TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

SAKAYYAH page 69

 A kan ƙafafunsa ya durƙusa ya zama na kansa na dai-dai kan cikinta ahankali ya dafa cikin, cikin amintacciyar murya mai ɗauke da nutsuwa da tarin kulawa ya fara yi mata addu'a na tsawon minti bakwai sai kuma ya ɗago ya kalleta ita ɗin ma shi take kallo muryansa ɗauke da Amintaccen kulawa da jin ƙai yace.

“Minha Viddaa meke damunki?”.

Numfashi ta fesar kana ta girgiza kai tare da cewa.

“Bakomai fa”.

Juyawa yayi ya kalli Asma'u dake kallon Khausar cike da tausayi yace.

“Asma'u menene matsalar ta?”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin.

“Yah Moddibo daga zuwa na zuwa yanzu fa tashiga ban ɗaki yakai ƙafa bakwai tana fitsari”.

Da sauri ya kalleta kana yace.

 “Ba abinda yake Miki ciwo?”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Yah Mu'allim nifa ba abinda ke min ciwo”.

Da damuwa asaman fuskarsa yace.

“Toh ba abinda kikeji?”.

Kai ta gyaɗa tare da cewa.

“Wallahi ba abinda ke min ciwo”.

Yana cigaba da massage ɗin ƙafanta yace.

“Yanzu kuma Dr Jameel ya kirani yace muje asibiti”.

Langwaɓar da kai tayi tare d cewa.

“Nifa ba abinda ke yimin ciwo Yah Mu'allim ai da akwai zan faɗa muku amma wallahi babu?”.

Numfashi ya fesar kana yace.

“Toh amma dai bari na sanarwar Didi halin da ake ciki”.

Ganin yanda ya damu yasa ta gyaɗa masa kai tace.

“Toh shikenan ba laifi kaje ka faɗawa Didi”.

Dai-dai lokacin kuma wayar Asma'u ta hau ruri ahankali Asma'u ta ɗauka ganin Ummi yasa tayi saurin Picking ta kai kunnenta suka gaisa da Ummi sai kuma taji kamar muryan Momy tana gyara zamanta tace.

“A'a Ummu ina kike?”.

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

“Ina gidan Momyn Khausar ne na kwana biyu banji labarinta bane shine nazo kuma dana zo ma muke ta hiranku sai nace bari in kira ku inji Labarin ku”.

Murmushi Asma'u tayi kana tace.

“Nima kuma yau ina gidan Khausar ce ki bawa Momy wayar”.

Wayar Ummi ta bawa Momy suka gaisa Ahankali momy tace.

“Ya dai Asma'u ya jikin Ƙawar taki lafiya ko?”.

Kallon Khausar dake lumshe Idanu Asma'u tayi tare da cewa.

“Momy lafiya lau sai dai yau tunda gari ya waye take ta yawan fitsari dai take tayi banfi awa biyu da zuwaba fa, amma tayi fitsari yakai sau bakwai”.

Ahankali Momy tace.

“Ikon Allah toh kuje asibiti mana”.

Tana gyara zaman wayar akunnenta tace.

“Eh na kira Dr na faɗa masa yace dai yanzu babu wata matsala tunda Babu abinda yake mata ciwo amma Yah Moddibo yace zai je ya faɗawa Didi yaji mai zata ce”.

Cikin sauƙe Ajiyar zuciya da fargaba irin na duk wata Uwa ke shiga idan ƴarta na fama da ƙaratowan naƙudan tsohon ciki tace.

“Ikon Allah toh bata wayar”.

Wayar Asma'u ta miƙa mata karɓa Khausar tayi tare da faɗin.

“Momy ya gajiya?”.

Cikin sanyi Momy tace.

“Lafiya lau Khausar meke ke damunki?”.

Langwaɓar da kai tayi tace.

“Momy Nifa ba abinda ke yimin ciwo”.

Ahankali tace.

“Toh amma kuma iya fitsarin kike?”.

Kai ta gyada kana ta ɗaura hannunta ɗaya akan cikin tace.

