TOP HAUSA NOVELS atOptions = { 'key' : '20e08520dad54dbf6d9e963271

MIN QALB 🥰 PAGE 20-21

 09032345899

[3/29, 11:34 AM] Zafafa: *_MQ 20_*







*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*


*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆🏾‍♀️🙎🏽‍♀️


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽‍♀️👯🏽‍♀️


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*


*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾🤞🏾





*************

Jin mutum ta bayansu a tsaye yasa anty zarah Dan dagowa tana qoqarin juyawa Amatu tasaki wani sabon ihu dayasata dawo da kallonta Kan Salman cikin damuwa da tausayin Amatun tace"


Salman please ka danyi Mata ahankali kodan juna biyun jikinta.....


Daga salman din har MD cak tunanin kowannensu ya tsaya da maganar da Zarah din tafada,


Zame hannunsa yayi da sauri tareda barin gurin kansa na Dan sarawa sbd ihunta daya cika part din gaba daya,

Yana fita qofar gym dinsa dake maqale data shigowa palonsu yashiga Yana qoqarin clearing mind dinsa da cewa''


Khalil wane irin shirme kasani aciki¿¿

Matarka ce and she's pregnant....

MAHMOUD just stay out of this.


Geamin din dayazo Yi yafara Yana komawa asalin MD ZABEERA dinsa.


Salman kuwa shiru yayi Yana nazarin kalmar a cikin kansa duk da dai ba yanzu ne yasani ba tun kafin yadawo Nuratu ta sanar dashi komai 

Kawai abin rudewar anan shine shedan dake saka Masa wasi wasin hakan sbd Amatun data shiga kansa hakan kawai yake jin bazai Bari Nuratu ta cutatar da itaba Koda Bata ciki,

Abu daya daya sake tsaya Masa arai shine Sam idanuwansa da iliminsa na likitanci duk da bana mata ba sun kasa gasgatar Masa da akwai ciki a jikin Amatun.


Kallon fuskarta yayi ahankali yasaki murmushi ganin hawaye shabe shabe a fuskarsu su duka ukun,ita da usi harda anty zarah din ma.


Handkerchief dinsa dayake daukeda tambarin asibitinsa da sunansa ajiki yaciro daga aljihunansa ya miqawa usi yace"


Usman share Mata hawayenta.


Daqyar da fitina da koke koke ta ihu da komai aka dubata yasa Usman yaje motarsa ya dauko wasu magunguna da allurai yayi Mata da kansa yabata maganin Yana Mata sannu tareda tsokar yanda idanuwanta suka kumbura sbd kukan raki.


Saidata ci abinci da sauran maganin yaga anty zarah takaita daki ta kwanta tafito tace Masa tayi bacci kafin yatashi suka fito tareda usi dakejin kamar karya tafi yabarta ta bangare daya Kuma kallon koina yakeyi Yana jaddada daula da dukiya irinta wannan ahalin zabeera.


Sashen Salman din suka nufa cikin motarsa sbd kowane sashe zuwa sashen akwai 'yar tafiya shiyasa duka yawancinsu da motacinsu suke zuwa sashen juna sai dai idan kaso motsa jiki kaje da qafa.


A palon Salman din suka zauna Nan USI yaqara ware Ido Yana kalle kalle badan yayiwa Dr khalil alqawarin bashi ba abin wani har abada ba da yau Allah ne kadai yasan abubuwan dazai sanfe daga cikin zabeera dinnan Dan tun a part dinsu anty zarah yaga abubuwan dauka Amma hakanan ya hadiye ya dauke Kai sbd karya kunyatar da Dr khalil.


Abinci lafiyayye aka aiko daga part din mahaifiyarsa Haj Maryam aka jera Masa a dining suka zauna ci shida usi dasukai sabo cikin qanqanin lokaci sbd gano tsananin qauna da kulawa dake tsakaninsu shida Yar uwarsa Amatu.


