TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

SAKAYYAH page 67

 Ahankali ya shaƙi ƙamashin jikinta tare da kallon plate da cup dake gabanta wanda da alama akwai abinda taci kafin ta bin ba ba kwanta.

A dai-dai lokacin kuma Momy ta fito daga Kitchen idanunta suka sauƙa akan Moddibo dake zaune a hannun kujeran Khausar na zaune gefensa ta manna kanta da kafaɗarsa yayin da hannunsa ɗaya ke bayanta yana shafawa ganin haka yasa Momy saurin komawa kitchen.


Ahankali Moddibo ya ɗago kansa tare da kallon ƙofar Falon jin sautin muryan da ko agigin bacci ya farka zai gane ta muryan Hajja Nana.

Khausar kuwa cikin yanayin baccin da take ji ta buɗe idanunta ta kalli Hajja Nana sai kuma ta maida idanunta kan Moddibo ahankali ta sake maida idanunta kan Hajja Nana tare da cewa.

“Da sassafen nan?Wannan wani irin sammako kika yi?”.

Cikin sauri Hajja Nana ta kallesu tare da faɗin.

“Toh ƴar nema wato karota ma kike yi?,Ni ina nan tunda kuka zo na gaza bacci ina ta begenki ina son ganin ki shiyasa ana fitowa masallaci nace wa Baffa Liman da Abba su kawoni amma shine kike cewa nayi sammako toh ai ba gidanki naje ba sai ki bari idan gidanki naje kiyi min iyaka da zuwa”.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.

“Toh ki zauna mana kina tsaye”.

Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa tsakiyar falon madadin ta zauna kan kushin sai ta zame ƙasa ta zauna tare da kamo ƙafafuwan Khausar ta fara jan yatsun sai kuma ta maida idanunta kan cikinta cikin mamaki ta riƙe haɓa tare da faɗin.

“Ohhh Allah mai iko, Allah mai kyauta da daɗi”.

Sai kuma ta maida kallonta kan Moddibo.

Moddibo kuwa kansa ya ɗan jujjuya kana ya juya ƙwayar idanunsa sai kuma ya sanya hannunsa na dama ya shafa sajensa ya fahimci kallon cikin Khausar yasa take yi masa kallon irin sannu. Jarabebbe mayatacce har ka ɗirka mata ciki? fahimtar hakan yasa ya kauda kansa.

Hajja Nana kam ganin yanda ya jujjuya idanunsa yasa ta jinjina kai tare da faɗin.

“Hmmm Allah Ubangiji ya shirye ka ke kuma Allah ya sauƙeki lafiya”.

Cike da kunya Khausar ta sake manna kanta da kafaɗan Moddibo kana ta motsa laɓɓanta ta furta.

“Ameen”.

Cikin ɗan ɗaga sautin murya Moddibo yace.

“Amin Amin Ameen ya Allah, Allah ya amsa addu'ar ki mun gode da addu'a”.

Kallonsa tayi tana mamakin yanda zamani ya sauya sukam a zamaninsu ko kusa da makamancin wannan ba'a yi ga yadda ya wani ƙwaƙumeta a farkon surka.


Momy dake kitchen kuwa jiyo kaman muryan Hajja Nana yasa ta leƙo.

Ganin tabbas Hajja Nana ce yasa cikin sauri ta fito tare da cewa.

“A'a Hajja Nana, dama naji kamar Muryar ki na dan kasa kunne ashe dai ke ɗin ce”.

Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.

“Wallahi fa tun randa mukayi waya kika cemin tazo nake ta son zuwa washe garin ranan kuma Mashin ɗin Abba ya samu matsala shine malam Liman yace na bari sai yasa mai a mota kafin muzo, tunda zai zo ya marabci su Abualeey yanzu ma tare muke suna falo da Lamiɗo”.

Kai Momy ta gyada tare da faɗin.

“Kai Masha Allah sannun ku da zuwa.

Ahankali Moddibo ya juya da naiyyar gaisheta

Sai ya ga har ta shige kitchen Momy kuwa already ta gama haɗa breakfast Sultan Cheaps ta soya wanda yaji Vegetables da naman rago mai laushi sai kuma Ƙosai data soya wanda keta tururi wanda Khausar ce tace tana so sai kuma Koko wanda duk zaɓin Khausar ne sai kuma tea dake ƙamshin Kanunfari, Citta Na'a'na'a ta fito dasu.

Anutse. Moddibo ya sunkuyar da kansa kana yace.

“Momy Barka da safiya".

Cike da kulawa tace.

“Barka dai Moddibo ka iso?”.

Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Eh Momy ina kwana”.

“Lafiya lau Alhamdulillah ya gida”.

Kallonta ta mayar kan Khausar tace.

“Ki tashi ki samu ku abinci kuci”.

Juyawa Khausar tayi tare da kallon Momy kana tace.

“Momy kinyi min ƙosan?”.

Kai Momy ta gyaɗa cike da tarin ƙaunarta tace.

“Nayi miki mana ai dole na inyi miki”.

Hajja Nana dake cigaba da matsawa Khausar Kafa tayi dariya tare da faɗin.

“Aikam dole kiyi mata naga abin na musamman ne”.

Baki Khausar ta ɗan tura tare da hararan Hajja Nana kana ta ɗan janye jikinta daga na Moddibo wanda shi har ga Allah yama manta Momy na wajen jin ta ɗan matsa ne yasa ya kalleta.

Ganin yana kallonta yasa ta juya mishi ido alamar yaga Momy na nan.

Fahimtar hakan yasa ya gyara zama sai kuma ya zame ya zauna akan tattausan Carpet ɗin ya zamana suna fuskantar juna yayin da Hajja Nana ke gefensu.

Kulan farkon ta jawo ta buɗe idanunta suka sauƙa akan ƙosan dake zuba wani irin tururi da ƙamshi ajiyar zuciya mai sanyi ta sauƙe irin yanda duk wata mai ciki keji asanda ta samu abinda take so.

Flaks din dake gefe ta jawo ta buɗe sai taga tea.

Fuska ta kwaɓe kamar za tayi kuka tace.

“Momy kunun fa?”.

Momy na ƙoƙarin janyo Flaks din gabanta tace.

“Gashi nan ki buɗe mana ki gani ke kina da ci da zuci”.

Ɗan Murmushi tayi kana ta buɗe tare da cewa.

“Kai Momy Ubangiji Allah yabar min ke Allah ya miki Albarka Ubangiji ya miki sakayya da gidan Aljanna”.

Murmushi momy tayi tare da faɗin.

“Ameen ya Allah Mamana”.

Murmushi Hajja Nana dake gefe tayi kana ta kalli Khausar sai kuma ta kalli Momy ahankali tace.

“Ubangiji Allah ya rabaku lafiya”.

Cikin sanyi Khausar tace.

“Ameen”.

Moddibo kuwa fuskarsa ɗauke da murmushi ya gyara zama tare da cewa.

“Ameen ya Allah aini ina ga yau tukuici na musamman zan banki tunda kika zo kike mana addu'a da fatan Alkhairi ”.

Baki Hajja Nana ta taɓe tare da cewa.

“Allah yasa dagaske kake”.

Cikin tabbatar wa yace.

“Dagaske nake mana ai ina ga ke tare zamu tafi dake kiyi ta mana addu'ar nan sannan kiyi ta kula mana da ita”.

Ɗan zare idanu Hajja Nana tayi kana ta hararesa tace.