“Eh fitsarin ne kawai sai dai yanzu dana shiga ina ganin har da wani ruwa yake fito min”.

“Ok ki faɗawa Dr toh”.

Cewar Momy suka katse kiran.

Dai-dai lokacin kuma Moddibo ya shigo bayansa Didi,Niyna Innayi ce ke biye dashi abaya cikin sauri Didi ta zauna kusa da ita hakan yasa Asma'u ta ɗan matsa gefe tace.

“Ɗiyata me yake damunki?,Ba abinda yake Miki ciwo?”.

Kai ta girgiza tare da faɗin.

“A'a abinda yake min ciwo”.

Cike da kulawa Didi tace.

“Duk da haka dai mu tafi asibiti”.

Kai Khausar ta gyaɗa.


 Nan take suka tafi asibiti kafin su isa ma Already an shirya komai.

Suna isa aka karɓesu aka shirya komai kana akayi duk kan abinda ya kama na gwaje-gwaje.

Bayan an gama gwaje-gwaje Dr Jameel ya fito zuwa lokacin kuma  ruwan dake zuban nan zubansa ya ƙaru sosai shigowa yayi kana ya kalli Niyna ya kalli Didi kallonsa Didi tayi kana ta miƙe tabi bayansa zuwa office ɗin sa tace.

“Jameel ya akayi?”.

Ƙofan ya ɗan tura tare da zama kan kujera kana ta zauna gefe sai kuma Moddibo dake biye dasu yazo ya zauna gefen Didi gyaran murya Dr Jameel yayi tare da kallon Didi yace.

“Kinga Didi tun cikin nan yana da wata bakwai munyi  Sikaynin komai lafiya sannan ko kwanan nan bai daɗe ba still munyi Sikaynin komai lafiya”.

Cikin bugawar zuciya Moddibo ke kallonsa cikin sauƙe numfashi ya cigaba da cewa.

“Kuma ko yanzu ma Alhamdulillah zaman yaro lafiya to Amma kuma kinga yanzu ruwa yana ta zuba mata kuma ba alamun naƙuda tare da ita”.

Numfashi Didi ta sauƙe tare da cewa.

“A wannan Normal ne in dai wannan ne ruwan zaƙine”.

Kai Dr Jameel ya jinjina kana yace.

“Eh nima ina ga kamar Normal ne?”.

Cike da gamsuwa ta gyaɗa masa kai tare da faɗin.

“Eh dan nima wani lokaci yana kai kusan sati kafin naƙuda yazo ya tashi idan na ƙuda ya tashi kuma baya wuce awa ɗaya ko biyu shikenan na haihu”.

Cikin rauni da tarin tausayi Moddibo ya juya ya kalleta yace.

“Didi Amma ba matsala?”.

Kai ta gyada tare da cewa.

“In sha Allahu ba matsala wannan ana ce mishi zaƙi zaƙine yake zuba”.

Numfashi Dr Jameel ya fesar kana yace.

“For now dai zaƙine yake zuba amma yanzu zaku tafi gida, tunda ba haihuwar bane amma kullum da daddare kafin ku kwanta azo in duba ta saboda kada ruwan ya canza ya zama wanda yaro ke rayuwa a cikine ke zuba, amma for now ba matsala”.

Hararansa Moddibo yayi tare da faɗin.

“Toh munji”.

Murmushi Dr Jameel yayi tare da cewa.

“Ha'a Yayanmu laifin me nayi kuma?”.

Murmushi Didi tayi daga nan dai suka tattara suka koma gida.

Haka Khausar suka yini da Asma'u sai dai har zuwa lokacin ruwan nata zuba sai dai ba sosai yake zuba ba, da daddare  bayan sunje asibiti Dr Eshaa ce ta duba ta tace in sha Allah babu wata matsalar komai kuma ba haihuwa bace...


Kwance Khausar take agefen Moddibo yayin da hannunsa ke kan cikinta yana tofa mata addu'oi.

Ahankali ta juya ta kallesa tare da cewa.

“Yah Mu'allim!”.

Idanunsa dake lumshe ya buɗe kana yace.

