TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 1-2 page 35-38

 


**

Ɗan Jim tayi tana kallon sa  , kallon idanun sa tayi yanda yayi maganan kasan iya gaskiyar sa yake faɗi . Ba zan shiga moton ba . Ta furta tana kallon Gyefen ta tare da kame Hannayen ta . Ƙaran ringing din wayar sa ne ya katse masa magana da yake shirin yi mata . Murmushi yayi kana ya ɗaga kiran yana mai gyara zaman Ear phone din dake maƙale a kunnen sa . Mom...” 


Ya furta yana Lumshe Lulun idanun sa tare da ware su bisa Kyaƙyƙyawar fuskar Amrah dake gaban sa . Ba tare da Amrah taji mene aka fadi daga Ɗaya bangaren ba sai ji tayi yace " Mom na ganta yau , Yau na Ga Amrah ..” Wani irin Dariya taga yana cikin nuna nishaɗi da jin matsanan cin farin ciki . Ohk Mom” . Ya furta yana Datse kiran nasa . Kallon Amrah yayi a karo na biyu wani kiran yana ƙara shigo masa . Sorry please ”. Ya yi maganan yana Kuma ɗaukar Wani  kiran . Cikin gurɓataciyar Hausan shi ya fara Mata magana“ Eh na same ta , na gode Sosai da kika kasance wurin yi mun silar ganin wannan kyaƙyƙyawar Kuma matar Aure na . Wani irin Miƙewa Nana tayi daga Ƙwancen da take a cinyar Mommyn ta . Cikin Rawar murya tace “No ban gane ba , kasan me kake faɗi kuwa Aslaam..? Ina sane mana Nana kike Ko.? Ya ƙare maganan yana haɗe Fuska tamkar ba shi ba . Itako Amrah Saurin kallon sa tayi tana tunanin wacce Nanan ce.? Me kuma ke faruwa ?. 


Muryar Aslaam ne ya katse mata tunanin ta yana cewa " bana zo Nigeria bane don na cutar da Amrah nazo nan ne don Na Auri Amrah , daga bisani Mu koma Spain . “Huhmm ...! Nana Ta sauke Ajiyar zuciya mai nauyin gaske ,kamin tace “ Zan baka ko nawa ne tun daga dubu ɗari biyar har zuwa Million 1 ko ma sama da haka .  Wani irin murmushi Aslaam yayi kana yace " Baki san Waye Aslaam ba .? Dubu Dari biyar fa kika ce . Ohk lemme told you one thing, Tun ina Secondary school na wuce Karfin Naira dubu Dari biyar . A yanzu kuma sai dai Ni ba baki , Bama Kudin kasar Nigeriya ba , Ni kudin kyauta ne zan baki in Dollars . Just because kece sanadin haduwa ta da Amrah thank you very much, sai kinji Alart . Kamin Nana tayi Wani magana tuni ya Datse kiran yana kallon Amrah Wacce ta saki baki mamaki ne yasa ta zubda Ƙwallah na tausaya ma kanta . Tambayar Kan ta take yi mene tayi ma Nana har take kokarin ganin ta salwantar da Rayuwar ta ?.  Gani tayi Aslaaamm ya kai hannun sa yana buɗe mata moton yana yin ƙasa da Kansa tare da dan durƙusar da kan sa kaman bawa a gaban Saurauniya . Cike da Kulawa da nuna soyayya ya furta “ Please Amrah 🙏🏻”. 