“Kunyi ƙarya nikam bazan zama mai aikin kuba kuda gacan innare kuna tare da ita ai magana ta ƙare duk kular da kuke buƙata zaku samu”.

Kai ta jinjina kana tayi Murmushi tare da faɗin.

“Aikam itama munzo dasu jiya ma take cewa tana son zuwa wajen ki sai Khausar ke cewa ai kema zaki zo shiyasa bata jeba”.

Ɗan gyara zama Hajja Nana tayi tare da faɗin.

“Aikam toh shikenan”.

Khausar kuwa ƙosai ta zuba kusan guda goma kana ta zuba Kokan sai kuma ta zuba wa Moddibo Sultan Cheaps da Perpe Chicken mug ta ɗauka ta haɗa masa tea mai kauri.


Hajja Nana ma ƙosan Khausar ta zuba mata tana kallon ƙosan da yayi kyau a ido ta kalli Momy tace.

“Ƙosan ya isa haka, asamin shayi sai ahaɗa min da biredi”.

Kai Momy ta gyaɗa kana ta miƙe ta ɗauko Bread Mai yanka-yanka Karɓa Hajja Nana tayi ta shiga haɗa breading, ƙosai da tea tana sha.

Khausar kuwa Ƙosai da Kokon ta shiga sha cikin tsananin mararin abin.


Ahankali ta gutsiri Ƙosan da cikin tsakiyarsa ke ɗauke da diddigin nama kana ta kuma kurɓan kokon daya sha kayan ƙamshi yawun bakinta sai tsinkewa yake saboda yanda ya mata masifar daɗi.


Moddibo kam cike da mamaki yake kallon yanda Khausar ke cin ƙosai da Koko tsakaninta da Allah.

Hajja Nana dake kai biredi da Ƙosai baki ta kalli Moddibo daya zubawa Khausar idanu yana cew.

“Ni mamaki nake bata cin abinci fa agida”.

Murmushi Hajja Nana tayi tana kallon yanda Khausar ke shan Koko tsakaninta da Allah tace.

“Ai dama haka wani yake in dai yana da ciki baici agidansa amma da zaran yaje unguwa zai ci abinci”.

Kansa ya girgiza tare da cewa.

“To ai can ko munje gidan Lalla Khadijah bata cin abinci amma kinga tunda muka zo nan cin abinci fa takeyi”.

Momy dake fita zata kaiwa Abba da Man Liman nasu tayi Murmushi tare da faɗin.

“Sosai ma kam tunda  aka zo nan abinci take ci babu kama hannun yaro taci ta ƙara ɗayan daren ma munyi  hira mun gama tace min yunwa take ji sai da naje na dama mata Quaker oats tasha kafin tayi bacci”.

Cike da farin Moddibo ke sakin murmushi yana kallon Khausar dake ɗan Cunno baki gaba Momy kuwa idanunta akan Hajja Nana ta cigaba da cewa.

“Sannan da safe kafin ta kwanta plate da kuka zo kuka samu shima indomei taci tasha tea kafin ta kwanta tayi bacci anan gashi yanzu ma tana ta ɗurawa”.

Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da faɗin.

“Toh Momy yunwa nake ji na daɗe bana cin abinci fa”.

Dariya Momy tayi kana tace.

“Keee dama haka kike da cin abinci nayi mamaki ma da akace wai ciki ya hanaki cin abinci.

 Don banyi tunanin akwai abinda zai hana ki cin abinci ba, tunda ke ciwo ma baya hana ki cin abinci”.

Kanta ta sunkuyar ƙasa ta cigaba da cin ƙosanta kallonta Moddibo yayi ganin ta gama cinye duk ƙosan hannu tasa ta sake janyo kular ɗan ware idanunsa yayi tare da faɗin.

“Minha bazai Miki yawa ba?”.

Kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kai tace.

“Um-um kaɗan zan ƙara naji cikina ya ƙoshi amma bakina bai gaji dashi ba”.

Yana rufe kulan yace.

“Toh ki bari sai anjima”.

Marairaice fuska tayi ganin haka yasa Momy cewa.

“Ki bari na rage Miki ƙullu a fridge idan kina so anjima zan sake soya miki ”.

Gyatsa tayi kana ta gyaɗa kai tare da faɗin.

“Toh shikenan”.

Ta ida maganar tana jingina bayanta da jikin kujera.

Ahankali Moddibo ya matsa kusa da kujeran da take ya ɗan jawota jikinsa tare da cewa.

 “Zo, Zo zonan kada ki kwanta, ki ɗan zauna tukun mu samu abincin yabi jikinki”.

Ya faɗa yana manna kanta da kafaɗarsa yayin da hannunsa ɗaya ke kan cikinta yana shafawa shi kuma yana cigaba da cin abinci da hannunsa na dama.

Ahaka suka gama cin abinci suna taɓa hira jefi-jefi.


Suna gama cin abinci Momy ta shigo idanunta akan Khausar tace.

“Toh tashi ki tattare wurin”.

Kai ta gyaɗa tare da faɗin.

“Toh”.

Kana ta yunƙura zata miƙe.


Ahankali Moddibo ya kalli Momy kana yace.

“Momy bari na tattare”.

Ɗan ware idanu Momy tayi kana tace.

“Ta isa tana zaune ka tattare mata kwanika”.

Cikin sanyi yace.

“Momy toh ta gaji ne kuma ta cika cikinta da yawa bata son motsi”.

Kai Momy ta girgiza tare da faɗin.

“Aikuwa dole tayi motsi maza tashi ki tattare su”.

Ta ƙare maganar tana kallon Khausar.

Hajja Nana dake kallonsu ta ɗan taɓe baki tace.

“Kai dai kai dai kam wannan akwai ka da tsirfa iri-iri yo in Mai ciki bata motsa jiki ba mai za tayi!? Ko kaine zakayi mata naƙudar”.

Ɗan hararan Hajja Nana Khausar tayi sai kuma ta kalli Momy tare da cewa.

“Nima fa bance yayi ba shi yace zaiyi”.

Ta ƙarashe maganar tana kwashe kwanukan ta kai kitchen kana ta dawo ta zauna bayan ta dawo sun zauna Momy suka gaisa da Hajja Nana bayan sun gaisa suna cigaba da hira.

Asiya ta shigo cikin sassarfa kamar an jefota cikin yanayin tashin hankali tace.

“Momy dan Allah kizo kiga Ummana baki ɗaya yau tunda gari ya waye atsaye take bata zauna ba kona minti ɗaya fa gaba ɗaya yau jikinta ya tashi!”.

Da damuwa Momy ta miƙe cikin sauri tabi bayan Asiya suka nufi Side ɗin Hajiya Bunayya.

Khausar kam ahankali ta juya ta kalli Hajja Nana itama Hajja Nana kallonta tayi sai kuma ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace.

“Yah Mu'allim nace maka batun jikin Umma da Amina ayi musu addu'a sannan ka turo Dr Jameel yazo ya duba su amma Yah Mu'allim har yanzu baka ce komai akai ba”.

Ahankali Moddibo ya dafe kansa da hannunsa na hagu yace.

“Wallahi na manta, koyie haƙuri mantawa na keyi Minha”.

Kamar za tayi kuka tace.

“Yanzu fa kaji abinda Asiya tace”.


Hajja Nana da batasan meke faruwa ba ta kalli Khausar tare da cewa.

“Meke damunta?”.

Cikin rauni Khausar tayi ƙasa da kanta kana ta kwashe labarin duk yanda ta faɗawa Moddibo ta faɗawa Hajja Nana.


Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sauƙe tare da jinjina kanta tace.

“Ai dama haka duniya take idan kace tukunyar wani bazai tafasa ba naka ko ɗumi bazai yiba arayuwa ka taka ahankali kada ka shiga hurumin da bana kaba duk lokacin daka shiga hurumin da bana kaba sai ka samu abinda zai shiga huruminka”.

Araunane Khausar ta risinar da kanta Hajja Nana kuwa cikin jimami ta cigaba da faɗin.

“Ya hanaka zaune ya hana ka tsaye yanzu wa gari ya waya ita wancan ta haukace ƴarta ta zama mai wari ita gata nan ƴarta ta zama wata halitta daban gashi ita kuma yanzu ƴarta tazo tana cewa tunda gari ya waye bata zauna ba ta isa ta zauna tsutsotsi na cinta”.

Ahankali Khausar ta rausayar da kanta hawaye na kwaranyowa daga idanunta tace.

“Hajja Nana Ni tausayi suke bani musamman Amina tana bani tausayi gaba ɗaya sai kinga yanda ta dawo ita ma Umman na ban tausayi bata isa ta zauna bafa Hajja Nana wlh ko jiya data shigo nan mu gaisa tsutsotsin har bin ƙafarta suke yi sai in taji kiga tana ta buge-bugen ƙafart kamar itama so suke su haukatata gaba ɗaya ”.

Cikin sauƙe numfashi Hajja Nana ta gyara zama tare da cewa.

“Dama haka duniya take”.

Still idanunta na zubda hawaye ta kalli Moddibo tare da faɗin.

“Ni dai ina so a samar mata magani ayi mata addu'a ane ma mata sauƙi awajen Allah”.


Acan Side ɗin Hajiya Bunayya kuwa Momy na shiga ta sameta atsaye sai bubbuga ƙafa take saboda yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke gefenta tana zazzaro harshenta waje.

Da sauri Momy ta ƙarasa wajenta ta riƙe hannunta kana tace.

“Yaya ki zauna mana”.

Kai ta girgiza cikin tarin damuwa tace.

“Ina Momyn Khausar bazan iya zamaba idan na zauna ji nake har cikin hanjina tsutsotsin suke ci suna gigitani na rasa yanda zanyi na cutar dake arayuwa gashi nima yanzu na samu abinda yake cutar dani na rasa yanda zanyi a rayuwata”.

Cike da tarin tausayinta Momy ta girgiza kai tare da faɗin.

“Bakomai in sha Allah zaki samu lafiya”.

Kai ta girgiza tana cigaba da buga ƙafarta kana tace.

“A'a nikam nasan na nemowa kaina abinda yafi ƙarfina Momyn Khausar ki yafe min ki cewa Khausar ta yafe min”.

Cikin sauri momy ta juya tare da faɗin.

“Ki kwantar da hankalinki Yaya bari naje na kira Lamiɗo yazo ya kai ki asibiti ”.

Ta ida maganar tare da nufar Side ɗin Lamiɗo.


Cikin kiɗima tace.

“Wallahi Lamiɗo Yaya ce babu lafiya gaba ɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye ta kiɗime ta gigice ga Amina ma ita ma baki ɗaya yau jikinta nata abin ya sake motsa wa”.

Anutse Lamiɗo ya juya ya kalleta kana yace.

“Hmmm shine baki ɗaya kika gigice haka?, Mutanen dake suka cutar Sakayyah ce ta sauƙa akan su shine zaki gigice haka?”.

Kai ta girgiza kana tace.

“Nikam basu cutar dani ba kuma koda sun cutar dani na yafe musu Duniya da lahira”.

Gyaran murya Man Liman yayi tare da cewa.

“Wayene ba lafiya?”.

Zama Momy tayi muryanta ɗauke da damuwa tace.

“Uwar gidata ce babu lafiya Baffa Liman jinyan kuma ya kiɗima mu”.

Kai ya jinjina yace.

“Toh kunje asibiti ne?”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Munje asibiti. Likitocin da kansu sunce bana asibitinba ne na gidane sai kaga yarinyar mijin da aka Aura mata ne bisa duk kan alamu tsafi yayi da ita ita kuma Yayan dai baza ka tantance ba”.

Zama Lamiɗo ya gyara kana yace.

“Ki daina cewa ba za'a tantance ba ki fito kice sihiri tayi Miki keda Khausar ya dawo kanta haka zaki faɗa masa ki fito fili ki faɗa masa abinda ta miki Saboda ko baki faɗa ba Allah ya sani kuma taga Sakayyar abinda ta aikata”.

Kai Momy ke girgiza masa shikam cikin tsanar Muguwar ɗabi'ar Hajiya Bunayya ya cigaba da cewa.

“Ita kuma Amina dama ai ƙulle ƙulle sukayi Ni kaina tsoron Al'amarin Naseer nake yi suka nuna dole-dole sai Naseer ya auri Amina yaje yayi tsafi da ita ya dawo da ita me zance musu su suka jawa kansu jiki magayi.

Ai dama sai dana ce duk abinda ya faru babu Ni aciki ba hannuna bare ƙafata aciki”. 

Cike da nutsuwa Man Liman ya kalli lamiɗo tare da faɗin.

“A'a Lamiɗo baza ayi haka ba ai ita rayuwa rai da lafiya ita ake bibiya ake duban Lamarinsu kuma komai lalacewan Amina jinin kace tsatsonka ce kana Hajiya Bunayya komai lalacewan ta Matarka ce Uwar ƴaƴan kace”.

Da sauri ya girgiza kai yace.

“Uwar ƴaƴana ne babu yanda na iya amma Ni na saketa na saki Hajiya Bunayya tun wata ɗaya daya wuce Ni yanzu babu alaƙa tsakanina da ita na barta dai ta sauna a gida nane albarkacin Asiya da Sulaiman, taje can rayuwarta da ban rayuwata da ban”.

Mommy kam kallonsa take cike da matsanancin mamaki jin cewa ya saki Hajiya Bunayya ko kaɗan batayi farin cikin jin haka ba sai ma damuwarta ɗaya karu.


Man Liman kuwa cike da nutsuwa yace.

“Ai baza ayi haka ba yanzu idan babu matsala kayi min jagora muje in gansu Babu abinda yafi ƙarfin Ubangiji zanyi musu abinda Allah Ubangiji ya sanar dani”.

Kai Lamiɗo ya girgiza kana yace.

“Baffa Liman ka barsu baka san su bane”

Cikin rauni Momy ta kallesa kana tace.

“Dan Allah Lamiɗo kayi haƙuri ka taushi zuciyarka”.

Ahankali Lamiɗo ya ɗago ya kalleta kana ta girgiza kai ganin yanda ta tashi hankalinta yace.

“Kina jifa da bakinta tace ita tayi sihiri ta kashe Ramadan ”.

Cikin sauri Momy tace.

“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un yanzu kai Lamiɗo sai ka yarda ita tayi sihiri ta kashe Ramadan?”.

Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

“Ehem ita ta faɗa da bakinta ai ”.

Cikin sauƙe numfashi ta kalli Man Liman ta kalli Lamiɗo tace.

“Amma ka manta tun lokacin da Ramadan yayi accident an gaya mana cewa yana da brein Cancer tun lokacin daya karye ka manta cewa Likita ya faɗa mana kuma ko kai kanka kasan cewa ciwon kan da Ramadan yayi dare ɗayane sannan kuma an tabbatar mana da cewa ciwon ne ya kashe sa”.