“Na'am Minha ya akayi?meke damunki meke kiki ciwo”.

Ya ƙare maganar cikin tsananin kulawa, tausayi, jin ƙai.

Kai ta girgiza tare da faɗin.

“Babu abinda ke yimin ciwo amma Yah Mu'allim dan Allah don darajar Annabi ka cewa Momyna tazo mana”.

Cikin sauri ya miƙe ya zauna ya kalleta  tare da cewa.

“Meyesa kika ce haka Minha?”.

Kai ta girgiza asanyaye tace.

“Ni dai kawai nafi so Momyna tazo ina son ganinta kaga bata taɓa zuwa ba kuma ina so in na haihu tazo  kaga ga abin na zuba kuma Dr Jameel yace in sha Allah nan da sati ɗaya zan haihu kaga ai tazo yafi”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Amma dai ba abinda yake Miki ciwo ko?”.

Tana riƙe tafin hannunsa acikin nata tace.

“Um bakomai kawai ina so Momyna tazo kuma dan Allah in zata zo taxo min da Raudhat in yaso in na haihu kafin suna Hajja Nana ma tazo kaji ko Yah Mu'allim”.

Cikin sanyi yace.

“An gama Minha in Sha Allahu Momy za tazo”.

Cikin jin daɗi tace.

“Yaushe za'a faɗa mata?”.

Kallon haɗeɗɗen agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi ganin 10pm yayi ya sanya shi sauƙe numfashi yace.

“Kinga karfe goma tayi sai gobe zan faɗa mata”.

Marairaice fuska tayi tare da cewa.

“Um-um Yah Mu'allim a faɗa mata yanzu mana”.

Kai ya girgiza kana yace.

“Minha idan na faɗa mata yanzu kinga dai lafiyarki lau, toh Amman in taji zatayi zaton baki da lafiya ne karshe muzo mu hanata bacci”.

Idanunta ta narkar acikin nasa tare da cewa..

“A'a Yah Mu'allim baza ta tsorata ba ai zanyi waya da ita zata fahimta”.

Sake kallon agogo yayi yace.

“Mu dai bari har sai da safe”.

Kamar za tayi kuka tace.

“Ni dai Um-um mu faɗa mata yanzu”.

Ganin yanda ta damu yasa yace.

“Toh shikenan”.

Ya ƙarashe Maganar tare da ɗaukar wayarsa yayi dearlin number mommy.


    A can Nigeria kuwa dai-dai lokacin Momy ce tare da Amina zaune a falonta cikin sanyi Amina tace.

“Momy kinji ɗazu an kirani ko?”.

Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa.

“Eh Amina naji".

Cikin fesar da numfashi da kuma yanda nutsuwa da nadama ya baibaye rayuwarta tace.

“Kin san waye ne ya kirani”.

Cikin sanyi gami da rauni ta gyara zamanta tare da faɗin.

“Baban Samira Sani ne fa yazo wajena”.

Da mamaki Momy tace.

“Kai haba dai?”.

Araunane ta gyaɗa kanta tare da cewa.

“Wallahi”.

Ajiyar zuciya Momy ta sauke tace.

“Lafiya dai?”.

Kanta ta sunkuyar ƙasa idanunta na ciko da ruwan hawaye tace.

“Wai cewa yayi yana sona zai Aureni”.

Shiru Momy tayi kana ta ronƙofar da kanta kafin sai kuma ta ɗago kanta ta kalleta.

Amina kuwa cikin sanyi ta cigaba da cewa.

“Momy nikam kuma da zama hakan nan tunda ya sanni kawai zan Aureshi kawai yafi min tunda tuntuni na gama iddah kuma babu wanda yake zuwa wajena”.

Cike da tausayinta Momy tace.

“In dai har kin gamsu kinga zaki Aureshi ai babu laifi, tunda dama mun sanshi mutum ne mai mutunci da kamala da daraja”.

Tana wasa da yatsun hannunta tace.