**

Ihun kiran sunan Zuwai ne yasa matan gidan Saurin miƙewa,sauran matan Auren na fitowa daga Ɗakunan su ciki kam harda Baba Zuwai wacce ta fito tana gyara daurin ƙirjin ta  . Wacece Zuwai a cikin gidan nan .? Zaid yayi maganan tamkar Wani Boss . Tun da Baba Zuwai take bata taɓa tsorata irin na yau ba . Ganin shatalelen Namiji tamkar Soja yana wani irin huci akan ta . Larai ne ta kalle sa tana cewa “ Waye kai Bawan ALLAH”. Kallon ƙasa da Sama yayi mata yana watsarwa cike da Wulaƙanci irin na Zaid ya furta “ Kece Zuwai Din kenan”. A'a Wallahi bani bace, Ni sunana Inna Larai.  Jin haka yasa Baba Zuwai a dan rikice ta furta “ Ni..n..nic ...nice Zuwai . Ohhh Kece Zuwai , to nazo ne nayi Miki kashedi akan matata . Wallahi na rantse da ALLAH duk ranan da kika kara kuskuren taba mun Amrah sai nazo an tashi gidan nan . A gaban idanun ku sai naga An hake an rushe gidan nan ko tobali ba zan bari ba . Dafe Ƙirji Baba Zuwai da Wasu daga cikin matan Gidan su kayi . Kamin Inna Larai tace " Kawa Girman ALLAH kayi Haƙuri Yaron nan . Juyawa Zaid yayi yana faɗin that's the last Warning. Daga yanzu Na gama magana . Humm Wani irin ajiyar zuciya Zuwai ta sauke mai ƙarfin gaske kana tace " Mun shiga uku mu dai . Tun da yarinyar nan ta taho Gidan nan masifu muke gani iri iri , yanzu kuma har ta kai ga Gidan da muke ciki ne za'a rushe ? Gidan dake Dauke da mutane fiye da 70 saba'in a ciki . Kowa ya kasa motsi daga Inda yake , ita kuwa Lanti Wani murmushi tayi tana cabe baki tare da furta “ Haƙƙi kenan . Haƙƙin ma ta marainiya yanzu kuka fara gani”. 


Ohh To pa..! Ikon Allah.” .

Inna Larai ta furta tana kallon Lanti kamin ta cigaba da cewa " Ai ke yau take Miki sallah , zuba ruwa a ƙasa kisha don farin ciki . To Bara kiji Wallahi billahil azeem Amrah ba zata Auri wannan tanbadadden yaron ba. Ji rashin mutunci har cikin gida zai zo ya dage iyayen ta ,wanda suka ci fitsarin ta da kashin ta da wahalar ta baki daya . A'a fa habawa Larai ƙarya bai kamata daga gare ki ba . Kika wahala da ita a yaushe . ALLAH dai ya kula da Amrah har ta kai Iyanxu . Don haka maza kiyi istigfari. 


Takaici ne ya kama Baba Zuwai , tun da take ba'a taba ci mata mutunci irin na yau ba a rayuwar ta . Cikin kumburi da cika Wuya ta furta “ Na yanke hukunci Aminu shine zai Auri Amrah a cikin gidan nan. Aminu....? Lanti ta furta tana cabe baki kamin daga bisani ta wani sheƙe da dariya tana tafe hannu tare da cewa " To pah wannan Hukunci haka ? . To bari mu gani ai dai mu namu ido . Tayaya Amrah zata Auri Sauna shashasha bugage mai bin yan farauta kullum yana Aikin buda sigari Shine kamilalliyar yarinya kaman Amrah zata Aura ? , Kai Zuwai kije dai ki ƙara tunani don Malam ba zai taba yarda da Wannan hadin ba . 


“Eiye...” yanzu Aminu ne kike kira da Wannan sunan . Salamatu mahaifiyar Aminu ta katse Lanti cike da zafi tana cigaba da cewa " Alhamdulillah, shi yana da Asali da tushe . Ai haɗa Auren su taimako ne aka yi mata . Karuwa kuma yar zina dana na sunnah ya Aura .? Humm Ai wannan rufa mata Asiri yayi , don wannan wanda ya shigo cikin gidan nan ba Auren ta zaiyi ba , yanzu Auren kwarya tabi kwarya ake yi . Sai dai su gama lalube tan da kwakule ta . Kyaunta ne ke ribatar su , sannan Ai kin san Ɗan Zina bai kyau ba . Aikuwa dai”. Zuwai ta katse Salamatu tana kallon Lanti wacce maganan nasu sosai yayi mata zafi . Sai kawai ta Girgiza kai tana cewa ' Dadi abun ko wannen ku akwai ƴammata a gaban sa . Abun da kuma kayi shi za'a yi maka  mtswwwww , ta ja dogon Tsaki tana wuce su zuwa Madafi don ta iza itacen murhun nata . 

**

Zauren gidan Zaid ya nufa wanda har a lokacin Nurain dukan bakin Zulai yake yi , inda jini yayi kace² fuskar ta yayi hummmm kaman an saka lemo ta ciki . Riƙe sa Zaid yayi yana cewa " It's Okay, mu tafi Amrah fa ta fita , ban san inda taje ba . Dakatawa Nurain yayi da dukan Zulai yana cewa " Gobe don Allah ku kara kula mun matata.! 