USI na Ido biyu da kayan Dadin dake jere a dining din take yaji hakurinsa na Kama mutuncin Kai ya qare take ya washe baki Yana cewa''


Allah ya taimakeni saura kadan yau nadauki azumin alhamis da Dr ya doramu akai nidasu kawu 

Kawuma yau dayaji Dr yayi tafiya wlh win dauka yayi yace mu huta kwana biyu kafin Dr din yadawo sbd duk litinin da alhamis taredamu yakeshan ruwa acan gida.


Dariya sosai Salman yayi Yana sakejin Usin na burgesa sbd baya boye boye yace"


Kace yau dai akwai ciye ciye sai ciki yakasa dauka.


Lumshe ido USI yayi bayan yazuba kakkauran soyayyan kwai cikin bakinsa dayaji kayan qamshi da albasa take yasaki murmushi Yana sakawa Dr khalil da adduar samun nasara a rayuwa Dan komai suke samu a rayuwa sbd shine

Yagama Basu duk wani Abu da suka kasa samu a rayuwarsu ta kadaici, talauci,garari da rashin sanin daraja.


Sosai salman yaji tausayi da qaunarsu tareda son samun Lada da adduar da Dr khalil ke samu daga garesu sbd kyautatawa da kulawar dayake Basu amatsayinsu na wainda basuda shi,


A iya firar da yayi da USI ya fahimci su din talakawane masu tsananin buqatar taimako Wanda yasa Dr Khalil shigowa rayuwarsu ya taimakesu har suke ganinsa a Wanda yafi musu kowa da komai,

Idan baiyi kuskuren tunaninba yanasa ran sbd tallafawa rayuwarsune yasa ya auri Amatun batareda sanin iyayensu ba,

To Amma Kuma a yanda labari yazo a zuwan Amatu zabeera ance batada mahaifi ita din marainiyace,

To shi kawu waye tunda ba'a ce sunada kawun ba a takaice cewa akayi basuda kowa,

Gashi yanzu yanatajin sunan kawu a bakunansu,

Da akwai inda wani Abu ya maqale to,

Akwai Abinda dagasu sai Dr ne suka San abinsu koma dai menene yasan Dr khalil ya boye ne sbd wani dalili me kyau.


To gashi shima Amatu da USI sunshiga ransa alokaci daya,

Yaji yanason kasancewa acikin farin ciki da walwalar da Amatu da ahalinta zasu samu.


Bayan sun Gama cin abinci shigewa yayi ya kwanta yabar USI yanata faman kallon wani action film Yana cin wani lafiyyan dabino me laushi daya Gama daukan sanyi a fridge.


Sai azabar salman din yatashi bacci zuwa lokacin shima usi ya Dan miqe a kujera yayi baccinsa sanyin AC na hudasa hankali kwance.


Tayar dashi salman yayi tareda nuna Masa dayan bedroom dinsa yace yaje yayi wanka zai kawo Masa Kaya.


Dakinsa yakoma ya hadowa usi din manyan kayansa designers masu kyau da tsada kusan kala shida da takalma na alfarma da agogai ya hado Masa tareda wata qaramar akwati yasa aciki yakawo Masa

saiga usi yayi wanka ya shirya tsaf cikin qananan kayan dasuka fiddo da ma'anarsa da kyawun dayake dashi shima hardasu feso turaren da duk ya shaqa a jikinsa saiya saki murmushi abinsa Yana sake godewa Salman da yiwa Dr khalil addua.


Dasuka fito Saida suka koma yasake dubo Amatu zuwa lokacin har ta tashi bacci itama tayi wanka taci abinci tasha magani tana zaune Palo anty zarah na gefenta tana miqo Mata yam balls datasa akai Mata tana ci tana tunanin Dr Khalil da har lokacin basuyi Magana ba.


Kwankwasa qofa akayi hafsatu tazo daga kicin tabude suka shigo suna yar fira kamar wainda sukai shekaru atare duk da Dr salman ne me jan usi din da firar sbd yasake sosai dashi Dan dama can shi Dr Salman yanada Magana sosai da son raha da Wasa.


Tunda taga USI da kayan dake jikinsa ta sake baki tana kallonsa cikeda mamaki tana cewa''


Usi a Ina ka......


