TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

Min QALB 🥰 PAGE 14-15

 3/23, 1:35 PM] Zafafa: *_MIN QALB 14_*

_mamuhgee_


ANNUR PERFUMES ANNUR PERFUMES!!!!!!


JAMA'A MA'ABOTA SON QAMSHI DAN SANYAYA ZUCIYA Ina kuke kuzo ga sabuwar duniyar turare sabon tashe ANNUR PERFUMES sunkawo muku,

Turarensu qarshene,

Qamshinsu na daban,

Kayansu tabbataccine,

Aikinsu ingantacce ne

shin kataba/kintaba amfani da ANNUR PERFUMES kuwa?

To maza qarzayo karki Bari ayi badakeba dankuwa kayansu lamba dayane Kuma amintaccine masu guarantee domin kuwa mun tabbatar.


ANNUR PERFUMES donjindadin customers  munkawo muku dadadan turaruka na musamman  masu nishadan tarda Amarya da uwar gida harma da angonta kamar haka turaren wuta humra kala daban daban kwalaccha  Dana matsi na infection biki ko suna dyadya ko sari  ina kano gaida layin  massanlachin imamu malik koku kira number waya kamar haka 07086341096 ko 07069037534 muna munamaraba daku saikunzo.


ANNUR PERFUMES


TURAREN WUTA

KHUMRAH. 

KULACCAM

MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)

DECORATIONS ..

KAYAN INFECTION DANA MATSI (STEAMING)


TANA KANO: GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!


**************

Ringin numbern usi din keyi harta katse bai daga ba tasake Danna Kiran tana cewa'


Usi idan muka hadu saina fasa maka baki da kai tunda har zaka iya bacci baka kirani kaji Yaya ta kasancemin ba a wannan zabeerar da kallo daya Andi da Modibbo sukewa mutum sai cikinsa ya mur'da,


Uwa uba arasa gurin ajeni sai anan cikin wannan me bada tsoron da matarsa.


Kira biyar tayi Masa Amma baa daukaba takira wayar iyami cikin sa'a kuwa ta dauka Nan suka jima suna mgn iyamin na maimaita Mata karta taba duk Abinda zata gani na kowa karkuma ta jawowa kanta fitina ko rigima ta jawo musu kafin aka miqawa kawu wayar Shima dai yayi Mata maganar karta taba abun kowa sbd kada 'yan kudin Nan dasuka samu su qare a gun kashe rigima Shima usi sunfada Masa kada ya kuskura ya janyo rigima sbd tanadin kudin Nan zasuyi sbd abinci dakuma qarasa hada takardun komawarsa karatu.


Fadawa lafiyayyan gadon tayi ta kwanta tana lumshe ido bayan tagama wayar

Tai wani juyi tana lulluba da bargon me shegen laushi sbd sanyin AC dake ratsata ta lumshe ido tana cewa'"


Masu kudi wato ko a gurin bacci sunfi talaka samun nutsuwa 

Da agidanmu ne da yanxu radion kawu da qarar dakan turmin maman junior da qarar bude tukunyar maman basiru sun Hana mutum bacci,

Rufe idanu tayi tana sake gyara kwanciya take bacci me dadi yayi gaba da ita ga gajiya ga lafiyyan abinci dataci ga lafiyayyan gurin kwanciyar dakuma sanyin AC ga ba hayaniya ai Dole baccinta yau yayi dadi.


Saida garin ya hantse ta tashi tana wata irin miqa me Dadi fuskarta a sake da farin cikin irin baccin data samu tana qoqarin saukowa gadon ne zarah tashigo daukeda sababbin brushes da toothpaste masu kyau tana kallonta tace"


Amatu Yaya? kintashi lfy? Ya babyn dr?


Qarasa saukowa gadon tayi tana sake yin wata doguwar miqar datasa zarah saurin ajiye kayan hannunta tana riqeta tace"


Amatu zakiwa kanki illa idan kina irin wannan miqar

Idan kinajin gajiya ne za'asa ayi Miki tausa ahankali Amma Dan Allah ki daina kinji??


Kallon sakarai amatu ta Mata Jin hadda miqar ma yanxu wani tsurku zaa kawo sbd ciki...

Amma dai ko yayane bazata Bari banxa ta wucetaba tubda damace tasamu gwara ta dama kafin Takoma inda tafito Dan haka sai ta 'dan yamutsa fuska tana 'dan dafe bayanta tace"


Anty zarah ko Ina jikina ciwo yakeyi na gajiya shiyasa nake 'yar miqar ko zanji jikin ya sake Amma tunda kince za'amin tausa inaga idan anyi zanji jikin ya saki.