“Hakane kam Momy kuma ma kinga ya bada hujjan cewa zamu zauna cikin aminci, tunda dama nida Samira mun saba zanje in zauna in maye mata gurbin Mahaifiyarta sannan kuma muyita mata addu'a Allah ya fito mata da mijin Aure na Alkhairi ”.

Kai Momy ta jinjina cike da gamsuwa tace.

“Toh shikenan Amina Allah ya tabbatar da abinda yafi Alkhairi ”.

Ahankali tace.

“Dama shine nace bari na faɗa Miki saboda ki faɗawa Abbana, nikam na yarda shiɗin in Aureshi dama Momy Ni yanzu waye zai kalleni ya Aureni in ba tsohon ba?”.

Cikin kwantar mata da hankali Momy ta ɗan muskuta tare da cewa.

“Bakomai Amina in  Sha Allahu zan faɗawa Abbanku Allah kuma ya sanya Alkhairi kuma ai mutum ne mai mutunci”.

Cikin sanyi Amina tace.

“Ameen ya Allah”.

Suna cikin hiran ne kira ya shigo wayarta da mamaki tace.

 “Toh Moddibo kuma”.

Sai kuma ta amsa kiran ta kai kunnenta tare da faɗin.

“Assalamu Alaikum ”.

Anutse Moddibo yace.

“Wa'alaikum Salam Barka da dare Momy kina bacci na tashe ki ko?”.

Murmushi tayi tare da faɗin.

“A'a idona biyu muna hira da Amina ce ma”.

Kai ya gyaɗa yana shafa cikin Khausar yace.

“Masha Allah”.

Sai kuma yayi shiru cike da kulawa tace.

“Lafiya  kuwa Moddibo?,Me yake faruwa faɗa min mana?”.

Kansa ya sunkuyar ƙasa tare da ɗagowa ya kalli Khausar sai kuma ya maida hankalinsa kan wayar yace.

“Momy Khausar ce kin san yau tun da safe”.

Sai kuma yayi shiru ya rasa ta ina zai fadi maganar.

Ganin haka ne yasa Khausar ta karɓi wayar tasa akunnenta tare da faɗin.

“Momy”.

Cikin sauƙe ajiyar zuciya Momy tace.

“Na'am Mamana lafiya kuwa?”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Lafiya lau Momy?”.

Tana ɗan jingina da jikin kushin momy tace.

”Toh me yake faruwa?”.

Tana gyara zamanta tace.

“Bakomai fa Momy  kinga yau munje asibiti an duba ance ba matsalar komai, kuma in sha Allahu nan da sati ɗaya ko kwana biyar zan haihu shiyasa nake so ki tambayi Abba in ya barki kizo”.

Da damuwa Momy tace .

“Amma dai kin tabbatar Babu komai”.

Idanunta ta lumshe tare da buɗe su akansa tace.

“Allah Momy ba komai kawai dai ina so kizo ne kuma dan Allah Momy kizo da Raudhat yanzu ki tura mana hoton Passport ɗinki amiki booking”.

Murmushi Momy tayi tare da cewa.

“Da gaggawa haka Mamana?,Ba dai abinda kike ji?”.

Kai ta gyaɗa tare da faɗin.

“Bafa abinda nake ji” 

Cikin ɗan radaɗine Mommy tace.

“Ok toh shikenan zan faɗawa Abbanku idan ya amince zanzo, tunda ga Amina da sauƙi zata zauna da ƙannen ku kafin mu dawo”.

Tana ɗan lumshe Idanunta tace.

“Toh shikenan Momy ina Aminan?,Ki bata mu gaisa”.

Momy na ƙoƙarin miƙa wa Amina wayar tace.

“Gata nan”.

Jin Amina ta karɓi wayar Khausar tace.

“Amina ina yini”.

Asanyaye Amina tace.

“Lafiya Khausar ya gida ya labarin Addah Asiya ”.

Khausar na jinginar da kanta kafadarta Moddibo tace.

“Munyi waya ma tace kwanan nan zasu zo hutu akwai bikin abokinsa da za'a yi zasu zo”.

Ahankali Amina ta gyara zaman wayar akunnenta tare da cewa.