Kai Abba dake gefe ya jinjina Momy kuwa cikin rauni ta cigaba da faɗin.

“Ko Sihiri da tace tayi Ni banyi Imani Sihirinta da tayi shi ya kashe min ɗana ba imma shine ya kashesa tsakaninta da Ubangijinta kuma ko cikina da take cewa ita tayi sihiri ya zube wallahi bata isa tayi Sihiri cikina ya zube ba face dama Allah ya ƙadarta waɗanan cikin bazan haifesu su taka doron ƙasa ba,  shine kaɗai amma Ni bata isa ta kashe min ɗa ba bata isa zubar min da ciki ba wa'adin sa ne yayi”.

Cikin sanyi ta ƙare maganar tana mai zubda hawaye ta cigaba da cewa.

“Kuma ai ita in tayi zalunci mu bai kamata mu saka mata da zaluncin ba sai mu barta da Allah shi yasa Sakayyar da zaiyi mana”.

Jikin Lamiɗo ne yayi sanyi jin abinda ta faɗa sai kuma ya kalli Man Liman dake cewa.

“Kayi haƙuri muje mu dubata”.

Ahankali Yah Abba ya gyara zamansa tare dasa baki acikin tattaunawar su yace.

“Ayyah Lamiɗo ayi haƙuri adubasu ai rai da lafiya ake dubawa”.

Kai ya gyada tare da cewa.

“Shikenan”.

Momy ce ta fara miƙewa ta fita Lamiɗo na biye da ita sai kuma Man Liman da Yah Abba Abaya.


Suna shiga falon Hajiya Bunayya suka sameta atsaye sai bubbuga ƙafanta take tana tsalle ga ƴan mili-milin tsutsotsin nan na bin ƙafafunta yayin da Amina ke kwance kan 3sitter  tana karkata kanta tare da zaro harshenta Man Liman na ganinta yace.

“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”.

Juyawa yayi ya kalli Hajiya Bunayya kana ya kalli Amina sai kuma ya sake juyawa ya kalli Momy tare da faɗin.

“Momyn Khausar akwai Zam-zam?”.

Kai ta gyaɗa tace.

“Eh akwai”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.

“Toh ki temako min dashi”.

Da sauri tace.

“Toh”.

Kana cikin hanzari taje ta dauko Zam-zam Babban gora ta kawo karɓa yayi kana yace.

“Allah yasa kuna da ganyen Magarya ko ɗanye ko bushesh-she amma idan akwai ɗanye anfi buƙatar shi”.

Ajiyar zuciya Momy ta sauke kana tace.

“Alhamdulillah akwai ɗanye abayan window na adan kwai bishiyarsa”.

Cikin sauke numfashi yace.

“Toh Alhamdulillah aje atsinko akawo min”.

Cikin sauri ta juya taje ta tsinko ganyen Magarya ta kawo masa tana kawowa ya karɓa kallon Asiya dake kuka yayi kana yace.

“Asiya idan akwai sabon roba mai haske ki kawo min”.

Cikin sauri tace.

“Toh”.

Kana ta shiga kitchen ta ɗauko roba mai ɗan girma karɓa yayi yasa rabin Zam-zam ɗin aciki zama yayi ya Tofa Ayatul Shifaa gaba ɗaya aciki idan ya gama tofawa yasa ganyen Magarya guda bakwai aciki kallon Asiya yayi yace ta kawo masa karamin kofi cikin minti ɗaya ta kawo kofin ruwan addu'ar ya ɗebo ya bawa Amina yace.

“Karɓi kishi”.

Akarkace Amina ta miƙe tare da kauda kai gefe.

Cikin tausasa murya ya sake cewa.

“Karɓi kisha”.

Still juyawa tayi alamar bazata shaba.


Kallon Lamiɗo Man Liman yayi tare da cewa.

”A danneta Abata tasha”.

Cikin takaici Lamiɗo ya girgiza kai kana yace.

“Ta karɓa tasha sai adanneta ai jiki magayi lafiyarta ne ko lafiyanmu”.

Man Liman na gyara alkyabbarsa yace.

“Ayi haƙuri Abata ai sihirin da aka yi mata ne an haɗa mai tafiya da siffar maciji bayin kanta bane bazata sha ɗinba”.

Cikin rauni Asiya ta kalli Lamiɗo tace.

“Ayyah Abba don Allah Abata ”.

Ta ƙare maganar tare da karban kofin ta matsa kusa da Amina.

Amina na ƙoƙarin ture kofin Lamiɗo yayi saurin kama hannayenta kana ya rike kanta Asiya ta ɗura mata ruwan Tofi da ganyen Magaryan tasha mai ɗan yawa amma sauran ya zube.

Ahankali ta fara yin gyatsa lokaci ɗaya jikinta ya saki ta koma ta kwanta kan kujeran atake bacci ya ɗauke ta.


Tana yin Bacci Man Liman ya sauƙe ajiyar zuciya yace.

“Alhamdulillah tunda har tayi bacci in Allah yaso ya yarda zata rabu da abinda ke tare da ita amma wannan yaron da kuka Aura mata ya cika taƙadirin Jahili makirin mutum mushirki”.

Kai Lamiɗo ya girgiza tare kana yace.

“Su suka siyawa kansu”.

Cikin kuka da nadama Hajiya Bunayya ta durƙusa gaban Man Liman tace.

“Dan Allah nima ataimaka min mana abani abinda zansha inji sauƙi atemaka min”.

Kai Man Liman ya gyada yace.

“Ba matsala in Sha Allahu”.

Sai Kuma ya tsiyayi ruwan Zam-zam daban akofi yasa ganyen Magarya aciki yayi mata Tofi kana ya bata yace ta taune ganyen Magarya Zam-zam ɗin shi kai ta gyaɗa kana tayi kamar yanda yace tana gama yi taji kamar fitsari take ji cikin sauri ta nufi bedroom ɗin ta ta wuce Bathroom.


Man Liman kuwa kallon Asiya yayi tare da cewa.

“Idan ta farka wannan ruwan daya rage ta samu tayi wanka dashi awajen da babu najasa”.

Kai Asiya ta gyaɗa tare da faɗin.

“Toh In Sha Allahu”.

Yana kallon Aminan dake bacci yace.

“Kuma in sha Allah akwai tofin da zan mata amma da Zam-zam ɗin ne sai dai zai ɗauke Ni tsawon kwana biyu in sha Allah idan anyi shi in zamu zo daurin Auren su Jameelu zamu zo dashi da izinin Ubangiji zata samu sauki”.

Kai Asiya ta gyaɗa kafin cikin sanyi tace 

“Umman mufa?”.

Ɗan gyara tsayuwar sa yayi kana yace.

“Toh bamu san mai Ubangiji zaiyi ba amma itama in sha Allah muna kyautata zaton Allah zai bata lafiya”.

Cikin sanyi da ɗan jin nutsuwa tace.

“Allah yasa mun gode”.

Nan Lamiɗo da Man Liman da Yah Abba suka fita.

Momy kuwa cikin jin sassauci tace.

“Alhamdulillah Amina ta samu sauki”.

Kai Asiya ta gyaɗa.

Momy kuwa ganin Hajiya Bunayya ta tafi daki yasa tayi zaton sauki ta samu tana kallon Asiya tace.