Da sauri yace"


Dr Salman ne ya......


Katsesa shima Salman din yayi da cewa"


Wai Kai itace yayarka ko Kaine yayanta da kake Jin shakkarta ne.,


Sosai Kai usi yayi Yana murmushi yace"


Dr bakasan Amatu bane da zafin Rai yanzu Nan saitace zata fasamin Kai ko baki.


Dariya Dr da anty zarah suka sake 

Anty zarah tace"


To lallai Nima naji tace zata fasa maka Kai da baki yafi so goma Amma bantaba ganin anyi ba.


Kallon Amatun usi yayi Yana cewa'


Anty zarah dafa tanayi yanxune anan batama ganni ba bare tayi 

Amma ada tsaf zata saka wata Jakarta me kama data wanzamai ta kwadamin akai ko baki 

Jakar Nan yanda kikasan da qarfe akayita tsabar qarfi.


Dariya duk su duka suka sake sosai hadda hafsatu dake jera abincin Rana a dining 

Itama Amatu dariyar tayi tana cewa''


Usi tashi kabar Nan kafin na fasa maka baki wlh...


Kinji ko anty zarah tasake fada

Ai a yini tana cewa zata fasa bakina da kaina yafi so ashirin

Kawu ne duk ta fada sai yayi sadakar ruwa wa qadangaru su Sha Wai yana fidda Mata baki kada fada Babu cikawa ya fado Mata.


Filon kujerar datake ta dauka ta jefa Masa da qarfi tana cewa''


Kamar anyi a kunnen kawu 

Kuma Allah saina fadawa Dr yau bakayi azumi ba dan Banga alamarsa atare dakaiba yanda nasanka kamar mace da mugun Jin azumi.


Kallonta yayi da sauri kafin ya kalli Dr Salman yana Dan nutsuwa yace"


Idan Kika fada Masa to kisani banine kawai banyiba 

Kawuma ya ajiye yace wlh saiya huta.


Zaro Ido tayi itada anty zarah tace"


Kawu ma ya ajiye?


Eh Mana iyami ce kawai ta dauka abinta sai kwadayayyun gidan dasuka Saba duk akayi ana raba musu abubuwan abinci basusan yayi tafiya ba sunacan duk sun dauka.


Shiru Amatu tayi tana sakin murmushi kewa da tsananin qaunar Dr khalil da girmansa na sake cikata sbd ya kawowa gidansu rayuwa me inganci da samun tsira,

Duk litinin da alhamis yakeyin azumi harya koyawa su kawu 

Suma sauran Yan gidan tuni suka dauka sbd duk litinin da alhamis din Yana kawo kayan abinci a raba gidan Dan Shan ruwa Wanda wasu suna musu kwana biyu Basu qareba,


Da farko sbd samun kayan dayake kawowa suke azumin Amma yanzu kusan dukkaninsu abin yafara zama jikinsu Kuma kowannensu yasha ruwa takanas sukewa Dr khalil adduarsa ta daban sbd yakawo sauyi da walwala a rahuwarsu gidan gaba daya.


Anty zarah ma cikin jinjinawa Dr khalil tace"


Allah ya biyawa dr buqatocinsa na alkhairi sbd wannnan aikin ladar dayayi.


Amin Amatu tace tana kallon Dr Salman dashima yaji yana sake ganin girman Dr khalil zabeera tareda yiwa kansa kwadayin Lada da kyautawa su Amatun.


Anan sukaci abincin Rana taredasu Amatu kafin suka fito suka wuce Salman zai maida usi gida.


Bayan tafiyarsu cikin kulawa anty zarah tace"


Nagode Amatu.


Juyowa Amatu tayi ta kalleta cikin rashin fahimta tace"


Anty zarah me akayi?