“Allah ya kawo su lafiya ya jiki?”.

“Alhamdulillah”.

Cewar Khausar tana lunshe idanu.

Cike da kulawa Amina tace.

“Toh Allah ya raba lafiya”.

Daga nan sukayi sallama.

Nan take Momy ta mike taje ta faɗawa Lamiɗo ba gardama Lamiɗo ya amince tare da yi mata fatan Alkhairi kana ya fara yi mata booking ɗin tafiya cikin ikon Allah ya ga nan da kwana huɗu akwai jirgin da zai tashi daga Abuja zuwa Morocco direct cikin Rabat zai sauƙa nan take yayi mata komai da komai a online kasancewar ranan juma'a ce kuma jirginsu zai tashi ranan Laraba


Ranan Lahadi da yamma Khausar da Moddibo ne zaune a Falon Didi suna hira Ahankali ta yunƙura ta miƙe jin kamar tana jin fitsari ta nufi bedroom ɗin Rahama cak ta tsaya tare da juyawa ta kalli Didi dake cewa.

“Ha'a lafiya?”.

Ganin wani ruwa daya tsinko mata yake bin ƙafafunta cikin sauri Moddibo ya matso kusa dasu tare da cewa.

“Lafiya?”.

Kallon Didi tayi kana ta kalli Innayi sai kuma ta maida kallonta kan Moddibo da damuwa ya bayyana asaman fuskarsa Ahankali tace.

“Nima ban sani ba”.

Cikin wani irin yanayi Moddibo yace.

“Ya salam”.

Ganin yanda ruwan ke gudu akasa cikin sauri Didi tace.

“Ɗaukwta mu tafi asibiti” 

Da sauri ya ɗauketa ya sata Amota Didi na gidan gaba tare da Ibraahim dake mazaunin Driver sai kuma Moddibo dake rungume da Khausar baya.

Sai kuma ɗaya motar da hadimai ne aciki sai Innayi da Niyna da kuma jakadiya direct suka nufi asibiti.


Bayan anyi mata gwaje-gwaje bayan wani lokaci Dr Eshaa ta fito tare da Kiran Didi bayanta Didi tabi cikin sauri Moddibo yabi bayanta yana cewa.

“Dr Lafiya meke faruwa?”.

Zama tayi akan kujeranta tare da kallon Moddibo sai kuma ta kalli Didi tace.

“Toh gaskiya da farko dai ba muyi tunanin haihuwar Nan zai zo da gardama haka ba saboda komai naga da baby lafiya lau Toh amma kuma daga ɗazu zuwa yanzu ruwan da yaro yake rayuwa aciki ne yake zubowa wanda kwata-kwata naƙuda bai tashi ba bare ta iya haihuwa dole sai an nata C'S”.

Cikin sauri gami da wani irin azabebben bugawan zuciya Moddibo ya dafe kansa tare da cewa.

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Theater Kuma?".

Cikin sauri da son kwantar masa da hankali Dr Eshaa tace.

“Bakomai fa ai Theater ba wani abu na tashin hankali ko kiɗima bane”.

Still hannunsa na dafe da kansa yace.

”Allah ko?”.

Kai ta jinjina cikin tabbarwa tace.

“In sha Allahu bakomai babu abinda zai faru sai alkhairi wasu ma da yawa basu bari suyi naƙuda kawai sai ayi musu Theater”.

Cikin sauri da damuwa Didi tace.

“Toh yanzu yaushe za'a Theater?”.

Juyawa tayi ta kalli agogon hannunta kana ta maida kallonta kan Dr Jameel dake shigowa cikin sauƙe numfashi ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

“Gaskiya Theater zai kai kamar ƙarfe biyu na ranan gobe za'a yi”.

Cikin Jimami Didi tace.

“Toh amma ba matsala zuwa goben ko?”.

Kai ya gyaɗa yana gyara zaman farin glass ɗin idanunsa tare da cewa.

“Eh in Sha Allahu bakomai saboda ba wani ciwo take jiba ruwan ne dai kuma already kafin lokacin zai ɗan ƙara sa zubowa ne gaba ɗaya zai kuma iya riƙe yaron”.