“Barin tafi ina da baƙi kinsan Hajja Nana nacan” 

Cikin ƙaunarta da sake jinjina kyawun halinta Asiya tace.

“Toh Mun gode”.

Lamiɗo Man Liman da Yah Abba kuwa Side ɗin Lamiɗo suka koma...


Momy na shiga falon Moddibo ya mike kana yace.

“Toh Momy Ni zan wuce”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Toh mun gode”.

Khausar kuwa cikin sanyi ta kallesa kana tace.

“Dan Allah Yah Mu'allim kada ka manta Dr Jameel yazo ya duba Umma”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“In sha Allahu bazan manta ba Minha baza ki rakani bane”.

Kanta ta langwaɓar tare da ƙyafta ƙwayar idanunta ciki nasa sai kuma ta daura hannunta na dama kan ƙafarta tace.

“Ayyah kayi haƙuri baki ɗaya Ƙafafuna rawa suke”.

Lallausan murmushi ya sakar mata tare da motsa laɓɓansa cikin ƙasa da murya yanda ita kaɗai zata ji yace.

“Toh sai nazo da daddare”.

Kallonsa tayi da sauri tace.

“Me kuma za kazo yi da daddare?”.

Yana ɗan lumshe Idanunsa cikin nata yace.

“Bakyaso in kawo Dr Jameel ɗin ne?”.

Ahankali tace.

“Ina so mana”.

Kai ya gyaɗa yana gyara tsayuwar sa yace.

“Toh idan nazo kuma ki shirya zamu tafi tare”.

Langwaɓar da kai tayi tare da faɗin.

“Ayyah Yah Mu'allim ka barni in kwana mana”.

Kai ya girgiza tare da faɗin.

“Bazan iya ba dole fa yau zamu tafi muje mu kwana tare”.

Sake langwaɓar da kai tayi tare da marairaice fuska tace.

“Dan Allah Yah Mu'allim ”.

Cikin sauri ya ɗan tsuke fuska yace.

“Kada ma ki haɗani da Allah ki cuceni”.

Shiru tayi ganin kallon da Momy ke mata me nuni da alamun gargaɗi.

Shi kuwa Modibbo Hajja Nana ya kalla jin tana cewa.

“Idan Allah ya kaimu gobe ko jibi in ba matsala zamu tafi jahar Gombe muje kaga asalin masarautar su Khausar kuna mahaifarta”.

Cikin murmushi Khausar tace.

“Gobe dai zaifi dan Allah Yan Mu'allim kace gobe”.

Kai ya jinjina cike da jin yana son yaje yaga Masarautar su yace.

“Allah ya kaimu goben in ya samu in kuma bai samuba sai jibi, za dai muje kafin ayi bikin”.

Amin suka amsa kana shi kuma ya juya fita.


Yana isa gida kai tsaye Side ɗin su Dr Jameel ya shiga nan yasa masu suna ta maganar abinda za'a yi kasancewar yau  saura kwana huɗu ne ɗaurin Auren kasancewar yau ya kasance Litinin.

Talata Laraba Alhamis juma'a za'a ɗaura Auren.

Nan dai suka cigaba da hiransu.


Acan gidansu Asma'u ma shirye shiryen biki ya kankama.


Alhamdulillah washe gare suka tafi Gombe.

Harda Dr Jameel da Lallai Khadijah da Rahma harda Didi da Innayi da Galadima suka je dan ya gabatar da masarautar su.

Kwana su biyu suka dawo Gembilan.


Alhamdulillah zuwa yanzu Amina ta fara samun sauyi dan yanzu ta daina zare harshenta.


Hajia Bunayya kuwa abu kam sai gaba gaba.

Samira Sani kuwa jin Amina ta samu sauƙine da yadda akayi yasa itama ta zo ta kokawa Momyn kuma Alhamdulillah yau dasuka dawo daga Gombe.

Man Liman yayi mata tofi, ya bata ya bawa Amina.


Alhamdulillah cikin kuɗirar Ubangiji kafin zuwa la'asar Samira ta fahimci zuban ruwan nan ya ragu sosai.

Amina kuwa sosai itama mummurɗewa da jikinta keyi ya fara raguwa.


Nan ya sake yi musu tofi cikin zam-zam ɗin na wasu keɓantattun ayoyi da sauri kamar haka.

*Al-araf ayata 117, 118, 119, 120, 121 da kuma  122.  Sai Suratul Yunus daga ayata 79, 80, 81, 82, Sai kuma suratul Ta-ha aya ta 65 66, 67, 68, 69, 70, Sai kuma suratul al-Kafurune gaba ɗayanta, da kuma suratul al-ikhlas dukanta sai suratul al-falaq itama dua da kuma suratul An-nas itama dukanta  da forko zaki samu zam-zam ki zuba mai yawa a tsabtacecen mazubi ko roba ko kwarya, ki tabbatar zam-zam ɗin zai ishe ki sha da kuma yin wanka, sai zuba a robar kana kisa kanyen magariyar guda bakwai an fison ɗanye Amman busheshenma ba matsala zaki daka guda bakwai in ɗanyen nema ki daka bakwai, sai ki zuba a Zam-zam ɗin kana ki karanta ayoyin Alkur'ani mai tsarkin dana lissafa Miki da surorin ki ɗan motsashi zakiga ya ɗan buga kumfa sai ki ɗiba a cup wanda zakisha ki ƙoshi kuyi gyatsa, sai ki zauna bisa yaƙini da niyar Allah ya yaye Miki matsalarki ko wacce iri yace Sihiri, ko tsafi, Sammu, ko kambun baka, ko cutar da ba'a gane kantaba ko sharrin iska. Kisha koyi hamdala kana ki ɗauki sauran na cikin robar ki samu sarkakekken wurin da babu najasa kiyi niya da duk matsalarki kiyi wanka. Wlh da izinin Ubangiji zakiji sauƙi ki samu sauyi anaso na farko dai kiyishi da Zam-zam inda hali duk bayan wata shida ko shekara ɗaya kiyi kiyiwa yaranki da mijinki dan makarine mai girma in ba hali saboda tsadar da Zam-zam keyi in kinyi na forkon da Zam-zam to na biyu kiyi da ruwan sama na uku da duk ruwan da ya sauwaƙa gareki, inda hali ko yaushe da Zam-zam in ba hali ayi na forkon da Zam-zam in bai samuba ayi da ruwan sama na roƙon da na biyun da na ukun, kiyishi maƙo maƙo ko wata wata ana dai son duk bayan wata shida ko shekara ɗaya kiyi, yar uwa ko ɗanki, ƴarki mijinki ƙanwarki ƴaƴan yar uwa ki ko ɗan uwa duk inda kukaga yaro ko yarinya sun cika rashin ji gagara rawan kai gardama da alamun kwaucewa hanya kuyi masu yanada matuƙar fa'ida da falala, sadakace fisabilillahi idan kinji daɗinshi kiyi niya kiyiwa Mahaifiyata Fatima Dedde na ƙu'huwa ƙafa uku da fatan Allah ya jiƙanta ya kai haske da ni'ima Qabarinta. Ni kuma inada wata buƙata mai girma da falala da daraja a wurin Allah kuyi min addu'a kisa yaranki suyi min addu'a kice su roƙawa Aysha Aliyu Muhammad Garkuwa Allah ya biya mata buƙatarta akan alkhairi, ya raya mata ƴaƴanta Muhammad Jabeer da Maimuna Ikhram da Ibraahim ya shirye su ya basu ilimi mai amfani da albarka yasa su zama abin alfahari ga Musulunci da Musulmai mazan ya basu mata na gari da zuraya ɗaiyi ba, macen ya bata miji na gari da zuri'a ɗaiyiba, kana Allah ya bani wasu ƴaƴan masu albarka da nisan kwana tagwaye inyiwa Deddena takwara da Babana in samu Aliyu Haiydar da Fatima Khausar in samu auta A'isha takwarar kakata mafi soyuwa*


Man Lima  da Hajja Nana ma bayan sunyi sallar la'asar da Baffa Liman da Yah Abba suka kama hanyar komawa Jauro Yaya.