Matar ka fa kace .? Wannan wani irin magana ce ? , Ban gane ba .? Zaid ya jero masa maganan a lokaci daya . Yass matata ce .”Ƙarya ne wannan malam mind your self . Amrah Tawace Ni kaɗai yaudarar Aminan takan mu zaka yi ne .? Ni yarda da kai nurain, na yarda da kai fiye da Kowa Ni Aboki nawa , but why now ?, So kake kasani a tension.? Da gaske Nurain kake ko wasa .? 


Juyawa Nurann yayi yana barin Zauren yayin da Zaid ya biyo bayan sa a fusace . Yana shan gaban Nurain tare da Daga murya a zafafe yake furta “ Nurain magana nake yi , Are You serious or yhu are jocking.? Humm ba wasa nake yi ba , da gaske na ke yi ? . Nurain yayi maganan yana gyara agogon hannun sa , wanda ya Glass din ya fashe sakamakon jibgar Zulai da yayi.   Kai a wannan karon ba zan iya sadaukar Maka da Amrah ba , ba iya son ko sha'awar ta nake yi na dan lokaci ba . So nake na riƙe hannun ta ,nasa ta farin ciki na kasance miji a gare ta na har abada . So yhu have to find another Wife , wannan ita tawa ce. Lumshe Sexy eyes din sa Nurain yayi kamin yace “ That is very Good yayi kyau ”. Buhhh bari na faɗa maka Wani Abu da baka sani ba . Amrah tace Wannan Wacce na taso da Soyayyar ta , kai yanzu kasan ta yanzu ka fara son ta ,amma Ni tun tana karamar yarinya nake son ta . Don haka ka bar mun Amrah ba taka Bace , Amrah ta wace . Mtswww . kai malam ka dawo hankalin ka , zan iya yi maka komai Wallahi a yanzu . Ohk . Nurain yace yana nufar moton sa tare da shigewa yana mata key . 


Wani irin zafin zuciya ne ya ciyo Zaid shima nan take ya nufi moton sa ,kan sa ya dau zafi Ainun , A Zuciyar shi furtawa yake "Amanata zai ci kenan .? That's the Great mistake da Zaka tafka a Rayuwar Nurain... Amrah tawa ce , bana kowa bane Nine mijin ta . Saurin yin burki yayi ganin Amrah da Wani saurayi a bakin layin , sai Nurain dake fitowa daga moton shi cikin sauri Zaid ya budo Murfin Moton yana nufar inda suke . Kallon kallo suke yi tsakanin su duka . Kamin Zaid Da Nurain su hada baki wurin cewa “ Waye kai ..? Kallon Su Aslaaamm yayi yana kafe su da tsayayyun idanun sa , kana yace " Aslaam..” . Ba sunan ka muke son sani ba , me kake yi anan , waya baka izinin kula matata.? Cewan Nurain yana wani irin huci . Murmushi Aslaaamm yayi kana yace “ No..! Kace duka muna layin jarangiyar masoyan ta , Ohk Ai ba Abin damuwa bane , Kowa sai ya fafata  iya rabon sa . Wanda yayi nasara shikenan . Wanda ya zama failure sai ya dau hakuri , Amma Amrah tawace ”. 


Wani irin kallo Zaid yayi ma Aslaam kana yace “ Daga Wani ƙasar mahaukatan kake ? Oya faɗa mun , London, America Japan Ina sauraren ka . Daga Spain . Ohhhh yayi kyau to is better for you ka hakura ka cire Amrah a zuciyar ka Cox she's mine. 


Hayaniyar ce ya fara tashi A wurin , Ko ina na jikin Amrah rawa yake , musamman yanda Taga Nurain na mata Wani irin kallo wanda ta kasa Fahimtar Saƙon hakan .motsa bakin ta tayi cikin Muryar kuka ta furta “ Don Allah kuyi hakuri... ”. Amrah wuce gida yanzu ....Nurain ya furta yana kafe ta da idanun sa . Ba tare da ta jira jin me zai kuma cewa ba , da sauri ta juya tana barin wurin tare da nufar Hanyar layin su . tafiya take yi tana Wani irin kuka mai ban tausayi , gaba ɗaya ta gama ficewa cikin hayyacin ta .

