kana namiji ina kai ina dukan mace Please, wannan abun haushi ne . Enough Please Zaid .! Bana son Maganan nan , muje magana na gaba . Yayi maganan a Miskilance . Hummmm Yanzu kasan menene? Zaid yayi maganan yana kallon Nurayn Wanda yake kallon sa shima tare da jiran jin mene zai fito daga bakin sa . Ina jin ka Sir ” . Nurayn yayi Maganan yana kallon Zaid Wanda ya sakin masa murmushi don yasan Halin Aminin nasa idan yace masa Sir , To ba lallai ko da ya faɗa masa magana ya dauka ba , nan take zaice bai yarda ba ,ko ba zai yi ba . Sir din na rashin mutunci ne 😹 .  At least Nurayn muje gidan su Naana muba iyayen ta haƙuri komai ya wuce . Kaga zaku yi rayuwar auren ku da Amrah Hankali kwance kowa ya huta....Wani irin kallo Nurayn ke bin Zaid dashi kamin yace " Wane ya isa ya hanani jin dadin rayuwa ta da matata.? Ni tun ina primary school na daina bada Haƙuri koda nayi laifi . Tun ina yaro ina kafiya bana bada Haƙuri indai ya wuce Mom da Dad . Mace daya ce take sarrafa bugun zuciya ta itace kadai take juya taswirar rayuwa ta...itace zan iya durƙusa mata da komai nawa , su waye iyayen Naana? Mene suke dashi ba zan bada Haƙurin ba Zaid.! Su kaini duk inda zasu kaini inda kudin da zan siye uwar ta da uban ta duk abin da suka mallaka😱................

 Tsayawa Zaid yayi yana kallon Nurayn ganin yanda yake huci tare da hura hanci na Jaraba , Oh Allah ya huci Zuciyar ka Oga sir . Zaid ya maida masa da Maganan yana ɗaga masa hannu alamun jinjinawa . Ɗan murmushi Nurayn yayi yana sasasautawa kana yace " Oh ka rama kenan . Dama ka isa kayi mun ban rama ba . Yanzu mu shiga daga ciki  , cewan Zaid yana mai kallon Nurayn Wanda yayi ɗan jimmm Kanan mai tunanin Wani Abu sai kuma ya furta “ Bana tunanin zan shiga wurin Mommy, saboda ina zuwa maganann ɗaya zata yi mun , shine Maganan Amrah . To Meye Don tayi maka Maganan Amrah ai dama abun da ya kamata kenan Nurayn, ka dawo da Amrah cikin Mutane . Ya isa Zaid ...! Nurayn ya katse Zaid yana mai bin sa da wani irin kallo kana yace " muyi magana iyaka magana tsakanin mu , kar kara mun magana akan matata , saboda Nasan har yanzu kana son Amrah ....na dawo da ita cikin Mutane dama daji na kaita take rayuwa eh ? Ko kuwa so kake ka ganta kai da kan ka . Kawai kayi magana kai tsaye ba kunbiya ƙunbiya . To Amrah tawa ce..! Wani Abu ne ya tokare Zuciyar Zaid amma sai ya dake yana sakin wani yar murmushi kamin yace "  Nurayn Da Gaske na so Amrah soyayyar da ban taba yi ba , amma kuma na barka maka ita saboda Matsayin ka na Amini na , ban ji zafin maganan ka ba , cox tun ba yau ba tun kamin Nasan Amrah haka tun kafin ka fara soyayya da Amrah kake kishin ta . So for now ba laifi don ka nuna kishi akan matar ka . Amma please ka fahimce Ni , a yanzu mu aje duk wani abu da ya faru Allah ya ƙaddara Amrah ba tawa bace taka ce ... To ka sassauta fushin nan da kishin nan akan ta . Itama zata so . Kaga kaga Zaid ya isa Don Allah...! Nurayn ya kuma katse Zaid cike da gajiya da maganganun sa . Wai magana kake yi akan na daina kishi akan Amrah? Abotan mu tana nan har abada Zaid ,amma kuma Ni ba zan taba lamuntar kana mun maganan Amrah ba .  



Nurayn Na Barka maka Amrah fa .! Saboda Ni Nasan girman soyayyar da kake mata , Ni nawa soyayya Nasan yanda yake haka Nasan Nurayn ka rasa Amrah a wannan lokacin komai zai iya faruwa dakai , don Allah ka bar wannan zancen ka natsu ka gyara komai naka . Kana Hauka baka sani ba . Ohk Ni ne mahaukacin Zaid? . Nurayn yayi Maganan yana kallon Zaid  , Ohk naji ka Kirani da koma Meye indai akan Amrah ne . 


