TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

'Yar Tsakar Gida 3 page 3-4


A hankali Amrah ke bin Bedroom din da kallo wanda yayi mata faɗi gashi Sunan dare ne amma yayi mata nisa sakamakon Tunanin Rayuwar ta da take tun daga farko har zuwa yanzu , wanda take ganin al'amuran duniyar nata yayi mata girma . Lumshe idanun ta tayi tana juyar da fuskar ta tare da kai hannun ta tana ɗaukar pillow din Gyefen ta tana ɗaurawa bisa Ƙirjin ta dake Buga mata da sauri da sauri kan ta na wani irin sara mata . Nurry me nayi maka ? Wani laifi nayi maka da zaka mareni akan ta ? Itace fa tayi mun laifi wanda babu mahaifiyar da zata yi mawa ƴar da take so irin abun da tayi mun.  Na tsane ta Wallahi bana Son ta ..! Wani irin kuka ta fashe dashi mai rauni da sanyi mai kuma narkar da zuciyar duk wani mai sauraren ta . A hankali ta cigaba da rera kukan ta idanun ta na kam Dumb light din Bedroom din inda take Hasko 2:02am. A hankali ta Lumshe idanun ta tana tuno da Kalaman Mom Aslaaamm wanda suka gama ɗazu kamin ta fita . Sosai matan ta burgeta musamman yanda take mata da kuma yanda ta ji labarin yanda Ta kula da Mahaifinta a lokacin da yake neman mai kulawar a rayuwar sa , ta ceto rayuwar sa ta kuma mutunta tashi ya zama Mutum...Mom Kina da halarci ALLAH Ubangiji ya taimaka Miki ya kuma jibinci al'amarin ki . Ke kuma Ammie Hafsat Wal'h bana son ki sam . Kuma ba zan taɓa zama inuwa dake ba , ai Ba Su Baba Zuwai bane kaɗai ya kamata Baba Adamu yace “ Kar a maida su ba , har dake don naki yafi na kowa ”. Maganann Amrah take yi tamkar zautacciya ita kadai . Kamin daga bisani ta ja wani irin Nannauyan Ajiyar zuciya tana Lumshe Lulun idanun ta wanda suka ƙara girma na Tsaban kuka . 


Hannun ta tasa tana shafa Gyefen ta a hankali kewar sa ke ratsa ta , tuno da yanda kullum take barci a ƙirjinsa yana shafa ta tare da nuna mata kulawa a haka Barci ke ɗaukar ta , amma a yanzu gashi ta buɗe idanun ta sam bata ganin sa , kece Silar komai Ammie Hafsat me nayi Miki...? Wani irin kuka ta kuma fashewa dashi mai tsuma zuciya da ban tausayi . Kusan mintuna Uku tana a haka , a hankali ta sauke ƙafafun ta tana Nufar Privacy don ta Ɗauro Alwala ta kai kukan ta gun mai duka . 

**

2:30am. 

Ƙarfe biyu da rabi.

Ƙwance take Tsawon dare suna masha'an su . A haka Barci ya dauke Nurayn ba tare da yasan me suka Aikata ba ko kuma wacece a tare dashi ba . Ita ko Naana wannan dare ya zama mata wani dare da ta tsinci kan ta ciki matsanancin farin ciki . Sam ta kasa Barci ta Juya ta kwanta a gyefen sa ta kwanta a Kirjin sa ta yi kissing din nan tayi na can . A yanxu ma kwance take tana tsotsan Pink lips ɗin shi tana wani jan masa cikin salo na tsaban iskanci uhmm💋.  Ware sexy eyes ɗin shi ya fara yi yana mutsika lumsassun idanun sa , cikin wani irin sauri Nurayn ya tashi yana bin Fuskar Naana da kallo ...Hi lab😘 tayi Maganan tana kai bakin ta tare da kokarin kissing Kuncin sa . 


Naana...! 

Ya furta sunan nata cike da wani iri mamaki da ta'ajibi da tsantsan ɓacin rai . Waya ce kizo nan.? Uban me ya kawo ki har Bedroom ɗina.? . 


It's Ohk darling, laifi ne don mata ta zo ta kula da mijin ta.? .


What....? 


Mijin ki..? Ya Furta kalmar yana bin ta da Kallo ganin yanda ta sauka daga Bed ɗin nasa tana tsaya masa Tsirara, wani sarawa kan sa yayi da ƙarfi, a hankali abubuwan da suka faru suka fara Dawo masa . Ohhh my God...! Ya furta yana wani rintse idanun sa da ƙarfi . 