Murmushi tayi tana kallon Amatun gaba daya tace"


Amatu kinkawo dariya da walwala acikin rayuwar kadaicin Dana samu kaina acikin gidan nan,


Tsawon shekarun aurena Banda ranar Dana taba zaunawa acikin gidan nayi fira nayi dariya harda qyaqyatawa saida Kika shigo cikinsa,

Banda abokin fira,abokin nishadi acikin gidana,

Maimakon nakawo sauyi da walwala acikin gidan Nan da rayuwar MD sai Nima kadaici da rashin walwala da rashin farin ciki suka aureni sai gidan yaqarasa zama cikin duhun dayake ciki tuntuni.,


Amma zuwanki amatu yakawo walwala da annushuwa acikin gidan Nan Wanda ko hafsatu datake amatsayin me aiki na hango walwala atareda ita bayan zuwanki cikinmu

Shiyasa nake Miki godiya sbd ko ahaka kin shayar damu yanda walwala da nishadi sukeda Dadi a rayuwa.


Murmushi tasaki tana gyara zama tace"


Anty zarah banbaki kwatan Abinda kikamin arayuba,

Kin qaunaceni a yanda nake Kika Kuma karbeni hannu biyu bayan kingama sanin waceceni,

Kinbani matsayin qanwa kamar ta jini bayan baki hada komai Dani wannan shine babbar kyautar Dana samu a rayuwata ta samunki keda Dr khalil,


Dr khalil shi yariga yazama wani jigo atare Dani da bazan iya Babu Shiba Wanda nake fatar dagake harshi mutuwace kawai zata rabamu,


Farin ciki Kuma Babu Wanda yake bawa wani farin ciki a rayuwa sai Allah saikuma Kai da kanka idan ka ture komai ka bawa kanka mahimmanci,


Anty zarah kece da kanki zaki kawo walwala da sauyi a gidan aurenki idan kinso,

Bansan meye zaman aureba tunda banzauna da Dr ba saidai ni nawa tunanin daga lokacinda Kika auri mutum to duk mulkinsa da dukiyarsa da muqaminsa da duk wani Jin kansa to fa anzama daya 

Idan bai aje Dan kansa ba ke zaki aje masa,


Anty zarah kinsa tsoro da shakkun mijinki fiyeda sonsa acikin ranki Wanda shike sa kiga an tsufa da jikoki da 'yaya da komai saikiga mace mijinta na Mata fada ko dixgawa a gabansu Wanda ita ta daukar Masa hakan tun anada kuriciyar aurensu.,


Mijinki mijinkine baida wani suna bayan wannan hakama kema bakida wani suna bayan na matarsa ko bayaso Dan haka anty zarah ki aje tsoro da shakka ki gyara rayuwar aurenki sbd bazan zauna Nan dakuba dazanta kawo dariya a fuskarki kece zaki kawo dariya a fuskarki data mijinki,

Dan haka Dan Allah anty zarah ki gyara sbd kada lokaci ya qure Miki.


Zugum tayi tana sauraren Abinda Amatun ke fada tanajin kamar da wuya al'amarin.


Murmushi Amatu ta sake tana cewa''


Anty zarah tunanin me kikeyi?


Miqewa tayi tana cewa''


Sam ni Banga abin tsoro ko shakku ba  agun Rabin ranki a takaice ma ni tsaf zan gyare Miki zamansa matsalar da aka samu itace ni ko qamshinsa na jiyo gabana faduwa yakeyi sai naji zuciyata tana bugawa da sauri kamar zata fito daga qirgina,

Idan na kalli fuskarsa kuwa rasa nutsuwata nakeyi,

Bansan meyasaba shikadaine nakejin hakan akansa,

Shi kadaine bana iya yiwa fuskarsa kallo biyu sbd dukan da zuciyata takeyi,

Meyasa idan.........


AMATULLAH"""yakira sunanta gaba daya batareda yasan yayi hakan ba sbd zantukanta dake juya kansa da tunaninsa....


Juyowa sukayi su duka hadda anty zarah datai qaramin suman zaune Jin abubuwan da Amatu ke fada akan MD Wanda idan shedan ya Rudi fahimtarta to zata ce ne wannan so ne me zafi.....


Saurin girgiza kanta tayi tana Dan bugawa tace"


Tunani ne 

Amatu matar Dan uwan MD ce

Tanama daukeda cikinsa

Bazata taba son wani ba bayan Dr khalil bare Dan uwansa MAHMOUD tunanin banxana ne kawai.