Murmushi zaran tasaki tana sakinta Takoma gaban mirror ta dauko toothpastes din different flavors kusan kala biyar tace"


Ga Macleans ki bude kowanne kiji Wanda qamshinsa ya Miki Wanda bazai tayar Miki da zuciyab saiki ringa amfani dashi.


Karba tayi tana washe baki tana duddubasu tace"


Duka ma sunmin abarminsu kowanne  ma qamshinsa zaimin sauran gida zanje dasu idan zantafi.


'yar dariya zarah tayi tana girgiza Kai rashin damuwar amatun na sake burgeta musamman data 'dan Fara lura tun jiya inda amatun tafito tana tareda yunwa gskia Dr be kyautaba barinsu su wahala haka tana matsayin matarsa bayan duk arzikin dayakedashi.


Fita tayi Takoma kicin ita Kuma amatu toilet tashiga tafara yin brush da kusan toothpaste kala hudu kowanne saidata fasa ta 'dan lakata tayi dashi take bakinta suka ringa bada wani qamshi masu Dadi dasuka sakata yin wanka cikin nutsuwa da annashuwa.


Tana fitowa saidatayi sallah kafin ta shirya cikin doguwar rigar jallabiya Mara nauyi Wanda duk zaran ce takawo Mata daga gani duk nata ne Amma suka sabbi ne Babu Wanda ta taba sakawa.


Tana cikin fesa turare tana lumshe ido cikin jin Dadi tace"

wainnan turaren dasu zankoma gida idan zankoma ma komai saina dauka naje dashi bazanga irin wannan Batinba nabariba.


Turarukan ta kwashe duka tabude wardrobe tazubasu cikin Jakarta daga can qasa ta rufe zip din tadawo gaban mudubin tana gyara zaman rigarta a jikinta saiga zarah tashigo tana kallonta Jin dakin yacika da qamshin turaruka yasata Dan 'yin tari tana cewa'"


Amatu wannan turarukan bazasu cutatar dakeba kuwa¿

Qamshin yayi yawa Zo muje dining muci breakfast idan Kuma akwai Abinda kike buqata ba Wanda akayi ba sai hafsatu ta Dora miki ga Dr khalil ma yazo Yana palon MD suna Magana.


Ba qaramin Jin Dadin zuwan Dr khalil tayi ba sbd sanar dashi Abinda su zarah din ke shirin Yi na Kiran wani Dr shiyasa ta farayin gaba tana cewa''


Ni komaima aka dafa yamin zanci Amma Dr nakeson Fara gani anty zarah Dan Allah kinji.


Biyota tayi tana cewa''

Wannan rashin hkr haka amatu bazaki jira yagama yazo yasameki har dakin ba.


A palon ganin Dr khalil baida lokacin fitowa daga gurin MD yasa ta marairaicewa zarah fuska tana taba cikinta 

Take zarah ta tashi da kanta ta hado Mata nata abincin a tray sbd kada yinwa tai Mata illa sbd cikin dake jikinta bazata iya jiransu ba.


Dakinta Takoma acan tayi zaman Yan bori akan carpet tafara cin lafiyayyan breakfast din tana bude plate din farfesun kifin da akayi kawai sbd ita dayaji kayan qamshi da 'dan yaji batasan lokacinda tasaki dariyar farin cikiba tana diba takai bakinta saiga Dr khalil yayi knocking yashigo fuskarsa tayi wani iri na yanayin damuwar dake tattare da ita.


Tsayawa yayi daga bakin qofar ya qura Mata ido yanda take cin abincin sosai cikin Jin dadinsa dakuma bayyanarda baqone agareta sai yaji jikinsa yasake yin sanyi ya rintse ido Yana Jin zafin zuciyarsa na qaruwa sbd baisan ta Ina zaifara da wannan qaqqarfar rigimarba sbd Nan ana Magana ne akan ciki da aure Wanda baa Wasa dasu sbd komai dadewa gskia zata fito idan akwai idan Babu,

Ta Yaya zaifara neman mafita?

Ta Yaya zaifara neman inda mafitar cikin amatu zata fito?