Murmushi Naana tayi tana juyawa tare da ɗaukar Wani rigar suit din sa tana kokarin saka ma jikin ta . 


Miƙewa Nurayn yayi cikin wani irin rashin sanin me ma zai mata ya furta " Naana yaushe kika raina Ni haka ? . Shekarun ki nawa suke ? Ni Sa'an wasan ki ne ? Ƙanwa ta Nusaiba ta girme Miki nesa ba kusa ba , wanda Ni kam tsakani na da nusaiba shekaru ne kusan Goma. Topa me ya kawo wanna Maganan kuma ? Naga ai nan da dan lokaci kadan za mu zama Real life couple. Wani irin Mari tasssss wanda sai da wuta ya gilma mata , tana wani saurin dafe Kuncin ta tare da sakin wata irin ihu . Juyawa yayi yana zaran belt Wanda bata san dashi ba . 


Yau zan Miki tarbiyyar da baki samu ba a wurin Iyayen ki , sai na kwana uku ina gana Miki azaba daga Ni sai ke , zan koya Miki tarbiyya daga baya sai ki nemi miji kiyi Aure . Ni Mijin Amrah ne , daga ita babu wata mace da zata samu gurbi a zuciyar Nurayn . 


Cikin wani irin kuka Naana ta Furta " Nurayn Mari na kayi ? Wallahi koda Masifa sai na zama matar ka . Wani irin duka ya kai mata da belt yana samun Jikin ta , nan take ta zube tana fara masa kuka irin na su na ƴaƴan babu ƙwaɓo a Tunanin ta Nurayn ba dukan kirki zai mata ba , wani irin duka yake mata Wanda ko wani daya sai shatin belt ya bayyana . Wannan yasa ta fara ihu iya karfin ta , tana kiran sunan " Mommy Daddy duka a banza . Domin gaba ɗaya Nurayn ya burkice mata ya koma mata wannan fusataccen da ta sani mai taurin kai irin sa ,wanda a yanzu ta dauka ta sauya ashe rashin imanin nan nasa yana nan . Dukan ta yake tamkar zai kaita lahira yana faɗin " Ni nace ina Son ki..? Kece kika ce kika so since before now , yanxu Kuma bana Ra'ayin ki , sai na gana Miki Azaban da babu mahalukin da ya taba yi Miki irin shi a rayuwa .


Nurayn zan mutu na tuba Wayyo Mommy....! Koda ma bakin ta mari yayi nan take baki ya kumbure yana fidda jini sharrrrr......" 


Ihun da ya cika House compound din ne yasa Joseph da Gate man din sauri Fitowa Joseph na wani irin girgir da kai tare da kallon Side din da Suke Jiyo Ihun . Jikin Gate man din ne ya hau Rawa kar² Muryar sa na Rawa yace “ Joseph ina tunanin babu lapiya fa ?. WHO told you that.? Just forget bro ...! Komai lapiya yake , kawai dadin sex ne yasa ta wannan Ihun, cox kasan Oga da iya aiki...." Tab amma tun da nake ban taɓa sanin inyamuri mahaukaci bane sai akan ka Joseph 😹 . Kana jin duka da bulala kana maganan banza wai dadin Sex wannan wani irin daɗi ne kuwa ? ,Cewan Gate man yana kallon Joseph dake ta raba Idanu yana jin tamkar ya je ya shiga Bedroom din Oga yaga yanda ake wannan aika aika , a tunanin sa shi fa Sambatu ne da Ihun daɗi Naana keyi . Kai baka ji Ƙaran yanda Oga ke bugun ta da Gwatso ba .? 


Joseph You don't have Sense? . Ƙwaƙwalwar ka akwai matsala babu shakka wannan duka take sha bana wasa ba , na fitar rai ma kuwa . Ni fa ina tunanin Ƙwaƙwalwar oga da Matsala . Wai ma Oga ya kirata yace tazo ?. Wani irin bugawa ƙirjin Joseph yayi , cikin sauri yace " A'a nine..." Kai ne .? 


Gate man din yayi Maganan yana zare Idanu tare da daga Muryar da bai sani ba da wannan daren . Ba Oga yace baya buƙatar kowa ba ? . Idanun Joseph ne suka Fito cikin wani irin murya ya furta " Jesus... Yana wani hade hannayen sa biyu kamin Gate man kawai yaga Joseph ya juya yana rugawa tare da nufar Hanyar Gate. Haba nan shima ya bi bayan sa yana riƙe Joseph kai inyamuri me kake nufi.? . 