Ganin Dr Salman ne yakira sunanta yasa anty zarah sakin ajiyar zuciya a boye 

Ita Kuma Amatun murmushi ta sakar Masa tana cewa''


Harka dawo¿


Gabaki daya kansa juyawa yakeyi Wanda hakan har akan fuskarsa ya nuna confusion sai kawai ya miqa Mata ledar hannunsa daya siyo Mata tarikicen kayan chocolates dasu cookies ya juya baice ko kala ba.


Yana fita Saida ya zauna cikin motarsa ya yamutsa kansa Yana cewa''


Amatu MD ZABEERA takeso bayan tana matsayin matar khalil zabeera kokuwa kansa ne bai fahimci yanda abin yakeba????


Kasa yadda yayi yaja motarsa yana qoqarin yakice tunanin dama duk Abinda kunnuwansa sukajiyo Masa.



Bayan fitarsa kuwa cikin farin cikin abubuwan daya kawo Mata din tazauna gefen anty zarah suna bubbudewa suna cin wasu suna dauko wata firar tasu maman junior tana bawa anty zarah din labari suna dariya hankalinsu kwance.


Sasai Tasha chocolates din Wanda har Saida anty zarah tace ta daina sbd ciwon Mara Amma haka ta share tunda tasan ba wani ciki ajikinta sasha kayan zakinta harsai dataji cikinta kamar zai Yi ciwo ta aje sauran cikin fridge.






Da daddare tana qoqarin zama bayan futowarta daga wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci masu Dan akuri ta saka wularsu sai qamshin turaren Dr khalil takeyi Wanda yabata datace tanason qamshinsa saiga kiransa yashiga saidatai wani wuntsilawa sbd farin cikin ganin kiransa sbd dazu yakira da numbernsa tacan tayi saving.


Tana dauka tafara zuba Masa qirafin da batai Masa dazu ba sbd gaban anty zarah ne tace"


Nifa ban daina fushiba katafi kabarni zabeera ni kadai.


Murmushi me sauri yayi Yana qara Jin sonta har cikin ransa a natse yace"


Baga zarah Nan ba.


Shiru tayi kafin ahankali tace"


A cikin zabeera da wajenta a yanzu Babu inda nakejina cikin tsaro da kulawa idan har bakanan,

Dr kariga ka koyar Dani Jin rashin tsaro idan baka kusa Dan Allah kadawo da wuri tsoro da fargaba nakeji idan baka kusa.


Nutsuwa maganarta ta qara Masa yaji sanyi Yana qara samun nutsuwa yace Mata"


Inshallah Amatu idan Ina Nan kina cikin tsarona Babu Abinda zanbari yasameki sai qaddara.


Nasani Dr""""tafada tana Dan yamutsa fuska sbd mararta data Fara murdawa gashi dama ita qa'idane duk wata saitayita baqar wahala idan zatayi period,

Tunda tazo zabeera Dr khalil sbd cikin da akace tanadashi Yana gano tana ciwon period yake kaita asibiti duk wata tana ganin Dr Fatima ana Yan dubaru har tagama period din tukuna.


Fira sukeyi tana daddaurewa ahankali sbd ciwon marar gadan gadan yakeson taso Mata sai alokacin tagane Abinda anty zarah ke nufi data daina cin zaqi.


Jin kamar tanajin bacci yasa yayi Mata addua kamar yanda ya Saba duk dare kafin ya kashe wayar saidai hakanan yakejin kamar ba lafiya takeba.


Lallabawa tayi ta kwanta tana juye juye hardai abin yataso Mata sosai Nan tafara hawaye tana Kiran sunan Allah.



Bayan kusan awa biyu da Gama wayarsu ya yakasa samun nutsuwa ya  kalli agogo yaga yanzu su can a Nigerian dare yayi sosai sai ya janyo wayarsa yashiga massage yayiwa zarah text yasan tana tareda MD Amma dai idan har tagani zataje ta dubo Amatu tagano masa.