Acan ɓangaren Hajiya Bunayya ma tunda tasha wannan ruwan tofin sai tsutsotsin suka yawaita fita yayin da suke cinta da gasken gaske sai dai tana shiga ruwan ɗumi zai lafa amma bazai wuce awa biyu zuwa uku ba zai sake dawowa haka tayi wannan yinin ranan zunibi da sakayyan aikinta na bibiyarta.


Daddare bayan sallar Isha'i Moddibo ne da Dr Jameel zaune afalon Hajiya Bunayya tana zaune Sai murtsukuku take yi akan kujeran jin yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke zaune gefenta bisa duk kan alamu Alhamdulillah ta fara samun sauƙi har nishinma duk ta daina .

Anutse Dr Jameel ya kalli Hajiya Bunayya kana yace.

“Akwai tests ɗin da za'a Miki.

Sai kiyi ƙoƙari kije asibitu aduba ki acan”.

Cikin sanyi tace .

“Nagode Nagode Dr Jameel Allah ya saka da Alkhairi ”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Bakomai”.

Kana suka miƙe suka fita dai-dai  lokacin kuma Dr Zakariyya da Asiya ne zaune amota suna hira fitowa su Dr Jameel ne yasa Asiya yiwa Dr Zakariyya sallama ta fita kana Dr Jameel ya shiga Motar.


Moddibo kuwa bayan Khausar dake shiga Side ɗin Momy ya nufa yana shiga falon yaga ba kowa sai Raudat dake kallon Catoon yace.

“Raudy ina Addah Khausy?”.

Hankalinta na kan kallon tace.

“Tana ɗakinta”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Momy fa?”.

Still idanunta na kan tv tace.

“Tana gidan Ummin Jameel Yah Haiydar ya kaita”.

Kai ya gyaɗa kana ya shiga ɗakin Khausar zaune ya sameta agaban Weldrop ɗin ta gabanta littafaine tana ta duddubawa.

Da mamaki ta kallesa kana tace.

“Yah Mu'allim har nan kuma?”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Eh ai gidan mune”.

Kai ta gyaɗa hannunta na kan littafin tace.

“Eh nasani ai yanzu in Momy tazo ta same mufa?”.

Murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.

“Eh dai-dai kenan idan Momy tazo ta ganni zata san ina buƙatar matata zata kora min ke mu tafi tun da ke yanzu kin iya gardama da taurin kai ”.


Kanta ta langwaɓar tare da cewa.

“Ayyah Yah Mu'allim ba gardama da taurin kai bane kaga idan mun koma kafin na sake ganin Momy fa zai daɗe ”.

Yana gyara zamansa gefenta yace.

“Amma Ni bakya jin tausayina tunda muka zo fa kike bari na ina rayuwa Ni kadai kamar Maraya Babu kowa  kusa dani”.

Kallonsa tayi tace.

“Yah Mu'allim aima mun kusa komawa dai kayi haƙuri kwana nawa ya rage”.

Ta ƙare maganar tana cigaba da dudduba littattafan sai kuma ta ajiyesu ta gefensa kallon yanda ta hargitsa Littattafan yayi kana yace.

“Me kike nema?”.

Tana cigaba da abinda take tace.

“Wani littafi na nake nema?”.

Da mamaki yace.

“Littafi kuma?”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Eh”.

Kamar mai raɗa ya sake matsawa kusa da ita yace.

“Toh me zakiyi dashi?”.

Kanta na kan tulin littattafan tace.

“Wani abu ne aciki?".

Da mamaki yace.

“Wani abu ne kuma aciki?,ki bari gobe sai ki duba”.

Kai ta girgiza tare da faɗin.

“Ina so ne in tabbatar yana nan ko baya nan saboda da nazo na samu Raudat tana wasa takarduna da jakar makarantana ta bubbuɗe min ban sani ba ko ta jefar min da littafin ”.

Cikin mamakin yanda take neman littafin yace 

“Toh littafin na wani Subjects ne?”.

Tana ɗan tura baki tace.

“Um-um fa littafin bana karatu bane?”.

Yana ɗan ƙara matsota yace.

“Ikon Allah toh littafin na menene?”.

Ya ƙare maganar yana dudduba littattafan data tutturo gefensa yayin da take sake zaro na cikin jakar ganin basu cikine yasa ta jawo durowan ƙasan Weldrop ɗin tare da cewa.

”Toh ban sani ba bari in duba ko suna cikin nan ne”.

Dai-dai lokacin yaga wani note Book An rubuta *SPECIAL MAN* da manyan baƙi Aransa ya maimaita Special Man ahankali ya jawo littafin yana ɗan jujjuyawa Khausar kuwa baki ɗaya hankalin ta na cikin durowan Weldrop ɗin.

Ahankali ya buɗe shafin farko na littafin.

ga mamakinsa sai yaga Drawing ɗin hoton fuskarsa ne rauɗau ba abinda aka bari har sajensa.

Cikin tarin wani irin mamaki al,ajabi da kuma kaɗuwa ya kalli gefen shafin.

A gefen kuwa Drawing ɗin fuskarsa ne acikin aji hannunsa na kan Black board kamar yana rubutu cikin sauri ya kalli rubutun da akayi da kalo wanda akayi musu design yanda ya kasance na musamman haka sunansa ya kasance na Musamman _Aliyu Youseef Mohammed Mouley (Moddibo)_

 da mamaki ya kalli inda aka rubuta sunansa anyi zanen ❤️ sai kuma ya maida idanunsa inda akayi Drawing ɗin fuskarsa yaga date and time ɗin da akayi rubutun Drawings ɗin.

Idanunsa ya jujjuya ya kalleta amma baki ɗaya hankalinta na kan tarin himilin sauran littafan.

Kallonsa ya mayar kan date ɗin idan har baiyi kuskure ba toh shekaru huɗu kenan ranan dasu Khausar suka fara zuwa SS3 cikin mamaki da wani irin yanayi ya buɗe page ɗin gaba sai yaga Drawing ɗin Fuskarsa ne amma ba'a fitar da fuskan sosai ba sai sajensa aƙasan ta rubuta.

_One's if I remember your face, my actionable will be change to cool,  is your Breed brightly my heart always yo be sunshine , i really love you with deep voice. Uncle Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_

Ahankali ya motsa laɓɓansa ya furta.

“Ya salam”.

Wani irin amintaccen numfashi ya fesar saboda jin kalaman suna Barka duk kan lakar jikinsa.

Fahimtar da yayi baki ɗaya littafin kamar akansa yake magana haka nan yaji wani abu yana sauƙa tun daga ƙwaƙwalwar kansa har zuwa babban yatsarsa a iya shafi biyu daya buɗe ya fuskanci gaba ɗaya Khausar ta rayune da soyayyar shi acikin zuciyarta shi kansa baisan meyesa ba ya dai tsinci kansa da naɗe takardan yasa cikin aljihunsa.

 tare juyawa yayi mata wani amintaccen rugguma yana mai kallonta yace.