Don Allah Ka taimake Ni , laifi na ne , Ni na sanar mata inda Oga yake , kuma ya faɗa mun baya buƙatar kowa , amma nayi tunanin zai buƙataci mace a tare dashi Cox You know oga is wominizer...🤥 . Gaba da banbamenen hanci Gate man din yayi tare da rike Rigar Joseph . Baka isa ba Wallahi, ai muna nan tare da kai , har safe Oga kaima ya Fito ka amshi naka hukuncin ...kar ka damu yanzu karfe Uku ne na Asuba.  Haba Gate man ya zamiyi haka dakai.? This is not good for you please my brother....Kai Da'allah rabu Dani, ba zaka saka Ni Nima a matsala ba ,yanda ka debo sai dai ya kare maka .

**

A hankali yake kallon Nusaiba wacce ta Fito daga Palourn Mom Sa'adah fuskar ta babu walwala don tana gaida Mom Sa'adah da mata Barka da Sapiya amma Mommy sam bata kalle ta ba , sai ma daga karshe wani irin kallon ƙiyayya da tsana da take ta aika mata dashi ba uhm' bare uh'um .  Sanye ta tadda shi cikin ƙayataccen Shigar sa wanda bata taɓa ganin sa da kaya na al'adun mu ba sai a yau . Ya Zaid....! Ta furta tana kare masa kallo Ganin shi sanye da wani irin yadi na maza mai ƙyaun gaske mai dauke da launin skyblue . Yayi ɗinkin su na zamani har da hular sa wanda matasa masu fama da Giyar kuɗi suke sakawa Tangaran, Ƙamshin nan nasa yake yi na musamman. Sosai yayi masifar kyau da kwarjini . Ganin sa take a lokacin tamkar Nurayn don kuwa duniyar tayi mata zafi ainun, Fashe masa da kuka tayi da gudu tana nufar sa tare da faɗawa jikin sa tana sakin masa Kuka tare da Furta " Ya Zaid Mommy ta tsane Ni Ya Zaid."


Saurin kai hannun sa yayi yana ɗago ta cike da kulawa kana cikin Arrogant Muryar nan nasa ya furta " Nussy me kike fadi haka , ya za'a yi Mommy ta tsane ki ? Laifi kika yi mata ne muje ki bata Haƙuri...ina Nurayn.? Ya jefo mata tambayoyin nasa a lokaci guda . Kallon sa Nusaiba tayi tana kara Fashewa da kuka kana tace" Ya Zaid Saboda Amrah ne Mommy take mun haka, sannan ya Nurayn bai kwana a gida ba . Ya Zaid ka taimake mu ka taimaki family ɗin mu a karo na biyu ka Auri Amrah , a yanzu ya Nurayn babu aure tsakanin sa da Amrah. Ka bari Naana ta Auri ya  Nurayn. 


Wani irin kallo Zaid ke bin Nusaiba da shi , kamin cikin Kullewar kai ya furta " Nurayn ya saki Amrah..? Gyaɗa masa kai tayi kamin tayi Wani magana ne taga Zaid ya saki ƙayataccen murmushi kamun yace" Nasan dama ke tawa ce Amrah . Saurin juyawa yayi yana komawa harabar compound din gidan yana shigewa moton sa cikin Sauri ba tare da kuma nasan inda ya nufa ba . Wani irin murmushi Nusaiba tayi tana hade hannayen ta biyu tare da goge Hawayen fuskar ta . Alhmdlh. Ta furta tana saka kafarta tare da komawa Izuwa Falon Mom Sa'adah .

**

Zaune suke a Dinning room ko wannen su fuskar sa cikin Annuri yake , Mom Aslaaamm,Amrah da kuma Aslaam . A hankali Amrah ke cin Irish din tana kai fork din bakin ta tare da shan tea din da Momy ta haɗa mata . Ba zaki ci Ƙwan ba Amrah.? Ɗan kallon Mom Aslaaamm Amrah tayi kana cikin sanyi tace " Mommy bana Son Ganin ƙwan duka wallahi kaina ciwo yake yi , ko za'a iya Ɗaukewa.? . Kamin Mommy tayi magana ne Aslaam yayi saurin saka hannun sa yana dauke bowl din kwan tare da miƙewa yana furta " I'm coming....! Ikeni...! Madam Ikeni....!! Ya hau kwaɗa kiran sunan Madam Ikeni wacce ta shigo da sauri kaman kuma kullum sanye Da Kayan ta na masu Girki . Yess sir . 