Gasu usi yanxu da Dole nauyinsu zai dawo kansa sbd inganta rayuwarsu su duka din ta yanda har abada komai zai faru bazasu Yi shaawar sake komawa rayuwar dasuka fito ba,

Idan har amatu zata iya saka kanta acikin irin wannan masifar me hadari akan kudi to tabbas zaiyi amfani da kudi da qarfinsa ya wadatasu da dukkanin abin buqata har sai amatu ta cire kwadayin kudi a ranta,

For now Abindake gabansa shine mafitar cikin jikinta da ake zaton akwai Amma bazai Yi rushing abubuwan ba tunda tana Nan hannun MD yasan Babu abin dazai sameta she's morethan safe anan Dan haka zata cigaba da zama anan zaije gurinsu kawu zaifara aikin kulawa dasu daga yanzu.


Gyaran murya yayi Yana sake gyara tsayuwa tayi saurin dagowa tana ganinsa ta miqe tana qarasa kwankwade sauran kakkauran tea din dake hannunta cikin cup tace"


Dr tun jiya kaina ke neman bugawa da son ganinka na.....


Quite amatu""yafada cikin 'yar tsawa ransa a 'dan bace.


Cak ta tsaya tana kallonsa ganin yanda bacin Rai ya bayyana a fuskarsa sosai sai hakan yasa jikinta yin sanyi tayi qasa da Kai tana kallonsa fuska a marairaice.


Ya dauke Kai sbd ganin zata sa zuciyarsa saukowa yace"


Kinsan zaman da kikeyi acikin zabeera?


Saurin matsowa tayi tareda katsesa da cewa"


Wlh dr aiki Na....


Amatu just keep quiet please,

Wane qarya kike tunanin zakimin bayan duk abin daya faru jiya gaban kowa and yanxu Ina tambayanki kinason kawo min wani different story

Ki saurara kiji usi yafadamun komai Wanda yasa nake mamakinki har yanzu

Amatu har kudi yayi mahimmancin dazaki 6ata sunan wani akansu,

Rayuwarsa kike neman batawafa gaba daya

Shin kinsan shi Wanda kikaso batawa rayuwar shine Wanda nafiso a rayuwata fiyeda kowa bayan iyayen dasuka haifeni???


Tsit tayi tana sake yin qasa da kanta cikin rashin Jin dadin yanda yake maganar cikin tsananin 'daci da bacin Rai 

akaro na farko a rayuwarta dataji nauyin wani mutum.


Juyowa yayi Yana kallonta yacigaba fa cewa"


Amatu wannan duk Abinda kike tunani ya wuce Nan

Wannan alamarin babbane bazaki ganeba sbd tunaninki kawai ya ta'allaqa ne kawai akan kudin dazaki samu 

Meyasa kudine kawai Abinda kike gani amatu wannan alamarin babbane meyasa bazaki ganeba,

Umme mahaifiyatace duk Abinda tasaki kizo kiyi tayine sbd rashin mafitar datake gani tana ciki 

Gashi yanzu kunsani a tsaka me wahala bansan yazanyi da kowannenku ba,

ku duka bazan iya barin wani Abu ya sameku ba kokuma wani mummunan hukunci ya hau kanku sbd kowaccenku nada matsayi me girma agurina gashi yanzu ta kowane bangaren nine zansan Yaya zanyi.


Kuna tunanin MD sakarai ne daza'a Zo Kai tsaye afadi wannan alamarin ace shine ya zauna ya dauka kawai sai sunansa ya baci?

Tabbas dakun aikata babban kuskure sbd ilimi da matsayin MD yawuce inda umme ke tunanin ke bakyama ciki sbd komai ma qaramin kanki bazai ganeba gameda waye MD Dan haka ki saurareni da kyau kiji,


Daga yanzu dakike cikin zabeera duk Abinda zakiyi da Wanda yake faruwa ki tabbatarda kina sanar Dani,


Karki kuskura Koda Wasa kiyi maganar Abinda yake ainihin gskiyar maganar Nan da kowa Koda kuwa zarah ce ko a waya karkiyi maganar da USI sbd kadama wani yaji,


Kince kinada ciki Dan haka zakici gaba da zama a me cikin harsai na samu mafitar fita cikin wannan shirmen da kuka faro,


And bayan zarah karkiyi muamala da kowa acikin zabeera batareda izininaba lastly Kuma karki yarda kiyi Abinda za'a zauna meeting akanki kokuma asan asalin waye ke acikin zabeerar Nan hakama karki yadda kiyi Abinda zaisa a fahimci bakida ciki idan nace karki kuskura I mean kada Koda Wasa ki kuskura


Duk Abinda kike so kifadamin zan kawo Miki shi Kuma kullum zan ringa zuwa Nan dubaki kafin na wuce office da idan nadawo and you better behave yourself duk da MD baida lokacin batawa agurin matarsa bare ke to yanada lura sosai zai iya ganoki a lokaci daya hakan Kuma na nufin samun matsalarmu..