1:00pm . 

Zaune Suke a tsakiyar Falon Daddy Kasantuwar week end ne , Daddy bai fiye zuwa ko ina a wannan rana ba . Lemo Nusaiba take sha a hankali da ganin ta kasan bata da karsashi don ba'a jima ba suka yi waya da Nana taji zallar madaran butulcin da Aslam yayi masu ,shine yanzu sam bata da sukuni . Shigowar Alart da taji ne yasa ta duba Wayan nata dake kusa Da ita , 2.million ta ga Alart din su , Wanda cikin sauri ta juya tana kallon Daddy tare da Saka Ihun farin ciki tana furta " Ohhhh Thank yhu so much Dad . Murmushi Daddy yayi yana cewa “ Zai ishe ki dai ko .” Saurin gyaɗa masa kai tayi tana furta “ Sosai Daddy . Mom Sa'adah ce wacce take zaune hannun ta dauke da Magazine tana duba news na Wannan satin , ta kalli Nusaiba tana cewa “ Duk Sanyayyar da zaki yanzu ba Zakiyi shi a nan Gida Nigeria ba sai kin haura kin tafi Dubai .? Bikin fa Saura kwana ki biyar ne yau .  Humm . Nusaiba ta numfasa kana tace “ Daddy Nifa tsoro nake ji wallahi...Ya Nurain he totally change , Ina ganin Kaman ba zai yarda Da Wannan Auren ba indai yarinyar nan tana na . Kallon Nusaiba suka yi duka , suna nazarin maganan nata , kamin Daddy yayi Murmushi yana cewa “ Zan saka A kawar da yarinyar na yan kwana ki , har ayi Auren sannan .” . Wow Dad Hakan ma is better . Kasa motsi Mommy tayi sam wannan maganan bai mata daɗi ba , amma kuma babu yanda zata yi dole tayi shiru ta hakura ta zuba ma sarautar ALLAH ido .


Kan Nurain ne ya kulle gamm . Kasa murɗa Handle Door ɗin yayi yana sauke hannun sa a hankali don wannan maganan Daddy da yayi na karshe a kunnen sa ya Sauka . A sarari ne ya furta “ Dole a yau Na yi nisa da Amrah , a yau zan Yi nisa da Matata nisar da babu wanda zai sam inda take . Nima kuma ba za'a ganni bare har a ɗaura Auren , Dad , mom bye . Ya furta yana saurin juyawa tare da nufar Part ɗin shi don ya tarkata duk wani Abu mai muhimmanci nasa ......!

Kan Nurain ne ya kulle gamm . Kasa murɗa Handle Door ɗin yayi yana sauke hannun sa a hankali don wannan maganan Daddy da yayi na karshe a kunnen sa ya Sauka . A sarari ne ya furta “ Dole a yau Na yi nisa da Amrah , a yau zan Yi nisa da Matata nisar da babu wanda zai san inda take . Nima kuma ba za'a ganni bare har a kai ga ɗaura wannan Auren , Dad , mom bye ...“ Ya furta yana saurin juyawa tare da nufar Part ɗin shi don ya tarkata duk wani Abu mai muhimmanci nasa ......!
Fitowa yayi daga Ɓangaren nasa hannun sa Ɗauke da brief case don bai tsaya daukar Trolly ɗin sa ba . Gaba ɗaya idanun sa sun gama Rufewa ga kishi ga baƙin cikin jin Maganan Daddy da yayi a yanzu . Nufar moton sa yayi Ƙirar Accura , Excouts ɗin sa ne suka rifo masa yayin da ɗaya daga cikin su sukayi Saurin buɗe masa moton . Humm Ɗan Numfasawa Nurayn yayi kana ya Juyo yana kallon Excouts din yana furta " Ba sai kun biyo Ni ba . Ohk sir.  Suka haɗa baki Wurin  furtawa . Ɗaya daga cikin su ne ya miƙa masa Keys din yana ɗan ƙame masa . Shiga moton Nurayn yayi yana Yin horn nan take Gate man ya ware katafaren Gate ɗin gidan yana ficewa da Moton , yana mai Ɗaukar Hanyar Gidan su Amrah . 