“Wai wani littafi kike nema ne?”

Batare data kallesa ba tace.

“Wani Littafina ne na musamman, nasan da wuya in Raudat bata ɓatar min da shiba dan haka taɓatar min da ɗan uwanshi da Nai ta rubutawa tun daga JSS one to 3”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Ko dai Diary kine?”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“Kusan haka amma shi babban littafine ai yama fi Diary daraja awajena”.

Gira daya ya dage tare da faɗin.

“Toh tashi mu tafi da safe sai muzo na tayaki dubawa”.

Kai ta langwaɓar kana tace.

“Allah ina so ba mamaki yanzu Raudat ta ɓatar min dashi. In dai ta baddashi wlh sai na daketa dan yana tunamin abubuwa da yawa a rayuwata”.

Kai ya girgiza tare da faɗin.

“In sha Allah ma bai ɓata ba kada ki damu kizo mu tafi da safe za'a zo mu duba”.

Ya ƙare maganar da ƙaguwar so yake ya ga su ƙeɓe daga shi sai ita.

Kai ta girgiza tana cigaba da hautsina littattafan tace.

“Um-um.ni dai ina son gani ”.

Fuska ya tsuke tare da cewa.

“Mu tafi nace ko?”.

Ganin yanda ya tsuke fuska yasa ta gyaɗa kai tare da faɗin.

“Toh”.

Kana tattare littafan ta mayar cikin drawer.

Hannunta ya jawo ya riƙe kana ya kalli gyalen jikinta ganin babu laifi yasa yace.

“Mu tafi toh”.

Suna fita motarsu Dr Jameel na fita agidan motarsu suka shiga kana suka tafi gida.


Suna shiga Falonsu ya rufe ƙofan kana ya ɓalle botir ɗin wuyan rigarsa ya zare ya ajiye kana ya jawota jikinsa ya rungumeta ajikinsa cikin sanyi ya kai bakinsa saitin kunnenta kana ya shiga raɗa mata abinda ta rubuta yana cewa.

“ _One's if I remember your face, my actionable will be change to cool,  is your Breed brightly my heart always you be sunshine , i really love you with deep voice Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_”

Cikin sauri ta ɗaga ido ta kallesa tare da wani irin fiddo idanun duka tamkar zasu faɗo ƙasa, ido ɗaya ya kashe mata kana yace.

“Tukuocin soyayyar da kike min nake son baki a daren yau”.

Baki ta tura tare da kwaɓe fuska kana tace.

“Waye ɗin?”.

Ido ya kashe mata tare da cewa.

“Keɗin mana”.

Ɗan ware idanunta tayi akansa kana tace.

“Kamarya tukuicin soyayyar da nake maka kuma?”.

Ta ƙare maganar cikin kunya da son waskewa.

Cikin wani irin yanayi yace.

“Shekara nawa kika yi kina dakon soyayyata azuciyarki?”.

Kallonsa tayi da mamaki sai kuma ta lumshe Idanunta tace.

“Kamarya kuma nayi dakon soyayyar ka azuciyata?”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Littafin da kike nema yana hannuna fa?”

Still kallonsa tayi tace.

“Wani littafi kuma?”.

Ɗan murmushi yayi kana ya hura mata sanyayyar iskan bakinsa yace.

“Littafinki da kike nema”.

Littafin ya zaro acikin rigarsa ya nuna mata cikin mamaki ta kallesa kafin tace.

“Yaushe ka ganshi?”.

Dariya yayi tare da cewa.

“Tun ɗazu har na karanta shi ma”.

Da sauri ta kife kanta akan ƙirjinsa cike da kunya murmushi yayi kana ya shiga tura yatsunsa ƙasan ƙafarta jin haka yasa ta ɗaura ƙafanta kan rumfar ƙafansa.

 A hankali ya fara tafiya da ita har suka isa bedroom.

Cikin sanyi ya kwantar da ita akan gado.

Kana yayi kissing ɗin goshinta da lips ɗin ta ahankali ya fara cire mata rigarta cikin wata kasalalliyar murya yace.

“Khausar da shin da gaske kina min soyayyar da baza ki iya furta min ita abaki ba Khausar?Meyesa baza ki faɗa min ba inji sanyi raina sai kiyita dakon soyayyata tsawon shekaru meyesa baki faɗa min ba meyesa baki nuna min ba? Da gaske kece kika rubuta littafin nan”.

Ahankali taja numfashi mai tsawo hannunta na cikin sumar kansa tana shafawa kana manyan yatsunta guda biyu na kan sajensa tace.

“Ni ba ni na rubuta ba.

Haka kawai ka'ida basona kake ba kalen ince ina sonka ka kashe ni?”.

Cikin sauƙe numfashi ya gyara ta ajikinsa tare da cewa.

“Wayace miki bana sonki? Minha”.

Idanunta ta lumshe zuciyarta na bugawa tace.

“Nasan baka soma kuma nima ba nice na rubutaba”.

Yana shafa sumar kanta yace.

“To amma tunda ke kina sona ai da kin faɗa min munyi ta cutar da juna tsawon lokaci?,bamu sani ba”.

Muryan cike da sanyi ta ɗan cije  gefen bakinta tace.

”Ni dai bance ina son wanda baisona”.

Saurin girgiza mata kai yayi tare da faɗin.

“Ki daina cewa bana sonki Minha”.

Sai kuma ya shiga romance ɗin ta yana shafa saman Breast ɗin ya cigaba da cewa.

“Kinsan dalilin zamana aƙasan nan kuwa?

Naƙi na koma Jami'atul Madina nayi aikin dana samune saboda ke tun lokacin dana fara sauke idanuna akan ki Allah ya jarabceni da sonki na soki alokacin da bakisan kanki ba Minha”.

Da wani irin sauri mai nuni da zallan farin ciki Khausar ta tallofo kansa tana kissing ɗin dogon hancinsa cikin kasala da shauƙi kana da yanayin da yake ji yaci gaba da cewa. 

“Sanadinki na zauna anan nasoki soyayyar da bazan iya yiwa kaina ba duk Drawing da kike yi na ki wasa ne ni duk wani motsin da kikayi a duniya idan na dawo sai nayi Drawing ɗin sa na ajiye babu abinda yake sani farin cikin gani a duniya kamar fure da kuma ke saboda furanni kansu kin fisu kyau sai dai suna ɗebi min kyewar rashin ganinki ne, kana suna cike min gurbin kallonki”.

Cikin mamaki Khausar ta ɗago ta kallesa ido cikin ido tace.

“Yah Mu'allim kenan kana sona da gaske?”.

Kai ya jinjina tare da faɗin.

“Minha ina sonki son da bansan adadinsa ba nayi Miki son da ba yiwa kowacce ƴa mace irinsa a duniya ba”.

Sai kuma ya miƙe da sauri, ya buɗe durowar dake jikin gadonshi, wasu manyan takardu masu kana da kalandu ya ja, a kan kadon ya zubasu.

Da sauri ta zubawa na forkon idanu.

Sai kuma ta kalleshi domin ta tuno yanayin da suka kasance a cikin mota a ranar daya rage mata hanya.

Da sauri yaja mata na ƙasashi.

Wani irin murmushin ne ya subce mata ganin zanenta tana rawa a gaban motarsu ranar da suka haɗu gidan Ummi.