Kin fahimci dukkanin abubuwan Dana fada right??


Gyada Masa Kai tayi ahankali tana Dan satar kallonsa sbd ganin yadauka zafi yanda yaketa fadan.


Ajiyar zuciya ya sauke tareda kallonta Yana sassauta fushinsa yace"


Shikenan karki saka damuwa ko tsoron komai aranki Ina Nan Babu Abinda zai sameki,

Usman ma tun jiya ninace kada ya dauka wayanki Koda kinkira sbd nasan zakuyi Magana Kuma wani zai iya jinku idan nafita zan Masa Magana yadauki wayarki tun jiya nasan labari Yana bakinki Wanda zaki basa.


Sai alokacin ta saki murmushi tana kallonsa Jin ya sauko gaba daya ta washe baki tana cewa"


Duk da haka saina fasa Masa baki idan nagansa tunda yaqi daga wayar.


Kallon fuskarta yayi Yana sauke wata ajiyar zuciya sbd gaba daya tagama sauke fushin dayazo dashi ya sakar Mata murmushi Yana cewa'


Shikenan basai idan kingansa ba zaki fada bakin

Makaranta zai tafi Kuma hostel zai zauna infact idan yatafi bazai dawoba saiya Gama karatun Amma dai zai dawo Daurin aure inaga.


Kallonsa tayi baki sake tace'


USI zaije makaranta?

Haj Mama ta biya ne???


Batareda ya kalletaba yana duba Kiran dake shigowa wayarsa yace"


Duk wani deal ko aiki ko kwangilane ma dake tsakaninki da umme babusa yaqare so ki cire zancensa completely a kanki Babu wannan zancen.


USI zaije school ne sbd shine burinki nikuma nauyine Dana dorawa kaina na cika dukkanin burinki.


Wani tsallen murna tayi tana Kiran sunansa daidai shigowar zarah tayi saurin kallon amatun tana cewa'


Amatu wannan tsallen fa 

Zaki yiwa kanki illa.


Kansa ta mayarda kallonta zatayi Magana ya rigata da cewa"


Zarah amatu sai kinyi da gske she's stubborn..


Cikin tsananin farin cikinta daya kasa boyuwa tace"


Anty zarah Dr jarumi ne 

 Babu kamarsa.....


Tsit sukayi zarah na dariya cikin Jin nauyin Abinda amatun ta fada shikuma idanuwansa ya zuba Mata jikinsa na mutuwa da qaunar yarinyar.


Atakam batama kawo tunanin komai gameda maganar yataba sai sake sako maganganunta takeyi ganin haka yasa zarah ficewa da sauri shikuma ya fito sbd yayi lattin zuwa asibiti itama biyosa tayi tayi Masa rakiya zuwa mota suna tafe tana Masa sambatun irin farin cikin datake ciki har suka Isa motarsa dayazo da ita har qofar part din nasu zarah ta kallesa tana sake cewa idan kaje Dr Dan Allah Ina sake gaidasu kawu 

Iyami ma kace Mata Inshallah bazan jawo rigimar kowaba.


Harya zauna cikin motar yace"


To nikuma fa Abinda nace?


Dariya tasaki kafin tace'"


Kai duk Abinda kafada narigama nafara aiki dashi tun lokacin.


Murmushi yasaki tareda gyada Kai Yana cewa"


Good AMATULLAH.


Juyawa tayi zata tafi cikin taushin murya yace"


Me zan kawo Miki idan zandawo.


Kallonsa tayi Wanda yasashi Jin wani iri kafin tana 'dan tunani tace"


Duk Abinda masu ciki keci shi zaka siyomin naci Kona rage zafin sunan me cikin da ake Kirana dashi.


Girgiza Kai yayi Yana cewa"


Shikenan koma ciki ki kula Kuma.


Sam yau farin cikinta yakasa boyuwa tana shigowa ciki Palo ta zauna tareda miqewa akan doguwar kujera tana kallon zarah data fito hanyar zuwa saman mijinta tasake bajewa tana cewa'


Anty zarah qafafuwana tsami sukemin sosai Kuma.