Ɓangaren su Baba Zuwai kuwa , suna tsaka da Wannan jimamin ne Suka ga Hajara ta banko ta faɗo masu tana haki . Inna Larai ne ta yanka Wani irin salati ganin yanda Hajara tayi gumi sharɓan tana Wani irin haki tamkar Numfashin ta zai fita . Ke Hajara lafiya .? Mene ke faruwa ?... Inna Larai sun kusa kashe Zulai ga ta can a zaure zasu kashe ta da duka . 

“Duka...? ”. 
Baba Zuwai tayi maganan tana nufar Hanyar Zauren Gidan , yayin da su Ikilima da Sauran matan gida suka rufa mata baya . Ƙwance suka tadda Zulai fuska yayi Humm ya sunduma , Tana cikin ruwa Alamu har fitsarin Wahala tayi . Dukan da Nurayn yayi mata tun da Uwar ta ta kawo ta duniya bata taɓa shan duka irin shi ba . Lalilah ha'illahu. ..” Kashe mun Zulai zasu yi.? Baba Zuwai tayi maganan tana kwarma uban ihu . 

Cikin Zafin nama Salamatu ta Ɗago ta tana faɗin “ Zulai Zulai buɗe idanun ki . A hankali Zulai ke bude idanun ta Wanda suke tsiyayar da Wasu irin Zafafan ƙwallah . Cike da Kullewar kai Ikilima ta furta “ Wai wa'annan Su waye ? , Kawai su shigo cikin Gida su kama Dukan Mace? Hauka suke yi ne ? Waye su ...? Ikilima ta ƙare maganan cike da Ɗaga Murya don ranta yayi matuƙar Ɓaci . Wani irin kallo Inna Larai tayi mata cike da Son gyaga mata ƙiyayyar Amrah ta furta “ Baki ji me suka ce bane ? , Me son Amrah ne , Saboda kuma Rashin kunya fa kiji Wai a gaban Mu yake kiran ta Matar sa ce . Har da kiran Sunan Zuwai gatsar. Wallahi yau a cikin gidan nan sai na tattaka Amrah sai na kusa kaita lahira da duka . Baba Zuwai tayi Maganan tana juyawa cikin gida fuuuuuuu ....don kuwa ta cika tayi fammm . Kama Zulai suka yi wacce take kuka da ido Ɗaya kumatun ta jin su take tamkar an daura mata Abu mai nauyi Saboda marin da tasha ” . Ikilima kuwa tsayawa tayi turus a zauren , Zuciyar ta sam bai mata Dadi ba . Komawa tayi Izuwa cikin tsakar gidan inda wani banbamin ya ƙara tashi . Kallon su tayi tana cewa “ Daga yau Amrah Ba zata sake zuwa Aikin ba.  Sannan kuma a yau Za'a yi magana da Baba Adamu da su Baba Iliya a haɗa Auren Aminu da Amrah kowa ya huta . 
**
Kasa Motsawa Tayi daga Wajen Gidan ,so take ta shiga Amma tana Tsoron hakan ,don tasan yau Na lahira sai ya fita jin dadi .  Ƙwallah ne ke riga rigen sakko ma Kuncin ta , rasa yanda zata yi kawai yasa ta zama a dakalin wajen gidan . Amratu ....! Muryar Baba Iliya ya katse ta cike da Doka Tsawa yake fadin ' Uban me kike yi a nan Wurin ke namiji ne.? Ko kuwa zagi zaki ja mana a makota kin sami dakali kin zauna kina sharɓan Hawaye. Saurin miƙewa Amrah tayi jikin ta ko ina Rawa yake yi kar³ . A'a Baba yanzu zan shiga ”. Mtswww Iskancin Banza munafuka ki zauna ki kwana anan idan kin so... ”. Yana faɗin Haka ya juya fuuuuu yana barin Inda take yana kutsawa Izuwa cikin gidan . 