Still da damuwa atare da ita tace.

“Allah ya kaimu lokacin”.

Sai kuma ya ƙarasa gefen Moddibo ya dafa kafadarsa ganin kamar duk ya rikice cike da kulawa ya ɗan bubbuga tare da cewa.

“Eh in Sha Allahu ba komai sai alkhairi ”.

Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.

“Toh amma babu matsala zan iya sanar mata C's za'a yi mata ”.

Kai Dr Jameel ya gyada tare da cewa.

“Of Cause ya kamata ka faɗa mata sannan ka kwantar mata da hankali.


Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fita kana ya ciro wayarsa tare da dearlin number Mommy Jin ta ɗaga yasa cikin sanyi yace.

“Momy yaushe Jirginku zai taso?”.

Ahankali tace.

“Yanzu ma ina Abuja idan Allah ya kaimu gobe Jirginmu 9:00 zai tashi”.

Cike da girmamawa yace.

“Toh Momy Allah ya kaimu”.

Da ɗan damuwa atare da ita tace.

“Lafiya dai Babana”.

Kai ya gyaɗa kana yace.

“Lafiya lau dama naƙudan ne ya tashi kuma ance”.

Sai kuma yayi shiru shin ya faɗa mata C's za'ayi wa ɗiyarta,

 Sai kuma ya katse mgnar sabida tunanin kada ya faɗa mata ya tsinka mata zuciya tare da tayar mata da hankali da sauri Momy tace.

“Ance me?”.

Da sauri yace.

“A'a ance ba matsala in Sha Allahu yanzu haka ma muna asibiti”.

Anutse tace.

“Masha Allah yanzu ina Khausar ɗin?”.

Yana gyara tsayuwar sa yace.

“Ni ina office ɗin Dr ita kuma tana ɗakin da aka kwantar da ita tare da Innayi da Niyna Ni kuma ina tare da Didi”.

Cikin sauke numfashi tace.

“Toh abawa Didi”.

Miƙa wa Didi wayar yayi Didi tace.

“Maman Khausar ”.

Cikin sanyi Momy ta gyaea zaman wayar akunnenta tare da cewa.

“Na'am ya gida ya yara?”.

“Lafiya lau Alhamdulillah ya hanya”.

Cewar Didi Momy kuwa Ahankali tace.

“Ya jikin ƴar taki”.

Didi na kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe kana ta maida hankalinta kan wayar tare da faɗin.

“Ba damuwa Maman Khausar in Sha Allahu ki kwantar da hankalinki gobe kina isowa Mai gidanki ko Amarya na bisa hanya”.

Cikin jin karfin gwiwa tace.

“Toh Allah ya kaimu rai da lafiya ”.

Cikin kwantar mata da hankali Didi tace.

“Kiyita mata addu'a Allah ya kawo mata da sauƙi”.

Kai Momy ta jinjina tare da cewa.

“In sha Allahu ina mata kuma zan cigaba dayi mata”.

Daga nan sukayi sallama bayan sun fito office ɗin Dr Jameel Moddibo ya wuce ɗakin da Khausar ke ciki.


 Yana shiga ya hangota kwance akan gado tayi shiru Ahankali ya ƙara sa ciki kana ya riƙo hannunta tare da cewa.

“Minha”.

Idanunta ta ɗago ta kallesa kana tace.

“Na'am”.

Yana matsa hannunta dake cikin nasa yace.

“Minha Me yake Miki ciwo?”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta jujjuya masa kai tare da cewa.

“Babu inda yake min ciwo Yah Mu'allim ”.

Ahankali ya zauna bakin gadon tare da janyo hannunta ya daura kan cinyarsa kana ya cire pillow ya ɗaura kanta akan cinyarsa yace.

“Minha naƙuda akwai zafi ko?”.

Idanunta ta zuba masa sai kuma ta girgiza kai tare da cewa.

“To ai ban fara bama Yah Mu'allim bare inji?”.

Murmushin karfin hali yayi kana yasa ya tsansa yana kwantar da gashin girarta tare da faɗin.