Qoqarin kawar da damuwar data sauko da ita daga Daman tayi tana qaqalo murmushi tace' 


Bari na dauko man massaging sai a Dan mammatsa Miki qafar.


Dauko oil din tayi takirawo hafsatu Nan suka zauna tana yankawa amatun manyan gwaiban datace tanaso tana Mata fira ita Kuma hafsatu na mammatsa Mata qafafunta dake miqe Kan glass table din da aka Fara Dora Mata pillow me laushi kafin tadora qafafun.


Sunyi nisa zarah ta Dan 'dago tareda juyawa ta kalli hanyar saukowarsa sbd qamshin turarensa na IMPERIAL MAJESTY data Fara shaqowa Yana doso palon.


Jin zarah tayi shiru daga labarin datake Bata tana yanka Mata gwaibar yasata dagowa ta kalleta saitaga tana kallon wani gefe fuskarta kamar da damuwa ahankali itama ta juya ta kalli inda take kallon Wanda yayi daidai da saukowarsa gaba daya Yana sanye cikin suit din _Alexander vanquish 11 bespoke_ ash kala dasukaiwa fatarsa kyau sosai sai wani irin kwarjini da sirrin kyau dake fita daga fuskarsa da Babu sakewa acikinta.

##mamuh#




#MIN QALB❤️

Mamuhgee


ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899[3/24, 10:27 AM] Zafafa: *_MIN QALB 15_*

_mamuhgee_



Jin idanuwa ajikinsa yasashi 'dan dagowa ya kalli inda suke Yana qarasa fitowa palon gaba daya

Su kuwa duk su biyun idanuwansu zube suke akansa Babu ko qyaftawa musamman amatu dake qare Masa kallon tsaf zuciyarta na harbawa sbd yaune karo na farko a rayuwarta datake kallon wani namijin data kasa dauke idanuwanta a kansa.


Ko inda suke bai qara kallaba ya dauke Kai fuskarsa na sake fitar musu da annuri ya nufi qofa zai fice zarah tayi saurin ajiye wuqa da gwaibar hannunta tana miqewa ta nufesa tana  cikin kulawa tace"


Fita zakayine gashi har an jere maka komai na breakfast a dining,

Ko zaka daure kaci ko ka.....


Zanyi a office idan naje I'm late already excuse me"

Rabata yayi ya wuce Yana daukar wayarsa datai ringin batareda yasake waiwayartaba ya fice.


Shiru tayi agurin tareda bin qofar daya fice din da kallo jikinta a matuqar sanyaye sbd a zaman aure kulawa da lokacinsa ne tasan bazai taba Bata ba gashi abin Yana damunta matuqa musamman idan a gaban mutane ne.


Qaqalo murmushi tayi tareda boye damuwarta ta juyo tadawo gefen amatun ta zauna tana kawo wani labarin daban sbd wancan datake Bata na farko ta manta Abinda take cewa.


Tsura Mata ido amatu tayi tana kallon hannunwanta dake yanka gwaibar duk sai taji bataji dadiba 

Sbd me zai dizga anty zarah din bayan ita kulawa ta nuna Masa¿


Dafa hannunta tayi tareda karban wuqar da gwaibar ta aje cikin plate dake Kan table tana qoqarin kawar Mata da damuwa ta saki murmushi tana cewa"


Anty zarah gwaibar Nan ta isheni haka babyb harya Fara zama qato daga zuwanmu jiya sbd ciye ciyen da  kike basa.


Sai alokacin tasaki fuskarta sosai cikin Jin dadin Abinda amatun ta kalla tace"


Ai dama so nakeyi yayi qatoto cikin qoshin lfy ta yanda iyayensa da kakanninsa zasu bani lambar yabo ta musamman.


Hmm anty zarah waye zai baki lambar yabo acikinsu Dan kin kula da renon cikinda ba'a so?

Dr ne kawai ke sonmu sai ke Dan haka Kona haihu ke zanbarwa babyn har sai kema kinsamu nai.