Baki ta turo ganin na ƙasanshi ranar da take kakkaɓe ɗan kwali ne sai kuma wani da bazata manceba na ranar data fara ganinshine da ta tsaya tana kallonshi harda karkata wuya ranar da ta fara zuwa JSS one kenan sai kuma wanda ta diƙo kan bishiyar ranar da suka zo da Asma'u sai wanda suka haɗu a rugar Jauro yaya.

Ya Salam sai kuma wasu wanda bisa alamun nashine da Yah Jameel.

Kawai sai ta faɗa jikinsa.

Ture takardun yayi tare da ruggumeta da kyau.


Kanta ta kwanta ajikinsa tana jin yanda hannunsa ke yawo a sassan jikinta tace.

“Amma kuma Yah Mu'allim kullum dukana kake yi ya za'a yi na yarda dagaske cewa kana sona”.

Yana sakin ajiyar zuciya yace.

“Dole ne yasa nake Miki wannan yanayin saboda na fahimci kamar J yana sonki so kuma irin na aure”.

Saurin kallonsa tayi ya jinjina mata kai yana cigaba da cewa.

“A duniya ban taɓa son abu J yaƙi shiba.

Kana J bai taɓa son abu naƙi shiba sai nazo na fahimci akan mace ma zamuyi tarayya akan soyayya kuma hakan zai zame mana masufa a amintakarmun shiyasa nasawa raina hantarar ki da nisantarki da ƙin kasancewa kusa dake saboda in yakice ki azuciyata J ya mallake ki dan nayi alkawarin mace bata isa ta shiga tsakanin amintakarmu ba”.

Idanunta ta lumshe tana jin wani irin ƙaunarsa na huda duk wani magudanan jinin jikinta ahankali ya cigaba da cewa.

“Abinda J ya faɗa min kenan a voice ɗin sa na ƙarshe yace min ya fahimci ina sonki yamin voice da ace alokacin yana raye zance J ai kaima kana sonta amma tun a voice ɗin yace min kana tunanin kamar ina son Khausar ko? Shiyasa kake hantararta dan ka yakiceta a zuciyarka.

Wai sabida zaka bar min ita ko?.

To ni ba sonta nake ina taya ka son abinda kake sone A.J ka Aureta dan naga zanenta da kayi a takardu, in su ka ɓoyesu shin zaka ita ɓoye na zuciyarta da ƙwaƙwalwar kane, AJ. Ka aureta. abinda J ya faɗa min Kenan ”.

Duk da nasan ya faɗane kawai Amman J ya soki Minha ya soki irin so na aure ashe ya gane ina sonki”.

Idanu ta tsira masa kana tace.

“Dagaske Yah Mu'allim?”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Sosai ma”.

Daga nan ya cigaba da romance ɗin ta ya dauki Kimanin minti arba'in da biyar akanta kafin ya jawota ya rungumeta yana sa mata albarka tare da cewa.

“Alhamdulillah ashe son da nake baso bane soyayya ce?”.

Tana sauƙe Ajiyar zuciya tace.

“Kamar ya?”.

Murmushi yayi tare da faɗin.

“Eh so na gefe ɗaya shi ake cewa so amma tunda kema kina sona kinga soyayya ce”.

Sake shiga jikinsa tayi kana tace.

“Dagaske Yah Mu'allim maganar daka ke faɗa?".

Cikin tabbarwa yace.

“Ki daina kokonto Minha Vidaa Ana uhubbuki kubban axeem”.

Wani irin farin cikine mara misaltawa ya mamaye gaba ɗaya ilahirin zuciyarta.

Awannan daren haka suka kwana cikin farin ciki da kwanciyar hankali...


Alhamdulillah haka rayuwa ta cigaba da tafiya ranan Alhamis akayi walima ranan juma'a aka ɗaura auren.


 Malam Liman da yazo ɗaurin Aure ya kawowa Amina da Samira magani da yayi alƙawar kamar yanda ya faɗa zuwa yanzu Alhamdulillah jikinu da sauƙi amma dan Amina har abinci takeci.

Samira kuwa ruwan ya rage zuba sosai a wuni haifi sau uku zai zuboba.


 Hajiya Bunayya kam abin nata babu sauƙi kullum gaba-gaba yake.


A ranan jumma'a akayi Dinner mai rai da lafi.


Alhamdulillah ranar Litinin sufa dawo Adamawa da amarensu Zakariya da Aseeya Asma'u  Da Dr Jameel Dija Yah Ali Su Didi sunje har falon bappa Jimeta.


Washe gari talata jirginsu ya ɗaga zuwa Morocco.

Misalin ƙarfe 2:00pm suka sauƙa acikin Morocco anan suka samu motoci daga Masarautar Mouley na jiransu suka shish-shiga kana suka tafi motocin ajere ajere suke tafiya a sai da sukayi nisa Khausar taga motarsu ta fita cikin sauran tawagar motocin ahankali ta kalli Moddibo dake gefenta kana tace.

“Yah Mu'allim ya naga su sunyi can mu munyi nan?”.

Yana ɗan shafa cikinta yace.

“Gida zamu tafi”.

Idanunta ta zare kana ta langwaɓar da kai tace.

“Yah Mu'allim gida kuma?

Baza muje inga gidansu ba? Ai kamata inyiwa Asma'u rakiya aminiyata fa”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Za kije amma ba yau ba sai kin huta”.

Kai ta gyaɗa direct motarsu Masarautar Mouley ta nufa.

Yayin da Amare aka wuce dasu gidajen su batare da rakiyan kowa ba daga Nigeria kasancewar ga Didi da Innayi sun sai Goggo Asma'u ta wadatar dan a cewarsu ai Asiya ga Khausar dijama ga Khausar ga Yah Abbanta.


Khausar kuwa suna isa abinci suka ci kasancewar an shirya musu komai kana ko wanne yayi wanka ya kwanta dan huce gajiya.



Bayan kwana biyu Moddibo ne zaune akan sallaya gabansa ɗauke da starm da Kur'ani ke kai, bayan ya dawo daga sallar Asbah yayin da Khausar ke gefensa ahankali ta ɗago kanta jin ringing ɗin wayarta kallon Moddibo tayi kasancewar ya fita kusa da wayar da ido ta mishi alamar ya dai wake kira?.

Juyawa yayi kana ya kalli screen ɗin wayar sai kuma ya kalleta yace.

“Asma'u ce”.

Da ɗan sauri ta miƙe ta karɓi wayar tare da amsawa takai kunnenta tare da cewa.

“Hello Besty na kiyi haƙuri laifin yayanki ne. Yah Mu'allim ne ya hanani zuwa wai in barku ku gurji amarc...

Sai kuma tayi shiru ba tare da ta ƙarasa mgnar ba, sabida jin muryan Asma'u a disashe kana yayi sanyi alamun taci kuka ta godewa Allah cikin raunin murya tace.

“Khausar”.

Da damuwa Khausar ta ɗan jingina bayanta da kafaɗar Moddibo kana tace.

“Subhanallah Asma'u meke faruwa”.

Cikin rauni da zubda hawaye Asma'u tace.

“Khausar zan mutu dan Allah ki cewa Yah Mudibbo kuzo ki ɗaukenu, wannan mutumin mungu ne ya kasheni ”.

Dariya mai sauti Khausar ta fashe dashi har tana ɗan bubbuga kanta da jikin kafaɗar Moddibo kana tace.

“Ya kashe ki kuma kike magana?”.....

Post a Comment

0 Comments