Kama hannu Biyu Amrah tayi tana zubewa anan Gwiwowin ta ƙasa tana Rushewa da Wani irin kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya . Wayyo ALLAH na. Ta furta tana wani jan numfashi kaman zai ɗauke daga gare ta . Amrah ...! Muryar Nurayn ya katse ta , Wanda jin hakan yasa ta Saurin dago manyan Lulun idanun ta Wanda suka yi jajir suka kumbura saboda tsaban kukan da tayi ...Kasa Amsa shi tayi sai bin sa take da Kallo tamkar yau ta fara Ganin sa a Duniya haka kuma hawayen idanun ta sun gagara Daina saukowa daga Ƙwarmin idanun ta . A hankali ya tsuguna inda take yana kai Hannun sa tare da gyara mata zaman Hijabin fuskar ta . Miƙewa yayi yana riƙo hannun ta , Wanda babu musu ta miƙe tana wani irin kuka mai ban tausayi . Ganin ya bude mata moton sa yasa ta motsa labɓan ta cikin dashewar murya ta furta “ Don Allah Noory kaje ka ba Baba Zuwai haƙuri , Zan mutu idan na shiga gidan , Baba.....Shiiiii ya katse ta yana Daura yatsar sa daya a bisa laɓɓan ta . Idanun sa ya zuba mata na kusan mintuna daya babu wanda yace Wani Abu kana ta tsinkayi Muryar sa yana cewa “ shiga mu tafi  ”.

Tsayawa Amrah tayi tana masa Ƙurrr kaman mai tunanin Wani Abu , Fuskar sa take kallo tana tuno da Rayuwar Yarintar su . Please...”. ya furta yana Lumshe mata sexy eyes din nan nasa . Hannun ta ta raba da nashi tana goge Hawayen fuskar ta tare da shigewa cikin moton yana rufowa tare da juyawa Yana nufar Mazaunin sa . Kallon Gyefen sa yayi yana jin Wani iri a zuciyar sa sam ba daɗi , kukan da take yi yafi komai daga masa hankali da sosa masa Rai , ji yake ina ma Ita Zuwai din ya buga akasin Ƴar ta Zulai . Lumshe idanun sa yayi yana tuna maganan Amrah a lokacin da ya fara shiga Rayuwar ta . A'a Ni ba zan bika ba , Wayyo Ruwa zai buge Ni kuma Baba Zuwai zata bigeni idan na koma . Huhmmmm Wani Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta tare da dawowa tunanin da ya faɗa . Amrah na..” . Ya furta yana kallon ta , A hankali ta kalle sa kamin tayi masa magana taga yana sakin mata Murmushin nan nasa wanda tasan shi dashi tun a yarinta wanda a yanzu take ganin ya gushe daga Fuskar sa , Ashe har yanzu Murmushin nan nasa yana nan .? Tayi maganan a zuciya haka idanun ta na tsaye a bisa nasa . Miƙa mata Hankie yayi yana cewa " Goge Hawayen ki ,daga yau ba zaki sake kuka ba . Nooryn ki ba zai bari su sake Sauka ba . Miƙa Hannun ta tayi tana Amsan Hankie din amma sai taji ya riƙe Taffan hannun ta yana haɗawa da nashi . Kallon Nurayn tayi wanda shima a dai dai wannan lokacin ita yake kallo . Ɗaga mata Gira yayi yana yi mata Alamun tayi murmushi da hannun sa 🤘🏻 . Wannan yasa Amrah Sakin dan Murmushi tana Cire hannun ta daga nasa ,tare da goge Hawayen fuskar ta ... ” .