Dariya sosai anty zarah tayi tana cewa''


Waye yake kyautar ciki tun baa haifesaba amatu,

Kuma ki daina cewa ba'a son abin dake cikinki sbd idan har ana maganar gata to na tabbata abin dazaki Haifa gata yagama yimasa yawa,

MD ZABEERA Dr ne Wanda yafi kowa qauna fiyeda komai da duk abin daya mallaka Dan haka Ina tabbatar Miki da Babu wani uba bayan Dr dazaifi MD qaunar abindake cikinki musamman sbd ni ba haihuwar nakeba Kinga kuwa Dole zai qaunaci 'dan Dan uwansa uwa uba Kuma Dr khalil shi yanzu ai bashida kamarku keda cikin Dan hakama ki daina cewa ba'a sonku mu Muna sonku Andi ma Yana sonku hakama Modibbo.


Gyada Kai kawai tayi tana daukar sauran fruits din dake gabanta tana cinyewa tana lumshe ido Dan dai tunda tazo idanba da daddare data kwanta ba bakinta bai zauna a rufeba komaima cin cire haushi take Masa sbd ganinsa kamar ba kudi aka saka aka siyoba komai akwai kamar a banza.



******

Zaune take tana sauraren 'yar guntuwar da nasiha tareda lallashi da 'yarta juwairiyya ke Mata cikin kulawa da tausasa harshe Amma ita Sam hankalinta baya kanta tayi nisa gurin tunanin abindake damunta,


Ganin hankalinta baya kanta yasa juwairiyya yin shiru tareda miqewa tana cewa"


Umme tafiya zanyi ga dadynsu Fatima na kirana Kuma gobene tafiyarmu Lagos sai gaf da azumi zamu dawo Inshallah.


Dagowa tayi ahankali ta kalleta batareda tace komaiba ta gyada Mata Kai tana shafa Kan Ahmad 'dan qaramin 'danta tace"


Allah yakaiku lfy.


Amin tace suka shiga bedroom din umme suna qarasa dauko sauran kayansu suka fice.


Shiru tacigaba dayi tana saqa da warwara,

Yarinya qarama kamar amatu itace tayi Wasa da tunaninta tasakata cikin wannan tunani da halin na baqin ciki har ana cewa itace Zara raini cikinda Babu ubanda yayishi,

Wlh bazata yarda ba tunda shirinta ya lalace na kowama saiya lalace Dan kuwa sai ansan wa aka taba,


Idanma MD ne ya ninkawa wannan makwadaiciyar kudi datake iya komai akan kudi ta kuwa kowa sai yaji ajikinsa wlh,


Amatu cikin dayayi sanadin baki Jin Dadi da gata acikin zabeera shine zaizama mugun sanadin barinki zabeera da mummunan hukunci tareda wulaqancin da sai Yan jarida sun buga,

Zanga yanda za'a haifi cikin da Babu.


Shigowar Haj maryam ce tasata kallon qofa tana sake ajiyar zuciya ganin yanda itama haj Maryam din duk ta hargitse sbd burinsu na shekara da shekaru ya lalace cikin mintuna goma a hannun yarinya qarama.


Zama tayi ummen nace mata'  Yaya nuratu?


Nuratu na can haryanxu kuka takeyi 

Wlh Nima aishatu nakasa yadda da khalil wata yake aure ba nuratu ba,

Yarinyar Nan fiyeda shekara goma take fama da son Khalil sai yanxu da ake maganar aure kwatsam wannan mugun labarin ya fada,

Labarin da mune muka qirqiresa Amma sai asamu wani juyin Masa a zancen

Ni dai wlh Kam wannan Abu ban amince dashi ba nabawa nuratu wuqa da nama nace ta qetare duk wata iyaka ta qwato Khalil dinta mukuma maji da sauran.


Cikin quluwa itama ummen tace"


Dukkansu zasu raina kansu ne harshi Khalil din saiyaga bacin raina.




***Da Rana lafiyyan faten dankali da Naman kaza da carrot akayi sbd ita kawai 

Haka ta zauna tacinye Wanda aka kawo Mata tas ta kora da ruwan roba masu sanyi Danma lemu masu sanyi taso Sha anty zarah din ta hanata da cewa saidai Tasha fruits drinks ba lallai su bawa baby lafiya ba 

Haka ta hkr badan taso ba Dan ita wannan cikin badan Shiba da duk abindake gidan saita ringa cinsa ba kakkautawa.


Baccin Rana tayi bayan tayi sallah sai yamma sosai ta tashi bayan tayi la'asar suka Fara waya da USI Nan yake fada Mata Dr yazo gida yafadawa su kawo shine 'dan wadda ta daukeki aiki Kuma zai ringa zuwa Yana dubamu kafin kidawo hakama ya tafi dashi anyi cike ciken makarantar dazashi har ilorin.