Yayi kyau . Cewan Zaid yana kallon sa kana ya miƙa masa hannu yana cewa “ Abotan mu tana nan kullum har abada ” . Riƙe hannun Zaid Nurayn yayi kana yace “ Abotan yana nan , amma yanzu yayi ƙasa 50% ne , idan kana so na yarda da kai na yarda da ka bar mun Amrah to kayi Aure na ganka da iyalan ka . Wani irin dariya Zaid ya hauyi ma Nurayn yana faɗin " Aaa Nurayn wai yaushe ka chanja haka ? Ina wannan miskilancin naka ? Dama duka iskanci ne , jubi yanda ka zage kana zuba da masifa tamkar Guguwar yaki . Murmushi Nurayn yayi yana Girgiza kai tare da cewa " Zaid ba zaka fahimta ba , ina cikin tension . Kamin yayi magana ne Suka ga motonn Aslaam na kunno kai Izuwa Farfajiyar gidan . Gyara tsayuwa Nurayn yayi yana kallon fitowar Aslaam Fuskar sa babu annuri a daure ko ba'a faɗa maka ba da Abun sa ya taho . 


A hankali Nurayn ke bin sa da kallo har ya tako inda yake bai ma sani ba domin kuwa sosai ya sha'afa da kallon Aslam din wanda fuskarsa yake gani tamkar na Amrah . Murmushin Da Aslaam ya gani ne a Fuskar Nurayn yasa shi Tsayawa a gaban sa yana kallon Zaid tare da basa hannu kana ya kalli nurayn wanda yake dawowa natsuwar shi . Aaslaam ya kake .? Kaine da kan ka ?. Mamaki ne ya kama Aslam jin yanda Nurayn yayi masa Magana a natse cike da mutuntawa ,tamkar ba shi bane yayi masu wannan tijaran . Tsayawa yayi yana kasa basa amsa don har ga ALLAH bakar tijara ya kawo sa ,akan ya faɗa masa inda Ƙanwar sa take . 


Hannu nurayn ya miƙa masa yana haɗawa dana Aslaaamm kana ya juya yana fadin “  Zaid bari mu je part dina idan mun fito sai ya shiga su gaisa da Mommy ”. Eh hakan ya kamata . Cewan Zaid yana saka Keys din sa aljihu a tare suka taka suna nufar ɓangaren Nurayn wanda ya manta da duniyar wurin ma sai a yanzu .

** 

Shiru Hajiya kaka tayi tana sauraren Maganan Daddyn Nurayn . Numfasawa Daddy yayi yana ƙara gyara zaman sa cike da ladabi Muryar sa a ƙasan na Hajiya yake cewa " A yau da misalin karfe biyu za'a maida Auren Hafsat da Kanol inshallah . Hummmm Hajiya ta sauke wani irin gwauron Numfashi kana ta furta “ Alhamdulillah ” . Amma Wani Hanzari ba gudu ba , Ni wannan abu yayi mun dai dai kuma naji daɗi ,kuma tabbas Kanol ya cika mutum mai Karamci da halarci ALLAH Ubangiji ya kaimu ya kuma saka a kulla alheri.  Tare da duka matan nasa ne za'a Daura ,tun da naji yana da mata biyu a can gidan su . Eh haka ake tunani Hajiya amma sai anjiman duka zamu gani,fatan ALLAH ya basu zama lafiya . Shi kuma Nurayn ya je yayi ta riƙon Amrah , wallahi Hajiya da ba don ke kika dakatar dani ba , da sai Nurayn ya gane kuren sa , shashashan yaro me ya ɗauki mutane ne?. Kayya , Kaga Ni dai nace ka rabu da Nurayn, shima Abun da yayi laifi ne ba laifi ba . Amma dai duka wannan zamu zauna . Shikenn Hajiya Ni zan wuce yanzu , a sanar ma Ammie Hafsat don ta ...too...Daddy dai yayi Maganan yana Mikewa tare da gyara babban rigar sa . To Allah ya taimaka ya nuna mana anjiman bari yanzu ayo mun kiran Hafsa din ba ta jima da motsawa daga nan ba ma . 

**

Gidan Ɓaidu

Gaba ɗaya abubuwa sun rikice bayyanar cikin larai ƙarara gashi ana tsoron fitar da zancen don gudun Mutane . Abu kunya babba wanda aka rasa wanda zai ma tunkare ta bare har asan waye mai cikin ? Baba Zuwai kam a yan kwanakin nan ta siɗe ta tsiyaye tsitttt duk wannan manyan maka makan Ɗuwawukan sunyi laƙwam sunyi tsuuuuuu saboda tashin hankali . Duk kuma wannan kunbiya kunbiyar maganan ba'a bari Kanol ya sani ba . Don bashi da labari . 

Kallon Baba Adamu kanol ɓaidu yayi kana cikin sanyi da ban haƙuri ya furta " Yaya Nasan matan nawa sun maka laifi babba , yaya mu yi haƙuri mu duba yayan mu a yafe masu . Kallon Kanol Baba Adamu yayi kana cikin Girgiza kai irin na baka san me ake ciki ba yace “ yanzu Me kake so ayi Auwalu.? ”. Gyara zama Kanol yayi kana ya furta " mashaallh Dama So nake a yau a maida aure na da mata na duka na kasance mijin su Larai Hafsa Zuwaira .....!

[9/3, 5:55 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🛖ƳAR TSAAKAR GIDAA🛖*

Romance love and Sympathetic Story.

Post a Comment

0 Comments