“Toh ai ma bazan bari kiyi naƙudan ba”.

Cikin sauri tace.

“Toh ai Yah Mu'allim ance dole sai mutum yayi naƙuda kafin ya haihu”.

Cikin rauni da rawar murya ta ƙare maganar lokacin ɗaya tsoro da fargaba ya mamaye mata zuciya.

Cikin sauri ya tallafota kanta tare da manna mata kiss agoshi yace.

“Bakomai kinga yanzu muka gama magana da Dr Eshaa ai kinsan Momy ma Theater akayi mata a haihuwar Ramadan da Raudhat ko?”.

Cikin sauri ta gyaɗa masa kai tare da cewa.

“Eh”.

Yana shafa kanta yace.

“Momy bata taɓa faɗa Miki cewa ba wahala ba?”.

Cikin lumshe idanu ta fesar da sanyayyar numfashi tare da faɗin.

“Haka dai take cewa haihuwa yafi Theater wuya”.

Sake janyota jikinsa yayi kana yace.

“Toh shiyasa na zaba Miki mai sauƙi Minha ayi C's  kawai lafiya lau kar wani abu ya samu Babynmu ya cutar dashi”.

Da sauri ta ɗaura hannunta akan cikin ta shafa tare da cewa.

“Yah Mu'allim”.

Cike da tsantsan so da kulawa yace.

“Na'am amma dai ai Baby lafiyarsa lau kina jin motsinsa?”

Dai-dai lokacin tayi saurin kamo hannunsa ta ɗaura akan cikin tace.

“Kaji yanzu ma yana motsi ko?”.

Kai ya jinjina tare da cewa.

“Tabbas naji Allah ya mishi albarka ya kawo shi kafiya”.

Kallonsa tayi cikin sanyi ta langwaɓar da kanta kana tace.

“Amma Yah Mu'allim ai Theater ma da zafi”.

Ɗan ware idanunsa yayi cikin son kwantar mata da hankali yace.

“Inji waye ba wani wuya munyi magana da Dr Eshaa, tace ayi Miki Theater kin san itama tana sonki bata so ki wahala, kuma itama Didi tace ayi kiki Theater yafi sauƙi”.

Dai-dai lokacin Didi ta shigo tana shiga ta riƙe hannunta tare da kallonta tace.

“Kada kiji tsoron Theater ba komai ɗiyata ai kinga Lalla Hafsat ma, haihuwar Hakeem ɗin ta Theater akayi mata kuma gashi nan lafiya lau itama lafiya lau kuma bayan shi duk yaranta da kanta take haifarsu”.

Shiru tayi tare da lumshe idanunta.

Cikin jin sanyi tace Didi taci gaba da cewa.

“Ki kwantar da hankalinki in Allah ya kaimu gobe za'a yi Miki Theater”.

Idanunta ta lumshe tare da cewa.

“Toh Allah ya kaimu bisa rai da lafiya ”.

Sai kuma ta maida kallonta kan Didi tace.

“An faɗa wa Momy na”.

Kai ya jinjina yace.

“Eh an faɗa mata gobe-gobe ma tana hanya in Sha Allahu yanzu ma haka tana Abuja kafin a shiga dake Theater jirginsu zai iso”.

Ahankali tace.

“Toh Allah ya kawo ta lafiya”.

Ameen ya amsa dai-dai lokacin kuma Dr Jameel da Dr Eshaa suka shigo.

Khausar na kallon Dr Jameel tace.

“Dr kuma zamu koma gida ne ko kuma zamu yita zama anan ne?”.

Hannunsa na cikin aljihu yace.

“Eh zaku zauna anan saboda ki kasance cikin kulawarmu”.

Kai ta jinjina cikin gamsuwa.

Dai-dai lokacin Asma'u kuma ta shigo, ganin Khausar ɗin zaune ras ana hira da itane yasata saki ajiyan zuciya tare da zama gefenta.

Daga nan sukaci gaba da hira kamarsu saboda bata jin komai.


Post a Comment

0 Comments