Saidatayi sallar magrib tukuna ta fito Palo ya zauna tareda miqe qafafu hafsatu na matsa Mata tana kallo cikin ranta tana cewa"


Amatu kinfa zamo hajiya 

Irin wannan Jin Dadi haka 


Gashi dama ba wani ciwo da qafafunta keyi tsaban son Jin Dadi da wuce wurine yasa take cewa ciwo suke Mata Dan a matsa Mata.


Wata tashar turawa take kallo ana wani film na adventure sai washe baki takeyi tana cin cake din data sa anty zarah tasa hafsatu tayi mata na inibi me laushi yaji butter sai ci take tana lumshe ido tana kallo tana Jan hafsatu da labari itama hafsatun na tayata fassarar qanxon kurege na turancin da akeyi Dan itama ba wani iyawa tayiba Amma ta dage tana fassara Mata.


Anty zarah ce ta fito daga dakinta ta nufosu cikin ado da kwalliya me kyau sai qamshi me Dadi take fitarwa amatu tabita da kallo cikin farin ciki tace''


Anty zarah kinyi kyau sosai

Amma meyasa zakiyi kwalliya yanxu da dare tunda kwantawa zakiyi?


Zama tayi kusa da ita tana murmushi tace"


Amatu MD na hanyar dawowa shiyasa.


Ohhh ohhh nagane anty zarah"

Taqarasa fada tana dariya.


Miqa Mata plate din cake din tayi tana cewa''

Anty zarah kici kiji yayi Dadi sosai.


Har takai hannu zata dauka saita fasa tana cewa"


Idan naji cikina zai cika bazan iya cin wani abincin ba kada MD yadawo nakasa tayasa cin abinci a dining.


Kallonta tana cewa' kici ko kadan anty zarah tunda kinaso.


Girgiza Kai tayi tana gyarawa amatun pillon data jingina dashi tana jawo Mata wani labarin take amatun tahau dariyar labarin datake Bata anty  zaran na tayata sunyi nisa sunata nishadinsu saiga bude qofar palon aka shigo Dr ne hannunsa daukeda qatuwar ledoji da amatu ta ajiye plate din cake din hannunta ta taso kenan saigashi a bayansa Shima ya shigo fuskarsa kawai ta kalla ta janye daga gefen Takoma gefen Dr ta tsaya tana Masa murmushi zatai Magana yace"


Baki gaida MD ba amatu.


Kallonsa tayi kafin ta kalli inda MD din yake Yana qarasa shigowa palon tayi qasa da murya tace"


Ina wuni sannu da dawowa.


Hannu kawai ya daga Mata ya nufi hanyar samansa anty zarah dake zaune ta miqe itama tana Masa sannu da dawowa to ita ya bude baki ya amsa Mata tareda Dan tsayawa ya kalleta kafin ya dauke Kai Yana cewa'


Karki jirani dinner nariga nayi dinner agurin Modibbo.


Kallonsa tayi Yana qoqarin wucewa tace"


Akawo maka ko fruits ne?


No thank you.


Wucewa yayi ya barta a tsaye tana binsa da kallo fuskarta na 'dan canzawa Amma Jin duk idanuwansu akanta yasa ta washe fuska tareda juyowa tadawo inda suke tana cewa"


Dr ko zakayi dinner tareda mu ne to?


Kallonta duk su duka sukeyi girmanta na qaruwa a idon Dr 

Tausayinta da qaunarta na shiga a zuciyar amatu tareda takaicin MD din ta yanda anty zarah ta Hana kanta cin komai sai yadawo Amma ya take hakan ya wucewarsa ko kwalliyar datayi danshi bai tsaya yayi Mata kallon ko mintu biyu ba ko me ya dauki kansa Dan ma yasamu mace me kirki da kyau kamar anty zarah tana sonsa wlh da itace koya Masa hankali zatayi taga qarshen kyau da Jan ajin banzansa.


Kamo hannun anty zarah din tayi suna zama palon tace"


Anty zarah Zo kici cake din Nan kiji Allah yayi Dadi sosai.


Ledojin hannunsa Dr ya miqawa amatu Yana cewa"


Nima a gajiye nake kamar MD shima yau a gajiye yake sosai Nima tunda muka hadu baicemin ko qala ba sbd gajiyar dayake tareda ita zanje na kwanta Saida safenku 

Amatu ki kula ok?¿


Gyada Masa Kai tayi tana cewa''


Nagode Saida safe.