Anty zarah na dakinta yau bataje dakinsaba sbd yanda yadawo tasan a gajiye yake bazaiso a takurasaba shiyasa tayi kwanciyarta dakinta tanata juye juye cikin tunanin daukar shawarar Amatu Amma tanajin shakku, 

Saiga massage dinsa yashigo tana karantawa ta miqe sanyeda kayan baccinta riga da wando irin na Amatun sak ta nufi dakin da sauri.


Salati tasaki me qarfi tana Shiga dakin cikin tashin hankali tayi kanta ganin tanata juye juye riqeda ciki tana wani irin numfashi da kukan azaba.


A rude takira Dr tana fada Masa cikin tashin hankali yake dama daya duba yaga yaune date din period dinta da sauri yace"


Kira umme Dan Allah ta taimaka Mata  takira Mata Dr Fatima.


Umme Kuma"""

Anty zarah tafada cikin mamaki sbd sanin kowa yasan umme Bata qaunar Amatu da Abinda yake cikinta.


Shikuma sanin umme ce kawai tasan Amatu batada ciki yasa yace aje gurinta sbd yasandai bazata tonaba yanzu.


Eh Zarah Kira umme Dan Allah Yi sauri.


Jiki na rawa ta Danna Kiran numbrn umme Saida tayita ringin kusan Kira biyar sai ana shida ta daga cikin bacci.


Umme zarah ce

Gamunan Amatu batajin Dadi zaki Kira Mana Dr Fatima ne Wai.


Wani qaton ashar ummen ta gundumo tana cewa''


Uban Dr Fatima zankira muku,

Zarah Kika sake kirana cikin Daren Nan saina mugun Bata miki wlh.


Kallon wayar da ummen ta kashe Mata tayi cikin mamaki da tsoron Ina mafita gashi idanba idonta yayi Mata qaryaba saitaga kamar jini a jikin dogon wandon Amatu din.


Wani razanannen qaramin ihu tasaki tareda jefar da wayarta tana fitowa da gudu tayi sama dakin MAHMOUD cikin sa'a Yana zaune yana aiki a laptop da cikin tashin hankali da rudewa tace"


Amatu ce ba lafiya kamarma jini cikinta zai lalace.....


Cak ya tsaya tareda dagowa ya kalleta ta daga Kai cikin rudewa tana kasa Magana.


Kallon agogo yayi batareda ya motsa yaga dare be

Zata sake Magana ya aje laptop din gefe tareda miqewa ya zura jallabiya Fara qal Kan singlets da short dake jikinsa ya dauki keys ya sauko zarah din na bayansa.


Kamar bazai Shiga dakinba saikuma ya Shiga daidai tayi wani juyin azaba zata fado qasan gado ya tareta da hannunwansa biyu 

Unfortunately sai idanuwansa suka sauka kan stain din jinin dake jikinta 

Ya rintse ido da sauri tareda dauke Kai Yana shawarar daukanta saikuma ganin halinda take ciki yasashi daukarta cak gaba daya yafito Yana cewa''


Zarah ki Kira zamu dawo zuwa da safe.

##mamuh#







ZAFAFA BIYAR👇👇👇


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


SARAN BOYE

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Or 09032345899

[3/30, 10:39 AM] Zafafa: *_MQ 21_*

30, 10:39 AM] Zafafa: *_MQ 21_*






*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*


*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆🏾‍♀️🙎🏽‍♀️


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaɗa ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯🏽‍♀️👯🏽‍♀️


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*


*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*🤞🏾🤞🏾🤞🏾🤞🏾






**********

Seat din gaba yasakata ciki tareda 'dan kwantar da seat din ya rufe ya zagaya yashiga motar ya tayar yabar gurin cikin gudu sosai,

Cikin mamaki securities suka firfito Amma suna ganinsa sukai saurin bude Masa gate din suna Masa adawo lfy kota kansu baibiba ya fice.



Anty zarah sai alokacin ta tsaya sake da idanuwa tana cewa"


To Ina zai iya da ita shi kadai daya Bari nabiyosu,

Kiran khalil ne yashigo wayarta cikin sauri ta dauka tana fada Masa MD ne yatafi Kai Amatun asibiti.....