Amsa wannan please daga yau duk girki kar a kara Amfani da kwai Bama buƙata . Ohk sir . Murmushi Mom Aslaaamm tayi tana dafa hannun Amrah tare da dan kafe ta da ido kaman mai Tunanin wani Abu sai kuma tace " me yasa baki faɗamun bakya son kwai ba , sorry Bara na dauko Miki Maganin ki maza gama karin kumallon naki . Kamin Amrah tayi mata magana ne Muryar Daddy ya katse su Alh Tama wanda Hakan yasa Amrah zuba ido tana ganin shigowan sa ,wanda da'alama yanzu ya dawo Gidan... Morning Daddy .' Aslaaamm ya katse shi , kamin Daddy ya dafa Ƙafadan shi yana furta " how was your night?. Kayi barci mai daɗi na farin ciki yau kaga Familyn Daddy . Murmushi Aslaaamm yayi cikin dan gurɓataciyar Hausan sa ya furta " Eh Daddy yanzu ma Baby Amrah take....Huuuuu Aslaaamm barsa ya ƙariko mana yaga baby Itama ko.? Muryar Mom Aslaaamm ya katse Su .


Dariya Aslaaamm yayi suna takawa inda Su Amrahn ke zaune . Daddy yanzu ta daina ji dani ALLAH. To ka girma yanzu . Barka da Sapiya Abba. Muryar Amrah ya katse su cikin sanyin nan nata . Kallon Ta Kanol yayi yana zama Gyefen ta tare da kai hannun sa yana riƙo ta a hankali ta kwantar da kan ta bisa jikin sa . Kusan mintuna uku suna a haka shi kadai yasan yanda yake ji a zuciyar sa . Amrah jikin naki da Sauki.? . Eh Dad taji sauki amma sai dai bata son kwai ko kaɗan i think har yanzu da zazzaɓi a jikin ta . Ko za'a kaita asibiti . ? Muryar Aslaaamm ya katse su . Ohhh Mommy ta furta kana tace " Hohoho Ni ...! Murmushi Duka suka yi Aslaaamm yana jan kujera tare da zama . Amrah kina Son Ganin Ammien ki ko.? Kiyi Haƙuri a satin nan zan dawo da Ammie zaki zauna da ita kema kiji dadin mahaifiya.... Saurin Ɗagowa Amrah tayi tana kallon Dad tama nan take idanun ta suka ciko da Ruwan hawaye . 


Wasu irin ƙwallah ne suka fara bin Kuncin ta 🥹 A'a Daddy Aa...Aa Abba don Allah kar ka dawo da ita rayuwar mu , bana Son ta , bata da tausayi ... Saurin aje tea mug Mom Aslaaamm tayi bakin ta na Rawa tana son dakatar da Amrah , amma kuma Sai Dad Tama ya daga mata hannu Alamun ta dakata . Cikin kuka Amrah take fadin , Abba na indai don nice zaka dawo Ammie Rayuwar ka kar dawo da ita bana buƙatar bude ido nagan ta a matsayin Mahaifiya ta . Ta rabani da Noory Abba wallahi bata da imani ...! Kawai sai ta fashe da kuka har da cira . Saurin shafa bayan ta Mom Aslaaamm tayi tana furta " is Ok . Ya Haƙuri Amrah na . 


Humm Gwauron numfashi Daddy tama ya sauke kana yace " Ohk Amrah abin da kike so shi Zanyi kinji ya isa haka ,ki daina kuka, Kina Son Nurayn..?? 


Ba Amrah kadai tayi mamakin Maganan Daddy ba har Mommy kallon sa tayi kamin Amrah tayi Magana ne Aaslaam yace " SO Kuma Dad .? Wani irin so , bata son shi yanzu , mutumin da ya mare ta wani irin namiji ne shi wanda baya iya sarrafa fushin sa , wai kuma akan matar ka wacce kake kirarin You Really love her , wannan wani irin Namiji ne ? Ko tana Son shi Ni ba zan yarda ta koma wurin sa ba , ina so ƙanwata ta samu miji mai kulawa da ita WHO will take good care of her ,ko muna tare ko Bama tare . Amma Nurayn bai cancanci Zama miji ba . Ko Amrah na Son shi sai na cire mata son shi . 