Yana fita zarah tasaki murmushi tana cewa"


Dr kayaushe kanason gyara Abinda MD yakeyi Dan kada aga laifinsa 

Kadaina damuwa Dan Nima Babu ranar dazanga laifin nasa.


Takaicin MD din yasake Kama amatun tasake dagewa Saida anty zarah din taci cake din sosai Tasha apple drink suka cigaba da firarsu 

Ganin hankalin zarah din na Kan hanyar sama yasa amatu sakin tsaki qarami tana miqewa tace"


Bacci zanyi Saida safe anty zarah.


Tana shigewa zaran tasa hafsatu ta kashe komai itama tashige 

Suna shigewa taje dakinta ta shirya ta nufi dakin MD.



Ahankali amatu tasaba da zarah da hafsatu sosai kamar sunyi shekaru atare,

Kulawar dasuke Bata da gatan datake samu daga garesu yasa hankalinta ya kwanta sosai acikinsu musamman ma  da kullum tana waya dasu kawu dasuketa sawa Dr khalil albarkar yanda yake kula dasu sosai Dan yanzu ranakun matsuwarsu sun qare ga USI anata shirye shiryen zuwa makaranta,

A duniya yanzu mutanen datake so a rayuwarta fiyeda komai da kowa sune USI,kawu,iyami,Dr da anty zarah sbd sune mutanenda tasan tabbas qaunarta sukeyi Babu wani qyama ko munafurci.


Dr ya Gina qaunarsa cikin ranta danasu kawu sbd Suma shine mutum daya qwal daya fito ya tsaya musu a rayuwa yake qaunarsu batareda qyama ba ko buqatan wani Abu daga garesu shiyasa dukkaninsu kowannensu ya bude baki Dr ne abakinsa sai anty zarah dinta.


Qaunar data kewa anty zarah din yasa take Jin tsanar MD matuqa cikin ranta sbd yanda tagama lurada Sam baya damuwa da alamarin zarah din kullum shine damuwarta shine kukanta shine jimaminta ko tausaya Mata bayayi da yanda take matuqar qaunarsa/sonsa da ganin girmansa,


Duk yanda zarah din take qoqarin boyewa hakan baya boyuwa ga Wanda yake zama taredasu shiyasama Sam ta tsani ko ganinsa matuqar Yana gida Bata fitowa sbd kar wataran tayi amsa zagin maguzawa akan Abinda yakewa antyn saidai duk Abinda zai faru yafaru ba ruwanta.


A bangaren Jin Dadi kuwa zatace itakam gwara da akayi Dan kuwa rayuwa ta sauya Mata sosai Dan ko jikinta da fatarta sum nuna suna cikin hutu sbd lafiyayyar rayuwar datake ciki,

Banza ta Fadi" kaman yanda take fada

Dadinta takeci ba qaqqautawa duk wani Abu me Dadi cewa takeyi tanaso ba Bata lokaci kuwa Zarah zatasa akawo Mata shi,


Hafsatu kanta ta qararda 'yar ta'addace a gidan Dan kuwa tunda amatu tazo Bata zaman awa biyu batai aikin hada mata wani abuba,

Itace ayi Mata gullisuwa,

Tuwon Madara,

Kwakwameti,

Cake,

Dambun nama,

Dambun kaza,

Furar Madara da Milo

Komaima ci takeyi ita Bata taba ganin me ciki irin wannan na amatu ba da baya tadar komai 

Komai ci takeyi hadda Wanda masu ciki baya shafa musu lafiya

Gashi ko ciwon Kan Nan na banza da masu ciki keyi ita batayi kullum daram dam take

Ga Dr ya Hana asa kowane likita ya duba matarsa yace shine zai ringa dubata musamman da kwanakin umme tasaka fitinar sai Modibbo yasa anyi scanning Dan asan ranar haihuwar cikin su Fara shiri.


Hankalinta bai wani tashiba sbd tasan Dr na Nan shine zaisan yanda za'ayi da Maganar scanning din itadai damuwarta 'dayace shine anty zarah data Fara maganar cikin baya girma sbd ta shanye kusan wata biyu a gidan gashi Koda tazo tace ciki wata biyu wata hudu kenan Amma Babu alamar tasowar cikin shine anty zaran ta daga hankalinta cewar cikin baida lafiya itama tanason ayi scanning.

##mamuh##





ZAFAFA BIAYAR


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


YANKAN BAYA

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

Post a Comment

0 Comments