What????""""yafada da sauri cikin firgici Yana cewa'"


Me umme tace?

Yaushe suka tafi??


Umme Bata daga wayarba gashi jini yafara balle Mata shine yatafi kaita da kansa,

Dr Ina fatan kada wani Abu yasamu cikin Nan Dan Allah ka Kira asibiti tun kafin su Isa kafada musu suyi duk iya qoqarinsu Dan Allah karsu Bari cikin Nan yasamu matsala.


kasa Magana yayi ya kashe wayar tareda Kiran Dr Fatima dayasan asibitin na hannunta yanzu tunda bayanan cikin tsananin damuwa da tashin hankali yayi Mata bayanin abindake faruwa.


Cikin sauke numfashi tace"


Karka damu Bari su iso Ina asibitin yau zanyi call(night) ne Inshallah za'ayi yanda aka Saba Mata duk wata,

Problem din dai shine sunriga sunga cewa tafara bleeding ya zamuyi da wannan?


Just handle everything please Dr Fatima 

Nabar Miki komai ki kula dashi nidai kawai please Dr Fatima Amatu azaban datake ciki nakeson kifara bi takai 

Inaji ajikina tana cikin azaba sosai Dan Allah Dr Fatima ki kularmin da ita gobe zan biyo jirgin Rana nadawo bazan iya daukaba 

Tafiyan kwana daya harta Fara shiga abubuwa iri iri.....


Calm down please Dr khalil komai zai zama daidai Inshallah Babu Abinda zai samu Amatun zanyi iya dukkanin qoqarina gurin ganin Babu Abinda zai sameta.


Thank you Dr""yace Yana kashe wayar sbd Jin ana buga office din datake.


Tun kafin ta aje wayar nurse Abida tashigo tana cewa'' 


Dr Fatima ga MD ZABEERA nan matar Dr Khalil ya kawo it's emergency mun karbeta ke ake jira.


Medical glass dinta kawai ta dauka ta miqe suka fito sister Abida nasake Mata bayanin taimakon gaggawar dasuka Bata.


Tana zuwa taga halinda Amatun take ciki take tasaki wani guntun murmushi sbd ganin yanda Dr khalil ya daga hankalinsa akan alamarin ba haka bane menstrual pains ne kawai.


Nan tahau dubata tareda Bata allurai Dan samu 'dan relief tareda qarin ruwa sai paracetamol data Bata.



Tana fitowa daga cikin emergency din sister Abida ta biyota tana cewa''


Dr Fatima zamuyi shifting nata ne zuwa Amenity ko kuwa?


Yes u can shift her Amma kafin Nan kufara taimaka Mata ta gyara so that kar jinin ya qarasa Bata Mata jiki,


Ok zamu Bata pad ne kokuwa abata cotton tayi amfani dashi,

And dose na injection dinta after 2 hours ne zamu sake Bata parainject din??


Yes after 2 hours ko Kuma 3 hours tunda menstrual pains ne kawai.


Ok.


Sister Abida na barin gurin Kiran Dr khalil ne yashigo wayarta saidata saki numfashi kafin ta dauka tana cewa''


Kafin kace komai Dr khalil please listen to me

Maganar gskia Dr yarinyar Nan tunda har kasan kowane wata irin wannan matsalar ta al'ada na damunta Kaine kawai zaka iya magance Mata matsalar sbd kada wata Rana abin ya zarce ya zamar Mata matsala babba,

Mu'amalar aure ne kawai zai kawo Mata qarshen wannan monthly pains din.


Zata sake Magana ya katseta da cewa"


Dr Fatima lafiyanta kalau yanzu dai ko??


Eh komai ya daidaita zuwa asuba zasu iya tafiya gida..


Ok thank you Fatima

Sauran maganar please mubarta idan nadawo zamuyita.