Aslaaamm Muryar Mom ya katse shi wanda tayi maganan cike da dan daga murya . Daddy ne ya kuma katse ta ta Hanyar daga mata hannu . Ohk that's very Good kuyi Breakfast yanzu Ni zan magana da Mommy . 


Shiru Amrah tayi tana gani su Daddy suka fice daga Dinning Room ɗin yayin da Aslaam ke kallon ta ya na observing mood din ta a wannan lokacin . Ɗago da Lulun idanun ta tayi tana zuba su a kan sa kana ta narke masa fuska tana furta " Ya Aslaam Noory bashi da laifi , Ammie ce mai laifi . Kafe ta yayi da ido kana ya Lumshe idanun sa yana furta " Ehem go ahead . Dan narai ² tayi da idanun ta kaman zata yi kuka tace " Ina jin kewar Noory Sosai ne .


Ohk yi breakfast za muyi magana . Gyada masa kai tayi tana Goge Ƙwallahn da suka zubo mata . 

**

Gidan Ɓaidu

Tun daga Farkon gidan mutane ne kowa ya Shigo ya fita ana ta tayasu murnar dawowan Kanol Ɓaidu, inda a tsakanin jiya har labarin dawown canonel Ɓaidu ya koma ma gwamnatin inda Tun karfe Goma na safe motocin jami'an sojoji dana gwamnati sun gama cika tun daga farko har ƙarshen Layin . Sai dai duk wannan abun Daddy tama baya a wannan wuri . 

Assalamu alaikum

Muryar Yalwa mai daddawa ya katse su , wacce tayi Rayuwa a layin daga Bisani ta koma wata ƙaramar hukuma hunkuyi da zama da mijin ta . Irin yan kauyen nan ne na titik . Gidan ne ya amsa ciki har da su Baba Zuwai wanda acewan ta zama salamun alum da kanol . Yalwa Barka kece a gidan.? Gamunan gafara dai . Yalwa tayi maganan tana sauke kullun Buhun kayan ta dake bisa kan ta . 


Inna Larai ne ta Fito daga daki tana wannan juyi a dole yanxu fa gwamanti nasu ne . Gaiswa yalwa tayi tana masu sam Barka , kana cike da jimami ta kalli Inna Larai tana Cewa " Allah sarki larai ashe kin yi Aure , sai kuma gashi Allah ya dawo da kanol rabon wani ya kori na wani. Saiii duka aka yi kamun Larai tace kaman ya nayi Aure waya faɗa Miki? Wannan wacce irin magana ce . Cike da gidadanci na yan kauye Yalwa tace " A'a ikon Allah jama'a wai larai ba tayi Aure ba , to Meye abun rufe mun Larai,Ni fa bakaramar yarinya bace , dama juna biyu na ganki dashi , Amma tun da baki so nasan kinyi Aure sai nace Allah ya raba lapiya 😱...............

Wani irin kallo Inna larai ke bin yalwa dashi kana Baba Zuwai ta muskuta cikin sauri tana faɗin " A'a haba yalwa kara duba dai da kyau . Tsawon sheƙaru Muna cikin gidan nan , kuma munaa zaune ne a matsayin matan Kanol Auwalu Ɓaidu . A'a a'a Fa da sake A dai duba Maganan nan fa na yalwa . Inna Lanti ta katse su wacce take da gindin rijiya tana zaune da Buta a gaba tana Alwala . A wani irin harziƙe Inna Larai ta kalli Lanti kana tace " Au yanzu har sharrin da za'a yi mun ya kai haka? Oh Ni Larai me nayi maku a cikin gidan nan? Kawai sai ta daga hannu tana kwarma ihu tare da tuma a nan ƙasa . Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Baba Zuwai ta Furta da sauran mutanen gida da sukayo kan Inna Larai... Caɓe baki Lanti tayi tana cewa " A juri rafi dai . 


Gaskiyar Magana Lanti abubuwan ki sun fara yawa dana mijin ki Malam Adamu ,abun naku yayi yawa , wannan cin mutuncin ya isa haka nan . Wallahi bani da mutunci Ni kin sani , kawai saboda abun duniya idanun ku ya rufe ehhh wannan fa miji namu ne , idan ba zai dawo damu ba babu Komai , Allah ya bamu yaya zasu kula damu gasu nan, dama ai haka rayuwa take mun gama wahala tun kamin ya zama har ya zama muka kuma wahala da ya'yan Kanol amma yanzu ana nema ayi ma larai sharri da tsufan ta ta manyantan ta . To don Allah duka a bar wannan magana ce ta aure Ni dai na Haƙura babu Komai Allah ya duba al'amaran mu , amma Tabbas a yau zan bar cikin gidan nan , ba za'a yi min sharrin da zai taɓa mun yaya da jikoki ba . Cewan Baba Zuwai tana sababi da Tijara . 