Kaiwa da komowa Zaid ke yi a tsakiyar Bedroom din sa . A hankali al'amarun suke dawo masa , A sarari cike da Zafin rai ya furta “ Ni zaka yaudara.? Wallahi baka isa wannan Bama zai taɓa yiwuwa ba .....! Ya ƙare maganan yana kai ma bango naushi da ƙarfi kana ya zube a Resting chair din sa idanun sa ya rintse a hankali yake tuno da kyaƙyƙyawar Fuskar Amrah , shigowan ta Toilet din sa , Da kuma yanda yayi kokarin haye mata da iskancin sa .  Idan kina kuka kyau kiye na karshe , idan kuwa kika yi murmushi Ji nake tamkar na shiɗi don tafiya da Duk imanina kikeyi Amrah . Ina son ki ..! I really love you and I know you know that ” .Ya furta yana miƙewa tare da Ɗaukar rigan suit din sa yana ɗaukar Keys ɗin shi tare da fita zuwa falon sa . Hoton Nuryan ne ya gilma masa wanda yake manne babban prime suka yi ,wanda hoton su yake a tare , duka fuskokin su cikin annuri yake.  Cikin Wani irin zafi da fusata ya nufi Hoton yana saka hannun sa tare da sauke shi daga bangon palourn wani irin cilli yayi da Hoton yana faɗawa tsakiyar Centre table din wurin ,nan take ya tarwatse Glasses din na fashewa a tsakiyar Carpet din falon . Na tsane ka , na tsane ka Nurayn . Ya furta kalmar tamkar Zautacce yana Wani irin Huci tamkar mayunwacin zaki . Da gudu Mai masa girki ya fito Wato Joseph . Boss What's Wrong here.? Wani irin kallo Zaid ya watsa masa yana juyawa a fusace yana nufar Farfajiyar gidan .  Moton sa ya nufa yana shigewa tare da yi ma mai gadin sa wani irin horn , a gigice Mai Gadin ya buɗe Gate ɗin ... ” .
Cikin Wani irin mahaukacin gudu ya fice da moton nasa. Gate man din yana faɗin " A dawo lapiya ranka ya dade yana maganan tare da Ɗaga masa Hannu amma kuma ina ko kallon sa bai yi ba sheƙa gudu yake yi tamkar Wanda aka basa mummunar labari . Domin kuwa saita moton da yayi Ba inda ya nufa a yanzu fache gidan Mom Sa'adah . Don yayi guzurin cin mutumci ma Aminin nasa Nuryan . Humm Sauke Wani irin numfashi Gate man din yayi yana faɗin “ Yau tabbas babu Oga babu lapiya , ALLAH dai yasa Hajiyar tasa tana lapiya , Amma Wannan Gudu haka tamkar Wanda aka sanar masa da mutuwar Uwa da Uba .? Duk maganan da yake yi yana yi ne a sarari tare da kuma mai da Gate ɗin yana rufewa . 

Airport .
4:30pm. 
Kallon Nurayn Amrah tayi wanda yake riƙe da hannun ta suna nufar jirgi wanda ita a yau ne ta fara ido biyu da jirgi tun da take a rayuwar ta . Yau ne ta ganta a airport . Gani tayi ya mika mawa Wani ma'aikacin Wurin key din moton sa yana masa A sauka lapiya Ranka yadaɗe .  Ba tare da Nuryn ya tankasa ba ya nufi jirgin ” . Jikin Amrah ne sosai yayi Sanyi cike da Mamaki ta furta “ Noory ina zamu je ?”. Tsayawa yayi a Stairs din Jirgin yana matsa mata tare da Tasa ta gaba yana furta “ Shiga mu tafi , idan mun je can zan Miki bayani ” . Wani irin bugawa ƙirjin ta yayi da ƙarfi , Kallon sa tayi nan take idanun ta suka kawo Ruwa hawayen da suka tsaya a yanxu suka dawowa da Saurin su . Noory Tsoro nake ji . Baba Zuwai....Who is she.?? Wacece ita Amrah...! Yayi magana wani irin jijiya na ratsowa ta wuyar sa , a rayuwar sa babu macen da ya tsana sama da Wannan mata wato Baba Zuwai . Zan kashe ta idan kika sake mun maganan ta.” . Ya furta idanun sa nan take suna juyewa wani irin jah yayi tamkar jini saboda tsaban zafin Rai da Zuciya . Jikin Amrah ne ya hau Rawa da Sauri ba tare da ta sani ba ta shige jirgin inda yake private jet ne , Su kaɗai ne a jirgin sai masu tashar jirgin . Zama yayi a gyefen ta yana jin ta tana rera masa kuka a hankali ta haɗe kan ta da hannayen ta . Sosai kukan nata ke damunsa a zuciya amma a halin yanzu shi kan sa ya gaza sarrafa kansa . Don ya dau alwashin barin garin nata da ita ...kuka take yi a hankali tana jin Matuƙan jirgin na fadin su shirya jirgi zai daga . A hankali jirgin ya fara Ɗagawa izuwa sararin samaniya . Ganin yanda ya cika yayi fammm yasa ta kauda kai itama tana cigaba da sharɓan kukan ta . Hannun sa taji yana zagayowa zuwa Kafadun ta yana kwantar da kan ta jikin sa . I'm sorry my Amrah , Ba Nigeria zan bari dake ba.  Lagos zamu sauka , acan zamu ci Amarcin mu .....” . Saurin Ɗagowa tayi tare da kallon fuskar sa zuwa ƙwayar idanun sa inda take ganin iya gaskiyar sa yake fadi . Amarci....!

Post a Comment

0 Comments