To kawai tace tareda kashe wayar ta wuce tabar gurin batareda ta juya taga MD dake zaune a bayantaba idanuwansa ne kawai ba'a kanta ba Amma hankalinsa gabaki daya akan zancen datayine tunda nurse Abida har Khalil dasuka Gama Magana yanzu,


Shiru yayi Yana qoqarin nazarin fahimtar zancen sbd idan har yayi amfani da iliminsa na 'dan Adam Koda baitaba haihuwaba ko samun ciki da amatarsa yasan dai Mai ciki Bata period,

Hakama Mai aure harda ciki baza'a ce Yana buqatar rayuwar auratayyaba kafin yasamu saukin cramps,


Bude idanuwansa dake lumshe yayi ahankali Yana tunanin Khalil na boye wani Abu gameda yarinyar Nan wanda yake da matuqar mahimmanci ko hadari,

Koma dai menene ba huruminsa bane Abu dayane zai fadawa Khalil yasan Abinda yakeyi.


Dakin da aka maidata ya qarasa yashiga lokacin ta bude idanuwanta daidai shigowar tasa sai idanuwansu suka shiga cikin na juna 

Ita tayi saurin yin qasa da idanuwanta sai kawai idon nata ya sauka kan farar jallabiyarsa da jini ya Bata daga gaba gurin cikinsa take tayi saurin rintse ido akaro na farko wata irin kunya me tsanani ta kamata saita samu kanta da kasa bude Ido ta kallesa.


Shi kuwa dauke Kai yayi tareda kallon inda yaga ta kalla din kafin ta rintse ido 

Idonsa ya sauka kan abindake rigarsa 

Saurin dagowa yayi ya kalleta yaga itama shi take kallo tana jiran reaction dinsa

Sai kawai shima yaji abin wani iri sbd shi ko so daya Koda Wasa baimasan ya kalar jinin Mata yakeba Dan ko amafarki baitaba ganin na matarsa ba bare gashi yanzu Yana ganin wannan ajikinsa ma......


Fuskewa yayi tareda juyawa yabar dakin tanajin wani irin yanayi kamar yanajin kunyar kansa.



Itama Jin tayi kamar qasa ta tsage ta shige har batasan lokacinda ta Dan daki kantaba tana cewa''


Wannan abun kunya yayi Miki yawa amatu.



Daga shi har ita kowannensu kasa hada fuska yayi da Dan uwansa sosai ya hade fuska har aka sallamesu suka dawo gida zuwa lokacin Tama fisa Jin kunya ganin yanda ya fuske ko nuna yanani baiyiba.


Har suka Isa bame motsi cikinsu ita tafara fita tayi ciki da sauri tana gyara zaman hijabin da Dr Fatima ta Bata ta sanyo.


Anty zarah dake safa da marwa a Palo sbd rashin sanin ya ake ciki gashi yabar wayoyinsa gida 

Tana ganin Amatu tayo kanta da sauri tana riqota zatai Magana kenan sai gashi shima yashigo fuskarsa na Kan agogo zatayi Masa gamana idanuwanta suka sauka akan rigarsa dake daukeda stain din jinin Amatu Wanda ta tabbatarda daga jikinta ya fito sai ta dago ta kalli fuskarsa dayake qoqarin rabata ya wuce 

Sai kawai taji wani irin yanayin kishinsa ya Dan shigeta 

Ta juyo ta kalli amatu da kunya qarara ta bayyana Kan fuskarta har tana sauke Kai 

sai ta watsar kawai da tunanin komai cikin kulawa tana Jan Amatun zuwa daki tace"


Amatu ya babynki?

Ina fatan Babu Abinda ya samesa??


Daga Mata Kai Amatun tayi zata sake mgn Kiran Dr khalil yashigo wayarta data Bari gida Kan gadonta.

##Mamuh#


Please Dan Allah kuyi manage inada uzuri ne yau🙏🙏🙏




ZAFAFA BIYAR👇👇👇


SIRADIN RAYUWA

safiyya huguma


MIN QALB

mamuhgee


SARAN BOYE

billyn Abdul


KIBIYAR AJALI

Miss xoxo 


ABINDAKE CIKIN ZUCIYATA

hafsat rano


Pay @09033181070

Post a Comment

0 Comments