Kutumelesi kambabbabba bala'i. 

Muryar Zulai da Hajara ya katse su ,wanda suka sha ɗan mara suna kallon kowa daya bayan daya ,kai ko ba'a faɗa maka ba kasan Babu tarbiyya . Ai Wallahi baba babu inda zaku tafi ,zama a gidan mahaifin ku daram , idan kuma da wanda zai fitar daku to sai na ganshi . Cewan Zulai tana kama ƙugu tare da wani irin Girgiza kai da gani ba sai an faɗa maka ba . Hajara ce ta juya tana kallon inda yalwa mai daddawa take kana ta nufe ta tana faɗin Yau sai kin san kin shigo cikin gidan yawa . Ke ga munafuka ko.? Duka zaki sha . 


Kamin Iyaye matan suuyi wani magana tuni ƴammatan gidan Ɓaidu sun danne Yalwa suna sauke mata power 💪🏻 ƙusshhh ƙushhh ƙushhh kake ji suna jibgar ta har da masu haɗa mata kai da bango duka na rashin ilimi da jahilci. Nan take fuskar yalwa yayi chinchin Goshin ta yayi tsini suntum, ko ihu ta kasa yi sai idanun ta daya dake tsiyayar hawaye . Salatin mazan gidan ne da yanda suka rifo ma su Zulai yasa su dakatawa da dukan Yalwa wanda mazan gidan suka amshe ta . Su kuwa matan iyayen cewa suke su kara ma ta . 


Cikin kuka yalwa ta Juya tana faɗin dama ba zaku taba  sauyawa ba , Allah ya saka mun , don naga gaskiya na faɗa shine aka mun haka... Gaskiyar Uwar ki inshallahu sai kin ga sakayyar Larai . Cewan baba Zuwai tana daga hannu tare da zanbarma kaman zata duke Yalwa . 


Ita kuwa Inna larai Maganan gaskiya hankalin ta ya tashi amma kuma kawai Dakewa tayi don Tabbas tana jin bakon al'amari a tare da ita . Muryar Baba Yusufu ne ya katse su wanda yaji komai dake faruwa . Gyaran murya yayi irin nasu na manya kamin yace " larai daga yau zaki koma sasan dan lami da zama , har na tsawon wata guda , kar ki ƙara fita dake da Zuwai. Maganan kuma zaku bar gida duka bai taso ba . Shi kan shi Kanol ba zai ji dadin hakan ba , laifi ne kun yi shiyasa Baba Adamu ya yanke wannan hukuncin.amma komai zai daidaita inshallah .don Allah kowa ya watse . Ku kuma Zulai ku same Ni a soro ina jiran ku yanzu .


Yana Gama Maganan ya juya yana Ficewa yayin da su zulai suka bi bayan sa .

**

Ɓangaren Nurayn kuwa sai da ya yaga Nana na shiɗewa don azaba sannan ya barta anan yana rufo Bedroom din tare da saka key. Resting room ɗin sa ya nufa yana kimtsa kan sa kamin ya tafi masallacin dake kusa dasu . Bayan ya dawo ne ya kuma wuce su Joseph dake ta aikin raba ido jikin sa sai kyarma yake yi . Oga Good morning....banza Yayi masa bai tanka sa ba. Yana nufar Falo kaman mintuna sha biyar ya fito ciki shigar sa na track suit marasa nauyi yana shigewa moton sa tare da barin gidan . 


Tafiya kawai yake yi a Moton amma Hankalin sa baya jikin sa , a hankali ya gyara zaman Ear phone din kunen sa kana yace " ina ne kace gidan Alh Muhammad tama yake ?. Ohk . Ohk ya kara furtawa a karo na biyu kana ya cigaba da Driving ɗin yana kai hannun sa tare da ƙara sautin cool music din dake tashi na wakar Alaan . 


Bin gidan yake da kallo kana a hankali ya fara horn tamkar zai shiga gidan iyayen sa a gadarance a kuma cike da Arrogancy nan nasa shi ga isashe😎.

Post a Comment

0 Comments